← Book details Triplets Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 90 OF 168

Sashe 90

Triplets Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mummynta kuwa ta san komai sarai, ta kyaleta ne sai ta yi laushi, sai ta buɗe baki da kanta ta ce da Areef ya yi hakuri ta tuba bazata kara ba, sai ta yi hankali ta koyi sanin darajar mutane. A koda yaushe idan gwaggon tana hira da Areef ɗin, idan ta tambayesa ya yi magana da Jehan ya ji ya jikinta yake kuwa? Sai dai ya ce mata e sun yi magana ta wayar Rimsha ko wayar Lion, yaki gayawa gwaggon gaskiyar basu magana, saboda mum ta ce mashi in dai ya sake ya bari gwaggo ta sani, to wlh daga shi har ita kanta mum ɗin gwaggo ba kyalesu zata yi ba, dan a kan Jehan fa ita bata ji bata gani, duk wanda zai taɓa mata Jehan zasu yi dirama daga nan har kotun bangon duniya, dan haka ya kiyaye kada ya yarda ya sake ya bari gwaggon ta san cewa basu waya kuma sanadiyyar hakance ta kwantar da Jehan ɗin rashin lafiya, shi dai ya san yadda zai yi kawai.

To shiyasa sam yaki yarda gwaggon tasan halin da ake ciki, amma fa shi ma yana azabtuwa matuƙa, yana ji a jikinsa, dan har zazzaɓi na kwana biyu sai da ya yi, kun san su dama basu iya so ba, idan suka fara son mutun, to wlh har ga Allah da gabaɗaya zuciyarsu suke son shi, babu wasa a ciki, hakan cema tasa su basu yin mata biyu, Baturen mutun mace ɗaya yake aura, dan su sunce ba zasu iya raba zuciyarsu gida biyu su bawa mata biyu ba, ɗaya ta ishesu, to wannan ɗayar gabaɗaya zuciyar tasu suke ɗauka su miƙa mata, shiyasa idan mace ta yi breaking heart nasu a soyayya har kashe kansu suna yi, ko kuma zuciyar ta buga su mutu, dan ba zasu iya jura ba. To dai shi ma Areef sai da ya yi zazzaɓi, gabaɗaya a daddafe yake yin duk wasu ayyuka na Lion, dan ma dai mumnyn Jehan ɗin ce ta ce ya yi hakan, da wlh ko kwatantawa ba zai taɓa iya yi ba, ba zai iya fitowa ya ce wa mum ɗin ba zai iya bane, kun san shi daban yake a cikin TRIPLETS, da Lion ne ko Aseef wlh ba mum ba ko uban mum ne ɓaro ɓaro zasu ce mata ba zasu yi ba, amma da yake shi Areef zuciyarsa daban da tasu, sai ya hakura ya daure ya bi abin da ta ce, dan ya ɗauki mum ɗin tamkar uwa tun da uwa ce ga matarsa farincikinsa, kuma mata ce ga uncle nasa da ya fi kauna, dole ya jure ya yi mata biyayya, banda haka wlh komai wahalar da shi da Jehan zata yi zai iya jurewa ya biye mata, dan yana sonta da gabaɗaya zuciyarsa.

A ɓangaren Aseef kuwa, har wa yau dai yana a wajen Sheikh Sultan abinsa, sai kwarara mashi ruwan adduo'i ake yi, saukar Alqur'ani mai girma babu kama hannun yaro, kullum yana hira da Heartbeat nasa sosai bawan Allah, suna faranta ran juna.

Har wa yau Akila da Jehan basu san menene ya faru da Rimsha ba, su dai an ce masu bata da lafiya ne kawai, so sun ɗauka zazzaɓi ne ita ma, da yake kuma Lion yana gari, sai basu nemi ganinta ba, dan suna tsoron shiga bedroom nasa, kuma already kunga a cikin bedroom na mijin nata take jinya, a in da ya yi dis virgin ɗin nata a wajen ake jinyarta baiwar Allah.

❉✷❉✷❉✷❉✷❉✷❉✷❉✷❉✷❉✷❉✷

Lion ne tsaye a harabar gidan nasu, sanye yake da wando three cuter da riga mai karamar hannu, ƴar ramar da face nasa ta yi ta fito ɓaro ɓaro, ya ɗan rage tsawon gashin kansa, ya kuma ɗaureta a bayan wuya, face nasa ta yi fayau da ita kamar wanda ya tashi daga zazzaɓi, sai tashin daddaɗar kamshi perfume nasa yake yi, ya harɗe hannayensa a saman Lion chest nasa, duniya duk ta yi mashi wani iri.

Donal ne ya kariso wajen da yake a tsaye É—in, sara mashi ya É—aga hannu ya yi cikin girmamawa kafin ya ce "Sir Alex said you're call me".

Shiru ya ɗan yi na ƴan mintoci da a kallah zasu kai uku zuwa biyar kafin calmly ya fara magana "There's some cases da suke a hannun Mark before ya koma U.s, akwai wani mutumi da ɗauko shi daga Abuja da na bashi a kan ya horar mani da shi before na buƙace shi, to ina bukatar mutumin a yanzu".

Wani irin kamewa Donal É—in ya yi tare da kara É—aga hannu ya sara mashi, sannan ya wuce izuwa É—akin da Mark yake kulle mutane.

Jim kaÉ—an ya dawo, Lion É—in yana tsaye a wajen bai motsa ba, cikin girmamawa ya sanar da shi babu kowa a cikin É—akin. Jinjinawa Donal É—in kai kawai ya yi, alamar ya ji ya tafi to. Da sauri ya juya ya bar wajen.

Shiru Lion É—in ya yi yana tunani, tabbas in dai babu kowa a wajen, to ba shakka Areef ne ya yanke masu hukunci. Kamar yanda ya yi hasashen kuwa hakan ce, Areef ne yasa aka kashe mutumin, dan dayaga Lion É—in ya shiga busy, sai ya bibiyi case É—in kawai ya yanke masu hukunci, su kuma malaman makarantarsu Rimsha ya sanya sojojin dake gidan suka basu horo mai tsanani, sannan ya sallamesu. Time da ya sallamesu ko takawa da kafafunsu basu iya yi, da rarrafe suka bar gidan, shi ma Areef oga ne wajen iya bada punishment idan ka shiga hannunsa.

Ya É—an É—auki lokaci a tsaye a harabar gidan kafin ya wuce izuwa garden, dan ya kwanta ya É—an huta, tun da wannan abin ya faru, bashi da wajen zama sai wannan garden É—in, ita ma ba dan daÉ—i yake zama a cikinta ba, kawai dan bashi da yadda zai yi ne, garden É—in yanzu duhu take yi mashi, Rimsha ita ce dama fitilar dake haske duk in da yake, so yanzu bata nan, ko'ina duhu yake yi mashi, sai dai ya runtse idanuwansa ya zauna a waje kawai, amma ba dan daÉ—i ba.

A ɓangaren gidan Abbi kuwa, A'A Salahuddeen ya turo yayyunsa dan a tambaya mashi auren Hanan, dan shi da gaske yana sonta, sai dai baya zuwa wajenta, a waya kawai suke yin hira, saboda yana jin zafin su haɗa idanu da maman Ayla, kun san kuma tana gidan Abbin, so ita kanta Aylar baya son haɗa idanu da ita, yanzu kunyar mutanen gidan ma yake ji, saboda abin da mahaifinsa ya yi, da farko ma kamar zai hakura da neman auren Hanan ɗin, sai da Imran ya karfafa mashi gwiwa, sannan ya turo yayyunsa.

Abbi ne ya yi masu jagora izuwa garin Katsina, dan su nemi auren Hanan ɗin daga hannun mahaifinta, shi kuma daddyn Jelly ya ce ba zai sami zuwa ba, saboda rashin lafiyar Ayla, almost wajen 3 months a yanzu kenan da kwanciya ciwon nata, amma bata warke garau ba, sai kuka abu kaɗan, duk ta zama wata birkitaciya baiwar Allah, so daddyn baya son ya matsa ko nan da can daga kusa da ita, duk da cewa mamarta tana kusa, amma ya fi son ya zauna ya kula da ita. Yau ɗaukarta ma ya yi suka tafi gidan Azharuddin Bature, saboda gidan babu kowa, Abbi da su Aunty sun tafi Katsina, maman Aylar ma ta bisu, dan su yi wa Hanan ɗin kara, Aunty ta ce tana son zuwa taga iyayen Hanan ɗin, shi ne Abbi ya ce to su je a tare, sun baro Aafia sai Hjy Hadiza da ba zama a gidan take yi ba, yanzu ma bata gidan, su Abbi suna fita ita ma ta fita, yanzu yawon bin malamai take yi, duk dan ta shawo kan Abbin, sai wahal take yi buƙata ta gagara biya, a matsayinta na uwa ta kasa zama ta yi jinyar Aafiar, sai gantali take yi a kan namijin da bai san ta yi ba, dan shi Abbi yanzu idan ba Aunty ba, baya ganin kowa a gabansa.

Shi kuwa Irfan ya koma school abinsa, dama bai kammala master nasa ba, shi ma Akil sun koma Madina shi da Umaishansa, cikinta ya girma sosai har ya shiga watannin haihuwa, a yanzu kula na musamman Akil yake bata. Saura Imran da Jelly ne kawai a tare da Hjy Umaiya, shi ma Imran É—in zai koma U.s, dama a can yafiye yawan zama, soyayyar jelly take dawo da shi Naija dama, so yanzu yana so ne ya É—auketa su koma can mai gabaÉ—aya, ya zama Naija sai dai su kawo ziyara, Ammie ce ta dakatar da su yasa bai tafi ba, ta ce bata yarda ba, ya zauna a nan tare da su, Akil ya tafi shi ma yana son ya tafi ya barsu da kewa, sai rarrashinta yake yi yana neman shawo kanta dan ta yarda, so har yanzu dai bata amsa mashi da to ba, amsar kawai yake jira jirginsu ya É—aga.

❉✷❉✷❉✷❉✷❉✷❉✷❉✷❉✷❉✷❉✷

Su Abbi sun dira garin Katsina lafiya, kai tsaye gidansu baban Sadiq suka nufa, sam Abbi bai manta hanyar ba, motoci biyu suka yi dama, na familyn A'A Salahuddeen É—aya, na Abbi, Aunty, Hanan É—in, sai mana Ayla, su kuma mota É—aya, .

A kofar gidan daga can É—an nesa suka yi parking na motocin nasu, sannan suka fito suka nufi gidan. A kofar gida suka tsaya, Hanan ta ce bari ta shiga ta duba baban nata, su Aunty su zo su karisa ciki tun da mata ne.

Ba musu suka bita izuwa ciki, su Abbin kuwa suka gyara tsayuwa a wajen, sai kallon kaskanci Æ´an uwan A'A É—in suke yi wa gidansu Hanan É—in, basu yi zaton a irin wannan lakar gidan za su wanko kafa su zo nemawa A'A mata ba, su duk a zatonsu a gidan Abbin matar take, sun É—auka Æ´arsa cema, dama idan baku manta ba gabaÉ—aya familyn A'A akwaisu da jiji da kai da alfahari, hakan yasa suka fara surutai a kan su fa a gaskiya sun fi karfin su nemi aure a irin wannan gidan.
Chapter 90 · 0% Book details