← Book details Triplets Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 168

Sashe 45

Triplets Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Almost 5 mins suna a haka, sannan ne ta matso da face nata dab da tasa, lallausan lips nasa ta sumbata, tare da kai hannu ta sakalo wuyarsa. Ganin yana bata wahala ne dan ya fita tsawo sosai, yasa ya rankwafo mata kaÉ—an, hakan ya bata damar samu ta fara kissing nasa cikin nutsuwa.

Kara kankameta sosai ya yi, yau wani irin kiss take yi mashi tamkar babu gobe, cikin salo ya shiga mayar mata da martani shima, tamkar zasu cinye juna.

Sun jima suna kissing na junansu kafin nan ya zame bakinsa daga nata, kasa kasa ya ce "Zan tafi, time ya cika, ki kula sosai my happiness". Ya kai karshen maganar tare da miƙewa da ita a jikinsa.

Kai tsaye palo ya nufa, har lokacin su daddy suna zaune suna ta mayar da zantuka. A tsakiyar palon ya sauketa, kunya tamkar zata shige cikin kasa, shi kuwa ko a jikinsa, sai ma kallon gwaggo da ya yi yana faÉ—in "Momma pray for us, zamu tafi". Ya kai karshen maganar tasa tare da nufar hanyar sauka kasa.

Gabaɗaya family suka rufa mashi baya, gwaggo idanunta sun cika taf da kwallah, ƴaƴanta har guda biyu zasu tafi Daular Mutuwa, waje mafi haɗari da bata taɓa jin biyunsa ba, ji take tamkar ta dakatar da su, sai dai kuma mahaifinta yana a can, tana kaunarsa shi ma, dole su je su ɗauko mata shi, hakan yasa ta danne ta jure, Aseef sai kuka yake yi a kan shi gaskiya zai bisu, ba zai yarda su tafi su barshi ba, koma yaya ne sai dai su tafi tare. Da kyar Lion ya shawo kansa ya hakura, suka ce mashi ya zauna ya kula da gwaggo da ƴan gida.

Shi kuwa Areef yana can yana haÉ—a kaya, sam bai sanar da Jehan da shi za su tafi ba. Bayan ya kammala haÉ—awa ne ya fito waje harabar gidan, a nan ya sami kowa da kowa, kai tsaye cikin mota ya fara nufa, sai da ya ajiye jakar tasa, sannan ya fito, kusa da gwaggo ya zo, cikin nustuwa ya ce mata "Momma be strong please, just pray for us, everything will going to be normal In Sha Allah".

Har lokacin idanunta cike tab da kwallah, addu'a ta fara zuba masu babu kama hannun yaro, sai amin amin kowa yake amsawa da shi.

Bayan ta kai karshen addu'ar ne, ba zato ba tsammani Jehan ta saki baki tana kallon jama'a, sai ji ta yi ya jawota ta faÉ—a jikinsa, rumgumeta sosai ya yi yana faÉ—in "Zan tafi my baby, ki kula mani da kanki sosai kin ji ko?".

Tamkar zata yi kuka ta ce "Dama har da kai za'a tafi Daular Mutuwar ne? Shi ne baka gaya mani ba?". Kara matseta sosai ya yi a jikinsa yana faÉ—in "Am so so sorry, mantawa nayi".

Dukan wasa ta fara kai mashi a kirjinsa tana faÉ—in "Ni bana son kaje, dan bana son wani abin ya sameka, ni dai ka fasa zuwa"."Da gaske baki son wani abin ya sameni?".

Da sauri ta gyaÉ—a mashi kai "E bana son wani abin mana ya sameka, ni bana son na rabu da kai". "To shikenan, pray for us, In Sha Allah babu abin da zai same mu". Ya kai karshen maganar yana mai kara matseta sosai a jikinsa.

Da alama sun mance da cewa a gaban family suke. Haka suka cigaba da zubawa juna kalaman kauna har sai da ya ishe su, while shi kuma Lion yana magana da gwaggo da kuma daddyn Rimsha. Bayan sun gama zuba kalaman love É—in ne ya saketa tare da nufar wajen motar tasu, sam yaki yarda ya juyo su haÉ—a idanu da ita, dan baya son ganin kukanta, ita kuwa hawaye wani na bin wani.

After some minutes Lion ya kammala maganarsa da su gwaggo, sannan ya juya ya nufi wajen motar, har Donal ya buÉ—e mashi kofar motar zai shiga, da gudu Rimsha ta tafi ta faÉ—a bayansa, tana sakin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro. Cikin kukan nata tana faÉ—in "Noorish ni zan bika, bazan iya bari ka tafi kai kaÉ—ai ba, gara muje tare kawai, gara komai zai faru ya faru a kan idona, ina tare da kai, ko mutuwa zan yi, nafi son na mutu a hannunka, please Noorish".

A hankali ya juyo ya rungumeta, har cikin ransa shi ma baya son rabuwa da ita, rabuwarsu babban ciwoce a gare shi, yasan zai sha wahala sosai, amma ba shi da zaɓi, dole ne ya barta a gida, dan bai san me zai je ya tarar a wajen ba.

Hakika har cikin zuciyarsa yake jin wannan kuka da take rerawa, amma sam ya kasa yi mata magana, ganin haka yasa daddynta ya kariso wajen, hannu yasa ya karɓeta daga jikin Lion ɗin. Ihu take zunduma masu bana wasa ba, faɗi take yi "Daddy ka ce ya tafi da ni, bana son ya barni, bana son rabuwa da shi".

Wucewa ya yi ya shiga cikin mota zuciyarsa na yi mashi zafin rabuwa da ita, shi kuma daddy wucewa da ita ya yi izuwa wajensu gwaggo. Yana zuwa gwaggo ta karɓeta suka hau rarrashi, amma ina, taki yin shiru, ihu take yi tana faɗin ita wlh zata bi mijinta........... RIMSHA MANYA MAI MIJI, TATTABARA UWAR SOYAYYA❤️😂

Da gudu Jehan ta juya ta bar wajen, ta koma cikin gida, dan ba zata iya ganin tafiyarsu ba, shi ma Aseef da sauri ya bar wajen, dan ba zai iya jurewa ba, dama da kyar Lion ya lallaɓa shi ya yi masu shiru.

Mark ne ya nufi motar su Lion É—in, dan ya ja su su tafi airport. Dai'dai zai buÉ—e kofar motar, Anaya ce ta zunduma ihu tana faÉ—in "Nashiga ukuna! Dama my da kai za'a tafi? Wlh ba zan iya jure rashinka ba! Ka dawo wlh ba zaka je ba, Rimsha fa ta ce mutuwa ake yi a can". Yau ga ikon Allah, iyaye dai suna ganin tsantsar rashin kunya ta yayan zamani, amma da yake duk jirgi É—aya ya kwasosu, wato duk jinin turawan ne, sai ya zama ko a jikinsu, basu damu da abin da Æ´aÆ´an nasu suke yi ba.

Da gudu Anayar ta tafi wajen Mark É—in, ta kuwa yi sa'a dai'dai lokacin ya juyo domin ya kalleta. Tana zuwa ta faÉ—a saman kirjinsa tana kuka, ita wlh ba zata bari ya tafi ba, ai ta ji Rimsha ta ce mutuwa ake yi a wajen.

Shi dai Azharuddin Bature, wato daddynta, baki ya saki yana ganin ikon Allah, a iya saninsa bai taɓa sanin ƴarsa tana soyayya ba, kwatsam sai ya ganta da wani? Lallai kuwa ya yi sakaci ba kaɗan ba. Ita dai Brr Naurat ko a jikinta, daɗi ma ta ji na cewa duk jikokin nata sai auren family suke yi, zumunci na kara ninkuwa.

Babu kunya Mark ya rungumeta sosai, kasa kasa ya fara rarrashinta. Ina ai kin sauraronsa ta yi, sai kuka take zuba mashi. Daddyn Rimsha bawan Allah, yana ganin abubuwa, shi ne dai ya sake zuwa ya kama Anayar, daddynta kam ya kasa motswa daga in da yake, duk ya yi la'asar, mamaki kamar zai kashe shi, wai ace kamar su Anaya sun san so? Shi yana matsayin daddynta sam bai san da zancen ba?! Abin ya bashi mamaki, sai kallon mummynta yake yi, ita ma shi take kallo, dan bata san komai ba............. Ni kuwa nace ta ina zaku sani? Ku ba ƴan boko ba, mummynta tana wajen aiki, kai kuma daddynta baka gari, ai kunma yi sa'a da Allah ya haɗata da Rimsha, da yanzu wani labari ake yi, da Mr Emmanuel ya jima da buɗe maku aiki, idan da rabo sai dai ku kanta da ciki ba tare da kun san ya aka yi ba, Allah ya baku amanar ƴaƴa, amma kun sake su kun tafi neman duniya, kun barwa masu aiki ragamar kula da su, tamkar ba ku aka bawa amana ba, tamkar ƴan aiki aka bawa amanarsu, ga duniyar yanzu yanda amana ta yi ƙaranci, baku san su masu aikin ya halinsu yake ba, yanda lesbian ya yawaita a duniyar nan, ku dai kawai kun sakar masu komai ba tare da dogon tunani da kuma yin aiki da faɗar Manzon Allah manzon tsira ba, wayewanku dai bai amfaneku ba! Wlh idan baku tuba ba, sai Allah ya kamaku, dan duk wani ɗa a duniyar nan, sai Allah ya tambayi iyayensa ta yanda suka kula da shi, hakki ne da kuma amana ya basu, dan haka sai ku kara zage dantse, Allah ka bamu dacewa.

Daddyn yana karɓar Anayar, Mark ya yi saurin shigewa cikin motar, shi ma zuciyarsa tana yi mashi zafi da kuna, Alex ya so ya rakasu, Lion ne ya hana shi, haka motocinsu ya tashi ya bar gidan, suka nufi airport, sai dai kafin su bar gidan, sai da Lion ya ja kunnan gataman a kan kada ya bari wani ya shiga gidan ko kuma wani ya fita ba tare da ya basu izini ba. A gabaɗaya sojoji goma sha biyu da suke gidan, sojoji uku Lion ya barsu a kan su cigaba da kula da family, ya tafi da guda tara.

Da yake motocin suna sharara uban gudu sosai, cikin ƙanƙanin lokaci suka isa airport ɗin, an gama shirya masu komai, dama tun jiya Lion ya shirya wasu abubuwa da zai buƙata, dan haka suna zuwa kawai suka ɗauki hanya, ba ɓata lokacin jirginsu ya ɗaga zuwa Enugu state........... TO FATAN MU DAI ALLAH YA TSARE HANYA, YA KUMA KAREKU DAGA SHARRIN QUEEN!!.
Chapter 45 · 0% Book details