← Book details Triplets Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 168

Sashe 16

Triplets Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A wani irin haukace ya damko wuyar Areef É—in ma, da É—ayar hannunsa, ya haÉ—esu su dukkansu biyu yana jin wani bakin azaba a cikin zuciyarsa, tafarfasa zuciyarsa take yi tamkar an É—aura dalma a wuta! Sam baya ji kuma baya gani, idanuwansa sun rufe, yau ne ya fito da ainahin zuciyarsa fili! Duk wajen an rasa mai iya gigin yi mishi magana, dama Areef É—in ne kawai yake da É—an kwarin gwiwar tinkararsa a irin wannan yanayi da yake ciki, to shi ma ga shi ya haÉ—a da shi ya shake. Aseef kam dama tun É—azun daya kifa kansa da jikin hannun sofa, bai sake É—agowa ba, duk abin da suke yi yana jinsu, amma ba zai iya É—agowa ba, bakinciki zata iya sanyawa ya haÉ—iyi zuciya ya mutu idan ya ga halin da suke ciki, to gara mishi ya cigaba da runtse idanuwansa kawai zai fi mashi alkhairi, Rimsha, Jehan da Akila dukkansu guduwa suka yi, suka fita daga palon, ko wace ta san halin masoyin nata sarai, sun san me zai biyo baya idan suka tsaya, gara musu su gudu abinsu.

Yau su Abba sun ga tashin hankali, an rasa mai bakin magana a cikinsu, su Imran duk sun haÉ—a malaman jikinsu waje guda, dan faÉ—ar ta manya ce!!, TGA da yake jarumi ma, kirjinsa sai dukan uku uku yake yi, cikinsa na murÉ—awa, bare kuma saura, ai su tsoronsu a tsananin bayyane ma yake.

Daddyn Rimsha ne kawai mai É—an kwarin gwiwan da ya kalli Gwaggo ya ce mata ta yi wa Lion magana wata kila zai É—an sassauto ya sakesu, idan ba haka ba to tabbas dukkansu zasu mutu, wlh har Areef É—in, dan ba shakar wasa ya yi musu ba.......

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️❤️🔥

*KINDADE KINA NEMAN ABUN DA ZAI SANYAKI QIBA,QIBA MEKYAU KIYI DIMIMI DUK INDA KIKA SHIGA BABU RAINI KINYI TA SIYA KINA ASARAR KUDINKI🤔
ALBISHIRINKI NAZO MIKI DA ABUN DA ZAKISHA BA TARE DA KINYI ASARAR KIDINKI BA 💃 Yana da matiƙar kyau sosai ko'ina naki zai chiko ki xama abar sha'awa duk mai buƙata ta nemeni ta wannan number 09067614054, kada ki bari ayi babu ke, kayanmu tested and trusted ne, guarantee ne*.

*KINDADE KINA NEMAN ABUNDA ZAI SANYA KISAMU XAMAN LFY TARE DA KWANCHIYAR HANKALI? TO BABYN HABIBI KIXO UMMU AFFAN TAXO MIKI DA SHAHARARRUN KUMA INGANTATTUN MAGUNGUNAN MATA, KAMA TUNDAGA KAN HUMRA, TURAREN WUTA,
INFECTION KILLER,
COLACCA,
SAI KAYAN GYARA PAGE.
KACA KACA.
YALLAGWADA.
JIGIDA.
RUWA RUWA.
BANI BANI.
WOMEN JELL BATA BATA.
DAFIN KAXA.
TANTABARA.
XABUWA.
CICCIƁI.
AND EXCLUSIVE, XUMA TASTED AND TRUSTED INA FARIN CHIKIN SANAR DA KU MUN FARA RAMADAN PROMO GAME BUQATA XA A IYA TUNTUBA NA TA WANNAN NUMBER
09067614054 JIGAWA STATE MUNA AIKAWA KO'INA CIKIN AMINCI DA YARDAR ALLAH,
BABYN HABIBI KARKIMANTA DA KAYANMU FIRST CLASS NE, DAGA KANSA AN RUFE KOFA, YANA DA INGANCI NA WUCE TUNANINKI*.

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥

https://whatsapp.com/channel/0029VaMOfZZI7BeKXPU9gK2S

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥

TSARAWA DA RUBUTAWA......✍️

❤️FATEEMA ZAHRA MUSA (💫PRINCESS TEEMA💋)

*Domin samun damar karanta littafin nan daga farko har karshe zaki iya nemana ta wannan number 08161390581*

E5

Daddyn Rimsha ne kawai mai É—an kwarin gwiwan da ya yi ta maza, ya kalli Gwaggo ya ce mata ta yi wa Lion magana, wata kila zai É—an sassauto ya sakesu, idan ba haka ba, to tabbas dukkansu zasu mutu wlh har Areef É—in, dan ba shakar wasa ya yi musu ba.

Ganin da gaske har da Areef zai iya mutuwa ne yasa ta miƙe da sauri ta isa wajen nasu.

Shi kuwa Areef ɗin sam bai yi ƙoƙarin kwatar kansa ba, dan yasan duk bala'i Lion ba zai taɓa kashe shi ba! In yaga zai mutu da gaske, dole ya sake shi, sai kawai ya zuba mashi idanu yana kallonsa, kuma dama hakan shi ne dai'dai a cewarsa, ya kamata su koyawa Lion ɗin tausayi ne, idan Areef ɗin ya zuba mashi idanu yana kallonsa, to zai ji tausayinsa ya sake shi, a haka zai koyi tausayi sosai a cewarsu.

Daga ɗan bayan Lion ɗin ta tsaya, gabaɗaya idanun jama'ar palon yana a kansu, kowa so yake ya ga ya Lion zai yi idan gwaggo ta yi mashi magana....... Ni ma PRINCESS TEEMA so nake yi naga ya zai yi😂

"Saif" ta ambata a hankali, tamkar bata son yin magana, kuma kamar tana jin tsoron yi mashi maganar.

Hakika ya ji sunan har cikin ransa, duk fushi da yake ciki bai hana ya ji muryar mahaifiyar tasa ta ratsa dukka ilahirin jikinsa ba, dama shi already zuciyarsa ta yardan mashi cewa ita ce mahaifiyarsu!.....

Ganin bai amsa ba, kuma bai sakesu bane, yasa ta É—an kara mastowa, gabaÉ—aya a tsorace take da ganin yanayin da É—an nata ya shiga, kirjinta sai dukan uku uku yake yi, amma hakan bai hana ta daure ta dafa kafaÉ—arsa da hannu É—aya ba. Cikin sanyin murya ta ce "Saif ka sakesu, kada ka yi masu illa ka ji ko?".

Wani irin dogon numfashi ya ja tare da saukewa a hankali, har cikin kashi da ɓargonsa ya ji sakonta! Ya ji sautin muryarta!. Ba musu ya zame hannayensa daga wuyoyin nasu. Nan take suka zube kasa, shi daddy ya suma already dama, shi kuma Areef tari ya fara yi da karfi karfi ba kakkautawa.

Uwa kenan, yau Lion ne yana cikin tsananin fushi haka har ayi mashi magana, kuma ya ji maganar ta ratsa shi? Lallai dai kam, uwa ta wuce wasa wlh!!.

Da sauri daddyn Rimsha ya yi kan Areef É—in bayan ya É—auko mashi ruwa a cikin fridge mai sanyi. Cike da kulawa ya dafa shi tare da kafa mashi robar ruwan a baki yana yi mashi sannu.

Shi kuwa Lion juyawa ya yi da nufin ya bar wajen, ya nufi bedroom nasa. Riko hannunsa ɗaya gwaggon ta yi, tana mai sake ambatar sunansa kirjinta na bugawa, dan tana tsoron kada su ce ba za su karɓeta a matsayin uwa ba, idan hakan ta kasance ba makawa zata iya mutuwa, dan tana bala'in sonsu, ko wani rana na duniya sai ta yi masu addu'a da fatan alkhairi tare da fatan Allah ya tsare mata su a duk in da suke, daidai da second guda basu taɓa barin cikin tunaninta ba, suna ranta fiye da tunanin mai tunani..... Allah sarki abin tausayi!.

Juyowa ya yi gareta cikin natsuwa, zuba mata idanu ya yi na Æ´an sakanni kafin kuma ya tsinci kansa da rungumeta a jikinsa.

Rungume shi ita ma ta yi, tare da sauke wani nauyayyar ajiyar zuciya mai cike da tarin abubuwa kala kala a cikinsa. Nan take kuma ta fara ruwan hawaye. Wani irin sanyi shi kuma ya ji tana ratsa zuciyarsa da ya rungumeta, hakan ce ta kara tabbatar mashi da cewa lallai ita ce mahaifiyarsu, domin kuwa tun da ya taso har izuwa yau, ba'a taɓa rana guda da ya shiga cikin fushi da ɓacin rai, ace zuciyarsa ta yi sanyi lokaci guda ba, ba'a taɓa ba! Wani lokaci ma, idan ya fusata sai ya zubawa tsakiyar kansa ruwan mai tsananin sanyi, saboda ya sami sauki, dan tamkar ci da wuta zuciyarsa take yi idan ransa ya ɓaci. Amma yau rana ta farko, ya shiga ɓacin rai, daga jin voice na gwaggo kuma ya sauko cikin sauki haka, dole ba'a banza ba! Dole ita ce mahaifiyarsu ta gaskiya! Ya sami nutsuwa sosai a kanta! Yana tsananin jinta a ransa ne fiye da tunanin mai tunani! Ji yake yi tamkar ya ɗauketa a saman kafaɗarsa su yi ta kewaye duniya kawai, saboda tsantsar so da yake yi mata, ashe ba'a banza yake kaunar Rimsha ba! Ashe ba'a banza ba duk da basu son mutane, amma suka yarda da daddyn Rimsha ya zauna a wajensu, sannan kuma suka kaunace shi sosai! Ashe ba'a banza ya ji cewa dole ya tsaya tsayin daka wajen ganin ya kwatarwa da daddyn Rimsha hakkinsa na zaluntarsa da aka yi ba. Ba'a banza su Areef suke tsananin kaunar daddyn Rimsha ba, ko dan kula da mahaifiyarsu da ya yi tamkar ba gobe, ai dole ma su ji kaunarsa, uwa ta wuce wasa!!. Daddyn Rimsha ya kula da gwaggon over, shiyasa Allah dan ya saka mashi, ya jarrabi TRIPLETS ɗin da kaunarsa over!. Allah sarki rayuwa kenan, Allah mai kyauta mai kari, mai saka maka ta in da baka yi zato ba, Shiyasa ake son komai zaka yi, to ka yi shi domin Allah, dan idan ya tashi saka maka, zai yi maka babbar sakayyar da baka taɓa zato ba, a gaskiya daddyn Rimsha ɗan uwa ne na kirki da kowa zai yi fatar samun irinsa, duk bakinciki da kunci da su Abban Imran suka jefa shi a ciki, suka raba shi da mahaifinsa da Hassan nasa da suka kwanta ciki ɗaya, duk da hakan bai hana shi yana taimaka masu ba, kuma dan Allah yake yi, shiyasa da ya gamu da jarabawa na rabuwa da familynsa, sai Allah ya kare mashi familyn nasa, suka shiga hannun na gari, duk in da suka je, an rukesu hannun biyu tsakani da Allah, dan shi ma ya ruke mutane da yawa tsakani da Allah, bugu da kari, sai Allah ya bashi surukai ɗaya tamkar da million, wanda ko wani uba zai yi wa ƴaƴansa fatan samun mazajen aure irinsu, Allah ka cigaba da dafa mana, kasa komai zamu yi, mu yi shi domin ka, dan mu samu rahamarka a koda yaushe.❤️

STORY

A hankali ya kwantar da kansa a saman kafaɗar gwaggon, yana sauke numfashi mai kama da gurnanin zaki. Hannu ta kai ta fara shafa lallausan gashin kansa, da yake ya rage tsawonsa ne, ya ɗan kwanto a kafaɗarta, to tana iya taɓa kansa.

Jin sautin kukan gwaggon yana tashi a hankali hankali ne yasa ya É—an É—ago kan nasa daga saman kafaÉ—ar tata. Ganin da gaske take kuka ne yasa ya sanya hannu ya fara goge mata hawayen nata ba tare da ya yi magana ba.
Chapter 16 · 0% Book details