Sashe 10
Triplets Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai yanzu gwaggo ta sake yarda cewa so gudan jini ne, yanzu idan ban da so me Dr William zai yi da ita? Irin wannan duniyar da suke ciki, ga kuÉ—i, kyau, isa da takama, abin ba'a magana.
Tamkar yanda Dr ya faÉ—a na cewa iyayensa suna hawa na uku, a can ya samesu, suna zaune a palonsu tare da Uncle Herry, Josephine da TGA, sai zuba hira suke yi. Jacob Roshan yana shan green tea, ita kuma mummynsu tana faman cin wasu korayen ganyayyaki masu karawa jiki lafiya da jini, ga wani makeken Tv dake gefe guda ta gabas maso tsakiya yana magana.
Tun da suka shigo palon gwaggo take bin ko'ina da kallo, ta kasa nutsuwa waje guda, gani take yi tamkar Dr William zai cutar da ita ne a irin wannan gida, ta tsorata da ganin wannan uban daular more rayuwar.
Shi kuwa, riko hannunta ya yi suka nufi saman wata luntsumemiyar sofa mai matuƙar laushi da kyau, fara kal tamkar yanzu aka cirota daga kwalinta. Komai na cikin palon sai kyalli yake yi, yana ɗaukar idanu, gal gal da su, nera ta yi kuka ta kuma zauna da kyau a wajen.
Ko da suka shigo palon, sam iyayen Dr basu nuna mata komai ba, sai ma karramata da suka yi, da fara'a mummynsu ta tarbeta, shi ma daddyn nasu, fuska ba yabo ba fallasa ya tarbesu, dan gwaggo dai baturiya ce ba bakar fata ba, sak Naurat take!. Josephine ta fi kowa murnar ganin gwaggo, saboda dama yayan nata yana yawan korinta a kusa da shi, a tunaninta tun da yanzu ya fara son mata, zai dai'na abin da yake yi mata. Su Uncle Herry duk sun yi tsantsar murna ba kaÉ—an ba.
Sam Dr William bai ɓata lokacin wajen sanar da iyayensa wace ce gwaggo a wajensa ba. A nan ne tsananin farincikinsu ya kara bayyana, sun ji daɗi sosai da ɗansu ya kawo macen da zai aura, nan take mum nasu ta ce gwaggo ta dawo kusa da ita ta zauna, tamkar za su cinyeta saboda so, sai tambayarta suke yi me take so ci a kawo mata?!.
Kan ka ce me an cike mata gabanta da lodin kayan cima kala kala, masu aiki sun fara zarya a cikin palon, suna kai kawo na kayan cima. Yau dai Gwaggo taga abin mamaki, abincin ma a baki suke ƙoƙarin tura mata, saboda so, kuma duk aikin mum ce, sai wani ririta take yi.
Ta É—ebo abinci a cikin spoon zata kaiwa gwaggon a baki kenan, cikin hanzari Dr ya ce "Mum kada ki bata, dan ita bata cin irin abincin mu, ba komai take ci ba!".
ÆŠan zaro blue eyes nata mum É—in ta yi kafin ta ce "Why?". Ko a jikinsa ya amsa mata da cewa "Be cause she is a Muslim, so ba komai take ci ba, akwai abin da ya zamana haramun a cikin addininsu su ci, haka idan muka je restaurant cin abinci ma, sai ta faÉ—i abin da za'a bata, bata cin irin nawa!". BABBAR MAGANA.
A tsananin razane mum da dad É—in dukka suka mike tsaye, tamkar sun ga wani abin tsoro. Nan take kuma suka canza fuska tamkar ba su ne suke dariya a yanzu ba, sun wani uban É—aure fuska tamkar hadari, shi daddy ma har da wani zaro idanu. Cikin tsawa mum É—in ta ce "To musulmar zaka aura ne?!".
Sosai gwaggo ta yi wani mahaukacin razana!, Ta tsorata na ganin canjin da suka yi lokaci guda, tamkar ba su ba.
Shi kuwa Dr, ko a jikinsa ya amsa musu da "Yeah mum, ita nake so, ita zan aura, kuma yanzu ma da muka zo, na zo ne na gaya muku zan musulta nima, be cause we're prepared to get a marriage together, so shi ne abin da ya kawo ni!". TASHIN SENSE!!!
Wani uban tsawa dad ya daka musu wanda ya sanya gwaggon mikewa da sauri. Shi ma Dr William mikewa ya yi tare da yi mata alama da hannunsa a kan ta zo. Da sauri ta tafi izuwa wajensa, jikinta sai kerma yake yi. Dr kuwa ko a jikinsa ya rumgumeta yana É—an shafa bayanta, alamar ta kwantar da hankalinta.
Mum ce ta katsesu da cewa ya sake wannan yarinya ko kuma wlh yanzu ransa ya ɓaci. A zahirin gaskiya tun da yake da iyayensa basu taɓa ɗaga mashi murya a magana bama bare har a kai ga tsawa, lalaɓa shi suke yi sosai kullum. Hakan tasa ya ji wlh yana kaunar shiga musulci, dan shi duk abin da ba'a so, to fa shi yake so. (Idan baku manta ba a baya dama Dr William ɗin ya faɗa, wannan kalma ta abin da ba'a so, shi Lion yake so, a wajensa ya gaji kalma, to hakan take!.)
"Mum why are you shouting like that? You already know that idan na ce zan yi abu fa, to sai na yi, so don't west your time to say something about that issue, be cause confirm sai na musulta, dan ina son A'isha, she is my life, my everything!!". BABBAR MAGANA!! YAU AKE YINTA!!
"William are you out of your sense?!" Cewar mum ɗin. Dad ne ya karɓi maganar da cewa "In dai har ka ce zaka musulta, to confirm zaka bar mani gidana! Kuma sai dai ka mance da mu a matsayin iyaye, ka nemi wasu!!".
A takaice ya ce "That's good daddy, i chose A'isha and Muslim religion, wai daddy ka manta abin da ba'a so shi nake so ne? To ko dan nunawa da kuka yi baku so, confirm sai na yi!!".
Ya kai karshen maganar tare da juyawa tare da gwaggon a jikinsa. "William don't go anywhere, come back and say sorry to your dad!". Cewar mum, ta yi maganar tamkar zata fashe da kuka, idanuwanta duk sun cika taf da kwallah, Allah ya gani a duk cikin Æ´aÆ´anta, ta fi son Dr William, kuma ta san halinsa sosai, tun da ya ce sai ya musulunta, to fa babu chanji sai ya yi ne, sai dai duk abin da zai faru ya faru. TIRKA SHI.
A ɓangaren shi ma daddyn, kirjinsa sai dukan uku uku yake yi, dan shi ma, ya fi son Dr William sama da kowa a cikin ƴaƴansa, ba zai iya rabuwa da shi ba, ba kuma zai iya ganinsa a cikin addinin musulunci ba, dan su irin kristocin nan ne masu tsauri a kan addininsu, ba za su iya yafe ɗansu ya musulunta ba! Gara su kashe shi da su barshi ya musulta.
Hakan tasa daddyn zuciya ta ɗebe shi ya yi yunkurin kashe gwaggo da wukar da mum take yanka ganyayyakin da take ci. Cikin ɓacin rai Dr William ya tare daddyn nasa, tare da kwace wukar, har ya ɗaga a zuciye zai cakawa daddyn nasu a ciki, gwaggon ta rike shi tana kuka tare da girgiza mashi kai a kan kada ya yi hakan, kada ya kashe daddynsa.
Wurgi ya yi da wukar tare da rungumeta suka nufi waje. Dafe saitin zuciyarsa dad ɗin ya yi, kan su yi wani yunkuri ya zube kasa sumamme, abin ya taɓa mishi zuciya over, kuma dama dole ya taɓa shi over, ace ɗa mafi soyuwa a gareka, ka fifita shi fiye da kowa, ka shagwaɓa shi, rana tsaka wata mace ta shiga tsakaninku, har yaron ya yi yunkurin kashe ka, saboda mace, ba dan macen da yake son ɗin ta rike shi ba, da tsab zai iya kashe ka saboda zuciya ta ɗebe shi, dole wannan abin ya taɓasu over, dan zuciyar iyaye ya wuci tunanin mutun, in ma musulmi ko Kristen, duk wanda aka ce shi ya haifi mutun, to wlh ya wuce abin wasa, zai so ɗan nan ne fiye da tunanin mai tunani, koda kuwa ba zai nunawa kowa ba, ba zai taɓa yuwuwa ace iyayen da suka haifeka ba su sonka ba, sai dai idan ba zasu nuna maka son ba, amma zuciyar iyaye daban yake da kowa, suna iya sadaukar da duk abin da suka mallaka saboda ƴaƴansu, ba'a banza da Allah ya ce bayan Allah da Manzonsa sai iyaye ne kawai za'ayi wa biyayya a shiga aljanna kai tsaye ba, so iyaye sun wuci wasa koma ya ya suke!! Fatanmu dai Allah Ubangijin ya bamu ikon bin umarninsu tare da kyautata musu!!.
Ko kaÉ—an Dr William bai juyo ba, duk da yana jin zafin rabuwarsa da iyayen nasa, amma hakan bai hana shi dagewa dan cika burkinsa ba. Ficewa ya yi daga gidan abinsa.
Shi kuma dad su Uncle Herry suka yi ƙoƙari tare da taimakon ma'aikatan gidan, suka nufi hospital da shi.
Ko awa ɗaya bai yi a asibiti ba rai ya yi halinsa, dama already yana da hawan jini, sara ce ta zo a kan gaɓa. Mutuwarsa ta sanya mum nasu shiga tsananin tashin hankali, wanda har sai da ya jawo mata bugawar zuciya, ita ma ba'afi awa uku da mutuwar dad ba rai ya yi halinsa, ta bi daddyn.
Hakika familyn Roshan su ga tashin hankali a wannan rana, harta yayyun daddyn da suke rike da mulki, a wannan rana sun sha kuka, an yi musu hotuna da videos suna kuka da hawayensu na rashin kaninsu da matarsa tamkar wasu yara ba adadi.
Sam Uncle Herry da Josephine sun ki gayawa jama'a gaskiyar abin da ya kashe Jacob da mum nasu, sun ɓoye ne saboda suna tsananin son Dr William, kuma suma sun ji suna son su musulta, sun san cewa idan har suka sanar da jama'a gaskiya, to ba shakka yayan daddy da yake kan mulki zai sanya a kashe Dr William, dan su basu yafe jininsu, ko yaya ka taɓosu sai sun rama, koda kuwa a cikinsu kake.