← Book details Triplets Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 97 OF 168

Sashe 97

Triplets Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*KINDADE KINA NEMAN ABUN DA ZAI SANYAKI QIBA,QIBA MEKYAU KIYI DIMIMI DUK INDA KIKA SHIGA BABU RAINI KINYI TA SIYA KINA ASARAR KUDINKI🤔
ALBISHIRINKI NAZO MIKI DA ABUN DA ZAKISHA BA TARE DA KINYI ASARAR KIDINKI BA 💃 Yana da matiƙar kyau sosai ko'ina naki zai chiko ki xama abar sha'awa duk mai buƙata ta nemeni ta wannan number 09067614054, kada ki bari ayi babu ke, kayanmu tested and trusted ne, guarantee ne*.

*KINDADE KINA NEMAN ABUNDA ZAI SANYA KISAMU XAMAN LFY TARE DA KWANCHIYAR HANKALI? TO BABYN HABIBI KIXO UMMU AFFAN TAXO MIKI DA SHAHARARRUN KUMA INGANTATTUN MAGUNGUNAN MATA, KAMA TUNDAGA KAN HUMRA, TURAREN WUTA,
INFECTION KILLER,
COLACCA,
SAI KAYAN GYARA PAGE.
KACA KACA.
YALLAGWADA.
JIGIDA.
RUWA RUWA.
BANI BANI.
WOMEN JELL BATA BATA.
DAFIN KAXA.
TANTABARA.
XABUWA.
CICCIƁI.
AND EXCLUSIVE, XUMA TASTED AND TRUSTED INA FARIN CHIKIN SANAR DA KU MUN FARA RAMADAN PROMO GAME BUQATA XA A IYA TUNTUBA NA TA WANNAN NUMBER
09067614054 JIGAWA STATE MUNA AIKAWA KO'INA CIKIN AMINCI DA YARDAR ALLAH,
BABYN HABIBI KARKIMANTA DA KAYANMU FIRST CLASS NE, DAGA KANSA AN RUFE KOFA, YANA DA INGANCI NA WUCE TUNANINKI*.

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥

https://whatsapp.com/channel/0029VaMOfZZI7BeKXPU9gK2S

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥

TSARAWA DA RUBUTAWA......✍️

❤️FATEEMA ZAHRA MUSA (💫PRINCESS TEEMA💋)

*Domin samun damar karanta littafin nan daga farko har karshe zaki iya nemana ta wannan number 08161390581*

Date: 10/5/2024

E29

Sai mamaki take yi a kan waye aka zankaÉ—awa waÉ—an nan uban alluran dukka, bata san dukka a jikinta suka kare ba, baiwar Allah bata san komai ba.

Gwaggon tana fita ta so ta kira Lion a waya ta sanar da shi Rimshar ta farfaÉ—o, kuma sun yi sa'a bata gane komai da ya faru da ita ba, saboda suman da ta yi. Da ta duba time a wayarta, sai ta kalli lokacin yin sallar issha ne a Washington yanzu, dan haka sai ta ce bari ta kyale shi sai anjuma ta sanar mashi, kamar tasan yana cikin yanayi mara daÉ—i.

Bedroom na mum ta nufa, ba ɓata lokaci ba ta gaya mata halin da ake ciki. Murna tamkar mum ta zuba ruwa a kasa ta sha, babban abin da ya fi sanyata murna ma shi ne yanda Rimsha bata gane komai da ya faru ba, da idanunta biyu aka yi komai ta sha wannan bakar azaba, da wlh ba zata koma wajen Lion ta daɗin rai ba, amma Alhdulimmahi da Allah yasa bata san komai ba, yanzu zata yi begen mijin nata, zata koma wajensa cikin so da kauna, ba za kuma ta ji tsoronsa ko ta rinƙa gudun shi ba, abin ya yi masu daɗi sosai, su wannan suma da ta yi ma taimaka masu sosai da sosai ya yi.

A tare suka nufo É—akin Lion É—in, sai godiya ga Allah subhanahu wata'ala suke yi. Bakinsu É—auke da sallama suka shiga cikin É—akin, tana kwance kamar yadda gwaggon ta barta.

Kusa da ita mum É—in ta zo ta zauna tana tambayarta ya jiki?. Hannun mum É—in ta riko tana faÉ—in. "Alhamdulillah mum".

Sannu ta cigaba da yi mata, ita kuma gwaggo alwala ta ɗauro dan ta yi sallar mangariba ta godewa Ubangiji da ya tashin masu Rimshar cikin ƙoshin lafiya.

Sosai Rimshar ta sha mamakin irin yanda suke ta ce mata sannu, abin ya É—an dameta, ta ji sannun yaki karewa, ita yanzu duk ba sannunsu bane a gabanta, Noorish nata kawai take son ya dawo su ga juna.

A ɓangaren shi kuma Lion ɗin, bayan sun yi sallar mangariba da issha, saman table suka haye dan su ci abinci, sam Lion baya jin ra'ayin cin abincin, saboda yanayi na sha'awa da yake a ciki, ga kuma damuwa na rashin farfaɗowar Meeshar tasa. Sai dai yunwarce ta yi mashi yawa over da har tasa ya haye saman table ɗin zai ci abincin.

Shi ma Areef ba dan daÉ—i zai ci abincin ba, dan kawar da yunwa kawai zai ci, banda haka yanayin da yake a ciki na kewar Jehan ya hana shi sukuni.

Shi kuwa Aseef suna zama a saman table ya kira Akila video call tare da ajiye wayar a yadda zasu ga juna, haka yake yi kullum, dan ya ce ba zai iya cin abinci ba tare da suna kallon juna ba. (Aseef ɗan dirama ne wlh😂 iskanci kala kala ya iya.)

Kamar dai kullum, sai da ya karɓi first spoon na ƴan uwan nasa, yana yi yana karewa Akila dake kwance a saman bed kallo, daga ita sai kayan barci riga da wando a jikinta, ta lafe a saman bed tare da rungume pillow a kirjinta tana kallonsa, Jehan dai har wa yau tana bedroom na gwaggo, ita kuma Akilar a normal bedroom nasu ita da su Jehan ɗin take, ba'a bedroom na mijin nata ba, tun da ya bar kasar ita ma ta baro bedroom ɗin.

Sai kallon shi take yi, ya kara kyau, ji take yi kamar ta zuro hannu ta shafi wannan lallausan kumatun nasa mai matuƙar ɗaukar hankali, ga sajensa ta kara kwanciya luf, duk sai ta shiga santin kyau ɗin da ya kara yi.

A nashi ɓangaren shi ma santin kyau ɗin gyaran da ta sha yake yi, ta yi fresh, ji yake yi kamar ya jawota ya rungume, sai zubawa juna shagwaɓa suke yi, ko kunyar su Lion basu ji, su kuwa su Lion ɗin ko a jikinsu, tamkar babu su a wajen, abincinsu sama sama kawai suke ci.

Kaɗan Lion ya tsakuri abincin ya miƙe bayan ya goge bakinsa, bedroom nasa ya nufa dan ya yi wanka ya fito ya duba ya jikin Mark yake, dan yau sam bai leƙa shi ba.

Mark ɗin yana part dake kusa da na Aseef, a nan yake jinya, an ɗaura mashi kafar tasa, yana samun lafiya Alhamdulillah, likitoci har huɗu Lion ya sanya suka zo suna kula da shi, dan already kun riga kun sani cewa Lion yana Kaunar Mark sosai, shi ne ma yasa ya ce a dawo mashi da shi gida ya yi jinya a gabansu, dan su rinƙa kallon halin da yake a ciki.

Bawan Allah yana shan wahala ba kaɗan ba, duk ya rame, kunsan yadda karaya take da azaba!. Kullum Anaya tana gefensa, bata taɓa yin nesa da shi, idan kuka ga ta fita daga bedroom ɗin, to sai dai idan likitoci ne suka zo zasu yi aikinsu, shi ne zata fita ta koma ɗayar ɗakin, dan a cikin part ɗin ɗakuna uku ne da palo guda, so ɗaya nata ne ɗaya na Mark ɗin, ɗayan babu kowa a ciki, idan likitoci sun zo, sai ta koma nata ɗakin, dan ta basu waje.

Mark yana kaunarta sosai, ita ma ba sai na sake faɗa ba kun sani, ita ce ma ta fara son shi kafin shi ya faɗa mata. Duk da yana a halin ciwo, amma hakan baya hanashi ya rinƙa kula da ita tare da gaya mata kalamai masu daɗi, dan ya rinƙa kwantar mata da hankali, saboda tana cikin damuwa sosai wlh, dayawan lokuta idan ta zauna bata da aikin yi sai yi mashi kuka, shiyasa yake iyaka bakin kokarinsa dan ya ga ta dai'na shiga damuwa tana farinciki. A yanzu dai kafar tasa ta kai matakin da za'a kwance mashi ita ya ɗan fara takawa, umarnin Lion kawai likitocin suke jira, dan su kwance mashi ya ɗan fara takawa.

Bayan ya yi wankar ya shirya cikin kayan barcinsa masu bala'in kyau da tsada, sai zuba kamshi yake yi tamkar a jikinsa ake kera perfume. Bedroom na Mark É—in ya nufa, yana tafiya cikin wannan nutsuwa tasa.

Kasa kasa ya yi sallama tare da shiga cikin É—akin. Anaya tana zaune a saman bed É—in kusa da mijin nata, hannunta na a ruke da cup mai É—auke da coffee, sai tiririn zafi yake yi, shi kuma Mark É—in yana É—an gefenta, yana zaune, daga bayansa ta sanya mashi pillow, da alama ma coffee É—in take ba shi a baki, ga É—aya daga cikin Drs dake kula da shi yana zaune a saman bedside drawer, da alama ita Anayar ita ta ce zata bashi coffee É—in a baki, hakan yasa Dr ya kyale mata ta bashi, dan duk abin da ta ce zata yi mashi, sai Mark É—in ya ce masu su kyale mashi ita ta yi mashi.

Kusa da bed ɗin ya ƙariso, a takaice ya tambayi Mark ɗin ya yake jin jikin nasa a yanzu?.

"Alhamdulillah sir". Ya bashi amsa cikin girmamawa. Anaya ta koya mashi faÉ—in Alhamdulillah.

Jinjina kai Lion É—in ya yi tare da tambayar Dr ba wata matsala. Babu ya amsa mashi da shi cikin gaggawa shi ma. Sallama ya yi masu tare da ficewa ya koma bedroom nasa.

Saman bed ya haye ya kwanta, shiru ya lumshe idanuwansa tamkar mai yin barci, a haka Areef ya shigo ya same shi, saman bed É—in ya nufa yana faÉ—in "His Excellence what is wrong with you? Since in the evening naga like you're not in a good mood".

ÆŠan waro idanunsa waje ya yi, in a cool voice ya fara magana "Areef am in too much of missing Meesha, abin ya kai ni makurar da i can't control myself, I can't stop myself daga kai kai'na gareta".

Shiru Areef É—in ya É—an yi. Hakika ya yi mugu mugun tausayawa Lion É—in, dan yasan wanene É—an uwan nasa, abin da zai sanya shi ya buÉ—e baki ya ce ya yi missing na wani abin, this thing is not be small thing ooo, duk sai ya ji ya shiga damuwa sosai, ya tausayawa Lion É—in sosai da sosai.

"Do you know something our Lion?". Shiru ya zuba mashi idanu ba tare da ya amsa ba.

"Ka sanya a É—auko maka ita, this is the only solution we have, zaman ta a kusa da kai ma zai taimaka maka sosai a kan duk wani abin da zaka yi, and then lastly Rimsha she is so special, she is very very smart, sometimes idan ta faÉ—i wani magana, zaka yi tunanin mace mai 30 years old ne ta faÉ—e shi, tana da hankali, nutsuwa and bata da yawan magana bare ka ce zata dameka da surutu ta hanaka yin aiki, so just ka É—auki kayarka kawai, ta dawo kusa da kai, now she is your power and she is your weakness".
Chapter 97 · 0% Book details