← Book details Triplets Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 136 OF 168

Sashe 136

Triplets Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gabaɗaya jiga jigan ƴan siyasar da suke a cikin wannan katafaren office ɗin babu wanda bai sha ruwan mamaki ya kuma girgiza da ganin Lion a tare da mace ba, duk da wasu daga cikinsu sun gan shi a airport lokacin da ya ɗauketa, basu ɗauka cewa yana tare da ita har a yanzu ba, duk sai suka tsareta da waɗan nan idanuwansu na turawa masu kama da glass ɗin, sai kallonta suke yi, hakan ba ƙaramin ɓata mashi rai ya yi ba, kun san shi da ɗan banzan kishi, duk da cewa dukka waɗan da suke cikin office ɗin sun haura sheƙaru hamsin, ba yara bane, shi ne ma kawai matashi mai jini a jika a cikinsu, amma kishi yasa ya daka masu wata uwar tsawa, wadda ya sanyasu wata uwar firgita, ba su kaɗai suka firgita ba harda ita kanta Rimshar.

Sarai yasan sun haife shi, wasu daga cikinsu ma sun yi jika da shi, amma hakan bai hana ya daka masu tsawar ba!.

Babu wanda bai razana na jin tsawar tasa ba a cikinsu, cike da izza da nuna isa ya tambayesu meeting suka zo yi ne ko kuma kallon matarsa?.

Wani irin mamaki ne ya kama Rimshar na ganin yadda waɗan nan jiga jigan ƙusoshin gwamnati kuma tattijawa suke girmama shi, kuma suke tsoronsa, bugu da kari ta ga ba yadda yake magana da ita ko TRIPLETS nasa haka yake magana da su ba, a nan yana magana ne da kaifi ɗaya da kuma tsantsar madarar isa da izza, magana ɗaya ba sake maimaitawa!!. E yanzu kam ta yarda ita kaɗai Lion ya canzawa, ita kaɗai yake yi wa magana cikin sanyi da tausasawa, a waje shi ɗin zaki ne mai firgita manya da kananan halittu da gaske!!.

Kusan gabaɗaya waɗan da suke a cikin office ɗin sai da suka yi kasa da kansu alamar suna bashi hakuri, saboda duk da yake yaro a cikinsu, shi ne shugaba a samansu, shi ne president nasu nan gaba kaɗan In Sha Allah, so basu da zaɓin da ya wuce su bashi hakuri tare da girmamawa.

Kara É—aure fuska tamau kamar hadari ya yi tare da ce masu shi ya fasa attending na meeting É—in ma, idan akwai wani abin da suka tattauna very important suna iya tura mashi ta massage's, zai duba ya gani idan ta yi mashi.

Yana kai karshen maganar bai saurari amsarsu ba ya kashe computer yana wani huci kamar wani zaki, sun ɓata mashi rai na irin kallon da suka tsare Rimsha da shi

Areef and sir Arvin ne suka shigo cikin computer room É—in, bakin Areef É—auke da sallama.

Ganin Lion a tare da Rimsha yasa Areef É—in É—an yin murmushi kaÉ—an, duk da yana cikin matsananciyar damuwa na halin da Jehan take a ciki, hakan bai hana ya É—an yi murmushin ba, shi ma sir Arvin duk da dama bai san wacece Rimshar ba, bai san face nata ba, sunanta kawai yake ji, ganin É—an uwan nasa a tare da ita yasa ya É—an yi murmushi yana faÉ—in "Kun haÉ—u kenan?".

Wani kallo Lion ɗin ya jefa masu, dan shi ransa a ɓace take basu sani ba, ya yi nadamar meyasa ma bai sanyata ta sa face mask ba da zasu yi attending na meeting ɗin, kawai sun tashi sun kalle mashi face ɗin mata a banza, da wasu shegun idanuwansu kamar ball.

"Saif kazo ka duba jikin Aseef fa baya jin daÉ—i". Cewar sir Arvin.

ÆŠan zaro idanu Lion É—in ya yi, no wonder mana yake jinsa duk sai a hankali, ashe da biyu, dole ya ji jikinsa tana yi mashi babu daÉ—i.

"What's wrong with him?". Ya faÉ—a yana kallonsu.

Hannu Areef ya kyastawa Rimshar da ta tsare Lion ɗin da kallo a saman face nata yana faɗin "Zazzaɓi ne yake damunsa, ke kuma Our Queen mu fa ba ɗaukar Lion muka zo yi ba, kin wani tsare shi da idanu kamar mun ce zamu gudun maki da shi".

Turo baki ta yi. "Kai Yah Areef ni ba shi nake kallo ba". Ta faÉ—a kamar zata yi kuka.

"To kai Areef ina ruwanka da ita? Kafa cika sa ido, ai gara ta tsare shi da idanu mana, ba nata bane shi É—in? Mallakinta ne fa, kin ji yi ta kallon abinki, naki ne ke kaÉ—ai". Cewar sir Arvin.

"Good morning". Ta faÉ—a tana satar kallon sir Arvin É—in, tana son kallon shi kai tsaye, saboda ta kalli mai kama da Noorish nata, amma tana jin kunyar su haÉ—a idanu.

Matsowa kusa da ita ya yi ya É—an rungumota kaÉ—an yana faÉ—in." Morning my sister how was your night?".

Kallon Lion Areef ya yi, dan yasan ba zasu shirya da sir Arvin ba, duk da cewa al'adarsu ce rungume mutun idan suna gaisawa, ko kuma su bashi hannu, to wlh shi dai Lion ya yaye wannan al'adar, matarsa da shi kaɗai zata haɗa hannu, sannan shi kaɗai zai rungumi kayarsa, sir Arvin bawan Allah shi bai sani bane, bai san kishin ɗan uwan nasa har ya kai haka ba, da ya sani shi ma ba zai taɓata ba.

Lion ɗin kuwa dama can ransa a ɓace na kallonta da waƴan can mutane suka yi, ga kuma su Areef ɗin sun gaya mashi Aseef bashi da lafiya, yanzu kuma sir Arvin ya ɗan rungumo Rimsha, me kuke tunani zai faru? Sai mun haɗe gobe idan mai dikka ya kaimu.🥱 (Dole goben nan na saka Maltinata a cikin fridge ta yi sanyi over, saboda naji daɗin kallon chaskalensu ina korawa🤌😂)

PRINCESS FATEEMA taku ta amana ❤️🔥

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥

*KINDADE KINA NEMAN ABUN DA ZAI SANYAKI QIBA,QIBA MEKYAU KIYI DIMIMI DUK INDA KIKA SHIGA BABU RAINI KINYI TA SIYA KINA ASARAR KUDINKI🤔
ALBISHIRINKI NAZO MIKI DA ABUN DA ZAKISHA BA TARE DA KINYI ASARAR KIDINKI BA 💃 Yana da matiƙar kyau sosai ko'ina naki zai chiko ki xama abar sha'awa duk mai buƙata ta nemeni ta wannan number 09067614054, kada ki bari ayi babu ke, kayanmu tested and trusted ne, guarantee ne*.

*KINDADE KINA NEMAN ABUNDA ZAI SANYA KISAMU XAMAN LFY TARE DA KWANCHIYAR HANKALI? TO BABYN HABIBI KIXO UMMU AFFAN TAXO MIKI DA SHAHARARRUN KUMA INGANTATTUN MAGUNGUNAN MATA, KAMA TUNDAGA KAN HUMRA, TURAREN WUTA,
INFECTION KILLER,
COLACCA,
SAI KAYAN GYARA PAGE.
KACA KACA.
YALLAGWADA.
JIGIDA.
RUWA RUWA.
BANI BANI.
WOMEN JELL BATA BATA.
DAFIN KAXA.
TANTABARA.
XABUWA.
CICCIƁI.
AND EXCLUSIVE, XUMA TASTED AND TRUSTED INA FARIN CHIKIN SANAR DA KU MUN FARA RAMADAN PROMO GAME BUQATA XA A IYA TUNTUBA NA TA WANNAN NUMBER
09067614054 JIGAWA STATE MUNA AIKAWA KO'INA CIKIN AMINCI DA YARDAR ALLAH,
BABYN HABIBI KARKIMANTA DA KAYANMU FIRST CLASS NE, DAGA KANSA AN RUFE KOFA, YANA DA INGANCI NA WUCE TUNANINKI*.

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥

https://whatsapp.com/channel/0029VaMOfZZI7BeKXPU9gK2S

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥

TSARAWA DA RUBUTAWA......✍️

❤️FATEEMA ZAHRA MUSA (💫PRINCESS TEEMA🔥🌹)

*Domin samun damar karanta littafin nan daga farko har karshe zaki iya nemana ta wannan number 08161390581 ban da kira*

Date: 1/6/2024

E43

Hannu ya kai ya ja gashin sir Arvin É—in da karfi ba tare da ya yi magana ba.

Wash sir Arvin É—in ya furta tare da sake Rimshar yana faÉ—in. "Menayi maka kuma?".

Areef ne ya amsa da cewa "Ka taɓa nashi one in million nasa mana, kai baka san ba'a taɓata ba ko?".

Ɗan zaro idanuwansa waje ya yi, abin mamaki ma ya bashi, sabida shi bai ɗauki hakan kamar wani abin azo a gani ba, kunga na farko shi bai musulta ba, kuma shi bai taɓa zama cikin bakaken fata ƴan Nigeria ba bare ya san da yin hakan da ya yi ba dai'dai bane, sannan bugu da kari shi bai zauna da ƴan uwan nasa ba bare har yasan abin da suke so da wanda basu so, shi ne yasa abin ya bashi mamaki.

Sake shi Lion ɗin ya yi tare da miƙewa tsaye, cikin nutsuwa ya miƙa mata hannunsa a kan ta kama ta miƙe su tafi.

Ɗan satar kallon sir Arvin ɗin ta yi, duk kunya ya kamata, amma haka ta miƙawa Lion ɗin hannunta. Kamawa ya yi tare da ɗan jawota ta miƙe tsaye, mannata da jikinsa ya yi suka nufi hanyar fita daga cikin room ɗin.

Da kallon sir Arvin and Areef É—in suka bi shi da shi har suka fice. Part na Aseef kai tsaye suka nufa, har lokacin yana kwance bawan Allah.

Kasa kasa Lion ya yi sallama a parlourn, babu kowa a ciki, bedroom suka wuce kai tsaye, sai kallon part ɗin Rimshar take yi, taga komai na TRIPLETS iri ɗaya, harta carpet da komai nasu iri ɗaya sak, colors ne kawai ya banbanta, abin ya yi matuƙar burgeta ba kaɗan kaɗan ba.

Sallama Lion ɗin ya sake yi kasa kasa kafin ya sa kai ya shige ciki, bawan Allah Aseef yana ƙudundune a cikin bargo.
Saman bedside drawer ya ce da Rimshar ta zauna, shi kuma sai ya haye saman bed É—in mai gabaÉ—aya.

Kasa da bargon kaɗan ya yi izuwa kirjin Aseef ɗin, idanuwansa a lumshe kamar mai yin barci, sai dai kuma ba barcin yake yi ba, zafin zazzaɓi kawai tasa yake jinsa a s sama.

"Our heartbeat". Lion ya ambaci sunansa kasa kasa. Da kyar ya iya amsa mashi da na'am.

"What's wrong with you?".

Duk da yana zazzaɓin hakan bai hana shi turo baki kamar biro ba, a shagwaɓe kamar zai yi kuka ya ce. "Ba Heartbeat bace, ba ita ce ta je ta yi wannan abin ba, kuma ni Allah ba zan iya zama ba tare da ita ba, mutuwa zan yi Lion". Ya kai karshen maganar yana buɗe idanuwansa da suke jajir sabida zazzaɓin.

Nisawa Lion ɗin ya yi kafin ya fara magana. "Wannan shi ne kawai abi da ya saka mana kai zazzaɓi?".

GyaÉ—a kai ya yi alamar e. "Okey tom tashi ka yi wanka muje mu yi breakfast, anjima zan kawo maka Heartbeat É—in taka".

Girgiza kai ya yi yana faÉ—in. "No Lion, bana son ganin wannan abin da ta yi, kada ka kawota, idan ka kawota zan mutu, kuma ba zan iya rayuwa ba ita a kusa da ni ba, pls ni kasan ya zaka yi".

Dogon hancin nan nasa Lion É—in ya ja kafin ya ce. "Za'a goge abin da ta yi É—in, yanzu dai je kayi wanka kazo muyi breakfast ko?".
Chapter 136 · 0% Book details