Sashe 163
Triplets Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Cikin jirgin ruwansu ya koma da ita, dama kunsan a cikin jirgin ruwa da akwai abubuwan kama kifi, rigar ruwa, da dai sauran abubuwa, so shi abubuwan kamun kifi ya je ya É—auko, sannan suka fito.
Ganin shi da abin kamun kifi a hannu yasa Mark ya ce. "Sir bari na kama maka".
Da yake ta gabansu Mark É—in suka bi, shi ne yasa Mark É—in ya gani.
Ba tare da ya tsaya daga tafiyar da yake yi ba ya ce. "No ka barshi kawai, baby ya ce kifin da daddynsa ya kama zai ci, so bari".
Yana magana yana tafiya, ita kuma ta wani kwanta mashi a saman bayansa tana aikin murÉ—a mashi dark black curly hairnsa ta bayan wuya.
Bakin ruwan ya koma ya fara aikin kamun kifi dan dole, idan ba haka ba babynsa dai ba zai ci komai ba.
(Wlh Rimsha ta san ta kan tsiya😂 yanzu His Excellence da kansa ta saka kamun kifi🤔 kai wannan yarinya tana yin son ranta, dole na zuga Lion ya kara aure, ya auro baturiya😒🥱)
Da kyar ya iya kama mata manya manyan kifi guda biyu, sannan ya ce ta sauka mashi a jiki ga shi ya kama mata bari ya kaiwa Mark ya je cikin jirgi ya gyara ya gasa mata.
Nan fa ta saka mashi kuka tana faÉ—in ita fa ba gashin su gas take so ba, da itace za'a hura wuta a gasa mata, haka babynta yake son ci.
"Meesha meyasa kike son saka mun ciwon kai ne? Itace kuma?".
Kuka ta sake saka mashi tana faÉ—in. "To ni Noorish laifi nane? Ba babynka bane yake son ci? Ni fa bana cin kifi, babynka ne nan yake son ci".
"To sauka bari su Mark su gasa maki da itacen".
Sake make mashi kafaɗa ta yi tana faɗin. "Baby gashin daddynsa yake son ci, ni dai kai nake so ka gasa mun, Allah idan ba kai ba na ƙoshi".
Tana magana tana kuka, har da hawayenta bibbiyu dan rigima.
Bashi da zaɓin da ya wuce ya gasa mata ɗin, domin kuwa yana tsananin son cikin nan nata, ga cikin watansa ɗaya kenan a duniya, amma sai rigima kala kala ta iya, kuma cikin yazo mata da laulayi tare da zaɓar abinci ne, yasan idan bai gasa mata ba to ba lallai ta ci abinci ba, abin da cikin yake so shi kawai take ci. Babbar magana.
Lion akwai shi da wani ra'ayi fa shi ma, ganin cewa dukka family suna ta burin Rimsha ta samu ciki, kowa so yake yaga ɗansa, shi ne fa sai ya ɓoye zancen ciki, yaki bari kowa ya sani, daga ita sai shi, ko gwaggo bai sanarwa ba, wai kada su sakawa matarsa ido, kada su damesu ita da babynsa, shi ne nan ya ɓoye menene yake damunta, ya ki bari gwaggon ta gwadata, ya ki bari kowa ya sani, kunga daga karshe ma ya ɗaukota sun bar gidan abinsa.
Ni kam PRINCESS FATEEMA TEEMA ina ganin ra'ayi kala kala a wajen Lion.
Sanya su Mark ya yi suka kawo mashi itacuwa busassu, sannan suka hura mashi wuta ta bakin ruwan, dan dole yau ya koyi gasa kifi, amma sai da Mark ya nuna mashi yadda zai haÉ—a kifin da kayan miya, da yake suna da komai a cikin jirgin
Kujera Mark ya kawo mashi ya zauna kusa da wutar yana gasawa. Ba dan tsananin tsoronsa da su Mark ɗin suke yi ba, da yau babu abin da zai hana basu yi mashi video ba, dan ko a mafarki basu taɓa tunanin zasu gansa a kusa da gas na girki bama bare kuma itace, sam basu taɓa yin gigin irin wannan tunani ba, sai ga shi yau saboda babynsa ya zauna a gaban itace mai ci da wuta yana gasa kifi, gaskiya mace duniya ce, duk wanda ya ce maka mace bata isa ba, to wlh bai shiga hannun macen da ta kai mace wadda ake cewa mace ba mun rako mata ba, kun san akwai mace wadda ta amsa sunan mace, sannan kuma akwai mun rako mata, sune zaku gansu sai a hankali, amma cikakkiyar hamshakiyar mace, ai ko namiji baya so sai ta juya shi son ranta.
A takaice dai yau ga His Excellence of United States yana aikin gasa kifi a bakin ruwa........😂
Kai mata duniya ne, dole haka ya yi wannan aiki ba dan ya so ba, sai dan yana son farincikin matar tasa da kuma abin da yake cikinta, a can gefe guda kuma Sir Safwan ya ɗake a saman kujerarsa cikin office nasa dake white house, ya haye kujera yana ta aiki tamkar Lion ɗin ne, babu wanda ya iya gane cewa ba Lion ɗin bane, kowa a matsayin Lion yake ɗaukarsa, ba su san ga shugaban kasarsu mai mulkarsu a nan bakin ruwa shi ma ana mulkarsa ba, ya mulki al'umma, ya juya su son ransa, shi ma kuma under 15 years girl ta mulkesa ta juyasa son ranta, wannan abin ni PRINCESS FATEEMA ZAHRA yana mugun yi mun daɗi..................😂(Team Lion kada wanda ta ji haushina kun ji na gaya maku😂 ato daɗi nake ji yadda Rimsha take murza kanbun mulkinta😂 ya gasa mana kifi muci😂 dama ni ina da Maltina mai sanyi 🥱)
Haka ya gasa wannan kifi tsab, sannan ya bar wajen tare da komawa ta gefe guda yana turɓune fuska. A saman laps nasa Rimshar ta zo ta zauna tana faɗin ya bata kifin a baki to.
Idan baku manta ba tun a book 1 Aseef baya cin namar kifi, hakan yasa dukka TRIPLETS basu damu da shi ba, ya zamana suma basu so, so har yanzu Lion wari kifi take yi mashi, bai iya ci ba, baya son karninta kuma. Amma a haka ya daure ya rinƙa bawa Rimshar a baki, dan ya samu ta ci abinci, yasan ba komai take ci ba sai abin da ta zaɓa.
Shi dai Mark izuwa yanzu ya gama sadaukarwa da cewa babu abin da mace ba zata sanya namiji ba, mace zata iya juya namiji son ranta idan ta san menene ciwon kanta.
A takaice sun É—auki tsawon lokaci a wajen wannan bakin ruwan, sun sha soyayya ba karya, Rimsha ta zuba sarautarta son ranta, abin gwanin birgewa, sai da lokacin da zasu tafi Nigeria ya yi ne gwaggo ta kira shi a waya a kan ya dawo zasu je Nigeria.
Okey ya amsa mata da shi, amma sai ana gobe zasu tafi sannan ya dawo gidan.
Wani irin kyau Rimshar ta kara, jikinta ya samu sauki sosai, dan ta samu hutu, ga kayan marmari da take ci sosai, sai ta kara fresh over. Sai dai kuma har yanzu babu wanda ya iya gane cewa tana da ciki, sam basu gane ba, dan cikin bai fito ba, kwata kwata 3 months ne cikin, domin two months suka yi a bakin ruwan kafin su dawo.
Sun shirya zuwa Nigeria gagarumin shiri, dan sun tsara idan suka je zasu yi ziyara sosai. Sai dai fa ko da suka je Nigeriar basu sauka a gidan Lion na Kaduna ba, a villa suka sauka, a fadar shugaban kasa, saboda yanzu in dai ba tafiyar sirri zasu yi ba, to babu in da zasu je su zauna a karamin waje, sun wuce wannan level É—in, ku kanku kunsan matsayi ta ci uban na da.
Daddyn Rimsha bai zo Nigeria ba shi, shi suka tarawa aikin a matsayinsa na vice president, suka tara mashi aiki suka tafi suka bar bawan Allah, mummy ta so zuwa, amma ina ba hali, haka ta hakura ya zauna tare da mijinta.
Sun sha yawo a Nigeria sosai da sosai, sun yi ziyara wajen Æ´an uwa da abokan arziki, har Bauchi sai da suka je wajen Æ´an uwan Dr Salman, sannan suka je Katsina wajen su Maman Sadiq. Jehan ce ta sanya Areef ya yi wa Maman Sadiq da Sadiq É—in gagarumin kyauta, katafaren dankareriyar gida na alfarma ya saya masu a cikin gari, ya ce su bar kauyen nan, sannan ya biyawa Sadiq da Yusuf school fees na tsawon su kammala karatun a wani katafaren school na Æ´aÆ´an manya, ya bawa Sadiq jari mai tsoka da zai iya isar sa ya rike ahali guda, shi ma baban Sadiq É—in ya bashi jarin sosai, da farko Jehan ta so hana shi ya bawa baban Sadiq É—in, ta ce ai munafikin uba ne mugu, sai da Rimsha ta roketa, sannan ne ta yi shiru ta hakura Areef É—in ya bashi 5m.
DaÉ—i kamar baban Sadiq ba zai mutu ba, nan take ya hau zuba masu godiya tare da godewa Maman Sadiq da ta rike su Jehan mutanen kirki. Ni kuwa nace É—an banza, sai yanzu kasan da cewa su mutanen kirki ne ba, da yake anji maiko, kai amma wannan hali naka dai tirr da shi.
Lion kuma Rimsha ta ce to ya biya masu kuɗi su je Makka su yi ibada, Okey ya amsa mata tare da cika mata abin da take so, su maman Sadiq za'a keta hazo zuwa ƙasa mai tsarki.
Bayan sun kammala zasu bar garin Katsina su koma Abuja ne Aafia ta ce da Uncle T zata je wajen Ummin Dr Nawid a gidan sarki kenan.
Ba musu suka ɗunguma zuwa can, dan ziyara suka zo, sai dai fa Lion da Rimsha basu bisu ba, sun kama hanyarsu sun bar garin, Rimsha ta tsayar mashi da rigimar sai dai ya kaita garin Ilorin, dan tana son ta je taga Kausar, dama kuma idan baku manta ba ya taɓa yi mata alkawarin zai kaita can, dan haka sai ya ɗauketa suka nufi can.
Su Aafia kuma sun je su duba Ummin Dr Nawid tana nan lafiya, a nan ne suka sami labarin Abbo ya dawo bai mutu ba, sai dai ya haukace yana yawo bola bola, ga ciwon kafa da yake fama da shi, kafar ta ruɓe har tana tsutsa, an nemi magani har an gaji babu sauƙi, hakan tasa aka raba auren Ummi da Abbon, da da farko ma an ɗaure shi ne, daga baya da aka ga wannan fa ba samun lafiya zai yi ba, sai aka sake shi ya shiga duniya ɗan banza.