← Book details Triplets Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 168

Sashe 49

Triplets Part 4 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Babbar magana, a tsananin razane Queen ta mike daga saman kujerar mulkin nata, sai dai kafin ta yi yunkurin yi wa mutanenta dake faÉ—a da Aseef É—in wani tsafi, tuni Aseef É—in ya kashe su dukka, babu imani babu tausayi ko É—igo a tattare da shi, haka ya yi masu kisan kiyashi, tamkar ba Heartbeat namu ba. Babban abin da ya girgizata ya kuma jijjiga tunaninta, bai wuce yanda ta ga Aseef É—in ya buÉ—e Areef daga lock da suka sanya shi ba, ita dai tasan cewa bayan ita babu wanda ya isa ya buÉ—e waÉ—an nan locks É—in, to ya aka yi Aseef ya buÉ—e shi? Kuma dai da tsafi ake buÉ—ewa, hakan na nufin shima yana da tsafi kenan?.

Ta saki baki tana mamaki, bata ankara ba sai gani ta yi dukkansu biyun sun miƙe tsaye, Areef sai tambaya yake yi ina Aseef ya samu karfi haka? Shi kuma Aseef ɗin sai tambayarsa yake yi ina Lion nasu yake? Wannan shi ne cakwakiya....... JAMA'A NI KAI'NA INA SON SANIN WANENE ASEEF FA? DAN A GASKIYA WANNAN ABIN AKWAI ƊAURE KAI.

Ganin Areef ɗin zai ɓata masu lokaci wajen tambayarsa wanene shi, sai ya riko hannunsa tare da jansa suka fita, har sun fita ɗakin, sai kuma Aseef ɗin ya dawo ya ɗauki jakar da Areef ya zo da ita. Ita kuwa Queen sai kallonsu take yi ta cikin ruwan tsafin, bata ɗaga hankalinta dan sun fito daga ɗakin ba, dan a cewarta, ai tana da zararan mukarrabanta da za su yi gunduwa gunduwa da su, su cinye namarsu ɗanya, dan haka sam bata wani damu ba, bata san cewa abin ba haka yake ba, ko a tsafin ma ai akwai iyayenka wajen yin shi, gaba ne da gabanta, ita har yanzu a iya Africa take tsafinta, su kuma tsafinsu bugawa suke yi da manyan kasashen duniya masu faɗa aji, su ba kananan kwari irinta bane, iyayenta ne a iskanci da bala'i. E KAM BABU SHAKKA IYAYENTA NE, GA ALAMA TA FARKO, ASEEF YA IYA SHIGOWA HAR YA KASHE MUTUMINTA MAI YANKA MUTANE, YA KUMA SHIGA CIKIN JAMA'ARTA DUK BATA IYA GANEWA BA, BABBAN ABIN TAMBAYAR MA SHI NE, TA YAYA YA SHIGO CIKIN DAULAR?.

Suna fitowa harabar wajen, wasu jiga jigan maza masu kama da su barbushi ne suka kewayesu, zaratan maza ne majiya karfin gaske, yanayin nunfashinsu ma kawai abin tsoro ne, dan suna numfashi yana fitar da hayaki tamkar waÉ—an da aka É—aurasu a saman garwashin wuta mai tsananin zafi, wasu jibga jibga da su, ga gashin kansu kamar jijiyar bishiya, a tsai tsai kamar kawon shaiÉ—an, idanunsu kawai abin tsoro ne, tamkar ba idanun bil adama ba, wasu jajir dawu tamkar sun zuwa jini ne a ciki, hannunsu kawai abin kallo ne, wasu dama dama da su, kirjin nan nasu a tsaye tamkar bishiyar kuka, sam yanayin halittarsu ya fita daban da ta mutane, kai daga gani kasan da tsafi suke amfani, da tsafi suka mayar da halittarsu hakan, jikkunansu babu riga, sai dai ta kasa ne kawai suka rufe, sun kasance su goma ne cif.

Hakika Areef ya tsorata da ganin waɗan nan halittu, ya girgiza na ganin munin halittarsu, sai dai bai sare ba, bai ji sanyin gwiwa ba, dan hukumar C.I.A idan ba gani suka yi an kashe su ba, to wlh basu taɓa tsarewa a kan abu, komai gani suke yi za su iya, haka Areef yake ganin kamar zai iya faɗa da su, yana ganin mutane tamkar gunguma gungumar kumaka da aka sassaka da dafaffiyar karfe, amma hakan bai sa ya ji ba zai iya yakarsu ba.

A tare waÉ—an nan gunguma gungumar mutane suka nufesu, suna taku kasa na amsawa da dib, dib, dib. Su kuwa suna tsaye suna kare masu kallo.

Sai da suka isa wajen ne Aseef ya ciro da wata sharɓeɓiyar wuka daga kugunsa, shi kuma Areef ya yi bismillah dan su fara yaki, sai kuma me? Yana ambatar wannan bismillahi gabaɗaya dakarun Queen ɗin suka ja baya da su, tamkar waɗan da aka janye da tsafi.

Ita dai Queen tana cikin faÉ—arta har wa yau, sai kallon abin al'ajabi da mamaki take yi, wani irin zaro shegun idanun tan nan ta yi na ganin yanda mukarraban nata suka ja baya daga tunkarar su Areef É—in, irin wannan jan baya kamar an janyesu haka? Abin ya É—aure mata kai. Amma bata sare ba, sai ta sake yin amfani da tsafinta ta sake turasu suka tunkari su Areef É—in.

A karo na biyuma bismillahi Areef ya yi, dan su TRIPLETS komai za su aikata, to fa da bismillah suke farawa, sunan Allah shi ne a farko kafin su yi komai, kun tuna lokacin da Lion zai shiga gidan Queen? Sai da ya yi bismillah, ko zama za su yi a saman sofa, sai sun yi bismillah, ta yanda koda akwai wani abin da aka kullah masu, to wannan sunan Allah da suka kira, zai zama sanadiyar warwarewar komai, idan suka yi bismillah za su zauna a waje, to duk wasu shaiÉ—anun dake zaune a wajen za su watse, kowa zai kama kansa, hakan zai sa da wuya su zauna a waje kuma kuga sun yi faÉ—a ko makamancinsa, saboda da sunan Allah suka fara zama, babu wani shaiÉ—ani a wajen da zai iya zugasu su yi faÉ—a, shiyasa kuke ganin kullum cikin Kaunar juna suke, babu faÉ—a babu kyaran juna.

A karo na biyu da ya yi bismillah ma, a dubu ɗari jakarun suka sake ja da baya, abin ya yi matuƙar girgiza Queen ba kaɗan ba, dan haka sai ta miƙe tsaye, cikin nuna isa da izza ta sanya hannu a saman ruwan tsafin nata, tare kuma da fara surutansu irin na matsafa, nan take ruwan nata ya fara juyawa kamar fanka.

Shi ma Aseef ya yi mamakin ganin yadda mukarraban Queen É—in suka kasa iso su, sai dai bai nuna ba, kuma already shi ma kun san musulmi ne, akwai dai wata a kasa, amma ban da haka, duk wata addu'ar da Areef zai yi, shima zai iya yinta, so dama kunsan already shi bai yi nisa a karatun addini bane, bai san ma'anonin wasu adduo'i ba, ya dai iya karantawa ne kawai, ita kanta bismillahi bai san me ma'anar yinta ba, ya dai san sunan Allah ne.

Wannan surutai da Queen take yi ba komai bane face karawa jama'ar tata karfi, da kuma dakiya. Haka kuwa aka yi, bayan ta gama surutanta, sai ta sake turasu ga su Areef É—in, bayin Allan, su kuma suna tsaye gam, babu alamar tsoro ko sarewa a tattare da su, sai ma kwarin gwiwar da suka sake ji mai karfi yana kara ratsasu.

Da wani irin mahaukacin zafi mukarraban Queen ɗin suka nufosu a karo na uku, dafe kai Areef ya yi yana faɗin "La ilahaillah anta subahanaka inni kuntunminazzalumin, wai ku idan za ku zo mu kashe juna kawai kuzo mana, amma saboda walaƙanci sai ku tinkaro mu, sai mun shirya kuma ku sake ja da baya, wannan abin fa ya fara kona mani rai, wani irin abu ne wannan? Ku yi maza ku karisu in ma kashe juna ne sai ayi komai a wuce wajen, ban son jan rai, zuciyata ta fara hasala".......faka faka kenan.

Bai kai karshen surutan nashi ba ya ji an taɓa shi, da sauri ya ɗago kansa, Aseef ne ya taɓa shi, yana ɗagowa ya ce mashi "To ai sai ka dai'na surutun haka ko? Mutanen da sun ɓace kamar haske, kai katsaya sai wani zuba magana kake yi kai kaɗai".

Zaro idanu ya yi yana faɗin "Ban gane sun ɓace ba? Ina kuma suka je? Ba kashe mu suka zo yi ba wai? Yaushe suka ɓace?". Duk waɗan nan tambayoyi ya jerosu ne da mamaki a saman face nasa.

Shiru Aseef ɗin ya yi na ƴan sakanni kafin ya ce "Oho time da ka fara surutanka mana, ni muje hai". Shiru Areef ɗin ma ya yi yana tunanin to a kan me za su ɓace kuma?. Bai san cewa wannan kalma ta lailahaillah anta subahanaka inni kuntuminazzalumin da ya faɗa bane yasa gabaɗaya suka yi wani irin ɓacewa ɓat, ita kanta Queen ɗin sai da kalmar ta sanyata ta yi wani irin baya baya ta faɗa a sama kujerarta na mulkin, karo na farko a rayuwarta da har wani jiri jiri take gani, kanta har wani sara mata yake yi...........
Chapter 49 · 0% Book details