← Book details Triplets Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 168

Sashe 9

Triplets Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

To kawai ta amsa musu da shi, amma sam nasihar bai shiga kunnenta ba. Har ta koma bata haÉ—u da su Abba ba, kuma bata tambayi ina suke ba, a lokacin yes suna school basu dawo hutu ba, dan idan baku manta ba, dama hutu suka zo gida har wannan abin ya faru a tsakaninsu da daddyn Rimsha, to yanzu sun kowa makaranta.

Shi ma daddyn Anaya yana ta fama da school bai bi ta kan gwaggon ba, a takaice dai kowa yana fama da kansa, hakan ce tasa har ta koma ba su haÉ—u ba

GWAGGO

Tana dawowa daga hutu suka cigaba da gashi a ɓangaren soyayarsu ita da Dr William, sam bata hana shi ya juyata yanda yake so, ya yi wasa da ita, sai dai daga cibiyarta zuwa sama kawai ta bashi dama, ta hana shi kasan sam, dan tana mutuwar tsoron Dr Salman, saboda shi ma mutun ne mai tsananin zafin rai idan aka yi mishi ba daidai ba, to dan shi take rage wasu abubuwa, take kamewa.

Yanzu suna da almost shekara ɗaya da watanni a tare da Dr William, suna zuba soyayarsu, kullum tamkar ranar suka fara haɗuwa, a koda yaushe begen juna suke yi, wasa wasa har suka zama abin kwatance a cikin school ɗin nasu, kowa da su yake kwatance ta ɓangaren soyayya. Sai dai har lokacin fa Dr William dangerous boss ne, dan baya ɗaukar raini, ko kallon gwaggo mutun ya yi sai ya yi mashi hukunci, ba shi da sauki sam.

Yau babu school ta gama duk abin da zata yi a gida, ta yi wanka tana shirye cikin wando short zuwa gwiwa, da ƴar ƙaramar riga zuwa kugunta mai ƙaramin hannu. Tana kwance a saman bed nata tana aikin latsa waya, chatting suke yi da Dr William, dan idan ka ganta da waya a hannu, to da shi take magana, ko daddyn Rimsha da daddyn Anaya da suke ƴan lelenta ma, yanzu ta daina nemansu a waya, a baya sai ta kirasu fin awa uku suna hira, dan duk cikin ƴan uwan nata, ta fi kaunarsu sama da komai, dama idan baku manta ba, na gaya muku twins ɗin nan, Azharuddin da Nawazuddeen mugun shiga rai gare su, duk in da suka zauna, sai an kaunace su, aji ba'a son rabuwa da su, to ita ma Gwaggo haka ne, amma yanzu tana manne da Dr William, tama manta yaushe da rabon ta da ta kira gida, ko an kirata daga gidan kuma, sai ta ce musu tana karatun exams, ko dai tana yin wani abin, bata taɓa bawa kowa lokacinta idan ba karatu da kuma Dr William ba.

Sai dai abin jin daÉ—i a tarayyar tasu da Dr É—aya ne, wato duk wannan soyayya da suke zubawa, sam basu wasa da karatu, suna dagewa sosai, idan Dr William ya zo first, gwaggo ce second, idan ta zo first shi ne second, ma'ana dai duk in da É—aya ya saka kafa a karatu, to É—ayan ma yana biye da shi, kamar abin haÉ—in baki, amsoshinsu a Exams ma iri É—aya ne, dan tare suke karatu, wani lokaci a gidanta yake kwana, su kwana karatu. Rashin wasa da karatunsu shi ne nasarar da suka cinma a soyayyar tasu, kuma shi ne kawai soyayyar tasu bai sa sun yi patali da shi ba.

A ɓangaren Dr William ma, iyayensa har sun gaji da tambayar a kan sauyawar da ya yi, yanzu sun zuba mashi idanu ne kawai suna kallon shi, sun yi, sun yi, su bibiyi abin da yake yi, amma yaki basu dama, hakan tasa dole suka hakura suna binshi da idanu kawai.

STORYN

Ta tada kai da pillow a saman bed nata daga ita sai wannan short ɗin wandon nata da kuma ƴar riga, ta rungumo pillow a kirjinta tana aikin chatting da shi. Sai zubawa Dr nata shagwaɓa take yi a kan ita tana kewarsa, sai biye mata yake yi yana bata hakuri.

Tamkar daga sama ta ga ya turo kofa ya shigo, dan yana da key a yanzu. Hakan na nufin duk chatting da suke yin nan ashe yana kan hanyar zuwa, kawai yaki gaya mata ne.

Da gudu ta diro kasa daga saman bed ɗin ta nufe shi, buɗe mata hannu ya yi ta faɗa jikinsa tana dariya. Rungumeta sosai ya yi yana ɗan shafa bayanta. Laluɓar hannunta ya yi a in da ya sanya mata wani shegen diamond ring mai bala'in tsada, nan take hannun nata ya fara kyalli. Bai bari ta fara zuba mishi tsalle da murna ba kawai ya ɗauketa cancak sai saman bed ɗin, tamkar dama a kusa yake.

Romancing na juna suka fara yi kamar yanda suka saba, sai dai a yau dai Dr William ya zo har wuya, ya kasa jurewa ya danne sha'awarsa, dan yana tsananin sha'awarta over.

Hana shi ta yi a in da ta saka mashi kuka, dole ba dan ya so ba ya rabu da ita tare da barin jikinta ya koma gefe guda a saman bed É—in ya zauna, ya haÉ—a kai da gwiwa yana sauke numfashi a hankali hankali.

Miƙewa ta yi jiki ba kwari ta dawo kusa da shi. Hannu ta kai tare da ɗago kan nasa tana ambatar sunansa.

Kasa amsa mata ya yi, saboda mawuyacin halin da yake ciki. Rungume shi ta yi a kirjinta tana bashi hakuri tare da saka mishi kuka, sam ba zata iya jurar ganin shi a cikin tashin hankali da damuwa ba, kun san zuciyar masoya! Ba abin da ba zasu iya yi wa junansu ba, in dai sun mace a wannan soyayyar tasu! To ita dai soyayyarsa ta yi mata mummunar kamu, makauniyar soyayya take yi mishi.

Haka shi ma a nashi ɓangaren, makauniyar soyayya yake yi mata! Ba zai iya ganinta cikin damuwa ba, duk yanda ya kai ga son abu, in dai bata so, to ko zai mutu! Haka yake hakura, sai dai ya yi ta fama da azabar raɗaɗi a cikin zuciyarsa, amma ba shakka zai hakura.

Ganin tabbas ya shiga tsakanin damuwa sosai na wuce misali ne yasa ta ce to ya zo ya biya bukatar tasa kawai, tana magana tana kuka.

Da kyar ya iya ɗago kallonsa izuwa gareta, hannu ya kai ya fara goge mata hawaye, muryarsa na rawa ya fara magana. "Ni da gaske nake sonki my beauty, ba nason abin da zai ɓata maki rai, ki bari kawai na hakura kin ji ko? Yanzu dai ki gaya mani, me zan yi na sameki? Ya zan yi ki zama matata mallakina, sai nayi yanda nake so dake babu wani sha'amaki?".

Cike da murna ta ce "Aure, aure ne kawai zai sanya na zama mallakinka ba wani shamaki, hakan kuma ba zai taɓa yiwu ba har sai ka zama musulmi, ba zai yiwu na aureka kana krista ba!". Cikin sauri ya ce mata "Na yarda, na yarda zan zama musulmi, ni dai kawai ki zama mallaki na!".

Sosai ta rungume shi tana murna tamkar ba gobe. Ganin tana murna ne yasa shi ma ya rungumeta sosai yana manna mata kiss a lips nata.

Haka suka kasance tsawon mintuna 20, sannan ya ce ta shirya bari suje gidansu sai ya gayawa mummynsa da daddynsa abin da ya yankewa kansa, a lokacin kuma TAG yana koyan tafiya.

Hakika ta yi tsananin murna, zata mallaki Dr ta. Cikin hanzari ta miƙe tare da faɗawa cikin toilet. Wanka ta yi cikin hanzari, yana zaune yana jiranta, amma shi kaɗai yasan halin da yake ciki na sha'awarta. A gabansa ta shafa Lotions nata kamar ko yaushe, sannan ta wuce zuwa dressing room.

Yau da yake ya ce gidan iyayensa za su je, sai ta mutunta su ta hanyar yin complete dressing mai kyau, wandon jeans ta sanya a ciki, tare da wani T-shirt da ya saya musu iri É—aya da shi.

Bayan ta gama sai ta sanya after dress baka a saman kayan, dan ta É—an suturta jikinta, still dai kanta babu É—ankwali ta fito.

Cike da tsantsar so da kauna tare da kulawa ya fara yabon irin kyan da ta yi, murmushi ta yi kafin ta taho ta faɗa jikinsa. Yana ƙoƙarin fara kissing nata, ta dakatar da shi ta hanyar sanya hannu ta rufe mishi baki.

"Haba my Dr, wai kai baka gajiya da shan lips na ne?".

Lumshe shanyayyun idanuwansa da suka sauya launi ya yi, cikin sanyin murya ya bata amsa da cewa "My beauty, ya za'ayi na gaji da shan lips naki? Ai ba zan taɓa gajiya ba, ni dai yanzu Please ki bani ko kaɗan ne, kin ji ko my wife?".

Harara ta wurga mishi kafin ta ce "Ai ba'a É—aura auren ba ko?".

Nisawa ya yi yana mai faÉ—in "To ai an kusa, kin ma tuna mini, tashi muje wajensu mummy da wuri, daga nan sai mu wuce a É—aura aure ko?".

Zata yi magana ya sanya mata yatsa a saman lips nata yana faÉ—in ta tashi su tafi da wuri. Ba musu ta tashi suka fice daga gidan.

A motar nasu ma, basu hakura ba, sai da suka É—an yi romancing junansu kafin ta kwantar da kanta a saman kafaÉ—arsa, shi kuma ya kunna motar suka bar gidan.

(Yanzu kun fara ganin daga in da TRIPLETS suka yi gadon nasu jarabar ko? Da uwa da uba dukka ba sauki😂 mu je dai zuwa.)

Yau dai Gwaggo ta zuba kauyanci na ganin gidansu Dr, bata taɓa tunanin daga wannan aljannar duniya ya fito ba, tana tunani dai irin normal masu kuɗin, ɗan dai'dai ɗin nan, bata san mahaukatan kuɗi karesu ba.

Sake baki ta yi kawai tana ta kallon gidan abinta. Sai da ya ja hannunta suka nufi ciki, lefter suka hau zuwa hawa na uku, dan ya san confirm su mummynsa suna wajen, dan sun fi yawan zama a wajen. Ita dai sai mamakin gidan take yi, dan gida ne irin high rise building ɗin nan, ga wani haɗaɗɗen lefter mai matuƙar kyau, abin ba'a cewa komai, dan ya wuce tunanin mai tunani, idan na ce zan tsaya zayyana muku gidan Jacob Roshan ba ƙaramin aiki bane, dan kuwa sai mu kare book nan kaf a kansa kawai, dan fa ya haɗa komai, babu abin more rayuwa da ɗan adam zai buƙata babu a cikin gidan.
Chapter 9 · 0% Book details