Sashe 82
Triplets Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sun sha kuka sosai, barema Rimsha, tafi kowa yin kuka a cikinsu, ita kuwa Jehan hawayenma bai gama barin kusa da idanunta ba, da alama ƙaƙalo kukan ma ta yi (ni ko wai menene zai sanya zuciyar Jehan da Lion yin laushi sosai ne?🤔 Wai duk wannan abin Jehan bata yi laushi ba?🤔 Kukan ma ƙaƙalo shi ta yi dan kada ace bata yi ba😂 kai jama'a Jehan dai har gobe da sauranta, shi dama Lion ba'a sanya shi a lissafi, dan ni na juya na juyo banga abin da zai sa zuciyarsa ta yi laushi ba, dan ko yanzu Rimsha ta yi mashi ba dai'dai ba zai bata a jikinta ne, sai dai daga baya ya yi dana sani, amma zuciyar nan tana nan babu abin da ya ragu a jikinta)
Akila ma ta sha kuka sosai, daga haka har barci ya É—aukesu.
After some hours.
Bayan sun yi sallar mangariba da issha ne Rimsha ta je wajen mummynta, dan dama mum É—in ta ce mata ta sameta a É—akinta. Tana zuwa mum ta zaunar da ita a bakin bed ta hau yi mata tata nasihar, ta É—aura daga kan nasu Brr Naurat, duk wata kunya ajiyeta a gefe mum ta yi, ta rungumi Æ´arta ta koya mata yadda zata zauna da mijinta lafiya, harta abin da yafi sanya namiji farinciki sai da mum ta gaya mata, ta ce ba zata tsaya nuna jin kunya ta cuci Æ´aÆ´anta a banza ba, su je gidan miji basu san yanda zasu kula da mijinsu ba, aure ya zo ya yi ta tangal tangal, gara mata ta ajiye kunya, ta jasu a jiki, ta gaya masu komai dallah dallah, hakan ne kawai zai bata daman samun kwanciyar hankalin kasancewarsu a gidan miji, barema Rimsha da take Æ´ar yarinya, ga mijin nata ba irin sauran maza bane ba, ai dole sai an koya mata abubuwa dallah dallah, É—an gara Jehan ma ta É—an girma.
Haka ta rinƙa yi mata nasiha sosai har sai da gwaggo ta zo ɗakin ta samesu, sai kuka Rimshar take yi sosai, gwaggon ce ta rarrasheta sannan ta ce tazo su tafi bari ta shiryata dan mijin nata ya iso. Wani irin daɗi ta ji Noorish nata ya iso, kamar zata tambayi gwaggon ina yake, sai kuma ta danne ta fasa dan ganin idon mummynta, da gwaggo ce kawai sai ta tambayeta ina yake, amma tun da mum tana nan, sai ta danne bata tambaya ba.
Riko hannunta gwaggon ta yi tare da mikar da ita suka nufi waje suna yi wa mum sai da safe.
Fitowa suka yi daga side na boys quarters É—in suka nufi cikin gidan. Sosai Rimsha ta yi mamakin ganin tsadaddun sabbin motoci dal dal har guda uku a parking space na gidan, motoci ne da suka amsa sunansu motoci masu numfashi, ko ba'a gaya mata ba, tasan dole su ne suka É—auko Noorish nata daga airport.
Wucewa suka yi izuwa cikin gida, tana sanya kafarta a palourn kasa kamshin perfume nasa ne ya fara dukan kofofin hancinta, sai ka rantse da Allah yanzu ya wuce a wajen, amma kuma ya jima da wucewa zuwa sama, dan Rimshar tana fita zuwa wajen mummynta, shi kuma yana shigowa, kasancewar tana part na boys quarters ne yasa bata ji diran motocin nasu ba, dan boys quarters ɗin ta baya yake, kuma motocin sabbi ne dal masu matuƙar tsada, kukansu a hankali yake fitowa, shi ne yasa basu ji ba.
Haurawa sama suka yi, kai tsaye bedroom na gwaggo gwaggon ta wuce da ita, shi kuma Lion yana cikin nasa bedroom ɗin, ya yi wanka yana sanye cikin kayan barcinsa tsadaddu masu kyan gaske, launin white color, ya zauna a balcony yana amsa waya nasu Aseef, sai kuka Aseef yake yi mashi a kan ya shammacesu ya tafi, shi dai Areef ya sani tun time da Lion ɗin ya bar gidan, Aseef ɗin suka ɓoyewa, sai yanzu ya sani, shi ne yake cewa shi wlh ba zai yarda ba, to rigimar da suke yi da Lion ɗin kenan.
Wanka gwaggo tasa Rimsha ta yi, bayan ta fito, gwaggon da kanta ta shiryata cikin wata dankareriyar doguwar riga mai matuƙar kyau, da suka fita da Tga ne gwaggon ta saya masu su ukun dukka iri ɗaya, da yake du Jehan mazajensu basu zo ba, sai ta ajiye masu nasu, ita kuma Rimsha suka hau shiryata, sai ta fito cas kamar wata ƴar tsana a cikin kayan, ta haɗu iya haɗuwa, gwaggo bata yi mata make up ba, ta ce su bar mata natural beautynta tafi kyau a haka.
Sai tsiya Akila take yi mata, sai kus, kus suke yi na munafurci, Akila tana gaya mata wasu zantukar a kunne, ita kuwa Jehan tuni ta fice zuwa bedroom nasu dan ta yi waya da Areef nata, ita kuma Akila ta tsaya ganin gulma, sai da aka yi wa Rimsha komai a gaban idanuwanta, gwaggo ta rufawa Rimshar wani haÉ—aÉ—É—en kuma tsadadden mayafi wanda ta feshe shi da tsadaddun Dubai perfume, ta rufa mata a kai ya sauko har saman face nata, tamkar za'a kai amarya, sai tsokanarta Akila take yi wai ta zama sabuwar amarya, gwaggo ta mai da ita sabuwar amarya.
A kule ta ce "Aunty Akila dama can ni sabuwar amarya ce, kuma kullum a sabuwa nake, ni ba zan zama tsohuwa ba bare yaya Saif ya auri wata".
Dariya sosai Brr Naurat ta kwashe da shi, Rimsha manya iyayen soyayya, wato dai bazata tsufa ba bare yaya Saif ya kara wani aure. Kuka ta saka masu, saboda Brr Naurat tana yi mata dariya.
Rungumota gwaggon ta yi tana faÉ—in "Babu wadda ta isa ta shigo maki gidanki, ko kin tsufa Saif ba zai kara aure ba, ki sha kuruminki abinki, ai ke Saif ne ma zai tsufa ya barki, dan ya ninka shekarunki sau biyu a yanzu, dan haka rabu da su, ke kaÉ—ai zaki yi zamanki a gidansa, ki ci karenki babu babbaka, ke da kike da Ni? Ai kawai kyalesu".
Brr Naurat ma cewa ta yi "A'a mayar da wukar sarkin raki, ai kishiya bana yi maki fatanta, ita ce musabbabin ruguje mana farincikinmu, amma kuma ke kin gudu baki tsira ba, dan already ni Saif ya fara aura kafin ke".
Buɗe nayafin da gwaggon ta rufa mata ta ɗan yi, ta fito da face nata tare da wurgawa Brr Naurat ɗin harara tana faɗin "Yaya Saif ɗin ne ya aure ki kafin Ni?". Yadda ta yi maganar sai da ta sanya su gwaggo wani irin mugun dariya sosai, Akila har da rike ciki, kai Rimsha duniya, ita fa idan akan Noorish nata ne zasu ɓata da kowa, kamar ba yanzu gwaggo ta gama gaya mata ita kaɗai ce a wajen Saif ba.
Rarrashinta gwaggon ta sake yi tare da riko hannunta tana faɗin "Zo mu tafi na kai ki wajen mijinki hai, yana can yana kewarki, daga shigowarsa ya tambayeni ina kike, na ce mashi zan kawo mashi ke, rabu da su Brr, so kawai suke yi ki ɓata kwalliyarki dan kada Noorish naki ya ga kyanki".
Da sauri ta É—ago daga cikin mayafin tana kallon gwaggon, tambayar kanta ta fara yi a kan a ina kuma gwaggo ta jiyo sunan Noorish? Ita Brr Naurat ta ruke sunan Meesha, ita kuma gwaggo ta ruke Noorish, wai yane suka sanyawa masoyan nan ido haka ne?.
Tana can tana tunani har suka shiga bedroom É—in bakin gwaggo É—auke da sallama.
Har lokacin yana zaune a balcony suna hira da TRIPLETS nasa a waya, kewarsu sosai yake yi, Allah ya gani sune bugun numfashinsa, yana sonsu fiye da baki ya musulta.
Jin sallamar gwaggo yasa ya miƙe ya dawo cikin bedroom ɗin.
Kallonta ya fara yi daga sama har kasa, shi baya iya ganin face nata, saboda tana cikin mayafi, ita kuma tana iya ganin face nasa, saboda mayafin bashi da wani kauri sosai, shara shara ne. A hankali ya zane wayar daga kunnensa tare da katse kiran yana mai cigaba da kallonsu har suka isa wajen bed nasa.
Karisowa cikin É—akin shima ya yi. A bakin bed gwaggo ta zaunar da Rimshar, ita kuma ta zauna a saman bedside drawer. Da ya zo shi ma sai ya zauna a bakin bed É—in kusa da Meeshan nasa. A hankali ya shaki kamshin perfume nata tare da lumshe idanuwansa, har cikin farfajiyar zuciyarsa ya ji wani irin sanyi na daban.
Calmly ya furta "Good evening momma".
Cool murmushi ta sakar mashi kafin ta ce "Ɗazun mun gaisa ai, yanzu dai ka Rimshar taka na kawo maka ita, amana na baka yarinyar nan Saif, kamar yanda na gaya maka ɗazun, yanzu ma zan sake gaya maka, ka kula da ita tamkar yanda kake kula da su Aseef, zamu yi magana dai da safe yanzu zan je na kwanta". Ta kai karshen maganar tare da miƙewa.
Good night ya yi mata yana mai kallonta, wucewa ta yi ta fice ta basu waje.
Tana fita ya fara latsa wayarsa, jim kaÉ—an ya kara wayar a kunne tare da mikewa tsaye, balcony ya sake komawa, Areef ya kira, bayan ya É—auka ne sai ya ce mashi da safe ya tabbatar bai manta ba ya kai Aseef wajen Sheikh Sultan, dama ya gaya mashi yau da safe, to sake tuna mashi ya yi, dan kada su mance, yana son Aseef ya sami lafiya sosai, yanzu ne ya gane menene matsalar ciwon na Aseef, tun da abu ne na tsafi, to babu maganinsa sai ayar Allah, shi ne yasa ya ce su kai shi wajen Sheikh Sultan ya yi koda sati É—aya ne, In Sha Allah za su sami sauki komai.
Bayan ya gama jaddadawa Areef É—in, sai ya yi mashi sallama tare da dawowa cikin bedroom É—in. Tana zaune tamkar yadda gwaggo ta ajiyeta, ta kudundune a cikin mayafi ta wani sunkuyar da kai. Kusa da ita ya zo ya zauna tare da zuba mata idanu.