← Book details Triplets Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 168

Sashe 60

Triplets Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin wata iriyar kasalalliyar murya, can kasa kasa Lion É—in ya ce "Areef ka É—auko Mark mu tafi, ya sami karaya a kafa, he can't walk by himself".

Zaro idanu sosai Areef É—in ya yi yana faÉ—in "Lion what are you saying? Mark fa ka ce?".

Jinjina mashi kai kawai ya yi ba tare da ya sake yin magana ba, saboda idan ma ba dan yana da taurin zuciya ba, Allah ko mikewa ba zai iya yi ba, dan tsananin yunwa, kuma dama already kun san shi baya da jumuriyar yunwa sosai, Areef ya fishi jure yunwa, amma shi da Aseef, sam basu shiri da zancen yunwa sam sam, sai dai kuma, basu cin abinci dayawa, idan sun ci kaɗan Alhamdulillah sun ƙoshi.

"I think Mark he already dead?". Ya faɗa fuskarsa ɗauke da mamaki ƙarara a bayyane.

Ko sannu Lion É—in bai sake ce masu ba.

"Where is he?". Cewar Areef É—in. Da kyar Lion É—in ya iya nuna mashi wata hanya da take a cikin fadar.

Da sauri ya nufi hanyar, shi kuma Lion É—in ya fara takowa a hankali yana nufo su Aseef.

Ganin yanda yake tafiya da kyar da kyar ne yasa Aseef É—in ya kariso wajensa da sauri. Yana zuwa ya taimaka mashi suka karisa wajen da su Dr Salman suke tsaye.

Ayla baiwar Allah azaba tasa ta sume, har lokacin kuma jini take zubarwa. Kallo É—aya Lion É—in ya yi mata ya kawar da kansa gefe guda, wani iri yake ji a cikin zuciyarsa, ga tunanin Meeshansa, ga bakincikin da yake ciki na cewar Aseef ba É—an uwansu bane, ga bakin cikin abin da su Josephine suka yi masu na cin amanar mahaifinsu, sannan suka ci amanarsu suma, abubuwa sun taru sun yi mashi yawa a cikin zuciyarsa, ba dan yana da dakiya da juriya ba, da ya jima da faÉ—uwa kasa, da makiya sun yi galaba a kansa, sai dai ya rigasu ya ce Allah, dan haka Allah yake dafa mashi a koda yaushe, hakan tasa a kullum sai dai ya kara tsayuwa da kafafunsa gam, ba dai ya je kasa ba.

Areef ne ya fito daga wannan Æ´ar siririyar hanyar É—auke da Mark É—in a saman kafaÉ—arsa, baya ko motsi, da alama a sume yake.

A kusa da Dr Salman ya kwantar da Mark É—in yana faÉ—in "Ina sauran sojojin kuma?". "The already dead, remain 2". Lion É—in ya bashi amsa a takaice tare da wucewa ya nufi kofar fita daga fadar, dan fadar dab take da ta ruguje.

Sake É—aukar Mark É—in Areef É—in ya yi, shi kuma Aseef ya É—auki Ayla dake sume gwanin ban tausayi, duk sun jigata na kin karawa, duk wanda ya gansu a wannan hali, babu shakka sai ya tausaya masu, yau Lion da kansa da kyar yake tafiya, ko daga nan kun san bala'in Daular Mutuwa ta wuce tunanin mai tunani.

Sun ɗan yi tafiya mai ɗan nisa kafin su kai wata kofa dake fuskantar gabas. A tab bakin kofar Lion ya tsaya ba tare da ya buɗeta ba. Sai kuma ya duƙa kasa a wajen, a hankali ya buɗe wata kofar kasa dake a wajen, sannan ya miƙe tsaye. In a cool voice ya ce masu su zo su shiga, nan ne kawai kofar da ta rage ta fita a gidan, duk saura sun ruguje, su yi sauri dan in da suke ɗin ma, dab yake da rugujewa, abu kaɗan ya rage.

Da sauri suka karisa wajen, É—aya bayan É—aya suka shi ga. Lion É—in ne ya sake ce da Areef ya koma ya É—auko sojoji biyu da suka saura da ransu.

A tare suka koma da Aseef, bayan Aseef É—in ya sauke Ayla a cikin wannan hanyar kenan.

Da sauri suka É—auko su. Suna fita daga cikin fadar ginin ta ruguzo a kan Æ´ar Queen É—in da ita kanta Queen É—in.

Daga in da suke suna jiyo sautin ihun ƴar Queen ɗin, amma babu wanda ma ya ji cewa tamkar mutunce take ihun neman taimako, ga shi ba halin ta gudu, dan Lion ya ɗaureta, haka gini ya ruguzo a kanta, da haka ta mutu. Sai dai fa sun sha ruwan mamakin jin ihun mutane sosai a lokacin da ginin yake rugujewa, hakan na nufin da akwai sauran mutane a cikin gidan, Allah sarkin ginin nata rugujewa a kansu, dan kofofin ɗakunan duk a rufe suke, ba halin su gudu, sai dai wasu daga cikinsu, sun samu sun iya buɗe kofar sun gudu, sun nufi sauran ɓangarori na cikin gidan, fatan mu dai Allah yasa su sami hanyar fita, suma su tsira, ko ina Mustapha da Kausar?.

Bayan sun shiga cikin wannan hanyar dukkansu, Lion ne na karshe da ya shiga, sai da ya tabbatar dukkansu sun shiga, bayan ya shiga, sai ya janyo kofar ya rufe.

Bayan ya Rufe ne ya tsaya ya tsare Aseef da dara daran idanuwan nan nasa. Ƴan kame kame Aseef ɗin ya fara yi, dan wlh idanun Lion mugun rikita mutun suke yi, musamman idan ya tsareka da su ba tare da ya yi magana ba, duk sai ka ji ka tsargu, ko da kuwa baka yi laifi ba, sai yasa ka rasa nutsuwarka, haka shi ma Aseef ɗin ya yi, duk sai ya rasa nutsuwarsa, ya kama ƴan kame kame kamar wani tsohon munafuki.

Ko sannu Lion ɗin bai ce mashi ba, ya sa kai ya nufi wajen da Ayla take kwance, ɗan duƙawa ya yi a kusa da ita, a hankali ya kai hannunsa ya saɓeta a saman kafaɗarsa, sannan ya ruke hannun Dr Salman da hannunsa ɗaya, bai ce da kowa komai ba ya kama hanyar fita.

Ganin haka yasa Aseef ya ɗauki soja guda ɗaya, shi kuma Areef ya ɗauki Mark, suka bar soja ɗaya a wajen. Kasancewar tafiyar Lion yana da sauri, hakan yasa ya yi masu nisa sosai. Can saman wani dutse ya kwantar da Aylar, sannan ya juyo ya dawo dan ya ɗauki sojansa ɗayan da yake a bakin kofar shiga hanyar. Duk sojojin suna a sume, kuma babu ruwan da za'a zuba masu su farfaɗo. Duk da ciwon da yake jikinsa, da wahalar da yasha, hakan bai sa ya ji cewa zai iya barin wannan sojan nasa a wajen ba, saboda amana da kuma sanin darajar rai irin nasa. Har cikin ransa yana jin zafin jikinsa, amma haka ya ciza laɓɓansa gam ya saɓi sojan nan a saman shoulder ɗinsa.

A hanya bai kai ga karisawa wajen da ya kwantar da Aylar ba, ya ci karo da Areef, karɓa mashi sojan Areef ɗin ya yi, ba musu ya miƙa mashi sojan suka cigaba da tafiya.

A takaice a haka sai da suka yi tafiyar kwana ɗaya da wuni ɗaya cur a cikin wannan hanyar, ba dan Allah ba, da ba zasu taɓa kai labari ba, sun sha wahalar da ko makiyinka ba zaka yi mashi fatar ko makamancin irin hakan ta faru da shi ba.

Da yake hanyar yana da faÉ—i, kuma yana da reshuna, ma'ana hanyar ta rabu kashi kashi. Kun tuna hanyar da su Rimsha suka bi suka fita? To É—aya ne daga cikin reshen wannan hanyar, ta kasu ne kashi kashi, to suma haka suka cigaba da tafiya a cikin wannan dutse, har Allah yasa suka fita.

A wajen fita ma ba karamar gwagwarmaya suka sha ba, dan an rasa wanda zai iya jijjige masu kofar ya buÉ—eta su fita, duk sun galabaita fiye da tunanin mai tunani, shi kansa Aseef É—an dirama, yanzu ya yi laushi, bare Heartbeat nasa da Dr Salman, ai ba'a magana bayin Allah.

Daga karshe dai Lion É—in ne ya daure ya cije ya buge masu kofar tare da taimakon Aseef, shi kam AREEF ya zama tamkar Aseef a baya yau, ya yi laushi over, ga bala'i yunwa.

Suna buge kofar wani irin hasken rana ne ya haske masu idanu, dukkansu sai da suka datse idanuwansu, kafin daga baya su sake buÉ—ewa a hankali.

Lion ne ya fara sako kafafunsa waje, dan shi ne babba, shi ne yakamata ya fara fita, dan yaga ya yanayin hanyar take. Kungurmin dajin nan ne da su Rimsha suka fita ta wajen, sai dai su Rimsha ta baya suka fito, su kuma ta gaba suka fito, dama kunsan hanyar tana da reshuna.

Ganin wannan dajin ne yasa ya ce su fito kawai su tafi, zasu cinma gari a gaba ai. Wahalar dai su fita gari ne, suna fita gari koma ina ne komai zai saukaka masu, dan su ko'ina suka je, to dole masu ruke da mulkin garin su tarbesu hannu bibbiyu, dan ko a kasar America da kanta moryiyinsu tana da matuƙar kaifi fiye da tunanin mai tunani, ga shi kuma su taurari ne na faɗin Washington DC da kewayenta, ta ko'ina ana ji da su fiye da tunanin mai tunani, so wahalar ta dai a yanzu su fita gari ne.

Cigaba da tafiya suka yi ta yamma maso arewa, bama su iya gane gabas ba bare yamma, su dai in da ya fi yi masu, in da suke ganin zai fi masu sauki, nan suka bi.

Da yake rani ya shigo, damuna ta tafi, sai ya zamana ƴaƴan itatuwan dake a dajin sun fara ƙarewa, haka dai suka cigaba da tafiya.

Sun yi tafiya mai nisa sosai daga in da suka fito, sannan ne Lion ya zauna a kasar wata bishiyar mangoro mai matukar girma, kusan kamar bishiyar kuka. Abin mamaki a kasar wannan bishiyar su Rimsha suka fara zama time da suka fito, dan hanyar da su Lion É—in suka biyo, ya zo ya haÉ—u da hanyar da su Rimsha suka biyo, dan idan baku manta ba, ta yamma su Lion É—in suka juya suka bi, hankan ce ta mayar da su ta wancan hanyar.

Dukkansu zama suka zo suka yi a kusa da Lion É—in, sauke Mark Areef ya yi, sannan ya shiga cikin dajin, dan ya nemo ruwa, su samu su yayyafawa sojojin nan su faffaÉ—o, idan suka farfaÉ—o, komai zai zo masu da sauki, zasu rage wahala ta É—aukarsu.
Chapter 60 · 0% Book details