← Book details Triplets Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 101 OF 168

Sashe 101

Triplets Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tsadaddiyar wayarsa da take a gefensa ne ta fara ringing, har ta katse bai ɗaga ba, kira ta biyu ta sake shigowa, ita ma har ta katse bai ɗaga ba, sai a na uku ne ya ɗauki kiran. Kara wayar ya yi a kunnensa ba tare da ya ce uppan ba, sai a lokacin ne kuma ya ɗago kansa tare da ajiye jaridar hannun nasa mai ɗauke da hoton Lion, sannan ya koma ya jingina da jikin chair ɗin yana sauraron abin da ake faɗa mashi a cikin wayar. Haƙiƙa babu wata banbanci dake a tsakanin fuskarsa da ta Lion, duk da idanuwansa suna a cikin black glass, baka iya gane wani irin kalace da su, amma hakan ba zai hana ka ga tsantsar kamanninsa da Lion ba.

Ya ɗan jima yana sauraron abin da ake faɗa ta cikin wayar ba tare da ya amsa ba, sai ya ɗago hannu yana duba time a jikin dankareriyar watch dake a hannunsa. Calmly ya furta "Am coming". Da zazzaƙar muryarsa mai muguwar kama da ta Lion, Iya abin da ya furta kenan tare da katse kiran. Nisawa ya yi tare da ɗan ɗago da kansa da nufin ya miƙe tsaye. Turo kofar office ɗin Secretariyarsa ta yi tare da shigowa tana faɗin "Sir ARVIN you have some visitors from West Building, Zhongnanhai".

Shiru ya yi mata bai amsa ba, ganin haka yasa ta juya ta fita, da alama ta yi mashi farinsani, hakan yasa ta san fassarar shirunsa.

Wanene ARVIN. ARVIN dai shi ne Defence minister na kasar China bakiɗaya, wato ministar tsaro ta kasa, duk wani mai kaki a karkashinsa yake, idan ana maganar duk wani mai kaki kuma mai muƙami, to fa gaɓaɗaya ake magana, duk wasu jiga jigan Generals na sojoji, ƴan'sanda da dai duk wasu masu muƙami, harta General of the army's a karkashinsa yake, shi ne Minister tsaro gabaɗaya, mutun ne mai matuƙar girman kai, jiji da kai, isa, izza da kuma taƙama, mahaifinsa shi ne Senate president na ƙasar, yana da kanne biyu, namiji ɗaya sai mace ɗaya, namijin yana da shekaru 27 a halin yanzu, ita kuma macen tana da 13 to 14 years old, mutun ne miskili, ga kuma ɗan banzan farinjini kamar ba gobe, jama'a kowa son shi yake yi, yana tare da mahaifinsa da kuma mahaifiyarsa, bashi da aure, ko budurwa bashi da ita, saboda shi gani yake yi ɓata lokaci ne ma ya tsaya sauraton mata, haka zalika kanin nasa ma bashi da mata. Wannan shi ne ɗan takaitaccen tarihin Sir ARVIN.

Miƙewa ya yi tsaye, dogo da shi tamkar Lion ne yake tsaye a wajen. Hannu ya kai ya rufe laptop dake a gabansa, kafin ya ɗauki tsadaddun wayoyinsa har biyu ya nufi waje cikin takun nuna isa, tsantsar lafiya da kuma izza.

Yana fitowa gabaɗaya kananan ma'aikatan dake wajen suka fara duƙawa suna yi mashi mubaya'a, kun san halin Chinawa da iya duƙawa kasa su gaishe da mutum, ko sannu zasu cewa mutun sai sun ɗan dukar da kansu kasa, so yana fitowa haka suka fara duka mashi cikin girma da girmamawa, ko kaɗan bai ɗago idanu ya kalli ko mutun ɗaya ba, dama na gaya maku yana da bala'in girman kai.

Sai da ya fito harabar wajen ne wasu jiga jigan bodyguards masu ji da lafiya da karfi, su goma sha biyu ciff suka take mashi baya har zuwa wajen wani haÉ—aÉ—É—en parking space dake a wajen, gabakiÉ—aya bodyguards É—in Chinawa ne, jajir da su kamar tsada, ga su da faÉ—i, basu da tsawo sosai, kamar yanda kuka sani ne, bodyguards É—in suna sanye cikin black suit kamar yanda kowasu bodyguards suke sanyawa.

A hanzarce wani ƙosasshe kuma lafiyayyen bodyguard ya kai hannu ya buɗe mashi wata dankareriyar mota kirar *ROLLS-ROYCE* Fara tas da ita tana wani ɗaukar ido, sai ka rantse da Allah yanzu aka fito da ita daga laida, wasu luntsuma luntsumar sofas ne a cikin wannan mota masu matuƙar laushi, kun san idan aka ce luntsuma luntsuma, ana nufin masu lumewa da mutun saboda laushi da tsantsar kyau, wani irin azababben daddaɗar kamshin car perfume ne yake tashi daga cikinta, ga wani irin sanyi A.c dake tasowa, kai tsayawa zayyana maku haɗuwar wannan mota ma ɓata lokaci ne, dan ya wuce misali.

Cikin nutsuwa tamkar Lion haka ya shiga cikin motar ya zauna, zuciyarsa cike taf da tunanin wanene Lion? Meyasa suke muguwar kama haka? Why Lion ya yi kama ba da iya shi kawai ba, har da kanwarsa Pinky? Shi Lion da yake Americans, shi kuma da yake Chinese me haÉ—insu? Ga ita ma Pinky da take nan. Abin ya dame shi sosai, haka bodyguards nasa suka shiga ciki sauran tsala tsalan motocinsa guda shidda dake a wajen.

A jere kai guda motocin suka tashi gwanin birgewa, kai daga gani kasan babba ne zai bar wajen, dan motocin nasu ma kawai abin kallo ne, a haka suka nufi tampatsetsen gate na ma'aikatar. Tun kafin su iso jiga jigan masu gadi sun wangale masu gate É—in, da gudun gaske suka danna hancin motocin waje, motar Æ´an'sanda mai lode da jam'ai har guda uku ne suka rufa masu baya tare da sakin jiniya tamkar filin yaki zasu tafi.

Kai tsaye..............

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️❤️🔥

*KINDADE KINA NEMAN ABUN DA ZAI SANYAKI QIBA,QIBA MEKYAU KIYI DIMIMI DUK INDA KIKA SHIGA BABU RAINI KINYI TA SIYA KINA ASARAR KUDINKI🤔
ALBISHIRINKI NAZO MIKI DA ABUN DA ZAKISHA BA TARE DA KINYI ASARAR KIDINKI BA 💃 Yana da matiƙar kyau sosai ko'ina naki zai chiko ki xama abar sha'awa duk mai buƙata ta nemeni ta wannan number 09067614054, kada ki bari ayi babu ke, kayanmu tested and trusted ne, guarantee ne*.

*KINDADE KINA NEMAN ABUNDA ZAI SANYA KISAMU XAMAN LFY TARE DA KWANCHIYAR HANKALI? TO BABYN HABIBI KIXO UMMU AFFAN TAXO MIKI DA SHAHARARRUN KUMA INGANTATTUN MAGUNGUNAN MATA, KAMA TUNDAGA KAN HUMRA, TURAREN WUTA,
INFECTION KILLER,
COLACCA,
SAI KAYAN GYARA PAGE.
KACA KACA.
YALLAGWADA.
JIGIDA.
RUWA RUWA.
BANI BANI.
WOMEN JELL BATA BATA.
DAFIN KAXA.
TANTABARA.
XABUWA.
CICCIƁI.
AND EXCLUSIVE, XUMA TASTED AND TRUSTED INA FARIN CHIKIN SANAR DA KU MUN FARA RAMADAN PROMO GAME BUQATA XA A IYA TUNTUBA NA TA WANNAN NUMBER
09067614054 JIGAWA STATE MUNA AIKAWA KO'INA CIKIN AMINCI DA YARDAR ALLAH,
BABYN HABIBI KARKIMANTA DA KAYANMU FIRST CLASS NE, DAGA KANSA AN RUFE KOFA, YANA DA INGANCI NA WUCE TUNANINKI*.

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥

https://whatsapp.com/channel/0029VaMOfZZI7BeKXPU9gK2S

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥

TSARAWA DA RUBUTAWA......✍️

❤️FATEEMA ZAHRA MUSA (💫PRINCESS TEEMA💋)

*Domin samun damar karanta littafin nan daga farko har karshe zaki iya nemana ta wannan number 08161390581*

Date: 14/5/2024

E31

Kai tsaye Zhongguncu motocin suka nufa, katafaren unguwa ce wadda ta ji manya manyan tsara tsaran gine gine na zamani har ta ƙoshi, ko'ina ka ɗaga idanu ka kallah sai ka ji baka son kawar da kanka daga wannan wajen, tsaruwa iya tsurwa, haɗuwa iya haɗuwa, shunfuɗaɗɗiyar titin da ta keta cikin unguwar ma kawai ya isa mutun ya saki baki daga safe har yamma yana kalle kalle kayan alatun da aka shunfuɗawa wannan titi, abubuwa ne kala kala, wajen tafiyar mutun a kafa daban, wajen tafiyar keke daban, wajen tafiyar mota daban, haka titin nan yake, gwanin birgewa, baki ma ya yi kaɗan ya zayyano yadda haɗuwar titin take, sai dai ku kawata a ranku.

Tun da motocin Sir Arvin suka hau saman wannan titi babu wata mota da ta gifta har suka nufi wata dankareriyar gini na alfarma, wadda ake yi wa yaƙabi na karshen burin ɗan adam, kunsan ɗan adam da shegen buri over, to duk wani burinka idan ka sanya kafarka a cikin irin wannan gida fa shikenan angama, sai ka ji tamkar bama a duniya kake ba, bene ne hawa biyar, gini ne na tiles da glass, abin dai ba'a magana, gate ɗin gidan ma kawai abin kallo ne.

Tun kafin jerin gwanon motocin su iso an wangale masu tampatsetsen gate É—in, da alama gate É—in da na'ura take amfani, dan babu gateman a wajen sam.

Kai tsaye suka danna hancin motocin nasu cikin gidan a jere, wani tampatsetsen parking space suka nufa, ya haɗu ya gaji da haɗuwa, wasu shegun tsadaddun motoci ne maƙare a parking space ɗin, tamkar companyn kera motoci suka shiga, kowani mota ka ɗaga idanu ka kallah sai ka sake kallah, saboda tsabar kyau.

A jere waje guda motocin nasu suka dakata, tamkar abin haÉ—in baki haka suka kashe motocin gwanin birgewa, tare da fitowa lokaci guda, da alama already sun saba yin hakan ne.

Wannan bodyguard na ɗazun da ya buɗewa Sir Arvin kofar mota a office, shi ne nan ya sake zuwa ya buɗe mashi a yanzu ma. Yana buɗe mashi ya fito da sauri ya nufi tsadaddiya kuma haɗaɗiyar elevator su, cikin sauri yake tafiya tamkar wanda ya ƙosa da su iso gidan, kamar wani abin yana jiransa a ciki.

Haƙiƙa gidansu Sir Arvin ya wuce baki ya zayyano kyansa, kun fa san yadda ginin Chinawa yake, ba wasa ba! Sun iya tsara gini sosai.

A harabar gidan waÉ—an nan jiga jigan bodyguards É—in nasa suka dakata cirko cirko kamar masu jiran umurnin su aiwatar da wani abin, su kuma Æ´an'sandan nan sun wuce wajen wasu tsadaddun kujeru dake wajen wani tsalelen pili da aka kewaye da glass dan hutawa.

Hawa na biyu Sir Arvin ya wuce kai tsaye.

Wani irin haɗaɗɗen parlour ne mai girma wadda ya haɗiye luntsuma luntsuman sofas set har kala uku, komai na more rayuwa wadda ɗan adam mai bala'in buri zai buƙata da akwai a cikin wannan gida, dukiya ta yi masu mubaya'a ainun, wani irin azababben daddaɗar kamshi air freshener ne mai bala'in daɗi ne yake tashi a cikin parlourn, tsayawa zayyana maku kyan parlour ma ba zai yiwu ba, dan duk iya misalin mai misali ba zai iya misilta haɗuwar wannan parlour ba.
Chapter 101 · 0% Book details