← Book details Triplets Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 86 OF 168

Sashe 86

Triplets Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Saman bed ɗin ya haye, kallo ɗaya ya yi wa jinin dake malale a saman bed ɗin ya kawar da kansa gefe, cike da zulumi ya kai kallonsa a saman face nata, gwaggo ta lulluɓe mata jikinta da bargo, wlh har wani kumbura face nata ya yi cikin ƙanƙanin lokaci, duk ta sauya, idan ba ka yi mata farin sani ba, ba zaka taɓa cewa ita ɗin bace ba, ta sauya over, face nata ya kumbura sossi.

A hankali ya kai hannunsa ya yaye bargon dake a jikin nata, nisawa ya yi kafin ya miƙe, cikin dabara ya ɗauketa cak, dan motsata daga in da take ma babban haɗari ne ga lafiyarta, barinta a haka shi ne mafi a'ala a garesu, idan suka kuskura suka motsata har jikinta ya jijjiga, to ba shakka zasu ɓaro mata wani babban matsale ga lafiyarta da rayuwarta, yanzu haka ma basu san a iya ina matsalar ta tsaya ba, sai ta farfaɗo zasu iya ganewa. Wannan shi ne tashin hankali.

Cikin dabara ya ɗagata kamar wanda ya ɗaga jaririn kwai irin wanda bai yi ɓawon nan ba, wanda yake iya ledar ciki ne kawai, kun san idan za'a ɗauki irin wannan kwan dole abi a hankula, saboda kada ya fashe, to a hana Lion ɗin ya ɗagata zuwa saman sofa mai zaman mutum uku da yake a cikin bedroom ɗin, ya kwantar da ita, sannan ya dawo ya cire bed sheet ɗin gabaɗaya tare da ajiyewa a gefe guda.

Da kyar ya iya É—auko wani bed sheet ya shunfuÉ—a, dan har ga Allah shi bai iya shunfuÉ—a gado ba, ba aikin da ya iya dangane da aikin gida, haka ya shunfuÉ—a bed É—in ko kyau bai yi ba, bed sheet É—in ma ba'a dai'dai ya sanya ta ba, ya dai sakata ne kawai, shi dai ba ya samu ya cire wannan na jinin ba? Ai shikenan kuma, koma a yaya ya shunfuÉ—a wannan haka zasu kwanta.

Komawa ya yi ya É—aukota a hankula, a saman bed É—in ya shumfuÉ—eta, sai kara kumbura face nata yake yi tamkar ba lafiya ba. Duv na bed sheet É—in ya jawo ya rufa mata, sannan ya sauko ya É—auki bed sheet É—in da ya cire ya kai wajen kayan wanki, ya nufi toilet dan ya yi wanka.

Bayan ya fito ya shirya cikin jallabiya fara tas, dan an fara kiraye kirayen sallar asuba. Dadduma ya shunfuÉ—a tare da fara gabatar da nafilfilu, daga karshe ya yi shafi'e da witiri kafin alfijir ta keto, bayan ta keto sai ya yi rakatainil fajir ya fito zuwa masallaci, har lokacin da kallo É—aya zaka yi mashi kasan cewa yana cikin tsananin tashin hankali na wuce misali, yau dai ya canza daga suffa É—aya da aka san shi, dan tashin hankali ta bayyana mashi a saman face nasa.

Ko da ya dawo daga masallaci bai zame ko'ina ba face bedroom ɗin nasa, bai kalli in da take ba, dan ya san ko motsawa ba ta yi ba, ta shiga doguwar suma ne. Wanka ya kara yi tare da shiryawa cikin kananan kaya masu matuƙar kyau da tsada, sannan ya fito tare da ɗaukar wayarsa. Saman bed ɗin ya haye, sai zuba uban kamshi perfume nasa yake yi, kusa da ita ya kariso. Tamkar gawa haka take kwance baiwar Allah.

Ranƙwafowa kanta ya yi, a dai'dai saitin kunnenta ya kawo ɗan bakinsa, kasa kasa ya fara yi mata raɗa, bai bawa kowa damar jin abin da yake faɗa mata ba, shi kaɗai yasan me yake faɗa, ita da take sume ba jinsa take yi ba, amma ya zage sai yi mata raɗa yake yi, da kallo ɗaya zaka yi mashi kasan har yanzu a birkice yake, har yanzu akwai tashin hankali sosai a tattare da shi.

Ya É—an É—auki lokaci yana yi mata radar kafin ya É—ago ya sumbaci lallausan lips nata da suke a bushe sosai yanzu, saboda bakar azabar da ta sha ne yasa har suka yi wani irin bushewa tamkar babu ruwa da jini a jikinta.

A hankali ya diro kasa daga saman bed É—in ya nufi waje, har ya kai bakin kofa ya sake juyowa ya kalleta, sannan ya sa kai ya fice daga É—akin.

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️❤️🔥

*KINDADE KINA NEMAN ABUN DA ZAI SANYAKI QIBA,QIBA MEKYAU KIYI DIMIMI DUK INDA KIKA SHIGA BABU RAINI KINYI TA SIYA KINA ASARAR KUDINKI🤔
ALBISHIRINKI NAZO MIKI DA ABUN DA ZAKISHA BA TARE DA KINYI ASARAR KIDINKI BA 💃 Yana da matiƙar kyau sosai ko'ina naki zai chiko ki xama abar sha'awa duk mai buƙata ta nemeni ta wannan number 09067614054, kada ki bari ayi babu ke, kayanmu tested and trusted ne, guarantee ne*.

*KINDADE KINA NEMAN ABUNDA ZAI SANYA KISAMU XAMAN LFY TARE DA KWANCHIYAR HANKALI? TO BABYN HABIBI KIXO UMMU AFFAN TAXO MIKI DA SHAHARARRUN KUMA INGANTATTUN MAGUNGUNAN MATA, KAMA TUNDAGA KAN HUMRA, TURAREN WUTA,
INFECTION KILLER,
COLACCA,
SAI KAYAN GYARA PAGE.
KACA KACA.
YALLAGWADA.
JIGIDA.
RUWA RUWA.
BANI BANI.
WOMEN JELL BATA BATA.
DAFIN KAXA.
TANTABARA.
XABUWA.
CICCIƁI.
AND EXCLUSIVE, XUMA TASTED AND TRUSTED INA FARIN CHIKIN SANAR DA KU MUN FARA RAMADAN PROMO GAME BUQATA XA A IYA TUNTUBA NA TA WANNAN NUMBER
09067614054 JIGAWA STATE MUNA AIKAWA KO'INA CIKIN AMINCI DA YARDAR ALLAH,
BABYN HABIBI KARKIMANTA DA KAYANMU FIRST CLASS NE, DAGA KANSA AN RUFE KOFA, YANA DA INGANCI NA WUCE TUNANINKI*.

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥

https://whatsapp.com/channel/0029VaMOfZZI7BeKXPU9gK2S

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥

TSARAWA DA RUBUTAWA......✍️

❤️FATEEMA ZAHRA MUSA (💫PRINCESS TEEMA💋)

*Domin samun damar karanta littafin nan daga farko har karshe zaki iya nemana ta wannan number 08161390581*

Date: 6/5/2024

E25

A hankali ya diro kasa daga saman bed É—in ya nufi waje, har ya kai bakin kofa ya sake juyowa ya kalleta, sannan ya sa kai ya fice daga É—akin.

Yana fita ya nufi bedroom na gwaggo, ya zo zai shiga dai'dai lokacin ita kuma zata fito daga cikin É—akin, saura kaÉ—an su yi karo. Baya ya É—an yi yana faÉ—in "Good morning morning".

Tsare shi ta yi da idunuwa tana mai faÉ—in "Morning where are you going in this early morning?".

Shiru ya É—an yi na Æ´an sakanni kafin ya amsa mata da "Yesternight you said da akwai wasu drugs and injection da zan sayawa Meesha, that's what i came for, ki bani list É—in". Allah sarki bawan Allah duk a ruÉ—e yake, hakika yana tsananin kaunar Rimsha, kauna mara misaltuwa, hankalinsa a tashe yake sosai.

"Saif what is the time now?". Ta tambaye shi har lokacin bata kawar da kallonta daga kansa ba, tsananin tausayinsa ne cike fal a ranta.

"6:05". Ya bata amsa yana duba dankareriyar watch dake ɗaure a hannunsa. Ba shakka Lion ya shiga tashin hankali da damuwa na wuce misali, kuma dai kun san abin da zai sanya Lion ya canza daga wannan suffa guda ɗayar, abin da zai sanya shi har a iya gane yana cikin bakinciki da tashin hankali wanda ko TRIPLETS nasa duniyar farincikinsa basa iya ganewa, amma yau ga tashin hankali karara bayyane a face nasa har ya kasa hakura gari ta waye sosai ya je ya sayo mata magani, ko daga nan kun san abin ya kai mashi intaha, abin ya wuce misali a wajensa, kofa TRIPLETS nasa basa iya ganewa idan yana cikin damuwa or ɓacin rai ko kuma farinciki, saboda dakiya da juriya irin nasa, amma yau shi ne yake birkice haka, babu shakka abin ya wuce misali, soyayya tabarmar kaya, idan ka iya zama ka ji daɗi, akasinta kama? Kun san sauran.

"Saif nan fa ba U.s bane ba, they didn't open their shop's at this time around, sai irin 8 haka, now is to early ai". Ta kai karshen maganar tana mai kara yin kasa da muryarta sosai, tana yi mashi magana cikin sigar rarrashi da nuna tausayawa tare da tausasawa, dan ya ɗan ji sanyi a ransa, duk da ba ita ta renesu suka girma ba, bata san halinsu sosai ba, amma ta san cewa ba ƙaramin abu bane zai iya sanya jinin Dr William shiga damuwa har haka, bare kuma shi Lion da kusan komai irin na daddyn nasa ya ɗauko, Dr William akwai taurin zuciya na bala'i, to haka Lion ɗin ma yake, sun iya shanye abu.

Shiru ya É—an yi yana mai cigaba da kallon kasa, kwata kwata baya son su haÉ—a idanu, duk wani irin yanayi yake ji a jikinsa.

"Kanaji ko Saif? In Sha Allah Meesharka zata samu lafiya, babu abin da zai sameta, yanzu abin da nake so da kai ka nutsu ka kwantar da hankalinka, ka yi mata addu'a, zan je na dubata ne dama yanzu, kada ka damu zata warke kamar ba'ayi ba cikin ƙanƙanin lokaci In Sha Allah". Tana magana tana kallon jikinsa yadda yake wani irin tsuma alamar still dai yana cikin tashin hankali.

Rumgumeta ya yi tare da fara magana kasa kasa kamar mai raɗa "Momma i know kawai kin gaya mani hakan ne dan naji daɗi, i already knew that ko da Meesha zata samu sauki not now, ban taɓa jin daɗi cikin bakinciki ba sai yau momma, ko ba komai yau for the first time a rayuwata bayan TRIPLETS na an gaya mani magana da zai kwantar mani da hankali, a ko da yaushe ina yawan jin Sheikh Sultan yana faɗin duk wanda ya rasa uwa, to tamkar ya rasa komai na duniya ne, komai kuɗinsa komai mulkinsa ba zai taɓa jin daɗi ba idan babu mahaifiya a gefensa, kasancewar ban ma san ya uwar take ba, ban taso da ita ba, sai ina ganin kamar dukka shirmensa kawai yake faɗa, ban taɓa jin ciwon rashinki a tattare damu ba sai yau, am really happy da jin kalamanki masu sanyi a gareni, a kodayaushe idan abin bakinciki ya sameni, sai dai na barshi a cikin zuciyata, dan babu mai iya fahimtarta a duniyar nan, even su Areef ba kasafai suke iya fahimtata ba bare har su gaya mani magana mai daɗi da zai sanya ɓacin ra'ina na wuce, kullum ni kaɗai nake faɗa da zuciyata, a yau ne na gane cewa Sheikh Sultan ya yi gaskiya da ya ce rashin uwa musifa ce, i really love our momma". Ya kai karshen maganar yana kara kwantar da kansa a saman kafaɗunta.
Chapter 86 · 0% Book details