← Book details Triplets Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 112 OF 168

Sashe 112

Triplets Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Domin samun damar karanta littafin nan daga farko har karshe zaki iya nemana ta wannan number 08161390581*

Date: 20/5/2024

E35

Dan haka ya ji komai, a yanzu ya ji ba ita ta haife shi ba, saura Dr William.

Ya jima shiru yana tunanin kalar hukuncin da zai yi mata kafin ya É—ago kai ya kalleta. "Let's go". Shi ne abin da ya furta mata a sanyaye. Ya kai karshen maganar kuma tare da juyawa ya kwance wa sir Arvin hannayensa da ya É—aure mashi, sannan ya juyo da kallonsa a kan Dr William da yake tsaye yake binsu da kallon kawai.

"Before we go, I want to know who are you?". Ta faÉ—a tana mai dafe sai tin zuciyarta, dan a tsananin tsorace take, tana tsoron ta ji cewa Lion É—an gwaggo ne, duba da yanayin uban kamanin nan da yake a tsakaninsa da sir Arvin, idan har ya zamana da gaske É—an gwaggo ne kamar yadda take tunani, to ta san ba makawa sai ya hukuntata.

Ko kallon in da take bai sake yi ba, dan wani haushinta ma na musamman yake ji, yadda ta bar mashi ɗan uwa ya taso a Kristen, ta mayar mashi da mahaifi Kristen, bugu da kari ta raba zuciyar masoya, ta raba gwaggo da mijinta, sannan ta rabasu da iyayensu, basu ta so da ko guda ɗaya daga cikin iyayen nasu ba, ba uwar ba ba uban ba, kuma kaso tamani cikin ɗari na laifin ita ta aikata shi, domin da bata shiga tsakanin Dr William da gwaggo ba, wlh su Anderson basu isa su rabasu ba, basu isa su shiga tsakaninsu ba, saboda idan suna haɗe da kai, suna ibada sosai, to fa babu abin da ya isa ya rabasu sai mutuwa, shiga tsakanin nasu da ta yi ne, yasa suka rabu, bayan sun rabu kuma hankalin kowannansu a tashe, saboda suna son juna, dole damuwar da suke ciki ta rabuwar tasa ba zasu rinƙa ibada yadda ya kamata ba, da wannan dama su Anderson kuma suka fara yin amfani, so idan kuka duba abin kaso tamanin cikin ɗari laifin Cherish ɗin ce, hakan yasa Lion ɗin ya ji sam baya son sake ganin face nata ma a rayuwarsa!!.

Yana kwance sir Arvin ya miƙe tsaye tare da fara bin Cherish ɗin da kallo, yana mamakin yadda ta zauna ta zayyano waɗan nan bayanai dallah dallah kamar wadda ta aikatasu a yanzu, tsawon shekaru 32 bata mance komai ba, tsabar ita da kanta ta san ta zalinci mutane dayawa, wannan akwai mai bakar zuciya!.

Kasa ce mata ko uppan ya yi, saboda wani irin jiri ma da yake gani, kansa yana sara mashi, jin abin yake yi tamkar a mafarki. A hankali ya dawo da kallonsa a kan Lion dake ta faman latsa wayarsa kamar mai tura wata saƙon. Kyawawan laɓɓansa irin na TRIPLETS ya motsa yana son ya wa Lion ɗin magana, sai dai ina, bai kai ga yin maganar ba numfashinsa ta ɗauke diff.

Sulalewa ya yi zai zube ƙasa, tamkar Lion ɗin yana ganinsa, bai bari ya kai ƙasar ba ya taro shi da sauri, sir Arvin ɗin ya faɗa a saman Lion chest nasa. Hankali a tashe Dr William ya nufo wajen yana ambatar ARVIN!!! ARVIN!!! Yana magana ne da ɗaga murya.

Ita ma Dr Cherish cikin ɗaga murya ta fara ambatar sunansa tare da baro in da take da nufin ta kariso wajen. Wani irin gigitaccen tsawa da Lion ya daka masu ne yasa daga Dr William har Dr Cherish ɗin suka kasa karisowa in da yake, ya ce baya bukatar ganin Dr Cherish a kusa da su. Mayar da wayarsa cikin aljihunsa ya yi tare da gyara tsayuwarsa ya saɓi sir Arvin ɗin a saman kafaɗunsa, kai tsaye waje ya nufa da shi ba tare da ya bi ta kansu ba.

Da sauri suka rufa mashi baya, a haka suka fito harabar katafaren hospital É—in.

Ganinsu a haka yasa jiga jigan bodyguards ɗin sir Arvin ɗin suka yi sauri fara buɗe masu gidan baya na motocin nasu, a gidan baya na motar sir Arvin ɗin ya kwantar da shi, sannan ya ciro kuɗi dollars in his pocket ya bawa ɗaya daga cikin bodyguards ɗin a kan ya kaiwa mai taxi ɗin da ya kawosa. Lion yana da adalci sosai, baya taɓa tauye haƙƙin wani, baya taɓa tauye wani, a koma ina yake yana ƙoƙarin saukewa kowa hakkinsa da ya rataya a wuyarsa, ya ci sunansa na shi kaɗai ma gayyace mai zaman kanta, yana da tarin abubuwar da kwakwalwar zaratan maza dayawa ba zasu iya ɗauka ba, amma duk da haka baya barin wani abin nasa ta taɓa haƙƙin wani, a kowani hali yana ƙoƙarin yaga dai bai tauye wani ba, shiyasa mutanen U.s suke bala'in son shi, duk da bala'in zuciya, turin kai, zafin rai da kafiya da yake da shi, to yana da adalci sosai na wuce misali.

A haka su Cherish suka shiga wannan motocin, saboda sir Arvin, kai tsaye airport Lion ya ce da drivers É—in su wuce, dan ya kammala aikinsa, so bai ga abin da zai tsaya jira ba.

Abin mamaki kuma abin al'ajabi shi ne, suna isa airport suka isko gabaɗaya bodyguards na Lion ɗin a tare da su Handsome and Pinky. Sosai Dr Cherish ta yi mamakin ya aka yi su Pinky suka zo airport?. (Ni kuwa na ce mata an gaya maki Lion ɗin wasa ne? Ai bai fito ba sai da ya shirya, kuma kafin ya kai muƙamin da yake kai ya take irinku dayawa, ya takeku kamar ƙuda a gabansa🥱🧐)

Suna isa airport ɗin ya fito tare da sake saɓar sir Arvin ɗin a kafaɗarsa, cikin jet nasa ya nufa da shi, da mamaki su Cherish suka tsaya a baya suna kallon ikon Allah.

Jim kaÉ—an ya fito daga cikin jet É—in bayan ya kwantar da sir Arvin a saman luntsuma luntsuman sofas dake a ciki. A kofar shiga jet É—in ya tsaya tare da yi wa Handsome alama da hannu a kan yazo. GabaÉ—aya Handsome É—in yana ruÉ—e, sai wani kallon Lion É—in yake yi, saboda tsananin kamar da ya gani na sir Arvin, ita kuwa Pinky tana ganinsa ta taho da gudu ta rungume shi tana ambatar sunan sir Arvin, dan a tunaninta sir Arvin ne.

Hannu Lion ɗin ya kai ya ɗauketa cancak tamkar yadda sir Arvin ɗin yake yi mata, a saman Lion chest nasa ya ɗaurata, ba tare da ya kallin face nata ba ya juya tare da yi wa su Dr William dake tsaye alama da hannu a kan su zo, dai'dai lokacin kuma Handsome ɗin ya kariso wajen hannunsa ɗauke da password nasu shi da iyayen nasa, dan Lion ɗin da ya tura a ɗauko mashi su, sai ya ce bodyguards ɗin nasa su sanyasu su taho da password ɗin su gabaɗaya, dan U.s zasu wuce, bai ga dalilin zamansu a ƙasar China ba, ya gama aikin da zai yi, ba mai sake dakatar da shi kuma.

Sumbata Pinky ta kai mashi a kumatu tana tambayarsa yau ma yawo zasu je wata kasar kamar ranar? Duk a tunaninta sir Arvin ne, sai da Lion É—in ya juyo da face nasa tare da kallonsa a kanta da kyau, sannan ne ta zaro blue eyes nata waje sosai, dan ta ga ba sir Arvin bane, dama na gaya maku in dai ka yi wa É—aya daga cikinsu farin sani, to zaka iya banbantasu, dan suna da banbanci, ita kuma Pinky ai bama wanda ya kaita sanin sir Arvin, dole ta gane ba shi bane.

Ƙoƙarin sauka daga jikinsa ta yi, ta tsorata sosai har jikinta ya fara kerma, shiru Lion ɗin ya ɗan zuba mata idanu ba tare da ya ce mata ko uppan ba, sannan kuma bai sauketa ba, sai mutsu mutsu take yi tana son sauka daga jikin nasa, dan ta tsorata, kallon yadda jikinta yake kerma ya yi kafin ya mayar da kallonsa a kansu Dr William da suka iso wajen a yanzu, hanya ya basu a kan su wuce su shiga cikin jet ɗin da sauri kada su ɓata mashi lokaci.

Hannu Pinky ta kai ta ƙanƙame Handsome dake a kusa da Lion ɗin, kuka ta fara yi tana faɗin "Please Yah Handsome who's this man? Where's my baby?". Dama mafiya yawan lokuta baby take cewa sir Arvin.

Kasa bata amsa Handsome É—in ya yi, saboda shi ma dai bai san wanene bane, abin da zai iya cewa kawai shi ne yana jin Lion É—in tamkar É—an uwansa sir Arvin, shi ne kawai.

Ganin tana kuka ne yasa Lion ɗin ya ɗaura yatsarsa ɗaya a saman kyawawan lips nasa yana yi mata alama da ta yi mashi shiru, ya yi hakan kuma ba tare da ya sauketa daga ɗaukarta da ya yi ba. Tsananin tsoronsa yasa ta nutsu tsit ta dai'na kukan da take yi, bata da zaɓin da ya wuce ta kwantar da kanta a saman kafaɗunsa duk da tana tsoronsa.

Hannu ya sa ya nunawa Handsome ɗin ma cikin jet ɗin a kan ya wuce ciki su tafi. Ba musu ya shiga ciki tun da ya ga su Dr William ma sun shiga. A takaice sai da duk suka gama shi, Lion ɗin shi ne na ƙarshen da ya shiga, sannan aka rufe jet ɗin.

Zama ya yi a saman nasa luntsumemiyar sofar ba tare da ya sauke Pinky É—in daga jikinsa ba, duk da mahaifiyarta ta cuce su, hakan bai hana ya ji yana kaunar Pinky É—in da Handsome ba, saboda ba laifinsu bane, laifin wani baya shafar wani, bare kuma Pinky yarinyar akwai shiga rai ita ma kamar Rimsha.
Chapter 112 · 0% Book details