← Book details Triplets Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 168

Sashe 59

Triplets Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana É—ago idanu suka yi ido huÉ—u da Lion da yake zaune a saman kujerar mulkin Queen É—in. A dubu É—ari ya É—ago kan nasa da kyau, dan ya kalli shin abin da yake gani gaskiya ce.

Ba shakka Lion ɗin ne yake zaune kamar yanda ya gani tun farko, gabaɗaya jikinsa duk jini, da alama ya sha gwagwarmaya ba kaɗan ba, ya jingina kansa da jikin head na sofar, sai sauke numfashi yake yi a hankali hankali, yana wani irin nishi, alamar ya gaji over, daga hannunsa, kirjinsa, fuskarsa wajen kumatu, dukka jini ne ya ɓata shi, babu riga a jikinsa, ainahin kakkarfa kuma kyakkyawan surar jikinsa na cikakkun jaruman maza a bayyane, sai binsu da blue eyes nasa kawai yake yi abinsa.

A dubu Aseef ɗin ya miƙe tsaye yana kallonsa da kyau, a hankali ya fara bin cikin fadar da kallo. Can ya hango ƴar Queen ɗin a ɗaure da sarka, Lion ya yi mata ɗaurin goro, ita kuma Queen ɗin tana kwance flat a tsakiyar fadar, tamkar gawa, ko motsawa bata yi, da alama rai ya yi halinsa ne, ga kuma hannunta ɗaya babu shi, da alama Lion ya sare mata hannu ɗaya ne, alamu sun nuna ba karamar faɗa suka gwabza a tsakaninsu ba, dan kuwa sun ruguje komai na cikin fadar, babu abin da ya rage mai amfani a cikin fadar.

A hanzarce ya nufi Lion É—in, tsabar a galabaice Lion É—in yake ya kasa tambayarsa meya kawo shi nan? Ya aka yi kuma ya zo? Ya sha mamakin ganinsa sosai, sai dai ba zai iya yin wani magana ba.

Bai kai ga karisawa wajen Lion ɗin ba, sai ga Areef ya fito daga wata ɗaki dake a cikin fadar, hannunsa na ruke da wasu kyallaye farare guda biyu. Wajen Lion ɗin ya kariso yana faɗin "Saif bari na ɗaure maka hannun nan naka dake zubar da jini da wannan tsummar, sai na ɗaukeka mu fita daga wajen nan, idan ba haka ba, duk zamu mutu, kasan dai gabaɗaya gidan nan rugujewa zai yi ko? Tun da dama mafiya yawan ɓangarorin gidan ba ginasu aka yi ba, da tsafi aka yi su, to yanzu mai tsafin ma ta mutu, kaga suma dole ne su mutu, dan haka ka yi sauri muje". Ya kai karshen maganar yana karisowa kusa da Lion ɗin sosai.

ÆŠaga mashi hannu Lion É—in ya yi, alamar baya da bukatar a É—aure mashi hannun nasa, ya bar mashi abinsa. Bai yi ja in ja da shi ba, sai ya bar mashi, dan yasan ba zai ce a bar mashi hannunsa jininsa na zuba haka kawai a banza ba.

Da kyar Lion ɗin ya yunkura ya miƙe, wani irin jiri yake kallo, yau tsawon kwanaki bai ci komai ba, sai gwabza yaki yake yi da mukarraban Queen har ya iso gareta, shi ne yasa ya galabaita sosai, kuma ko da ya iso gareta, ba ƙaramin yaki suka yi da ita ba, ta wahala shi ma ya wahala kafin ya samu ya kasheta.

Na san zaku so jin ya akayi hakan ta faru, to ku saurara. Shi Lion already ko da ya shaki kamshin turaren da Queen ɗin ta shaka masu a gidanta, to shi bai suma ba, saboda askar na safe da ya yi, askar na safe idan ka nutsu ka yi shi, Ubangiji ya yi alkawarin Mala'iku ne zasu kula da kai, babu abin cutarwa da zai sameka har izuwa maraice, idan ka yi na maraice, to Mala'ikun zasu sake kulawa da kai har izuwa gobe da asuba, wannan faɗar Allah da manzonsa ne, kuma ya yi karatun Alkur'ani mai girma sosai kafin ya baro gida, sannan ya yi adduo'i ba kaɗan ba, dan yanda yaga Rimsha ta rikice, sai ya ɗauki abin serious, shi kuma Areef da yake bai san ya Daular Mutuwa take ba, tun da Rimsha ba matarsa bace, bai san halinta ba, sai bai ɗauki abin serious ba, bai yi wani addu'a ba, shi dai ya saɓi jaka kawai, ya lodi kaya kamar wanda zai je honey moon da matarsa, to a takaice dai shi Lion ko da ya shaki kamshin turaren, bata yi mashi komai ba, ya kwanta ne shiru kawai tamkar ya suma, dan yana son shigowa cikin Daular Mutuwar ta kowace hali, a tunanin Queen, ita ce ta yi wasa da kwakwalwarsu, ta kuma kafa masu tarko, ta yi nasara suka faɗa, bata san cewa ita ta faɗa tarkon ba, ba ita ta kamasu kamar yadda take tunani ba, Lion ne ya kamata a cikin tarkon nata da ta kafa masu da kanta, wasa da tunaninta sosai ya buga, bata taɓa tunanin hakan zai faru ba.

Lokacin da ta rufe shi a ɗakin duhu, ta kuma daure shi, duk yana jinsu, yana a cikin hayyacinsa, ya yi masu abin da zaki yake yi idan zai farauci abinci ne, kwanciyar ɗaukar rai ya yi masu, abin da basu taɓa zata ba. Waɗan nan sarkokin da suka ɗaure shi dai, already kun san sarkokin tsafi ne, dan haka yana karanta masu Alqur'ani mai girma, duk suka ruguje, suka zama gari, sai dai ya sha bakar wahala sosai kafin ya fita daga cikin ɗakin duhun.

Yana fita kuma bai nemi kowa ba, sai ita Queen ɗin, sam bai nemi ina su Areef suke ba, dan yasan idan ya kamata to tamkar ya gano dukkan in da ƴan uwansa suke ne, saɓanin shi Areef da ya tashi sai ya fara neman Lion ɗin, da yake kowa da irin kaifin kwakwalwarsa da tunaninsa, kuma babba kam ko da minti ɗaya ya fika, to ko yaya babba ne, ya fika, shi ne yasa Lion ɗin ya fisu hangen nesa, dan ya fisu a komai.

Yasha bakar wahala sosai a wajen neman Queen É—in, ya yi faÉ—a da mukarrabanta sosai. Tsawon kwanaki yana nemanta, a hanyarsa na neman nata ne ya kashe su barbushi, ya yi nasarar kashesu ne da taimakon Allah.

Haka ya yi ta fama har ya gano in da shegiyar fadar tata take.

Time da ya shigo fadar, babu kowa a ciki sai ita da ƴarta, duk ta tura mukarrabanta domin su kamo mata su Areef, bata san shi ma Lion ɗin ya fito ba, da taimakon sunan Allah ya ɓacewa idanuwan tsafinta, hakan tasa bata ga fitowarsa ba.

Tana ganinsa ta miƙe, da tsafinta ta yi ƙoƙarin damko wuyarsa ta janyo shi, dan ta hallaka shi.

Already kafin ya shigo cikin fadar tata da bismillah É—auke a bakinsa ya shigo, dan haka sai ta kasa kama shi É—in, ta yi ta faman gwadawa, amma ina takasa. Shi kuma yana tsaye gam, kamar wani jarumin sadaukin yaki.

Ganin ta kasa saka hannunta a jikinsa ne yasa ta fara ƙoƙarin tura mashi kayan tsafe tsafenta, dan su illatar da shi, to a nan ne aka samu wannan fashe fashen kaya da suka rinƙa yi a cikin fadar, sai da ta fasa komai nata da kanta.

Da ƴarta ta ga haka, sai ta yi ƙoƙarin tayata yakin, shi kuma Lion ya ɗauko wani wuka dake a wajen ajiye wukakensu, wuka ce mai tsananin kaifin gaske, ya yi amfani da ita ya sarewa Queen ɗin hannunta na dama ba tare da ta ankara ba, ya cire mata hannun tun daga sama wajen shoulder ta.

Yana datse hannun nata ya kai hannunsa ya cire zobben dake a jikin babbar yatsarta, wannan zobbe ba komai bane face karfin tsafinta, shi ne karfinta da komai nata, idan babu shi, to ita ba koman komai bace, already dama yasan da irin wannan zobbe, duk wasu cikakkun matsafa suna amfani da wannan zobbe, duk matsafan da basu da shi, to da sauransu, har yanzu basu kai shegu ba, akwai wata kungiyar matsafa da ya taɓa tarwatsawa a New York, suma haka ya datsewa shugabansu hannu, ya ɗauki wannan zobbe ya jefata a cikin wuta, daga nan alkadarin tsafin ta karye.

To ita ma Queen haka ya yi mata, yana cire zobben ya zura a aljihunsa, da ta ga haka, sai ta fara ƙoƙarin yin faɗar hannu da shi da hannu ɗaya, ga bakar azaba tana ji a hannun nata, amma saboda karfin hali, sai bata karaya ba, ta fara faɗa da shi, dan ta kwaci zobben.

Bugu ɗaya ya yi mata a bayan kunne ta wajen wuyarta, daga haka bai kara na biyu ba rai ya yi halinsa, dama kunsan ta tsufa, ta kai shekaru 45 zuwa 50 a duniya, to bugu ɗaya mai lafiya Lion ya yi mata, shikenan ta ce ga duniyarku. Already dama shi Lion kun sani, zaratan maza ma ya suka kare da shi? Da duka ɗaya yake kai mutun in da zai yi danasani har ƙarshen rayuwarsa, bare kuma ita Queen da take mace, macen ma tsohuwa, ai dukansa ɗaya ma ya yi mata yawa.

Ita kuma Æ´arta Lion É—in ya kamata ya É—aureta, a cewarsa, bai yi tunanin irin hukuncin da yakamata ya yi mata bama tukun nan.

Yana kashe Queen É—in kuma wasu zaratan maza suka shigo cikin fadar, matasan igbo ne, kyawawa da su majiya karfi, su goma sha biyu cif.
Ganin abin da yake faruwa ne yasa suka fara ƙoƙarin kashe Lion ɗin, to da sune ya yi faɗar nan da suka ji mashi ciwo, jikinsa duk jini, sun ji mashi ciwon ne kuma ta hanyar dogayen faratunan yatsun hannunsu da suke da shi, kun san soft skin nasa kuma, tana da laushi tamkar fatar jariri, ya ji hutu ya ƙoshi, to shi ne idan suka yagushe shi sai wajen ta yi jini, hakan yasa suka sami kalaba ta ji mashi ciwo sosai a jiki. A garin dukansu kuma ya yanke da wuka sosai a hannu, shi ne wajen da Areef ya ce zai ɗaure mashi yaki yarda. Wannan shi ne a takaice abin da ya faru, abin da yasa gine ginen wajen kuma suke ruguzowa da kansu, saboda already da tsafi aka yi su, to kuma tsafin dake a cikin gidan a halin yanzu ya karye, komai ya lalace, dole gidan ta ruguje.......... To kun ji yadda aka yi, har kullum PRINCESS TEEMA ce taku ta amana mai abin ban mamaki🤙.

STORY.
Chapter 59 · 0% Book details