← Book details Triplets Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 168

Sashe 14

Triplets Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zaro kananan idanunta na ƴan China Cherish ɗin ta yi tare da dafe kirji, a ruɗe ta ce "A'isha kisa fa kika ce? Please ki dai'na batun kisa, kin san Allah ya hana hakan". "Cherish idan kika ga ban kashe William ba! To wlh ba Dr Salman ba ne ubana, William ya cuceni! Ya zalunce ni! Yanzu ki gaya mini me zan cewa ƴan uwana da iyayena? Wlh billahi ba zan zubar da wannan cikin ba, sai na haife shi! Kuma ba zan bar Washington DC ba har sai na kashe William! Wai da kike wannan magana ma Cherish kin san waye babana kuwa? Ba makawa kashe ni zai yi idan ya ji abin da ya faru da ni, dan haka kada ma ki sake kawo mini maganar na yi hakuri a nan wajen!!"................SU GWAGGO AN JI WUYA, AN TUNA DA DR SALMAN,😂 WAI SAI YANZU TAKE TUNANIN ME ZATA JE TA GAYWA DR SALMAN?🤔 SOYAYYA RUWAN ZUMA!

Shiru baiwar Allah Cherish ta yi bata sake yin magana ba har Josephine ta dawo ta samesu zaune a wajen, zama ta yi suka cigaba da jira. Ita dai Cherish haka ta wuni sukuku da ita har izuwa dare, sannan ta wuce gidanta.

A takaice dai haka suka cigaba da rayuwa, gwaggo tana zuwa school, sai dai bata bari su haɗu da Dr, har cikinta ya girma ya isa haihuwa, Dr bai sake nemanta ba, bai sake leƙota ba, da alama ya mance da ita, baiwar Allah, ita kuma tana ta faman dakon soyayyarsa, a kullum tana tunaninsa fiye da yanda take tunanin komai na rayuwarta.

A haka har Allah ya sauketa lafiya, tashin farko ta haifo Æ´an ukunta tsala tsala da su, lafiyayyun yara masu jini a jika, kyawawan gaske, jinin Roshan. Ba abin da ya fi sakata cikin tashin hankali sama da yanda É—anta na farkon ya yi mugun kama da Dr William, harta blue eyes nasu. Biyu daga cikin yaran nata sun kasance farare ne over, ma'ana sun fi É—ayan haske, haka zalika su biyun da suka fi hasken, sun kasance kwayar idanunsu iriÉ—aya ne, sak irin na Dr, shi kuma É—ayan haskensa kamar na Dr ne, sannan yana kama da Josephine sak babu maraba, kai kace É—anta ne ma, saboda tsantsar kama.

Bayan ta dawo cikin hayyacinta ne ta zubawa Æ´aÆ´an idanu, tana kallonsu, basu da maraba da familyn Dr, dukka babu wanda ya É—aukota a cikinsu, duk su Josephine ne, jajir da su tamkar tsada, ga bala'in kyau tamkar su suka faÉ—i irin halittar da suke so ayi musu, abin ba'a cewa komai.

A lokacin ne kuma wani bakin shaiɗani ya shiga cikin tunanin gwaggon, nan ta fara tunanin to akan me zata rike yaran Dr? Ai kawai ta kai mashi kayansa, kada ta shayar da su, dan babansu ya cutar da ita, ya ci amanarta, ya ci amanar yarda da soyayya, tun da Allah yasa sun kammala karatu last month, kawai ta bashi yaransa, ita kuma ta koma Naija, idan har ta rike yaranma ai ya cuceta da yawa............. KUSKURE KU HUKUNTA WASU DA LAIFIN DA WASU SUKA YI MAKU,❌ DR SHI YA YI MAKI LAIFI BA TRIPLETS NAKI BA! KUSKURE KI CE BA ZAKI RUKE SU BA, DAN DR YA YI MAKI BA DAI'DAI BA!!

Wannan banzar tunanin ne yasa ta ɗaukesu tare da haɗa wasu kaya nata da kuma wani farar takarda da ta yi rubutu a kansa da yaren su na tatar, wato yaren Na'urat, ta haɗa da chains ɗin da Na'urat ta bata, dama chain ɗin guda shidda ne, ta bawa Josephine ɗaya, Cherish ɗaya, saura huɗu, sai ta zuba uku a cikin wani ɗan ƙaramin, bayan ta raba tambarin heart na ɗayar sarkar kenan. Sannan ta ɗebesu, sai hanata Josephine take yi tana bata hakuri, amma ina ta zuciya, shaiɗan ta buga mata ganga, kuma ta taka rawa, tukukin bakin ciki na abin da Dr ya yi mata ya dawo mata sabo, ji take yi tamkar ta kashe Dr kawai ma ta huta.

Haka ta ɗaukesu zuwa gidan Dr. Da sauri Josephine ta bi bayanta, dan kada su je su yi ɓatatciya da Dr, saboda ta san halinsa.

Ta kuwa yi sa'a yana gida zaune a palo, ya yi wani fresh da shi, ya yi ɓul ɓul abinsa.

Babu ko sallama ta shiga palon. A saman sofa ta É—aura yara jariran da ko kwana uku a duniya basu yi ba, nono ma sau É—aya ta gwada basu, da ta ji zafi ta ce ba zata iya ba, ta koma basu madara, daga karshe ta kwasosu zuwa wajensa.

Murje idanu Dr ya yi ya ce bai san da wannan zance ba, shi ba zai karɓi yaran ba, dan yaranta ne ba nasa ba, ta kwashesu ta fita ko kuma ya yi mata illa, ya sanyata ta yi dana sanin zuwanta duniya.

Kin kwashesu ta yi, ita ma sai ta hau dokin zuciya, a in da ta shiga gaya mashi bakaken maganganu over. Abin dai sam ya zamar musu babu daÉ—i. Daga karshe Dr ya É—auko sandar buka horking nasu Uncle Herry, ya ce ko ta É—auki yaran su fita, ko ya kasheta ita da yaran.

Ta dauka wasa yake yi, sai ta ce wlh ba zata É—auke su ba, ya yi abin da zai yi!!.

Babu wani tunani, babu tsoron Allah ya ɗaga sandar zai buga mata. A guje ta miƙe daga samar sofar ta nufi waje, shi kuwa yana sauke sandar sai tsakiyar kan ɗaya daga cikin jariran nan nasa. Nan take yaro ya sandare musu, ko motsawa bai yi ba, tamkar rai ya yi halinsa, amma ga jini yana malala daga kansa.

Ganin hanan yasa Dr ya yi wurgi da sandar ya yi kan yaran, dan ya tsorata sosai, yasan cewa idan wani abin ya samu yaron nan, to wlh gwamnati ba zata bar shi ba, duk da uncle nasa ne yake a kan mulki, tabbas sai an hukunta shi idan ya cutar da jariri, hukunci kuma mai tsaurin gaske.

Ita kuma gwaggon ta yi waje bata san me ya faru ba. Da gudu Josephine dake tsaye a bakin kofar palon tana ganin komai ta kariso cikin palon, dan ta duba jariran.

A matukar haukace Dr ya kwashesu zuwa asibiti dan a duba mashi yaron ya mutu ne ko yana raye, ba shi da kwanciyar hankali da zai iya dubasu!!.

Ita kuwa gwaggo, tun da ta bar palon bata sake waiwayo su ba, ta ce idan Dr ya ga dama ya kashe yaran ai nasa ne, dan haka sai ta wuce gida abinta.

Tana zuwa ta hau shirin komawa Nigeria, tun da sun kammala karatu. Sai dai fa, da kyar a daddafe ta yi kwana É—aya na rashin yaran nan. Washegari ta wuni tamkar mara lafiya. A daddafe ta kai yamma. Zuwa dare ta ji ba zata iya rayuwa babu yaranta ba, dan haka sai ta shirya ta tafi gidan Dr.

Abin mamaki abin al'ajabi, ko da ta je sai Dr ya ce wlh ba zai bayar da yaran nan ba, yara dai yaransa ne! Kuma ta fita mashi a gida dama shi ba sonta yake yi ba, idan har bata fita ba, sai ya sanyata ta yi danasani mai girma.

Da farko ta ki fita, sai da ta ga zai yi mata kaca kaca ne ta kama kanta tana kuka tare da danasanin sanin Dr da ta yi a rayuwarta, tamkar ranta zai fita haka ta bar gidan.

A ranar Josephine ta zo har gidanta suka kwana a tare, dan ta É—ebe mata kewa. Kwana kuka Gwaggon ta yi tana danasani kai mashi Æ´aÆ´anta da ta yi. Ita kuwa Josephine kwana rarrashinta ta yi. Abin gwanin ban tausayi, shaiÉ—an ya yi mummunar aika aika a tsakanin masoyan guda biyu.

A takaice a cikin satin Gwaggo ta shirya ta dawo Nigeria, dan ta zo ta gayawa Dr Salman abin da yake faruwa, saboda su je su karɓo mata yaranta, ba zata iya rayuwa babu su ba, zata mutu idan ba'a karɓo mata su ba.

Haka ta baro Washington ba tare da ta sake saka yaran nata a idanunta ba, bata san a wani hali suke ba, bata san ya suke a hannun Dr William ba, shin ya karɓesu a matsayin ƴaƴa ne ko yaya? Duk bata sani ba, bata sake sanin komai dan gane da su ba!!.

Tana dawowa gida Nigeria ta tarar da bakin labarin da ta gwammaci mutuwa a kansa. Wato ta tarar da labarin Dr Salman ya rasu da shi da Naurat da Amarya, a yanda aka ce accident suka yi dukkansu suka mutu. Abu kaɗan ya hana ƙwaƙwalwar gwaggo bai juye ba, ga rashin iyaye, ga rashin masoyi, ga kuma uwa uba rashin jariran ƴaƴanta, ga rashin ƴan uwa. Dole ta yi hauka data ga Dr William, dan ya cutar da rayuwarta, duk shi ne silar komai a rayuwarta. Da badan son shi ba, ai da ba zata mance da kowa ba har iyayenta su rasu bata sani ba!.

Tun tana kuka da hawaye, har hawayen nata suka dai'na fita. Cikin raɗaɗi da kunan rai ta nufi ɗaya daga cikin gidajen Dr Salman, in da aka ce mata nan Abba ya yi aure. Tana zuwa ta yi sa'a Abban yana gidan. Tana kuka tamkar zata mutu ta fara bashi labarin abubuwan da suka faru da ita, tun daga farko har karshe. Daga karshe ta rufe mashi da cewa, dan girman Allah ya taimaka ya karɓo mata ƴaƴanta a wajen Dr William, dan ba zata iya rayuwa babu su ba.
Chapter 14 · 0% Book details