← Book details Triplets Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 168

Sashe 53

Triplets Part 4 Complete Hausa Novel · about 6 min read

sau biyar dukka basu zama, wasu ta haifesu da rai su koma, wasu babu rai, a ciki na shidda ne muka haifi ƴan biyu dukka maza, kuma dukka Allah ya barɓi abinsa, shi na farkon, wato Hassan ɗin satinsa ɗaya a duniya ya rasu, na biyun kuma sai da ya yi wata biyar a tare da mu, sannan Allah ya karɓi abinsa, ni nasan mumini baya rabuwa da jarabawa ta Ubangiji, amma wlh wannan jarabawa ta ƴaƴa ya yi matuƙar girgiza mu, badan Aunty Aisha da take tare da mu ba, wlh da mun tabbaka babban kuskure, dan har cewa muka yi zamu sami wata mata mu biyata maƙudan kuɗaɗe, sai a sanya mata kwan haihuwata ta haifa mana yara ko uku ne, Aunty Aisha ce ta tsawatar mana sosai a kan hakan, a lokacin dai na bi umarninta ne kawai matsayinta na babba a kai'na, kuma ko ba komai Aunty Aisha ta nuna mana so da kauna nida Hassan fiye da tunanin kowa a lokacin da muke ƙasar Russia, amma banda haka wlh da a lokacin sam ba zan ɗauki maganarta ba, haka dai muka jure, ina ji ina gani dukka ƴan uwana daga mai yara uku sai mai yara biyu, shi babban yaya har matarsa ta haifi Imran, Akil, da kuma Akila, shi kuma yaya Deen, matarsa ta haifi Irfan, Aafia, and Umaisha har ma matar ta bar gidan a lokacin, ta bar Umaisha tana karama, Hassan matarsa ta haifi Feroz tana da cikin na biya, autanmu Maik dana rena da hannuna ma matarsa tana da ciki a lokaci, abin fa ba ƙaramin ɗaga mani hankali ya yi ba, Maryam da kanta ta ce na kara yin wani auren ko zamu sami ƴaƴan, naki yarda da zancenta, saboda bana son nayi mata kishiya, bana son kowa yazo ya takura mata, ina so ne ta yi rayuwar farinciki, ita kaɗai a cikin gidana, saboda mace ce ta gari, macece ƴar albarka, ta bani farincikin da ban taɓa tunani ba, tana da hankali da nutsuwa, ina tausayawa maraicinta, yanzu kuma ga rashin haihuwa, mun binne yara almost 7, amma shiru, a ƴan tsakanin nan muka sake samun ciki, a lokacin cikin matar Maik bai wani girma sosai ba, dan bai wuce 3 months ba, ita ma matar Hassan haka nata cikin bai fi wata uku ba, shiyasa ƴaƴan namu suka kasance shekarunsu ɗaya, sai dai ratan watanni, wato da Jalila, Anaya, da kuma Jehan kenan, sai dai fa ko da muka haifi Jehan ɗin, bamu wani jata a jiki sosai ba, dan muna ganin kamar ita ma mutuwa zata yi, amma da yake uwa da ƴa ba mai shiga tsakani, ita Maryam ta jata a jiki sosai, ni kam baya baya nake yi da ita, dan rasuwar Hussainin namu ya girgizani, na saba da shi sosai, ko ina zanje muna tare, yaro ɗan wata biyar amma ya san yawo, saboda fita da nake yi da shi, lokacin da ya rasu nasha wahala, har firgita nake yi a cikin barci ina kiran sunansa, to shi ne yasa na ki yarda na ja Jehan sosai a jikina, dan kada na sake shan wata wahala, sai da na ga Jehan ta cika shekara guda bata mutu ba, sannan ne na jata a jiki sosai, na fara nuna mata soyayya, mun so Jehan fiye da kanmu, baki ma ba zata iya faɗar adaddin soyayyar ba, haka muka cigaba da bata kulawa tamkar kwai a saman bajajjen faranti, Aunty Aisha ta fi mu nuna kula a kan Jehan, daga karshe ma haka muka hakura muka bar mata Jehan ɗin tana kwana a ɗakinta, dan ta kwace mana ita, shiyasa kuke gani a yanzu sun fi shakuwa, shakuwa ce da suka yi ta tun tile tile, ba ta yanzu bace ba, tun daga kan Jehan ɗin kuma bamu sake samun haihuwa ba har matar Hassan ta haifi Zaira, bayan haihuwar Zaira da wata ɗaya muma muka sami ciki, nan muka fara tattalin kayanmu, har Allah ya sauketa lafiya muka sake samun ƴa mace, a baya duk ƴaƴan da muka binne maza ne, yanzu kuma mata muka samu, ƴarmu ta biyu wato Rimsha, kama take da Maryam sak, while ita kuma Jehan kama take yi da ni sak, haka muka ɗauki son duniya muka ɗaurawa ƴaƴan nan namu guda biyu, muka cigaba da basu kulawa na wuce misali, sai dai sun fi shakuwa da Aunty Aisha, dan sun fi zama a wajenta, ni kuma ina kyale mata su ne dan su ɗebe mata kewar TRIPLETS nata da ta rasa, kullum maganar Aunty Aisha ɗaya idan tana yi wa su Jehan wasa, shi ne idan ta ga TRIPLETS nata, to sune mazajensu Jehan ba makawa, kuma zata yi ta addu'a a kan hakan, in dai tana raye ta gane ƴaƴan nata, to wlh ko sun yi aure sai sun auri su Jehan, kullum shi ne zancenta, a hankali hankali har ta zo ta fara dai'na zancen TRIPLETS ɗin nata, kamar wasa duk zancen ya bar bakinta baiwar Allah, haka muka rayu cikin farinciki, kullum muna waya da Shitu, shi ma ya jima da yin aure, suna da ƴarsu ɗaya Adiva, sa'ar Jehan ce yarinyar. Bamu tashi dawowa Nigeria ba har sai da su Jehan suka yi wayo, sai da Jehan ta kai primary 4 a school, wannan dalilin yasa sam basu jin Hausa, daga larabci, sai English da kuma yaren mamansu wato shuwa Arab, sai kuma kanuri da take yi masu kaɗan kaɗan, nima time to time ina yi masu fullanci, dan na koya wajen daddyna, sai dai Rimsha ce kawai ta ɗan iya fullanci, ita Jehan ko yaren mummyn nasu ma taki ta koya sosai, ita dai a barta da English, da shi kawai take magana, larabcinma sai taga daman yi, ga kafiyar bala'i, ga zafin rai, akwaita da iya tsare gida sosai, kuma dukka Aunty Aisha take zugata, ni dai bani da ta cewa, idan nayi magana Aunty Aisha ta hau surfa mani masifa, haka na zuba masu idanu, sai da muka dawo Nigeria ne na shiga harkar siyasa, da farko ina tsananin son siyasar, daga baya dana shiga cikinta, naga kazantar dake cikinta, sai naji ba zan iya ba, naso na barta, amma Maryam ta hanani, ta kuma kara mani kwarin gwiwa a kan lalllai na yi siyasa, lallai siyasa tana da bukatar mutun irina, zai tallafawa kasa ba kaɗan ba, ta dai nuna mani alfanonta sosai, na kuma gamsu, dan haka sai na sake zage dantse sosai, ina da abokan hamayya sosai, amma ban taɓa mayar da hankali nabi ta kansu ba, kawai harkar gabana nake yi, a lokacin ne Allah ya haɗani da Abubakar Salahuddeen, muka fara takun saka da shi, in takaice maku labari shi ne ya zama sanadiyar rugujewar farincikina da ni da familyna bakiɗaya, saboda na kama shi yana dillanci kayan maye da kuma mata izuwa kasashen waje, ya yi ya yi na rufa mashi asiri, dan takarar da zai tsaya, naki yarda na rufa mashi asiri, sai ya bukaci da na shigo cikin tafiyar tasu, nan ma naki yarda, to shi ne ya nemi salwantar mani da rayuwata da ta familyna, a lokacin da na shiga siyasa sunana ya fito, kamar hauka haka su yaya Deen suka yi ta nemana, har gida sun zo wajena, amma sai nece masu ni ban sansu ba, bani da wata alaƙa da su, dan haka su kama kansu, shi ma Hassan yazo har gida, naki yarda da shi, kuma sarai na san komai ma da yake tafiya a rayuwarsu, dan ina aika masu da makudan kuɗaɗe tun ina Dubai, har na dawo Nigeria ban dai'na idan suna cikin matsala ta kuɗi na taimaka masu ba, wannan shi ne labarina da abin da ya faru da ni a takaice kenan, kun san komai ba zai faɗu lokaci guda ba, amma ku ruke wannan ɗin kawai". Ya kai karshen maganar yana mai gyarawa ya kwanta, tare kuma da tada kansa da laps na Brr Naurat.
Chapter 53 · 0% Book details