← Book details Triplets Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 147 OF 168

Sashe 147

Triplets Part 4 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ban da kuka babu wani abin da take yi mashi. Areef ne ya kariso wajen tare da sa hannu ya É—auketa cak suka fito parlourn. Da sauri gabaÉ—aya familyn suka biyo bayansu, Aseef kam kamar zai yi kuka shi ma.

A saman doguwar sofa ya shimfiÉ—eta. Lion ne ya fara karisowa kanta yana kallon yadda take murkusoso kamar zata mutu, ga hawaye bibbiyu yana zuba daga idanuwanta.

"Areef kawo mun ita word room bari na dubata". Cewar Lion ɗin, ya kai karshen maganar tare da wucewa gaba, saboda kada ma Aseef ya saka masu kuka, shiyasa zasu yi saurin dubata, dan ba ƙaramin aikinsa bane ya fara kuka kamar yadda take yi.

Sake É—aukarta izuwa room É—in Areef É—in ya yi, haka gabaÉ—aya family suka sake É—unguma suka rufa masu baya.

A saman bed ya shimfiɗeta. Matan QUADRUPLE ƴan gata, ana ji dasu, da Lion da gwaggo haɗe da Dr William ne suka fara ƙoƙarin dubata, duk dan kada Aseef ya tsayar masu da iyashege a wajen, shiyasa suka haɗu gabaɗaya a kanta, dan su shawo kan matsalar da wuri. Duk da haka sun gudu basu tsira ba, dan sai da Aseef ɗin ya rinƙa zuba masu rigima a kan dan Allah kada su bari ta mutu, sai da sir Safwan ya riko shi suka fita waje.

Ita gwaggo abin da yake damun tunaninta ma a nan shi ne, ya zasu yi da Aseef idan aka ce ga Akila a labour room? Anya zai iya bari ta haihu ita kaÉ—ai kuwa? Wannan ko za'ayi yaya da shi tare da ita zasu yi wannan haihuwa, tana kuka yana yi, ciwon kai kawai ma idan ta yi shiga tsananin tashin hankali yake yi, duk ya fita daga cikin hayyacinsa, ya bi ya ruÉ—e ko abinci baya iya ci, ina ga kuma aka ce haihuwa zata yi? Ai shikenan kuma ranar dai sai dai family su runtse idanu, dan zasu ga abubuwa kala kala, shi bai yarda Heartbeat tasa ta sha wahala ba, gara mashi shi ya wahala ita ta ji daÉ—i bawan Allah.

Gwajin farko da su Lion suka yi mata suka tarar da ciki ne ma a jikinta na tsawon watanni almost uku, abin ya yi mugun basu mamaki, ga cikin nata babu laulayi babu komai, yanzu ma ƴar matsala aka samu cikin kamar yana son fita, shi ne yasa yake yi mata ciwo har haka, Allah mai iko, duk babu wanda ya san da ciki, shi kansa uban cikin bai san da zancen ba, kullum dai yana aikin yi mata kukan yana son baby's, ita ma sai dai ta yi ta Maganar har yanzu dukkansu matan QUADRUPLE babu wadda ta samu ciki, kullum cikin yin zancen suke yi, har ita kanta gwaggon kullum sai ta yi maganar da Dr William, ta ce mashi ƴaƴanta dai shiru har yanzu babu wadda ta sami ciki a cikinsu, sai dai ya ce mata ta yi hakuri lokaci ne, komai mai wucewa ne, Allah dai ya basu masu albarka, ashe ma Allah ya basu su ne basu sani ba, ai yau murna a wajensu ba'a magana, ga shi kuma gobe za'a rantsar da Lion, suna da babbbar shagali na walima da Areef and sir Safwan suka shirya, a wani katafaren diamond hall za'a gudanar da walimar, sai dai basu gayawa Lion ɗin ba, bazata suka shirya mashi kawai, sun shirya mashi abubuwa dayawa, kawai jiran goben nan suke yi ta zo, akwai shagali, ga hjy Rimsha First Lady da kanta, sai wani kara kyau ita ma take yi, ta yi wani dumur mur da ita, tana tafiya abubuwa suna juyi, kullum cikin rikita mana our Lion bawan Allah take yi, tasa ya yi ta biye mata kamar ba under 15 years da 32 years ba.........😂

Ganin Akila tana da ciki yasa gwaggo ta ce dukka sauran ma su zo a gwada su, irin wannan ciki na bazata haka, waya sani kila saura ma suna da shi.

Da sauri Brr Naurat ta ce haka za'ayi kam, duk su zo a gwadasu.

Da Anaya aka fara bayan gwaggon tasa an canzawa Akilar gado, ta ce Dr William ya ceci cikin Akilar kada ya fita, so yana ta fama da ita, shi kuma Lion ya koma gefe ya zauna yana tunani, shi dai har ga Allah baya son yara, bai shirya masu a yanzu ba, a cewarsa kuma babu ranar shirya masu ɗin, dan yara basu a tsarin rayuwarsa, ya kuwa yi sa'a dukka matan da aka gwadasu Rimshar ce kawai babu cikin a jikinta, Jehan and Anaya duk suna da ciki for two two months, cikin Akila yafi girma, ashe ba'a banza Jehan ta rinƙa yin zazzaɓi kwanaki ba, ashe cikin ne ita ma, ita dai Rimsha babu shi babu labarinsa, hakan yasa Lion ya yi farinciki ba kaɗan ba.

Gwaggo kuma ta yi bakin ciki ba kaÉ—an ba, dan tana da burin son ganin yaran Lion and sir Safwan, saboda sune masu kama da masoyinta Dr William, tana son ta sake ganin an haifa mata Dr William again, tana son ganin yarantar mai kama da Dr William, hakan yasa sam bata ji daÉ—in rashin samun cikin Rimsha ba, bugu da kari tun ranar da ta haifi QUADRUPLE soyayyar Lion da sir Safwan suka fi ninkuwa a cikin zuciyarta, ta fi sonsu sama da kowa, saboda wannan kama dai da suka yi da fist love É—in nata wato Dr William.

Wani irin tattali da kulawa na musamman aka fara bawa Akila, Anaya and Jehan, ta kowani ɓangare samun kulawa na musamman suke yi, Aseef kam nasa ba'a magana, tamkar zai koma cikin cikin Akalar, saboda tsananin son da yake yi wa wannan ciki, kowani bayan ƴan lokuta kaɗan sai ya zo ya kwantar da kansa a saman cikin nata wai ko zai ji motsin babynsa, kowani lokaci aikin kenan, shi ma Areef hakan yake fama.

Shi kam Lion ya rungumi Meesharsa sun cigaba da gashi abinsu, sai zuba love kamar wasu tattabaru, basu da damuwar komai.

Josephine ta tare a part É—in Aseef mai gabaÉ—aya, dan kula da Akila, saboda ita Josephine ta fi kaunar Aseef sama da kowa a cikin gidan, tana bala'in kaunarsa na wuce misali, shiyasa ma ta tare a part nasa, dan ta tabbatar da babu abin da ya samu Akila ko É—igo.

Washegari kamar yadda yake a dokance aka rantsar da Lion a cikin........

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥

*KINDADE KINA NEMAN ABUN DA ZAI SANYAKI QIBA,QIBA MEKYAU KIYI DIMIMI DUK INDA KIKA SHIGA BABU RAINI KINYI TA SIYA KINA ASARAR KUDINKI🤔
ALBISHIRINKI NAZO MIKI DA ABUN DA ZAKISHA BA TARE DA KINYI ASARAR KIDINKI BA 💃 Yana da matiƙar kyau sosai ko'ina naki zai chiko ki xama abar sha'awa duk mai buƙata ta nemeni ta wannan number 09067614054, kada ki bari ayi babu ke, kayanmu tested and trusted ne, guarantee ne*.

*KINDADE KINA NEMAN ABUNDA ZAI SANYA KISAMU XAMAN LFY TARE DA KWANCHIYAR HANKALI? TO BABYN HABIBI KIXO UMMU AFFAN TAXO MIKI DA SHAHARARRUN KUMA INGANTATTUN MAGUNGUNAN MATA, KAMA TUNDAGA KAN HUMRA, TURAREN WUTA,
INFECTION KILLER,
COLACCA,
SAI KAYAN GYARA PAGE.
KACA KACA.
YALLAGWADA.
JIGIDA.
RUWA RUWA.
BANI BANI.
WOMEN JELL BATA BATA.
DAFIN KAXA.
TANTABARA.
XABUWA.
CICCIƁI.
AND EXCLUSIVE, XUMA TASTED AND TRUSTED INA FARIN CHIKIN SANAR DA KU MUN FARA RAMADAN PROMO GAME BUQATA XA A IYA TUNTUBA NA TA WANNAN NUMBER
09067614054 JIGAWA STATE MUNA AIKAWA KO'INA CIKIN AMINCI DA YARDAR ALLAH,
BABYN HABIBI KARKIMANTA DA KAYANMU FIRST CLASS NE, DAGA KANSA AN RUFE KOFA, YANA DA INGANCI NA WUCE TUNANINKI*.

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥

https://whatsapp.com/channel/0029VaMOfZZI7BeKXPU9gK2S

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥

TSARAWA DA RUBUTAWA......✍️

❤️FATEEMA ZAHRA MUSA (💫PRINCESS TEEMA🔥🌹)

*Domin samun damar karanta littafin nan daga farko har karshe zaki iya nemana ta wannan number 08161390581 ban da kira*

E48

Washegari kamar yadda yake a dokance aka rantsar da Lion a cikin fadar shugaban kasa da yake a cikin white house, su ba'a EAGLE SQUARE suke rantsar da shuwagabanninsu ba, saboda they're DEVELOPED COUNTRIES, so komai nasu ba na kanana bane ba, basu wuce su ɗauki 10 mins wajen yin abin da zasu yi a wuce waje, saboda suna ɗaukar lokaci da mahimmanci fiye da komai a Rayuwarsu, basu wasa da lokaci, dan in ya wuce ya wuce kenan ba zai dawo ba, hakan tasa suke daraja lokacin fiye da komai nasu, sai dai kuma sun shirya party a cikin fadar shugaban kasar, wanda iya ƙusoshin gwamnati da iyalansu ne kawai zasu halakta, party ma ta shiryawa Lion ɗin wani shagalin, ga su Areef sun shirya mashi a gefe wanda bai san da shi ba.

Dukka wasu masu muƙaman gwammanati sai da suka harci cikin fadar shugaban kasar.
Chapter 147 · 0% Book details