← Book details Triplets Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 168

Sashe 66

Triplets Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bai kulata ba ya fice abinsa, duk abin da suke yi gwaggo dake saman dadduma tana jinsu, hakan yasa ta kara tsananta masu addu'a na samun lafiyar Rimshar. Shi kuma Lion yana fita ya koma bedroom nasa, ainahin wayarsa ya É—auko, ba wanda ya saya a Ilorin ba, na ainahin ya É—auko tare da kunnata. Duba time ya yi, karfe 2:40am dai'dai. Number his excellence ya kira, wayar ta yi ringin har ta kusa yanka sannan ya É—aga.

A takaice Lion É—in ya ce mashi "Zan shigo Usa gobe, ina da bukatar lokacinka at least 1 hour, so sai ka shirya". Yana gama faÉ—ar hakan ya katse kiran, duk da ciwon dake a jikinsa, hakan bai hana shi ya tashi ta fara shirin tafiya ba, acewarsa, gara kawai ayita ta kare.

Duk wani abin da zai buƙata ya shirya a cikin trolleynsa, sannan ya fito ya nufi bedroom na gwaggo, ita kaɗai ya gayawa zai tafi yanzu ba sai anjuma da safe ba, ta so ta dakatar da shi, ta so ya bari ya huta, amma ya nuna mata yana sauri, dole ne ya isa Washington gobe goben nan, dan haka kawai ta bishi da addu'a.

Ko TRIPLETS nasa bai gayawa ba, a cikin wannan dare ya fita daga gidan tare da Donal, a hanyarsu ta zuwa airport ne ya sanar da Donal ɗin cewa zai turo likita dan a ɗaura kafar Mark, so ya kula da shi sosai, bawan Allah ya azabtu matuka, baki ma ba zata iya faɗar azabar da Mark yake a ciki ba, kowa dai yasan yanda karaya take, idan baka taɓa karyewa ba, to an taɓa yi a kusa da kai, tana da matuƙar raɗaɗi na azaba.

A takaice dai Lion da private jet nasa ya bar Nigeria, dama tun da su TGA suka zo jirgin tana airport babu wanda ya taɓata, to da yake yanzu tafiya ce ta ujila, sauri yake yi, sai bai tsaya yin booking na jirgin kasuwa sun ɓata mashi lokaci ba, kawai ya yi amfani da nasa. Ya bar Nigeria karfe 4:30 na asuba, sai addu'a gwaggo take zuba mashi sosai da sosai, su kuma TRIPLETS sai barci suke zubawa a tsananin gajiye, basu da labarin Lion ya bar kasar!.

Yana dira Washington Tga ya zo ya É—aukesa, kamar yanda babu wanda ya san ya bar Nigeria sai gwaggo, haka babu wanda ya san ya dira a cikin Washington sai his excellence, ko Tga ma sai da ya kusa sauka ne ya kira shi a kan ya zo airport ya É—aukesa, so babu wanda ya sani.

Kai tsaye gida suka wuce da Tga ɗin, yana zuwa ya yi wanka tare da shiryawa, sannan ya samu ya zauna ya nutsu ya ci abincin mai yawa sosai, tun daren jiya yake jin yunwa, amma wannan matsala ta tsaya mashi a rai da har ta hana shi cin abincin, ji yake yi idan bai dira a cikin Washington ba, to ba zai iya samun sukuni ba, shi ne yasa bai iya zama ya ci abinci a gida Nigeria ba, ya daure sai da ya dawo nan, amma fa ya wahala matuƙa a cikin jirgin, dan ma dai ya yi ta shan Maltina ne.

Bayan ya ci abinci ya ɗan huta na ƴan mintoci, sai ya sake shiri tare da sanya face mask a fuskarsa ya fito, Tga ya so ya raka shi, amma ya hana kowa binsa, ya ce shi kaɗai zai tafi, basu da zaɓi, dole su hakura su kyale shi, amma sam basu so hakan ba, sojojin dake jibge a gidan nasu ba ƙaramin mamakin ganinsa suka yi ba, sun jima rabonsu da shi, sun yi kawarsa.

Da kansa ya ja mota, bai tsaya ko'ina ba sai white house wajen His excellence. Abu ne da kuka riga da kuka sani, baya neman permission a wajen kowa idan zai ga his excellence, kai tsaye ma yau palon gidan ya nufa, sam bai je fadar shugaban kasa ba, da yake already his excellence É—in ya san da zuwansa, sai ya bar duk abin da yake yi, ya tashi ya je ya samesa a cikin babbar palon nasa kawai.

Sannu da zuwa His excellence É—in ya yi mashi tare da fara tambayarsa ina su Michael nasa? Dakatar da shi Lion É—in ya yi, a takaice ya ce mashi "Where is Anderson?"

A tsananin razane his excellence É—in ya ce "Romeo what... What... What are you saying? Anderson is already died you know that... And now.......". Yana magana yana samun sarkewar word. Dakatar da shi Lion É—in ya yi ta hanyar É—aga mashi hannu ba tare da ya barshi ya kammala maganarsa ba, ya sake cewa mashi "Uncle i said where is Anderson?." Tashin hankali!.

"Romeo i told and you already know that Anderson is d......" Katse shi Lion ɗin ya yi ta hanyar ɗaga mashi hannu a karo na uku tare da miƙewa tsaye. Bai sake cewa da shi komai ba ya nufi waje abinsa.

A tsananin firgice his excellence ɗin ya miƙe tsaye, kana ganinsa kaga zallar mara gaskiya, nan take wata zufar wahala da shiga ruɗu ta fara tsastsafo mashi daga gefe da gefen fuskarsa, idanuwansa duk sun raina fata, ya yi wani wiki wiki da shi, duk wata alama ta rashin gaskiya tare da shiga tsananin tashin hankali sun bayyana a tattare da shi, a kiɗime ya nufi saman bene dan ya kai ga isa bedroom nasa.

Shi kuma Lion yana fita daga gidan bai zame ko'ina ba sai gidan kanin his excellence É—in, mai sunan Michael kenan.

Yana shiga palon bai sami kowa ba, kai tsaye ya haura sama izuwa bedroom ɗin na kakan nasu, rabonsa da ya taka kafa ya zo wannan gida yau ya kai tsawon shekaru takwas zuwa goma, yanzu ma ko da yazo securityn gidan basu gane shi ba, har sun nemi su ɓata mashi lokaci ta hanyar dakatar da shi, sai da ya cire masu face mask na face na shi sannan suka gane shi, cikin girmamawa suka barshi ya wuce, ya cire masu face mask ɗin ne kuma saboda baya son hayaniya, aikin da ya kawo shi kawai yake da bukatar yi ya fita.

Kamar yanda kuka sanine, dukka ilahirin familyn Roshan shahrarrun masu kuɗaɗene ta duniya, duniya na damawa da su, suna da karfin faɗa a ji a duniya bakiɗaya, ko'ina ka je ka ambaci sunansu an sansu, dan haka shima wannan kakan nasu shahrarren biloniya ne ta duniya, tsayawa zayyana maku kyan gidansa ma ba zai yiwu ba, saboda baki ba zata iya zayyana adadin dukiyar familyn Roshan ba, sai daidai kawai ku ƙawata a ranku.

Lion yana hayewa sama kai tsaye ya nufi bedroom É—in na kakan nasu, yana shigowa ya fara jin sautin karar tapi rap, rap, rap, tamkar jiransa ake yi ya shigo dama. Ba kowa ne yake wannan tapi ba face kakan nasa, da alama yasan da zuwan nasa, sam Lion É—in bai yi mamaki ba, sai ma karisa shigo cikin bedroom É—in da ya yi ba tare da ya jira an yi mashi izini ba.

A bakin katafaren bed na kakan nasa ya zauna tare da zubawa kakan nasa idanu yana yi mashi wani irin kallo wanda babu wani mahaluƙi da ya isa ya fassara ma'anarta sai shi da kansa, kallo ne mai cike da abubuwa da dama a cikinta. Dama daga ganin idanuwan Lion ɗin a halin yanzu kasan da akwai gagarumar abu a kasa.

"Romeo' Romeo Romeo' you are so special our Lion, you really try". Cewar kakan nasa.

Mai da kallonsa a saman yatsun hannunsa ya yi, sannan ya yi kasa da kansa, cikin sanyin murya ya ce "Why uncle? Why? Why you people did all that to us? Ina cikon TRIPLETS na? What happened to him?" And lastly where's Anderson?".

Cike da izza kakan nasa ya fara magana. "Romeo the time is out! And the game is over! Bari ka ji mu bamu É—auki É—aya daga cikin TRIPLETS naka haka kawai bisa raÉ—in kanmu ba, ina son ka sani mahaifiyarku ita ce da kanta ta sadaukar mana da cikonku, ita da kanta ta É—auke shi ta bayar, meyasa baka tambayeta ba? Ai ita zaku zarga! Mu a tsarin mu bamu amfani da yaron da ba iyayensa ne suka É—auke shi da kansu suka bamu ba, idan ma mun É—auki yaron da iyayensa basu bamu ba, to yaron ba zai yi mana amfani ba, dole sai wanda iyayensa suka bamu ne yake yin amfani a wajenmu, kamar yanda William ya gaya maku tun farko na cewa mahaifiyarku ta badaku, to hakan ce gaskiya! Mahaifiyarku ta bada guda É—aya ne daga cikinku, William É—in ma bai faÉ—i dai'dai ba, guda É—aya ta bada ba dukkanku ba, shi ne yasa Anderson ya É—auki wanda ta badan, dan haka ka dai'na neman Anderson, dan bashi da laifi, idan kuma kana ganin ba haka bane, ka koma Nigeriar ka je ka tambayi mahaifiyar taka, zata gaya maka ai, kada ka matsa a cikin wannan al'amari, idan ka matsa to ba shakka zaka fara danasanin zuwanka duniya, ka koma wajen mahaifiyarku ta gaya maka gaskiya!!"....................

Tashin hankali, wannan wani irin azababben cakwakiya ce? Gwaggo ce da kanta ta sadaukar da cikon TRIPLETS kenan? Kenan kila shiyasa bata yi maganar yaro ɗaya mai blue eyes ɗin ba tun da ta ganesu? Kenan dama tasan baya nan? Meyasa to zata yi hakan? In dai haka ne kenan tana da sa hannu a ciwon Rimsha? To wai meyasa? Menene dukka wannan abin? Wanene shi wannan Anderson ɗin? Abin da ɗaure kai! Ya ake son Lion ya yi da ransa? Kashe shi suke son yi ne? Wannan bala'i ai sai ta sa zuciyarsa ta buga, uwa fa! Ya ilahi ya lillahi. Ni kai'na PRINCESS TEEMA a wannan gaɓar ka'ina ya yi wani mummunar bugawa, zazzaɓi nake ji my peoples 🥺🥲💔 littafin TRIPLETS wan kill me with more cakwakiya and sarkakiyar.

HAR WA YAU TAKUCE FATEEMAH ZAHRA MUSA PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA MAI ABIN BAN MAMAKI🤙❤️ ASHA KARATU LAFIYA🥲💔

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️❤️🔥
Chapter 66 · 0% Book details