← Book details Triplets Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 168

Sashe 24

Triplets Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Turo É—an baki ta yi tare da sake kiransa, nan ma shiru bai É—auka ba. A kule ta É—aga wayar zata buga da kasa, Æ´ar kara wayar ta yi alamar shigowar sako. Cikin sauri ta fasa bugata da kasa tare da buÉ—e sakon.

Cool murmushi ta saki ganin sunan Noorinta, tun bata ga me sakon ya kunsa ba. A hanzarce ta buÉ—e ta fara karantawa kamar haka. "Idan kika fasa wayar nan, babu mai saya maki wani, ke da waya har abada Æ´ar rigima kawai". Shi ne abin da ya rubuta mata a sakon. Ta sani sarai ba wai yana kallonta bane, kawai ya riga da ya san hali ne, ya san abin da zai biyo baya idan bai É—auki kiran ba, ya san rigimarta sarai, shi ne yasa ya yi mata sakon tun wuri.

Juya dara daran fararen Sleeping eyes nata sama ta yi, har wani walwali suka yi, É—an girgiza kai ta yi tana magana kasa kasa ta yanda ita kaÉ—ai zata san me take faÉ—a. "Allah Noorin nan nawa ya rainani da yawa". Shi ne abin da take faÉ—a.

(E lallai Rimsha kin girma, wai NooRi ya rai'na ta?🤔 Ba shakka kin ga gadon kwanan Lion, dole ki ce haka😂)

Shi kuwa, sai da ya gama ja mata rai son ransa, sannan ya yi mata massage a kan ta zo boys quarters na gidan ta same shi. Da kamar ba zata je ba, dan ta yi fushi na shanyata da ya yi tun ɗazun tana jiranshi. Sai kuma ta tuna cewa bai ci komai ba bawan Allah, yunwa yake ji ga kuma ɓacin ran da ya shiga. Tuna hakan yasa ta ɗauki abincin na nufi wajen. Shi ma bene ne mai hawa ɗaya, babu wanda ya taɓa kwana a wajen, komai na cikin wajen sabbi ne.

Bakinta É—auke da sallama ta shigo cikin palon kasan. Babu kowa sai sanyin Ac da kamshin air freshener da kuma kamshin perfume É—in na Lion É—in dake tashi.

Haurawa sama ta yi, sai aikin turo baki take yi.

Bakinta É—auke da sallama ta shiga bedroom É—in da ta ji kamshin perfume É—in nasa ya fi yawa a ta wajen.

Yana kwance saman bed, daga shi sai ƴar wando short zuwa kaɗan daga cinyoyinsa, ga wandon ya kama shi sosai, ya manne da fatar jikinsa, ba dan kalar wandon da yake fari ba, da ba zaka taɓa tunanin ma ya saka ba, saboda mannewa da jikinsa da ta yi. Sai dai ya ja bargon dake saman bed ɗin izuwa kugunsa. Da alama wanka ya yi, dan ga gashin kansa da akwai danshin ruwa. Daga ta sama kuma, yana sanye da ƴar riga mara nauyi, irin waɗan nan T-shirt ɗin masu laushi sosai, sannan masu kananan hannu.

Tun da ta shigo ya tsareta da waÉ—an nan dara daran idanuwan nasa masu rikitarwa yana kallonta, tamkar zai cinyeta. Ta yi kyau ne over, ji ya yi tamkar ya tashi ya rungumota. Ita kuwa, sai aikin turo mashi É—an bakin nan nata take yi, ita a dole tana fushi.

A tsakiyar Chinese carpet dake a cikin bedroom É—in ta ajiye abincin. Zama ta yi a gefen abincin ba tare da ta kalli in da yake ba, ta fara magana "Yaya Saif sannu da hutawa, ga abinci nan na kawo maka, ka zo ka ci dan nasan kana jin yunwa".

Nisawa ya yi yana mai cigaba da kallonta, bai ce komai ba.

Almost 10 mins suka É—auka a haka, bai ce mata ko sannu ba, yana ta kallonta, ita kuma taki É—agowa su haÉ—a idanuwa.

Da ta ga bashi da niyar motsawa, sai ta miƙe tana kumbura kumatu ta nufi waje, ta ki yarda dai ta kalli in da yake. Ko sannu bai ce mata ba. Har ta fice daga cikin ɗakin.

Nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke tare da jawo wayarsa, ya yi mata massage a kan ko taku É—aya bai yarda ta kara ba a wajen tafiyarta, ta juyo ta dawo.

Tana gama karanta sakon ta zunduba ihu tamkar wanda aka kwalawa itace a tsakiyar kai, haushi kamar ta je ta shakesa, ga shi bata isa ta ki zuwa ba, dan idan har ta kara taku É—aya É—in ta shiga tsinuwan Mala'ikun Allah ne, har sai time É—in da ta zo ta bashi hakuri ya kuma yafe mata, sannan Mala'ikun za su dai'na tsine mata, wannan babban musifa ce bijirewa maganar miji, ko ba daÉ—i ayi hakuri a bi, shi ne zaman lafiya!!!.

Juyowa ta yi tana kuka da hawaye bibbiyu, da farko tafiyar yanga take yi ta kawo abincin, yanzu kuwa jan kafar take yi tana kuka dan haushi.

Yana kwance in da yake, bai motsa ba. Gaban bed É—in ta zo ta tsaya, kusa da shi, tana kuka, bata ce mashi ko kala ba.

Hannu ya kai ya jawota ta faɗa jikinsa, gyara mata kwanciya ya yi izuwa saman faffaɗar kirjinsa, ɗago haɓarta ya yi ya fara lashe hawayen da ya sa suka zubo ɗin. Duka ta fara kai mashi a kirjin nasa tana faɗin "Allah Noori mun ɓata". Ta yi maganar a shagwaɓe. Kara matseta a jikin nasa ya yi tare da matse ɗan bakin nata, kasa kasa ya ce ta yi shiru ya gaya mata wani abin mai daɗi.

Jin hakan yasa ta yi shiru tana shesshekar shagwaɓa tare da kumbura kumatu. "Meyasa kika cika rigima ne?". Ya faɗa a sanyaye. Turo baki ta yi bata bashi amsa ba.

"Don't you know that you're my happiness? You know how sad I was before you came here? Kin san da na kalli face naki ya naji kuwa?".

Da sauri ta ɗago tana faɗin "Ya ka ji to?". Lumshe idanuwansa ya yi, dan yanda ta ɗago fararen idanun nan nata, ba ƙaramin tafiya da shi suka yi ba, dan yanda ta ɗagosu, har wani walwali wal wal suka yi mashi.

"NooRi to ka gaya mani ya ka ji mana?". Tana magana tana shafa lallausan bakin gashin dake kwance a hannunsa da yake rungume da ita. Bai amsa mata ba, kuma bai buɗe idanuwansa ba. Sake tambayarsa ta yi tare da saka mashi kukan shagwaɓa.

Ba tare da ya buɗe idanuwansa ba, ya matso da ɗan bakinsa sai tin kunnanta, murya kasa kasa kamar mai raɗa, sai ka rantse da Allah baya motsa laɓɓansa, cikin wata iriyar murya mai tsayawa a ran masoya ya fara yi mata raɗa idanuwansa a lumshe. "Kina shigowa cikin bedroom nan, ina ganin beautiful face naki, sai na ji na mance komai, i feel like ban taɓa jin wani ɓacin rai ba, you're special!".

Da sauri ta zaro idanuwanta tare da juyowa da kallonta izuwa kan face nasa sosai. Idanuwansa a lumshe, magana yake yi cike da class tare da izza, cikin kuma kwanciyar hankali da nutsuwa, a ko da yaushe babu ko É—igon na hayaniya a cikin voice nasa, so silent zaka ji ta, bare kuma yanzu yanda yake magana kasa kasa, ya kuke tunanin muryar zata kasance? Hmmmm......

Hakika ya ji tsakanin kaunarta a ransa sosai saboda gwaggo, saboda yanda babanta ya kula da gwaggon, a haka ma bai san cewa Gwaggon ta fi son su Rimshar sama da kowa a cikin Æ´an uwanta ba, wata kila idan ya san hakan, ko kasa ba zai bari Meeshar tasa ta sake takawa ba, saboda so........ Mu dai je zuwa, uwa ai ba wasa ba, bare su da suka É—auki tsawon shakaru 31 zuwa 32 basu tare da ita, ai dole su so duk abin da uwar tasu take so fiye da tunanin mai tunani. Yau wani irin jin Rimsha yake yi a cikin ransa fiye da misali!.

Sosai ta zuba mashi idanu tana mamakin kalaman da yake yi, tamkar wanda ake gayamawa. Idan a baya ne ka ce mata ya iya wannan kalamai, ba zata taɓa yarda ba, babu ma wanda zai yi gigin yarda, ko TRIPLETS nasa ba za su taɓa yarda da cewa shi yake furta kalamai haka ba.

Duk da idanuwansa a rufe, a jikinsa ya ji tana kare mashi kallo, hakan yasa ya ɗaga mata gera ɗaya. Wani irin sihirtatcen kyau ya kara, ga gashin gerar nasa kullum kara cika suke yi sosai, tamkar ana saka masu taki, har ta kusa haɗe mashi, gasu a kwance luff, kyakkyawar jajir ɗin kumatunsa, wani irin laushi ne da su kamar fatar jariri, sai kyalli soft skin nasa take yi sosai da sosai, dogon hancin nan nasa, tamkar shi ya bawa kansa saboda yanda ya zauna ɗas a face nasa, sak hancin Dr William, lips nasa kuwa, ba'a magana, dan gabaɗayansu TRIPLETS Allah ya yi masu halittar lips mai matuƙar kyau da ɗaukar hankali, lips nasu na saman design of heart ne, na kasan kuma yana da ɗan faɗi kaɗan, gasu jajir dasu tamkar an saka masu red janbaki, ga laushi kamar fure, ga ɗan bakin nasu ɗan karami da shi, sai dara daran idanu tamkar na Dr Salman.

"Noorish, meyasa nake sanyaka farinciki idan ka kalleni?". Sai a lokacin ya waro idanunsa a kanta. A cikin idanunta ya kalli tsananin son ya ce yana sonta da take yi, tana tsananin so ta ji kalmar so daga bakinsa.

Shiru ya É—an, kafin ya ce "Ni ma ban san dalili ba, kawai dai idan na ganki, ina shiga farinciki".

Wani irin yawu ta haÉ—iye, dan ba hakan take son ji daga gare shi ba, amma ba komai. Shi ma yasan ba hakan take son ji ba, tana so ne ta ji ya ce saboda yana sonta, da gangan ya bata wani amsa da ban, yana tsananin jin daÉ—i idan yana ja mata rai.

"Noorish kazo ka ci abinci". Ta faÉ—a a takaice.

"Meesha saboda ban baki amsar da kike so bane zaki nuna mani baki son cigaba da yin hira da ni?."
Girgiza mashi kai ta yi tana sunkuyar da kanta ƙasa.

"To meyasa zaki nuna kin gaji da hirarmu?".

"Noorish ni fa nafi son ne ka ci abinci, gwaggo ta ce mani baka ci komai ba, to ka zo ka ci ga ji?". "Meesha meyasa kike koyan yin karya ne?".

Zaro idanu ta yi tana kallon wuyarsa.
Chapter 24 · 0% Book details