← Book details Triplets Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 168

Sashe 67

Triplets Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*KINDADE KINA NEMAN ABUN DA ZAI SANYAKI QIBA,QIBA MEKYAU KIYI DIMIMI DUK INDA KIKA SHIGA BABU RAINI KINYI TA SIYA KINA ASARAR KUDINKI🤔
ALBISHIRINKI NAZO MIKI DA ABUN DA ZAKISHA BA TARE DA KINYI ASARAR KIDINKI BA 💃 Yana da matiƙar kyau sosai ko'ina naki zai chiko ki xama abar sha'awa duk mai buƙata ta nemeni ta wannan number 09067614054, kada ki bari ayi babu ke, kayanmu tested and trusted ne, guarantee ne*.

*KINDADE KINA NEMAN ABUNDA ZAI SANYA KISAMU XAMAN LFY TARE DA KWANCHIYAR HANKALI? TO BABYN HABIBI KIXO UMMU AFFAN TAXO MIKI DA SHAHARARRUN KUMA INGANTATTUN MAGUNGUNAN MATA, KAMA TUNDAGA KAN HUMRA, TURAREN WUTA,
INFECTION KILLER,
COLACCA,
SAI KAYAN GYARA PAGE.
KACA KACA.
YALLAGWADA.
JIGIDA.
RUWA RUWA.
BANI BANI.
WOMEN JELL BATA BATA.
DAFIN KAXA.
TANTABARA.
XABUWA.
CICCIƁI.
AND EXCLUSIVE, XUMA TASTED AND TRUSTED INA FARIN CHIKIN SANAR DA KU MUN FARA RAMADAN PROMO GAME BUQATA XA A IYA TUNTUBA NA TA WANNAN NUMBER
09067614054 JIGAWA STATE MUNA AIKAWA KO'INA CIKIN AMINCI DA YARDAR ALLAH,
BABYN HABIBI KARKIMANTA DA KAYANMU FIRST CLASS NE, DAGA KANSA AN RUFE KOFA, YANA DA INGANCI NA WUCE TUNANINKI*.

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥

https://whatsapp.com/channel/0029VaMOfZZI7BeKXPU9gK2S

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥

TSARAWA DA RUBUTAWA......✍️

❤️FATEEMA ZAHRA MUSA (💫PRINCESS TEEMA💋)

*Domin samun damar karanta littafin nan daga farko har karshe zaki iya nemana ta wannan number 08161390581*

E18

Date: 28/4/2024

*Page na yau ban samu na yi editing nasa yanda ya kamata ba, saboda rashin chaji, so zaku iya samun typing errors, amin afuwa.*

Nisawa Lion É—in ya yi ba tare da ya ce komai ba, dan yana tattauna maganganun ne ma tukunnan.

"Haƙiƙa babu wasa a wannan al'amari, tun kuna cikin cikinta, tun cikinta yana da wata biyar aduniya ta bayar da ɗa ɗaya daga cikinku, wannan dalilin yasa da aka haifeku muka ɗauki guda ɗayan, wannan zance haka take, kuma duk in da zaka je ka zo hakan ce! Babu makawa kuma babu tantama a cikinta, muna da shaidu a kan hakan, na san dama zaka zo, zaka zo garemu Romeo, saboda tun da ka fara girma muka fahimci ka ci sunanka da WILLIAM ya sanya maka wato Lion, so our Lion already we know that you're special! Hakan yasa muka ajiye maka tarin hujjoji da zaka gansu a aikace, sai dai bamu yi tunanin zaka zo garemu da wuri haka ba, bamu yi tunanin zaka gane mu da wuri haka ba, anywhere mu bamu cutar da ku ba, ku tuhumi mahaifiyarku da kuma Josephine, sune suka yi komai!!".

Haƙiƙa a maganar kakan nasa babu karya a cikinsu, tabbas duk abinda ya faɗa gaskiya ce, gwaggo da bakinta tun cikinta yana da wata biyar, tun bata ma san me zata haifaba, ta bada guda ɗaya, to su kuma basu mantuwa, shiyasa da ta haihu suka ɗauki ɗayan, sai dai da akwai abin da ya saɓa a cikin maganar, wanda kuma dole a wajen Josephine da Cherish ne kawai za'a san ainahin menene wannan!. Wannan shi ne cakwakiya, Lion dai yana tsaka mai matuƙa wuya wanda fitarta sai Allah ya ƙaddara.

Nan ma dai shiru ya yi mashi bai yi magana ba. Gabaɗaya kakan nasa ya shiga ruɗu, saboda yin shiru Lion ba alkhairi bane, sun san shi tun yana ƙarami, idan ya yi shiru, to wani abin yake ƙullawa a cikin ransa, so haka har ya girma, shirunsa musiface a wajen marasa gaskiya masu cin amana da tauye haƙƙin ƴan adam.

Ganin yanda ya yi shirun ba ƙaramar ɗaga mashi hankali ya yi ba, dan haka sai ya sake cewa "Ni zan je office ana jirana".

Ya É—auki tsawon lokacin da a kallah zai kai 10mins kafin ya sake nisawa tare da É—ago idanuwansa ya sauke a kan kakan nasa, cikin tsananin nutsuwa ya fara magana. "Ni ban tambayeka waye ya baku cikon TRIPLETS da kuka É—auka ba, ni kawai na ce maka ne ina yake? Me kuka yi da shi? And lastly where's Anderson? Wanda ya baku wannan duk daga baya ne, zamu zo kan zance, for now dai amsa this two questions that i asked you! Where is my TRIPLETS? And where is Anderson?".

"Anderson is already died, you know that, so i don't know what do you want us to tell you again kuma".

Jinjina kai ya yi tare da faɗin "Okey Anderson is already died, wow this is so nice, agreed, amsa me da remaining question, where's my brother?". Ya kai karshen maganar yana miƙewa tsaye.

"Romeo your brother has gone since that time".

Sake jinjina mashi kai ya yi kafin nan ya fara takawa a hankali ya nufe shi, dama yana tsaye ne ta wajen mirror, ba halin yin baya baya, bashi da zaɓin da ya wuce ya tsaya kawai har Lion ɗin ya iso gare shi.

A hankali ya iso in da yake, hannu ya ɗaga cikin nutsuwa ya shafi lallausa kuma jajir ɗin kumatun kakan nasa, cikin sanyin murya ya ce "Okey let me try something, let me send you to the place that you send my brother!". Ya kai karshen maganar yana gangaro da hannunsa izuwa wuyar kakan nasa. Da karfi sosai ya shake ɗan tsohon, ransa a tsananin ɓace over, amma saboda ya gane suna neman hassala shi ne, sai ya ki bari ɓacin ran nasa ta yi tasiri, sai ya danne kawai.

Cikin kwanciyar hankali kakan nasa ya sanya hannu a saman hannun Lion ɗin, tamkar wanda ya kama hannun ƴar baby haka ya ɓanɓaro hannun Lion ɗin daga jikin wuyarsa tare kuma da murɗe ta baya da karfi, nan take yanayin kakan nasa ya fara sauyawa, cikin tsawa da wata iriyar murya wadda da ka ji ta kasan ba nasa bane, dan murya ce ta irin kartin mazan nan, da ita ya dakawa Lion ɗin tsawa, sam Muryar bata da daɗin ji, tamkar an tada injin jiƙa lalatatce.

Ba shakka abin mamaki ne canzawar kaka nasa da kuma irin karfin da yake da shi a matsayinsa na dattijo, sai dai kuma ko kaɗan Lion ɗin bai yi mamakin hakan ba, dan ya san fin hakan ma zasu aikata. Kasancewar yana da ciwo a hannun, sai murɗe mashi hannun da kakan nasa ya yi ta yi mashi muguwar zafi, hanan tasa ya kai ɗayar hannunsa yana ƙoƙarin sake shako wuyar kakan nasa, dan tsananin zafi da yake ji.

Sam kakan nasa bai bari hannunsa ya sake taɓa jikinsa ba, sai ya yi ƙoƙarin haɗe hannayen nasa dukka biyu ya ruke da hannu ɗaya. Da Lion ɗin ya fahimci wannan karfi fa ba na kakansa bane, dan haka yana da kyau su yi fito na fito, idan ba haka ba, idan ya zuba masu idanu to zasu yi mashi illa mai girma. Tuna hakan ne yasa bai bari kakan nasa ya kama ɗayar hannun nasa, sai ya yi ƙoƙarin kaucewa, hakan ya bawa kakan haushi ba kaɗan ba, sai ya yi wani irin kurma kururuwa kamar kukan giwa a dawa, nan take ya canza halittarsa izuwa wata halitta mai matuƙar girman, tana kama da ɓauna, wato saniyar dawa, ga wasu kawo guda biyu a kai.

Ko kaÉ—an Lion bai ji tsoro ba, sai ma nishaÉ—i da abin ya bashi, shi da ya yi faÉ—a da su barbushi jibga jibga mutane masu kama da samudawa, dan haka sai ya gyara tsayuwa tare da dakewa, shi hakan ma ta fi mashi, ya fi jin daÉ—i su yi fito na fito da su, ya ci ubansu Roshan babu sirki, ya kuma sanyasu su duka su gaya mashi gaskiya!!.

Gadan gadan wannan halitta da kakan nasa ya koma ya tunkarosa. Yana zuwa Lion É—in ya furta kalmar bismillahi tare da fara kokawa da shi. Sai dai ina ya riga da ya ambaci sunan Allah, babu wata tsafi da zata yi amfani a wajen, haka yasa suna fara yin faÉ—a kakan nasa ya koma ainahin halittarsa, sarai Lion É—in yasan da hakan, amma sai bai kyale shi ba, ya jibge shi da kyau da kyau, wani irin wawan mari ya kai mashi a kumatunsa wanda har sai da ya sanya shi ganin wani haske ya gilma mashi ta cikin idanuwansa, bai barshi ya dawo dai'dai ba ya kwashe kafafunsa, sai ga É—an tsoho ya zube kasa wargajam.

Guntun tsaki Lion É—in ya ja, ya so ace da matashin mai jini a jika zasu gwabza, dan ya ci ubansa, ya sauke mashi duk wata haushi da yake ji a kansa, ya jibgi banza, amma sai ya zamana da tsoho ne ba matashi ba, wannan tsohon idan ma ya ce zai dake shi, ai sai dai ya karisa gawar da ba tasa ba, dan wannan idan ya yi mashi duka É—aya lafiyayyiya ba makawa sai dai a É—auki gawarsa.

Wayar makekiyar Tv dake a É—akin Lion É—in ya tsinko, da karfi ya ja har sai da Tv ta faÉ—o kasa ta tarwatse, ko a jikinsa ya zo ya É—aure kakan nasa É—aurin goro, ta baya ya É—aure hannayen nasa, sannan ya É—aga shi cancak, bai sauke shi a ko'ina ba sai a saman tsakiyar bed nasa.

Ya sauke shi tare da zama a saman bedside drawer, kasa ya É—an yi da kansa yana É—an murza Æ´atsun hannunsa, ya É—an É—auki lokaci da a kallah zasu kai 10mins kafin ya É—ago kai tare da kai kallonsa izuwa kan É—an tsohon, a takaice ya ce "Are you ready to tell me the truth or not?".

Murya a tsarke, cike da tsoro ya ce "Zan faɗa maka komai". Yana magana yana zare ash eyes nasa, haƙiƙa ya tsorata na ganin tsafinsa taki yin aiki a kan Lion ɗin, ya ji matuƙar rashin daɗi, sam ba haka ya so ba, ya so ne ya jibgi Lion ɗin har sai ya yi laushi, sannan ya ɗaure shi kansa a kasa kafafuwansa a sama, sai dai bai san cewa ta Allah ba tasa ba, bai san cewa shi Lion ya rigada ya ruke Allah hannu bibbiyu ba, wanda kuma ya ruke Allah, tabbas babu shi babu taɓewa, wanda ya ce Allah shi ne komai nasa, to babu shakka Allah ba zai taɓa bashi kunya ba, Allah zai kula da lamuransa ba zai taɓa bashi kunya ba, ya Allah ka iya mana da iyawarka!.

Jinjina mashi kai Lion É—in ya yi tare da yi mashi alamar ya yi maganarsa yana jinsa.
Chapter 67 · 0% Book details