← Book details Triplets Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 150 OF 168

Sashe 150

Triplets Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sun kuwa yi sa'a, suna kunna Tv suka fara kallo daga in da suke cin abinci a dining hall na white house ɗin, kuma a lokacin daddyn Rimshar yana tare da su, sai bayan sun kammala cin abinci ne wani mutun mai kama da Lion ɗin sak ya zo ya ja daddyn Rimsha gefe suka fita waje, camera ta ɗaukesu, sai daddyn ya tafi tare da Mummyn suka jera a tare, tabbas Lion ɗin ne ko ace da face ɗin Lion ɗin aka yi amfani, kunga kuwa an ɗaure shi ne, saboda koda maganar ɓatar daddyn Rimshar ta bayyana to idan aka duba cameras da komai da komai za'a ga daddyn Rimsha tare da Lion ɗin suka fita cikin fadar suka keɓe waje guda, alhalin kuma ba Lion na gaskiya bane, tsafi ce kawai ta yi aiki a wajen, sai dai abin ban mamakin a nan shi ne ta ya aka yi suka fita da shi daga cikin white house ɗin, duk da abu ne na tsafi kuma Kiristoci ne cike a wajen ma'ana za'a iya rufe masu ido, amma abin da mamaki gaskiya, sannan ya aka yi sam su Lion ɗin basu lura da cewa daddyn baya a tare da su ba har suka dawo gida? Duk da cewa ma jama'a suna cike sosai a wajen, amma da mamaki ace family basu lura daddy da mummy basu a tare da su ba!.

Tsabar shiga tashin hankali wani irin azababben sarawa kan Lion ɗin ya yi, shi dai yasan bai kira daddyn Rimsha sun fita gefe ba, ga camera kuma ta nuna shi ne ya kirasa, yau ake yinta kenan, wannan shi ne bala'i, ya zamar masu dole su ɓoye batun ɓatar daddyn, idan ba haka ba Lion ɗin yana cikin tsaka mai wuya, to wai wani shafaffe da mai nema ya ɗauki daddyn? Ina kuma suka kai shi? Me zasu yi mashi? Allah sarki mummy baiwar Allah, bata san komai ba.

Nima Princess Teema ban san komai ba, Wayyo Allah na, yau bani ba shan Maltina, family suna cikin wani hali, ai bani ba zaman lafiya.....😭🥲

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥

*KINDADE KINA NEMAN ABUN DA ZAI SANYAKI QIBA,QIBA MEKYAU KIYI DIMIMI DUK INDA KIKA SHIGA BABU RAINI KINYI TA SIYA KINA ASARAR KUDINKI🤔
ALBISHIRINKI NAZO MIKI DA ABUN DA ZAKISHA BA TARE DA KINYI ASARAR KIDINKI BA 💃 Yana da matiƙar kyau sosai ko'ina naki zai chiko ki xama abar sha'awa duk mai buƙata ta nemeni ta wannan number 09067614054, kada ki bari ayi babu ke, kayanmu tested and trusted ne, guarantee ne*.

*KINDADE KINA NEMAN ABUNDA ZAI SANYA KISAMU XAMAN LFY TARE DA KWANCHIYAR HANKALI? TO BABYN HABIBI KIXO UMMU AFFAN TAXO MIKI DA SHAHARARRUN KUMA INGANTATTUN MAGUNGUNAN MATA, KAMA TUNDAGA KAN HUMRA, TURAREN WUTA,
INFECTION KILLER,
COLACCA,
SAI KAYAN GYARA PAGE.
KACA KACA.
YALLAGWADA.
JIGIDA.
RUWA RUWA.
BANI BANI.
WOMEN JELL BATA BATA.
DAFIN KAXA.
TANTABARA.
XABUWA.
CICCIƁI.
AND EXCLUSIVE, XUMA TASTED AND TRUSTED INA FARIN CHIKIN SANAR DA KU MUN FARA RAMADAN PROMO GAME BUQATA XA A IYA TUNTUBA NA TA WANNAN NUMBER
09067614054 JIGAWA STATE MUNA AIKAWA KO'INA CIKIN AMINCI DA YARDAR ALLAH,
BABYN HABIBI KARKIMANTA DA KAYANMU FIRST CLASS NE, DAGA KANSA AN RUFE KOFA, YANA DA INGANCI NA WUCE TUNANINKI*.

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥

https://whatsapp.com/channel/0029VaMOfZZI7BeKXPU9gK2S

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥

TSARAWA DA RUBUTAWA......✍️

❤️FATEEMA ZAHRA MUSA (💫PRINCESS TEEMA🔥🌹)

*Domin samun damar karanta littafin nan daga farko har karshe zaki iya nemana ta wannan number 08161390581 ban da kira*

E49

GabaÉ—aya jama'ar parlourn sai kallonsu ya koma a kan Lion É—in. A ruÉ—e gwaggo ta ce. "Saif ba ga shi nan a tare kuka fita da Nawazuddeen É—in ba? A ina yake to?".

Dr William ne ya sake jefa mashi wata tambayar na cewa "Son ina uncle É—in naku yake?".

Yana rufe baki Aseef ya karɓa da cewa. "Ga shi a tare kuka fito kuma har da mum, to ina yake?".

Areef kam shiru ya yi yana kallon ɗan uwan nasa, domin shi ya fahimci komai, ko ba'a gaya mashi ba ya gane matsalar, ya yi amfani da kwakwalwarsa ne wajen karantar yanayin da Lion ɗin yake a ciki, a nan ne ya fahimci cewa tabbas wanda ya fita da daddyn Rimsha dai ba Lion na gaskiya bane, kuma ba sir Safwan bane, to waye ne? Wannan shi ne abin da Areef bawan Allah yake ta ƙoƙarin iya ganewa.

Shi kuwa Lion tsabar tambayoyi da suke jefa mashi da ruɗewar da iyayen nasa suka yi tasa bai san lokacin da ya yi karyar da bai taɓa yin irinta ba, bai san lokacin da ya ce masu shi ne ya fita tare da daddyn Rimshar ba, ya ce masu a tare suka fita mantawa ya yi ne, ya aiki daddyn wani waje ne, dan haka su kwantar da hankulansu, kowa ta wuce bedroom nasa.

Jikake gabaÉ—aya parlourn ta É—auka da sauke nauyayyar ajiyar zuciyoyin family, hankula sun kwanta da jin cewa shi ne ya aiki daddy, Areef ne kawai yanayinsa bata canza ba sai sir Arvin da yake kokwanton akan amsar da É—an uwan nasa ya bayar.

Shi Areef abin da yasa yanayinsa bata sauya ba, saboda ya fahimci gaskiyar al'amarin tun farko, shi kuma sir Safwan duk da cewa ba tare suka taso suka girma da su Lion É—in ba, amma yana iya karantarsu a wani hali suke ciki, sannan yana iya gane maganarsu ta dai'dai da ba dai'dai ba, bugu da kari bugawar zuciyoyinsu yana tafiya ne a tare, idan baku manta ba su dukkansu idan É—aya yana cikin damuwa ko wani abin ya same shi, to ba shakka zuciyoyinsu suna bugawa a tare, so tabbas zuciyar sir Safwan tana yi mashi kuna kamar yadda na Lion É—in take yi mashi, hakan yasa yake tantanma a kan amsar da Lion É—in ya bayar, ya dai yi shiru ne kawai bai yi magana ba, saboda iyayen nasu su samu nutsuwa da kwanciyar hankali.

Haka suka lallaɓasu kowa ya wuce cikin bedroom nasa. Shi kuma Lion sama ya wuce wajen ɗakin bincikensu. Ko da ya je ɗakin ma ya kasa iya taɓuka komai, jikinsa duk a mace, zama kawai ya yi a saman sofa yana tunanin abin da yakamata ya yi, tsabar shiga tension ma bai san lokacin da ya shigo ɗakin binciken nasu ya baro Rimsha a parlourn ba, shap ya mance da ita, ya wuce kawai abinsa, hankalinsa ta yi gaba.

A tare sir Safwan da Areef suka shigo cikin room É—in. A saman sofa dake fuskantar na Lion É—in suka zauna, ya zamana suna fuskantar juna. Zubawa Lion É—in idanu sosai suka yi suna kallonsa.

Areef ne ya yi karfin halin cewa. "Lion menene gaskiya? Su waye suka sace uncle? Me kuma ya haÉ—asu da kai? And ya aka yi ya zama kai ne mutun na karshe da ya fita tare da uncle É—in daga nan ba'a sake ganinsa a wajen taron ba?!!".

Nisawa Lion É—in ya yi, shiru ya yi masu na akallah 10 mins, har sun fidda ran zai yi magana, sai kuma suna ji shi in a low voice yana faÉ—in. "Abin da na gaya maku shi ne gaskiya, tabbas ni na aiki uncle wani waje, zaku iya tafi ku rabu da ni pls".

"No Saif, abin da bakinka yake faÉ—a daban, abin da zuciyarka yake amsawa daban, tabbas bugawar zuciyarka da amsar da yake a bakinka ba abu guda bane, ka manta da cewa muna jin bugun zuciyar juna ne?". Cewar sir Safwan.

Shiru Lion É—in ya yi bai sake ce masu ko uppan ba, dan bashi da abin da zai sake ce masu kuma.

"Lion please tell us the truth, saboda mu samu nutsuwa, kuma mu san a wani mataki muke". Cewar Areef.

Aseef ne ya katse masu magana ta hanyar shigowa cikin É—akin bakinsa a É—auke da sallama. Saman sofar da Lion É—in yake shi ma ya zo ya zauna suna fuskantar juna da su Areef

Cikin dakiya da jarumta Aseef ɗin ya fara magana. "Lion lallai akwai abin da ya sami uncle, saboda ina jin zuciyata tana bugawa da sauri sauri, da alama kuma zuciyarka ce mai wannan bugawa da tasa nawa take bugawa a haka, kuma nasan babu shakka haka sauran ƴan uwana suke ji ko Areef?". Ya yi maganar ne cikin tsayayyiyar murya da babu shagwaɓa ko kaɗan a cikinta, kallo ɗaya zaka yi mashi kasan yana cikin tsananin damuwa na wuce misali.

Kawar da kai Lion ɗin ya yi yana faɗin. "Aseef duk abin da ka faɗa zata iya yiwu kana jin hakan, amma ba shi ne zai sa ka yi tunanin cewa bani ne na aiki uncle ba, yanzu ka je ka kwanta ka huta". Ya kai karshen maganar tare da miƙewa daga samar sofar da yake.

"Lion tabbas a wannan karon abin da kake gaya mana ba hakan bane ba, tabbas ina ji a jikina akwai abin da kake ɓoye mana". Cewar Aseef.

Lion ɗin yana ƙoƙarin sake yin magana kamar daga sama suka ji voice ɗin Rimsha a bakin kofa tana faɗin.

"Yah Aseef yana da gaskiya, wlh Noorish akwai abin da ka ɓoye mana, wanda ya fita tare da daddyna ba kai bane ba, wlh ba kai bane".

A tare suka juyo da kallonsu a kanta, abin ya yi matuƙar basu mamaki da al'ajabi, Lion bai taɓa tunanin zata gane ba shi bane ba ya fita a tare da daddyn.

Hawaye ne yake bin saman lallausan kumatunta, hawaye bibbiyu take yi, ta tsaya a bakin kofar shigowa tana kallonsu, while suma ita suke kallo.

"Rimsha waye ya ce maki ba Lion bane? Shi ne fa, jeki ki kwanta ki huta, yanzu kinga muna magana ne a kan siyasa, daddynki zai dawo anjuma, Lion ne ya aikesa". Cewar Areef.

Kara tsananta gudu hawayen da yake a saman kuncinta ya yi, tamkar am buÉ—e ruwan famfo, gabaÉ—ayanta a firgice take, ta shiga damuwa na wuce misali.

"Yah Areef wlh ba Yah Saif bane ya fita tare da daddy, wlh ba shi bane ba, ni ina jin a jikina sace daddyna aka yi". Da kyar take iya yin maganar nata.

Sir Safwan zai yi magana Lion É—in ya É—aga masu hannu alamar su yi shiru.

Tsit suka yi suna kallonsa.
Chapter 150 · 0% Book details