← Book details Triplets Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 108 OF 168

Sashe 108

Triplets Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A tsorace ta fara girgiza mashi kai tana faÉ—in "Dan Allah Yah Areef ka yi hakuri, please kada ka shiga, wlh ina jin tsoro sosai".

Jin yadda ta yi maganar ya fahimci ta rigada ta tsorata, idan ya ce zai yi dis virgin nata a yanzu, to tabbas zai lalatawa kansa jin daÉ—in rayuwa ne, saboda yadda ta tsoratan nan idan ya shigeta to har abada a tsoronsa zata kasance, koda sun saba, a haka zata É—auke abin da zafi, so is better ya shammaceta ne bata yi zaton hakan ba, sai ya fi mashi a kan tasan da hakan. Wannan dalilin yasa ya hakura ya rabu da ita, ya cigaba da wasa da ita dan ya nemawa kansa salama da saukin abin da yake ji.

A ɓangaren Aafia kuwa, tana fitowa daga bedroom na gwaggo waje ta nufa, a harabar gidan ta ɗan tsaya shiru tana tunanin duniya.

Ta É—an jima a haka kafin ta nufin garden na gidan zuciyarta cike taf da matsananciyar damuwa na rashin Dr Nawid, yanzu ya tabbata da gaske ya mutu? Abin da take ta tunawa kenan, almost wata 5 kenan a yanzu basu a tare, ya tafi ya barta, kullum da tunaninsa take kwana take tashi, kullum sai ta kira Umminsa a waya, dan su gaisa, idan kuma suka gama wayar to sai ta sha kuka sosai, saboda tausayin Ummin, ita kaÉ—ai tasan irin son da Ummin take yi wa Dr, ita kaÉ—ai tasan shakuwar da take a tsakanin wannan uwa da É—anta, Allah mai iko mai yin yanda yaso.

Zuciyarta cike taf da tunani ta shiga cikin garden É—in, saman sofa ta zauna tare da buga uban tagumi wasu siraran hawaye suna bin kuncinta, har ga Allah tana tsananin son Dr ba kaÉ—an ba.

"Why are you crying".

Tamkar daga sama haka ta ji voice nasa. A hanzarce ta É—ago kanta dan ta ga wanenen.

Yana zaune a saman sofar dake fuskantar, hannunsa na rike da wayarsa, É—ayan hannunsa na rike da cup mai É—auke da coffee, jikinsa na sanye da sleeping dressing launin ash color mai haske, ya saki gashin kansa mai kama dana Areef sak, shi ma dai irin Areef É—in ne, baya datse kashin nasa, hakan tasa take da tsawo har gadon bayansa kamar mace, sai tashin daddaÉ—ar kamshi perfume nasa yake yi, ya fito shan iskansa abinsa.

ÆŠan kawar da kanta gefe guda ta yi tana faÉ—in "Nothing". Sai dai zuciyarta na a cike da mamakin abin da ta kalla É—in, duk da tana cikin yanayi mara daÉ—i hakan bai hana ta shiga wani irin ruÉ—ani da ganin face nasa ba, daurewa kawai ta yi ta kawar da kanta gefe dan kada ta cika kallonsa.

Tsareta da ash eyes É—in nan nasa irin na Areef ya yi, kamar ba zai sake ce mata komai ba, sai kuma ya sake cewa "Ba'a kuka babu dalili, just tell me the season kawai".

Miƙewa ta yi da nufin ta bar wajen, dan bata san cewa da mutun a garden ɗin ba, da ta sani sam ba zata shigo ba, saboda ita kwata kwata bata son ma ayi mata magana, bata son hayaniya, shiyasa ta baro ɗakin gwaggon ma, dan Areef ya shigo zasu yi ta yin hira, ita kuma bata son jin magana a kusa da ita.

"Where are you going?". Ya tambaya tare da miƙewa tsaye, wani dogo da shi, sai ta zama ƴar gajera a gabansa, dan ba karya Tga yana da tsawo sosai, da kaɗan Lion ya fishi tsawo, shi kuma ya fi su Areef tsawo.

Bata kula shi ba, dan bata jin kamar ma zata yi magana, nufar hanyar fita kawai ta yi.

Zura wayarsa a cikin aljikun wandon barcin jikin nasa ya yi tare da riko hannunta É—aya cikin sauri yana faÉ—in "Ina zaki je? I think kin fito shan iska ne?".

Juyowa ta yi da sauri saboda ta kwace hannunta da ya rike, sai dai kuma ganin face nasa yasa ta kasa yunkurin kwace hannun nata, saboda kowa dai yasan ya fuskan Tga take, a ɗaure tamau kamar ta Lion, ba shi da wasa, so ganin yadda face ɗin nasa take ne tasa ta ji wasu Mala'ikun nutsuwa sun diro mata a jikinta, tsit ta yi, jikinta har ya fara kerma, saboda tsantsar tsoron ganin face ɗin nasa da ta yi, ga shi kuma bata taɓa tunani a rayuwarta ko da sunan wasa zata gan shi ba.

Shi kuwa tsareta da idanu ya yi yana kallonta from head to toe, lokaci guda ya ji wani irin sauyi a tattare da shi, ga shi kuma kayan barci ne ita ma a jikinta.

Shiru ya yi, ya kasa ce mata ko uppan. Ganin yadda yake ta binta da kallo ne yasa ta yi ta maza ta zame hannunta daga cikin nashi, da gudu ta bar wajen. Binta da kallo ya yi har sai da ta fice daga wajen, ji ya yi tamkar ya bita ya kamota, amma kuma sai ya kasa, komawa saman sofarsa da ya tashi ya yi ya zauna, jingina kansa da jikin head na sofar ya yi tare da lumshe idanuwansa. Ita kuma tana barin wajen ɗakinsu ta koma, nan ta isko Akila tana wannan aikin dai da suka saba na waya da habibinta sahibinta. (Nace ba wai su ko rasa abin faɗawa junansu ma basu yi ne?😂 Kullum suna maƙale da waya, kai Aseef ɗan soyayya ne😂 jinin Dr William ɗin ne da gaske yake gudu a jikinsa🥳 dan Dr da gwaggo sun zuba love ba karya)

Kusa da ita ta kwanta zuciyarta na harbawa da karfi karfi, bata taɓa tunanin zata ga Tga a zahiri ba, idan baku manta ba tana kallonsa a news sosai, shi ne mutun na farko da ta fara so a rayuwarta kafin Dr Nawid, tasan cewa ba zata sami Tga ɗin ba ko a mafarki baiwar Allah shi ne yasa kawai ta fara son Dr Nawid ta cire Tga a ranta, yau sai ga shi sun yi ido huɗu da shi, tun da ta zauna a gidan bata taɓa cin karo da shi ba sai yau, time da ya taimaketa daga hannun Abbo tana a sume ne, bata sani ba, so yaune karonta na farko da ganinsa da ta yi a gidan, wani irin bugu kirjinta yake yi da sauri da sauri.

A ɓangaren Lion kuwa, yana isa *GOLD CROSS HOSPITAL (GCH)* fitowa ya yi daga cikin taxi ɗin tare da gayawa mai taxi ɗin yana zuwa. Kai tsaye cikin hospital ɗin ya nufa.

Abin ya yi matukar bashi mamaki yadda securityn wajen suka yi matuƙar girmama shi har da duka mashi kasa, sam basu hana shi shiga ba, sai ma ƙoƙarin raka shi ciki da suka yi, abin ya bashi mamaki sosai, shi dai yasan basu san shi ba, dan sau ɗaya ya taɓa zuwa kasar China yin wani aiki, kuma sam bai taɓa zuwa wannan hospital ɗin ba, to ya akayi suke girmama shi haka?. Abin da bai sani ba shi ne, a matsayin Sir Arvin suke kallonsa, duk da ya sanya face mask, sun san Sir Arvin ɗin sosai, shi ma ba mutun ne da ya cika yawo haka ba face mask ba, mafiya yawan lokuta da face mask zaka ganshi, hakan yasa suka bawa Lion ɗin hanya shi ma, dan kallon sir Arvin kawai suke yi a wajen.

Katafaren hospital ne wanda yake cike taf da manya manyan jiga jigan security's a ta ko'ina, shi ne hospital ta biyu a girma, kyau da tsada a kasar China, an narka maƙudan kuɗaɗe sosai wajen gina shi, idan aka ce maku shi ne hospital na biyu a gabaɗaya faɗin kasar China, ai kunsa ba asibiti bane na wasa, so tsayawa zayyana maku haɗuwarsa ma sam ba zai yiwu ba, dan baki ba zai iya zayyano haduwarsa ba, ga uban ma'aikata dayawa sosai, sai ɗan wane da wane ne suke iya kwanciya jinya a cikinsa, saboda tsada da kyau, kwararrun likitoci ta duniya ne ke aiki a cikinsa.

Kai tsaye kyakkywar elevatornsu Lion ya nufa, hawa na 10 ya nufa kai tsaye, da alama yasan address na in da zai je ɗin tun kafin ya tako kafarsa izuwa cikin kasar. Sai wani girmama shi suke yi, ko da ya isa hawa na gomar ya fito daga cikin elevator, duk wata likita da zai wuce sai ta duƙar da kai ta girmama shi, tun abin yana bashi mamaki har ya dai'na.

Kai tsaye office na babbar likita wato Dr Cherish ya nufa, yana taku cikin nuna isa da ƙasaita, sak yadda Sir Arvin yake tafiya, dan shi ma akwai shi da nuna isa da izza, ga ɗan banzan girman kai kamar me, yana kallon mutane kamar kashi, abin nasu a jini yake!! Babu in da Sir Arvin ya baro Lion, tamkar a waje guda suka yi rayuwa, tamkar a tare suka girma, suna kasashe daban daban, amma komai nasu kusan iri ɗaya ne, kama daga halayya ɗabi'u, komai dai, sak TRIPLETS sir Arvin yake!!.

Babu ko excuse ya danna ciki office na Dr Cherish abinsa, manya manyan security's uku dake tsaron kofar office É—in babu wanda ya yi yunkurin hana shi, saboda a tunaninsu sir Arvin ne, dan yana zuwa hospital É—in time to time, so sun san shi, basu isa su hana shi ganin Dr Cherish ba.

Tana hakimce a saman dankareriyar office chair ɗinta, A.c na bugata ta ko'ina, idanuwanta na sanye da wani shegen tsadadden farin glass, ga wani tsadadden laptop a gabanta saman table, daga gefe uban tulin files ne na majinyata, kyau iya kyau ta yi, kayan jikinta dukka masu uban tsada ne, watch dake ɗaure a hannunta sak irin watch dake ɗaure a hannun Lion ɗin, tamkar daga company guda suka saya, da yake yau ba watch nasu na TRIPLETS na sanya ba, wata ce daban, sai aka yi sa'a ta yi iri ɗaya sak dana Dr Cherish ɗin, ta dake tare da hakincewa a saman chair, ta ɗaura kafa ɗaya bisa ɗaya, ga wasu tsadaddun waya har biyu a gefenta, daga dukkan alamu tana cikin kwanciyar hankali na wuce misali. Kowa dai yasan yadda office na babban Dr yake da haɗuwa da tsantsar kyau, ba sai na tsaya ɓata lokacina wajen zayyano maku haɗuwarsaba.
Chapter 108 · 0% Book details