Sashe 23
Triplets Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Subhanallahi zaro idanu sosai ya yi yana kallon yanda face nata ya dawo saboda kuka, idanu a kumbure. Nan take shi ma face nasa ta sauya, ɗaure fuska sosai ya yi, cikin nuna isa da magana kai tsaye ya ce wani mai karan kwanan ne ya taɓata da har ya sakata wannan irin kuka haka? Meya sameta?.
Jin yadda ya yi maganar babu wasa a tattare da shi ne yasa ta tsayar da kukan nata cak, da sauri ta waro jajayen idanun nata waje. Wani irin mahaukacin razana ta yi na ganin yanda fuskarsa take, ya É—aureta tamau, ya haÉ—e geran sama da kasa, sam babu wasa ko É—igo a tattare da shi.
Nan take wani irin tsoro ya kamata, dan bata san me zata ce mashi ba, ga shi ya ɓata rai over. Narai narai ta fara yi da idanu. Tsawa ya daka mata a kan wanene ya taɓata? Me aka yi mata da har zata yi irin wannan uban kuka haka?.
Kokarin barin jikinsa ta fara yi, dan ta gudu, ta koma cikin gida. Damko wuyar rigar jikinta ya yi, kasancewar rigar ɗan ƙaramin ne zuwa cibiya, sai gabaɗaya tula tulanta suka bayyana a waje. Da sauri ta koma jikin nasa ta kwanta tana mayar da numfashi, nan take ta nemi kukan nata ma ta rasa...... NI KO NACE AU, DAMA ASHE IYA SHEGE NE, DA KI GAYA MASHI ME YA SAMEKI MANA! KIGA YANDA ZAI YI BALL DAKE, DAN WLH IN DAI KIKA CE MASHI BAKI SON SHI NE SABODA DADDYNSA NA CI AMANAR GWAGGON, ZAKI YABAWA AYA ZAKINTA KUWA
Wani irin shock ya ji na komawa jikinsan nan da ta yi. Kankame shi ta yi, murya a dashe ta ce "Yaya Saif ni babu wanda ya taɓani".
Kai tsaye ya ce karya ne, ta gaya mashi wanda ya ɓata mata rai har ya sakata kuka haka, ko kuma ita ma ya hukunta ta, ya fara ta kanta. Shiru ta yi yana tunanin me zata yi mashi ne ya sauko? Me ya kamata ta yi mashi.
Can sai ta ce "Yaya Saif ciwon ciki ne fa yasa nake kuka, tun jiya da daddare cikina yake yi mani ciwo, kuma na kasa gayawa su daddy ne, dan a lokacin suna barci, da safe kuma na kasa iya fitowa waje, kuma muryata bata fita sosai bare na yi kuka da karfi su jini".
Hannu ya ɗaura a saman cikin nata. Nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke, hankalinsa ya ɗan kwanta, da ya yi tunanin ko wani ne ya taɓata, da yanzun nan ya karɓi hukunci.
Shafa shafaffen cikin nata ya fara yi yana kallon face nata, gam ta datse idanunta, dan ma kada su haÉ—a ido, sai sauke nauyayyar ajiyar zuciya take yi.
Zazzaƙar sexy voice nasa ne ya daki dodan kunne, a in da ya ce mata "Muje gida in dubaki ko? Daga nan kuma, sai ki gaya mani meyasa baki kirani a waya kin gaya mani baki da lafiya ba, meyasa kuma kika fita ba tare da sani na ba?".
Kara kankame shi ta yi tana faÉ—in "Kai NooRi yanzu ai na ji sauki, ni ba sai ka dubani ba, dan kada ka yi mani allura".
Matso da ɗan bakinsa saitin kunnenta ya yi, kasa kasa ya ce "Alluran ne baki so?". Jinjina mashi kai ta yi tana kara lafewa a jikin nasa, har ta mance da zancen cewa bata son shi......... Yo ba dole ta mance ba, soyayya wasa ce😂
"Okey to ba zan yi maki ba, dubaki kawai zan yi". "Noorish ina gwaggona?".
Ba tare da ya bata amsa ba, ya sanya hannu ya fara tattare mata gashin kanta da yake a watse. "Open your eyes". Ya faÉ—a a sanyaye.
Turo baki ta yi tana É—an waro idanun nata a hankali. Gyara mata kwanciya ya yi tare da ciro wayarsa, number Areef ya shiga, massage ya rubuta mashi a kan ya fito mata da hijabi.
"NooRi ba zaka gaya mani ina gwaggona take ba?". Ta yi maganar tamkar zata saka mashi kuka. Matso da face nasa daf da ita ya yi, kasa kasa ya fara magana kamar mai raÉ—a. "Ba kin gujeta jiya ba? Dan haka kada ki tambayeni".
Ɗan ɗago idanu ta yi tana kallon kyakkyawar sajensa dake a kwance luf, a hankali ta kai hannu tana shafawa. "NooRi waye ya taɓa maka sajenka?".
Ɗan zaro idanu ya yi yana kallonta, ko ya akayi tasan an taba oho mata, yarinyar nan ta gama karance face nasa tsab, yanzu taɓa sajen da gwaggo ta yi ma sai da ta gane, kai Rimsha ba dai basira ba, akwai kaifin ƙwaƙwalwa.
"Waye ya gaya maki an taɓa sajen nawa?". Turo baki ta yi tana faɗin "Ai nasan ba haka kake gyarawa ba, idan ka gyara ba haka yake kasancewa ba, dole bayan da ka gama gyarawa, akwai wanda ya taɓa shi, nasan yanda gyaranka yake ai". E lallai Rimsha ta daban ce, wato har ta haddace yanda yake gyara shagen nasa.
Wani irin daÉ—i ya ji har cikin zuciyarsa, hakan na nufin yana nan a cikin ranta fiye da komai, tana sane da komai na mijin nata.
Tsabar farinciki bai ma san time da ya kara matseta a jikinsa ba. "Wash Noori zaka balla ni fa". Ta yi maganar a shagwaɓe sosai.
Ɗago haɓarta ya yi tare da manna mata sumbata a ɗan bakin nata, buɗe bakin nata ta yi, da ɗan karfi ta cije shi a lips nasa. Tsareta da ido ya yi ba tare da ya ce komai ba, ga face nasa kuma tamkar hadari, a ɗaure tamau. Ganin hakan yasa ta yi ƙoƙarin sake cizon nasa.
Bata kai ga sakewa ba Areef ya yi masu knocking na glass ɗin motar. Da sauri ta ɗago kanta, ganin Areef ne yasa ta yi ƙoƙarin barin jikin Lion ɗin. Bai hanata ba, sai ma sauke glass ɗin motar da ya yi ya karɓi hijabin nata.
Juyawa Areef ɗin ya yi ya koma cikin gida, shi kuma Lion ya miƙa mata hijabin a kan ta sanya, da sauri ta karɓa ta sanya. Umarni ya yi wa Donal a kan yazo su tafi. A hanzarce ya dawo cikin motar tare da kunnata suka bar gidan.
Lokacin da suka dawo gida, da gudu Rimshar ta wuce É—akinsu, dan tana tunanin gwaggo tana can, sai da ta shiga, taga bata nan, da sauri ta dawo izuwa É—akin Lion, nan ma bata nan, É—akin daddynta ta nufa kai tsaye, a nan ta sami gwaggo kwance a saman bed, ta gama cin abinci ta yi wanka.
Da gudu ta haye saman bed É—in tana dariya, shi kuwa Lion, juyawa ya yi ya fice izuwa harabar gidan gabaÉ—aya.
Miƙewa gwaggon ta yi zaune, nan ta rungumo Rimshar suka fara hira, labari Rimshar ta fara bata na abubuwan da suka faru a baya, har da aurensu da Lion, irin rayuwar da suke yi da shi, da tafiyarsu ƙasar Russia da suka yi, sai dai ko kusa ko alama bata bata labarin Daular Mutuwa ba, da alama an shafe mata labarinsa a cikin brain nata.
Sosai gwaggon ta yi mata nasiha a kan kula da miji, sannan ta kara mata da cewa, tun da har haka ne, to Lion yana sonta, dan Allah ita ma ta nuna mashi soyayya sosai, ta ga akwai ciwo sosai a cikin rayuwarsa, ta kula da shi, a yanzu tana a sahun gaba cikin mutanan da suke saka shi farinciki, dan Allah ta kasance mai saka shi farinciki sosai.
Gabaɗaya sai Rimshar ta ji jikinta ya yi sanyi, ba shakka akwai ciwo sosai a cikin rayuwar TRIPLETS, ga kuɗi, ga mulki, ga mukami, ga isa da izza, ga kyau, dukka Allah ya hore masu, amma kuma tun suna cikin mahaifiyarsu suke fuskantar jarabawa, babbar bala'i ce tashi da girma cikin kafurci, hakika ba kowa da kake kallon cikin Daula na ɗumbin dukiya bane bashi da damuwa da matsaloli na rayuwa, kowa da kowa yana iya fuskantar jarabawar Ubangiji ta kowace siga a kuma lokacin da baka yi tsammani ba, so yana da kyau mu runƙa kyautatawa al'umma zato, mu kuma mayar da hankulanmu a kan abubuwan da suke gabanmu, kada mu sakawa wani mai ɗan arziki idanu, dan bamu san halin da yake ciki ba, mu kyalkyalin arzikin kawai muke gani, amma na ciki, tana ciki, Allah ka bamu dacewa, ka kuma bamu ikon cin jarabawarka a duk lokacin da ka jarrabemu.
Sosai Rimsha ta ji jikinta ya yi sanyi, ta kuma yi wa gwaggon alkawarin zata yi iyaka bakin kokarinta wajen ganin ta sanya Lion farinciki. Tambayarta gwaggon ta yi a kan ina Lion É—in yake, shiru ta É—an yi kafin ta ce "Nima ban san ina yake ba, lokacin da muka shigo dai na barshi a palon sama".
ÆŠaga idanu gwaggon ta yi, ta kai kallonta a saman katafaren agogon bango da yake manne a jikin bangon É—akin, karfe 11:30 dai'dai, dawo da kallonta a kan Rimshar ta yi tana faÉ—in "Rimsha ashe fa mun É—an É—auki lokaci muna hira fa, labarin naki ne akwai tsawo, yanzu dai jeki ki duba mani Saif É—in nan, bai ci abincin safe ba, ki kai mashi abinci ya ci dan Allah". Ta yi maganar cike da nuna kulawa ga Æ´aÆ´an nata.
To Rimshar ta amsa da shi tare da miƙewa, ta sauko kasa daga saman bed ɗin, waje kai tsaye ta nufa. Tana fita ta wuce bedroom nasu. Wanka ta tsala tare da zuba shirinta cikin wandon jeans fari tas da T-shirt pink color, ta ɗaure gashin kanta a tsakiyar kai tare da zubo jelar a bayanta, ta yi matuƙar kyau tamkar ita ta yi kanta. Perfume nata ta zuba, nan take ta fara zuba kamshi tamkar ba gobe.
High heel ta sanya a kafarta, sannan ta nufo waje. A palo ta kalli É—ayar wayarta a saman sofa, cikin hanzari ta É—auki wayar ta nufo palon kasa. Kitchen ta nufa ta É—auko abincin Lion tare da ficewa da sauri.
Garden ta nufa da abincin, dan tana tunanin zata same shi a wajen, sai dai ina baya nan, ta sha ruwan mamaki sosai. Saman table ta É—aura kayan abincin tare da zama a saman sofa ta ciro wayarta. Numbersa ta kira, wayar ta yi ringin har ta katse bai É—auka ba.