← Book details Triplets Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 168

Sashe 39

Triplets Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ganin suna neman su juyawa Meeshansa kwakwalwa, suna neman su sanyata ta birkice gabaɗaya, sai ya miƙe tsaye tare da nufar in da take, hannu yasa ya saɓeta a kafaɗarsa, sai kuka take yi, ya wuce da ita izuwa bedroom nasa.

Jama'ar palon ma babu wanda ya lura da su, sai jajanta wannan al'amari kawai suke yi a tsakaninsu. Yana shiga ya shinfiÉ—eta a saman bed nasa, sannan shi ma ya haye.

Rikota ya yi tare da fara yi mata raÉ—a a kunne, kan kace me, sai gata ta koma sakin murmushi, ga guntun hawaye a gefe, ga murmushi kuma a gefe, jim kaÉ—an ka fara dariya har da kyakyatawa, tamkar ba ita ce yanzu take zunduma ihu a palo ba, kome Noorish É—in nata yake ta gaya mata a kunnen?.

Juyowa ta yi da kyau ta shige jikinsa tana faÉ—in "Amma Noorish ba'a jirgin ruwa zamu tafi ba ko?". Shiru ya yi yana kallon kyakkyawar face nata, duk hawaye ya bubbushe.

"Bakison tafiya a jirgin ruwa ne?". Jinjina mashi kai ta yi tana faÉ—in "Ina tsoron mu nutse kasa ne".

Shiru ya É—an yi na Æ´an mintoci kafin ya ce "Ba kina son shiga cikin ruwa ba? Idan mun nutse ai sai ki yi wanka ko?".

Turo baki ta yi tana faÉ—in "A'a ba irin wannan ruwa ba". Shiru ya yi yana ta kallonta.

"I like your lips". Ya faÉ—a a sanyaye. ÆŠago idanunta da suke jajir saboda kuka ta yi, kai tsaye cikin idanunsa ta kai kallonta, ya tsareta da ido sosai.

"Noorish nima lips naka suna yi mani kyau over". Gyara kwanciyarsa ya yi, a in da ya rage tsawonsa, ya zama face nasu tana dai'dai da juna. Zubawa juna idanu kawai suka yi, suna zuba kallon tsantsar so da kaunar juna. Romeo and Juliet kenan!.

Sun ɗan ɗauki lokaci a haka kafin ita ta kawar da kallonta tare da shigewa cikin jikinsa tana dariya. Hannunsa ɗaya ya ɗaura a saman bayanta yana shafawa tare da ɗan ciza laɓɓansa na kasa kaɗan.

A can palo kuwa, cigaba da maganar neman mafita ta yanda za'a ɗauko Dr Salman suka rinƙa yi. Sai can Areef ya ce masu dan Allah su bar mutane su huta haka nan, ai sun san cewa ko babu kowa nasu a cikin Daular Mutuwar nan, in dai Lion ya ji abin da ake aikatawa a ciki, to zai san yanda za'ayi a ruguje gidan, ballantana da akwai nasu har rayuka uku a ciki, bugu da kari kuma da akwai matar Aseef a cikinsu, ai dole ko ba zasu yi rai ba, dole su fito da su, dan haka shi dan Allah su dai'na damunsa da zancen wannan gida ta Mutuwa, idan suna magana, jikinsa har tsuma yake yi, ji yake yi ba zai iya hakuri ba, ji yake yi a yau zai tafi ya ɗaukowa Aseef matarsa, ya kuma kashe Queen ya ɗauko Dr Salman.

Gwaggo ce ta danne shi, dan ba shakka suna kara ɓata mashi rai idan suna maganar, ji yake yi tamkar ya tashi ya tafi a lokacin.

Miƙewa ya yi yana faɗin "Baby yunwa nake ji, na dawo baki bani abinci ba". Ya yi maganar yana kallon Jehan. Harara ta wurga mashi, zata yi magana idanunta suka sauka a kan mummynta, fasa yin maganar kawai ta yi.

Wucewa ya yi yana faÉ—in "Dan Allah kowa ya je ya É—an huta, kunga lokacin yin sallar mangariba ta kusa, ku huta kafin lokacin ya cika, maganar nan ta isa haka, tun da mun gano matsalarmu, to In Sha Allah zamu yi maganinta cikin gaggawa". Ya kai karshen maganar tare da sauka izuwa bedroom nasa.

Gwaggo ce ta haɗa kan gabaɗaya matan, ta ce masu su je bedroom nata su huta, ina nufin su Ammie, Mummyn Rimsha, Aunty, da kuma mummy Anaya kenan, sune suka bi gwaggo, su kuma su Jelly, Anaya, Zaira, Umaisha, Jehan, suka wuce bedroom nasu Rimsha, Imran shi ya raka su Abba boys quarters na gidan, sannan ya wuce izuwa harabar gidan, dan ya sha iska abinsa, Aafia kuwa tana ɗakin gwaggon, dan dama tun shigowarsu aka kaita can, sai zuba barci take yi baiwar Allah, har wa yau, uncle Herry yana tare da Dr William a ɗakinsa, Dr William ɗin ya farfaɗo, amma ƴaƴan nasa sam sun ki zuwa wajensa, bare ma Lion, sam baya son haɗa hanya da su, ɗan gara Areef ma, time to time yana zuwa ya duba shi, wani likita Lion ya sanya aka kawo yana kula da shi, amma shi ko leƙawa yaki ya yi, daddyn kuma ba shi da burin da ya wuce ya ga yaran nasa, yana tsananin kaunar TRIPLETS nasa fiye da tunanin mai tunani, Aseef kam kowa ya sani, ɗan baruwana ne, yana can wajen gwaggo, dan haka shi yama mance da Dr William abinsa, yanzu ma da kyar suka lallaɓa shi ya wuce bedroom nasa, ban da haka ya ce shi wlh sai ya je Daular Mutuwa ya ɗauko matarsa.

Wanke Jehan ta je tayi, bayan ta fito ta duba time, karfe 6:10pm, mangariba ya kusa, ga shi Areef ya ce mata yana jin yunwa. Sauri sauri ta shirya cikin kananan kaya, sannan ta ɗaura after dress a samansu, sai binta da kallo su Jelly suke yi, ita kuwa, basu isheta kallo ba, ba wanda ya sami kallon arziki a cikinsu daga wajenta, tamkar ba ƴan uwanta bane, kun santa dama da iya tsare gida da jiji da kai, to ko sannu bata ce da su Umaisha ɗin ba, haka ta gama abin da zata yi, ta zuba perfume kamar ba gobe, sannan ta fito izuwa cikin kitchen, kafanta na sanye cikin flat shoe mai matuƙar kyau na Rimsha, dan ita bata da kaya a gidan har yanzu, kuma bata ce a saya mata ba, dana Rimsha kawai take amfani, duk da sun yi mata kaɗan, haka take sanyawa.

Abinci mai rai da lafiya ta shirya mashi a saman tray, sai dai dukka zaɓinta ta ɗebo, dan ita bata ma san irin abincin da yake so ba, shi ne yasa ta ɗauka mashi zaɓinta.

ÆŠauka ta yi ta nufi waje, kai tsaye bedroom nasa ta nufa. Baki É—auke da sallama ta shiga É—akin, wayam babu kowa a ciki, bata yi mamaki ba, dan tasan halinsa da son Æ´an uwansa, wata kila ya tafi wajensu ne.

A saman carpet ta É—aura mashi abincin, sannan ta koma saman bed nasa ta bakin ta zauna, sai kallon É—akin take yi, ko'ina tsab kamar sabo, sai tashin daddaÉ—ar kamshi mai kwantar da hankali yake yi, ga sanyi Ac mai ratsa zuciya.

Ta ɗan yi nisa cikin tunanin irin kyawawan halayensa da kuma tsanar madarar kyau da Allah ya yi mashi, kamar daga sama ta gan shi a gaban mirror yana tsaye, ya bata baya, kugunsa na ɗaure da white towel mai matuƙar kyau, daga wanka ya fito, jikinsa duk danshin ruwa, ga gashin kansa yana ɗan zubar da ruwa.

Kallo ɗaya ta yi mashi ta yi saurin kawar da kanta gefe guda, har cikin ranta ta tsorata da ganin kyakkyawar kuma kakkarfar surar jikinsa, suna da halitta mai matuƙar kyau da ɗaukar hankali over.

Ganin kamar baya kallonta ne yasa ta mike a hankali dan ta bar É—akin, saboda ta lura shi fa tsab zai iya yin komai a gabanta, dan ba kunya ne da su ba.

Tana tafiya tana tunanin irin yanayin jikinsa da ta gani, duk da kallo É—aya ta yi mashi, amma ya tsaya mata a rai, jikin nasa kamar madara, soft skin nasa luwai luwai da shi. A dai'dai tsakiyar É—akin, bata yi aune ba sai ji ta yi ya rungumeta ta baya tare da zuro hannayensa a saman shafaffen cikinta, a hankali ya kwanto da kansa a saman shoulder É—inta.

Dogon numfashi ta ja tare da saukewa a hankali, ya sanya mata sanyin gashin kansa a wuya.

"Hyyy baby, ina zaki je kuma?". Ya yi mata maganar a cikin kunne.

"Zan fita ne na baka waje ka shirya". "Ni nace maki ina son ki bani waje ne?". Ya kai karshen maganar tare da sumbatar lallausan wuyarta.

Shiru ta yi bata bashi amsa ba. "Ina abin da kika ajiye mani? A waya kin ce kina kewata, na dawo kuma shi ne ba zaki zo ki ganni ba, sai da na roka ko? Na rokanma kin zo kuma zaki tafi tun ban ganki ba, kin san adadin kewarki da nake yi kuwa? Kin san me nake ji kuwa?".

Hannayenta ta É—aura a saman nasa dake saman flat tummynta, kasa kasa ta ce "To ka bari sai ka gama shiryawa zan dawo, sai muga juna". "Why ba zaki zo ki tayani shiryawa É—in ba? Yakamata ace kin saka mani kaya da kanki, please mana my baby".

Kasa jurewa ta yi, dan wlh tana tsananin kewarsa sosai, ga shi yanda yake yi mata magana a cikin kunne kasa kasa, duk sai ya kara tsumata, hakan yasa ta kasa jurewa, a wannan karon ta kasa dannewa sai da ta juyo ta faÉ—a saman faffaÉ—ar kirjinsa da kyau.

Ajiyar zuciya ya sauke tare da rungumeta da kyau da kyau, tamkar wani ya ce zai kwace mashi ita. Da yake ita tana da tsawo sosai, Kamar gwaggo take, tafi Rimsha tsawo, sai tsayinta ya kai ta kwantar da kanta a saman ɓul ɓul ɗin breast nasa.

Hannu ya kai saman bayanta yana É—an shafawa izuwa mazaunanta masu burge shi, kowa yasan matan turawa basu da halittar mazaunai sosai, shiyasa dirarren halittar su Rimsha yake É—aukar hankulan TRIPLETS over, suna son mazaunan nasu sosai, barema Rimsha, Jehan, Akila, Umaisha, sun fi kowa diri a cikinsu, tamkar su suka yi wa kansu.......

"Baby". Ya ambata a hankali, kasa kasa ta amsa mashi da na'am. "Zaki tayani saka kayan?". Shiru ta É—an yi kafin ta ce e zata taya shi........... JEHAN DUNIYA, BAFA ABIN DA YARINYAR NAN BATA IYA BA, KAWAI TSIYA CE IRIN NATA, SAI TA NUNA KAMAR MA BATA SAN KOMAI BA, SABODA SHEGEN JAN AJI DA TSARE GIDA.

ÆŠaukarta ya yi cak, sai cikin dressing room ya sauketa, dressing room É—in nasa sak irin na Lion.

"Ki zaɓa mani kaya to". Ya faɗa tare da harɗe hannayensa a saman kirjinsa.
Chapter 39 · 0% Book details