← Book details Triplets Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 128 OF 168

Sashe 128

Triplets Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mummyn Rimsha ce ta ce "Au kinma taɓa ji kenan? Akila shin kun san me kuke yi kuwa? Yanzu dai kinga halin da kika jefa shi a ciki, ba tare kuma da ya yi maki laifin komai ba, kin ɗauki alhakinsa, kinsan kalar tsinuwar Mala'iku da zaki samu kuwa? Ace ma baki san yana so ko baya so ba, meyasa da zaki je yin lallen baki tambaye shi yana so ko baya so ba? Kin san da cewa komai zaki yi a yanzu sai idan yana so ko baki sani ba? Ki sani fa in dai mijinki bai yi maki laifin komai ba kika azabtar da shi, wlh babu in da zaki je sai Allah ya kamaki, koda ma ace ya yi maki wani laifin bai kamata ki rama da sharri ba, ki kyale shi ai Allah yana ganinku, kada ki yarda kiyi abu da gangan dan ki kuntatawa wani ma bare mijinki, kowa ya biki da sharri ki bishi da alkhairi, sai kiga Allah ya kareki daga wannan sharri da yake nufarki da shi, duk lokacin da kika yi abu da gangan dan ki cutar da wani, ki sani Mala'ikun Allah ta'ala suna tsine maki albarka, tsinuwar mutun ɗan adam ma kawai idan aka barki da shi ya zaki kare bare kuma tsinuwar Mala'iku? Common bakin mutane yana lalata mutun bare shinuwa bare kuma na Mala'iku, tun wuri na gaya maku ku shiga hankalinku ku san menene miji a gareku, ba abin wasa bane shi ɗin, yana da kyau ku kula sosai".

Da yake Rimsha da gangan ta yi ƙunshin nata, sai ta ji kamar da ita mum take yi, duk sai ta damu sosai, jikinta duk sai ya yi sanin, yanzu ace ita ma Lion idan ya ganta zai yi ta zuba amai kamar yadda Aseef ya yi ai ba kamar cutar da shi ta yi ba, meya yi mata da zata cutar da shi haka? Koda ma ace ya yi mata wani laifin meyasa zata cutar da shi ta abin da tasan baya so? Meyasa ba zata tsaya a iya fushin da ta yi da shi ɗin kawai ba? Meya yi mata har haka da ya cancanci hukuncin cutarwa daga gareta?. Sosai ta rinƙa tunani tare da danasanin yin wannan ƙunshi da ta yi, sai dai kuma bata jan ye fushin da take yi da shi ɗin ba, ta ce dai fushi kam ba zata fasa ba tun da ya nuna baya sonta...

Ƙasa da kai sosai Akilar ta yi tana sauraron nasihar ta mum, ya ratsata sosai da sosai, duk sai ta ji babu daɗi, ta ji ta matuƙar damu sosai.

Ita kuwa mum sosai ta yi masu nasiha mai ratsa jiki, sannan ta miƙe ta nufi nata part ɗin wanda yake a kusa dana gwaggon.

Tana shiga ta isko daddyn Rimsha yana tsaye a wajen mirror.

"Kin tafi wajen Æ´aÆ´anki kin manta da ni ko? Kefa ko kewata ma baki yi ba ko?". Ya faÉ—a yana juyo da kallonsa a kanta.

A gefen bed ta zauna tana mai bashi hakuri. Toilet ya nufa yana faɗa mata ba zai hakura ba, bari ya fito wanka zai ɗauki mataki...........🙄🙃

A ɓangaren Aseef kuwa, ya ci bakar wahala kafin ya samu ya dawo dai'dai, har wani firgicewa fuskarsa ta yi, bawan Allah ba laifinsa bane, a jininsu abin yake, gado aka ce ba karambani ba.

Shi ma dai Dr William ya ci bakar wahala kafin ya samu ya dawo dai'dai, bedroom nasa Areef ya wuce da shi, suka bar masu aiki da aikin gyaran parlourn, kowa ya wuce part nasa, dan su yi wanka su huta zuwa dare.

After some hours.

Lion da sir Arvin zaune suke a saman bed É—in na Lion da yake a cikin bedroom nasa, ita kuma Pinky tana a tare da Dr William, daga shi sai sir Arvin suka saba a gidan, sai kuma Lion tana É—an yarda da shi, albarkacin kamar da yake yi da sir Arvin yasa take yarda da shi idan zai É—auketa ko ya bata abu, tana yarda.

Sai hira suka yi gwanin ban sha'awa, da yake dukkansu ba sarakan yawan magana bane, sai ya zamana hiran nasu sama sama suke yinsa.

Areef ne ya shigo cikin bedroom ɗin bakinsa ɗauke da sallama, kayan barci masu bala'in kyau irin na jikinsu Lion ɗin ne a jikinsa, sai dai nasa ash color ne, Lion da sir Arvin kuma nasu white colors ne, da alama shi ma sir Arvin sarkin son farin abu ne, dan ko kayan Lion zai sanya farare kal kal yake ɗaukowa, son farin abin nan a jininsu yake. (Nima a jinina yake, fav color na kenan a duniya🥱 kusan komai idan zan saya in dai akwai fari, to shi zan ɗauka, kuma kun shaida😂)

Saman bed É—in ya haye yana faÉ—in "Our Lion what's wrong with you? And meyasa baku fito mun je dining room dan yin dinner ba?". Ya yi maganar yana mai karewa Lion É—in kallo, nazari face nasa yake yi, da yake shi ya san É—an uwan nasa fiye da sir Arvin, shiyasa yana shigowa ya fahimci akwai abin da yake damunsa, dan damuwar ta fito karara a saman face nasa, shi kuma sir Arvin sam bai gane ba, saboda dama bai san halinsu ba, da saura tukun nan.

"Areef Meesha fushi take yi da ni fa, taki zuwa in da nake, kuma she knew that i hate this thing that she did on her legs and hands, amma ta je ta yi har da wuyarta, because of tana fushi da ni". Ya faÉ—a yana mai É—auko wayarsa dake a saman bedside drawer.

Da yake shi Areef yasan menene matsalar da take a tsakaninsa da Rimshar, sai ya ce "Ok yanzu dai muje muyi dinner, daga baya zamu yi maganar Rimshar, dama shiyasa nace maka idan ka sauka a kasar China ka kirata a waya, saboda mata sai ana lallaɓasu".

"Yau kowa a bedroom nasa zai yi dinner, saboda rashin jituwa da yake a tsakanin momma da dad, bana son mu haÉ—u a dining room ba tare da na gayawa mum abin da yake faruwa ba, idan ba haka ba za'a samu matsala, dan dad ba zai ganta ya yi shiru ba, ita kuma ba zata saurare shi ba, so the solution kawai kowa ya yi dinner a bedroom nasa, zuwa gobe da safe ko anjima zan sameta na gaya mata abin da yake faruwa". Cewar Lion kenan.

Baki ɗauke da sallama Aseef ya shigo cikin ɗakin, duk ya yi wani iri da shi bawan Allah, wannan aman da ya rinƙa yi ta galabaitar da shi sosai, har ya ɗan yi rama, sai dara daran idanuwan nan nasa kamar ball.

A saman bed É—in shi ma ya haye yana faÉ—in "Ni Areef ka matsa bari na yi barci".

Fuska a É—auke da mamaki sir Arvin ya ce "What? Ina Æ´ar aljannarka take da zaka zo nan kace zaka yi barci? Ina ka barota?".

Areef ne ya capki zancen da cewa "Shi ne nima abin da zan tambaya kenan, ina ka baro Heartbeat da zaka zo nan ka ce mana bari ka kwanta, Heartbeat taka da kake ta kukan ta dawo ne fa! Ko ka manta ne?". Ya kai karshen maganar yana dariya, dan yasan me matsalar, da gangan ya yi mashi wannan tambayar.

Shi dai Lion ko a jikinsa, ƙoƙarin mikewa ma yake yi ya je wajen gwaggo, dan ya kalli Meesharsa, yana kewarta sosai, yana son ganin face nata ko zai sami saukin abin da yake ji.

"Ni Areef ku rabu dani, su fa mata idan ka biye masu wlh sai ka mutu bama kasan ka mutu É—in ba, sai ka ji ka kabari zaka gane".

Dariya kamar Areef zai mutu, shi dai yana burin daman yaga Aseef da Akila sun yi faɗa kamar yanda Lion da Rimsha suka yi a yanzu, dama sun ishesa, ji yake kamar duk ya shakesu, bini bini suna manne da matan nasu, to yau dai Allah ya kamasu dukkansu, matan nasu yau ji da sabon iskanci suke yi, ita kam Rimsha ai sai dua'i, wai fushi ma take da Lion, ita kuwa Akila ƙunshi, dole Aseef ya daka yaji sai ƙunshin nan ta goge............😂

Damko Areef ɗin Lion ya yi tare da haɗe hannayensa dukka biyu, dan Areef yana kule su har wuya, suna fama da zafi zai kara masu wani ta hanyar yi masu dariya, a maimaƙon ya tayasu shawo kan matsalarsu, amma saboda neman tsokana sai ya kama dariya, yau kam ba zasu barshi ba.

Da sauri Aseef ya sauka kasa daga saman bed ɗin ya je ya ɗauko igiya dan tsabar mugunta, so yake yi Lion ya ɗaure Areef ɗin, ɗaurin goro su jibge shi, saboda Areef ɗin yana kara masu zafi a kan zafi na abin da suke ji, idan ba iskanci ba yazo ya tasasu a gaba yana masu tambayoyi, idan sun gaya mashi ga yadda aka yi, sai ya zauna ya yi ta dariya har yana shakewa tare da yin tari tsabar mugunta, wlh dole yau su yi maganinsa. (Rifat yau Allah ya kama Areef ɗinki, kuma ba mai kwatarsa😂 dama tara mashi suke yi tun tuni, sai yau dubunsa ya cika)

Karɓar igiyar Lion ɗin ya yi tare da fara ƙoƙarin ɗaure hannayen Areef ɗin. Da sauri sir Arvin ya ce "A'a meyayi maku zaku ci zalinsa?."

Kin kula shi Lion É—in ya yi, Aseef sai faman dukan Areef É—in da pillow yake yi yana faÉ—in "Kai ma Allah yau ba zaka je wajen matarka ba, a nan zamu zauna kamar masu takaba a tare".

"Wannan ne kuma baku isa ba" Cewar sir Arvin, ya yi maganar tare da kai hannunsa zai kwaci igiyar da Lion ɗin yake ƙoƙarin ɗaure hannayen Areef ɗin da shi. Da sauri Aseef ya yi ƙoƙarin hana shi, amma ina tuni ya kwace igiyar yana faɗin "Areef jeka wajen matarka hai, shi Saif waye ya ce ya yi wa tasa Queen ɗin laifi? Kai kuma Aseef me kayi mata nema da har ta yi fushi da kai ɗin ma?".
Chapter 128 · 0% Book details