← Book details Triplets Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 168

Sashe 11

Triplets Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A lokacin da za'ayi jana'izarsu su mum, za'a kaisu mutuware, wato jana'izar kiristoci, an buƙaci da Dr William ya zo ya wuce gaba a matsayinsa na babban ɗansu, amma sam baya wajen, hasalima bai san da zancen mutuwar ba, duk da cewa labarin ya baza gari, abin ku da manyan mutane, sai dai shi bai sami labari ba, dan yana babbar masallaci jumma'ar musulmai dake garin, tun da ya bar gidan suka wuce can da gwaggon, kafin ya tafi kuma sai da ya kashe wayarsa, a cewarsa kada ma su mum ɗin su kira shi, dan confirm sai ya musulunta. TASHIN SENSE.

Kasancewar ba'a sami Dr William ko a waya ba, haka aka ce Uncle Herry ya wuce gaba, Josephine ta bi bayansa, dan da aka tambayesu ina Dr William, sai suka cewa jama'a ai Dr William baya nan, sun dai ki faÉ—ar gaskiya. Haka aka kai gawarwakinsu mum É—in mutuware, sai kuka su Josephine É—in suke yi tamkar ransu zai fita.

A ɓangaren Dr William kuwa, suna fita Masallaci ya wuce da gwaggon, a in da ya je ya gayawa liman ga abin da yake tafe da su, ya gaya mashi aure suke son yi, kuma iyayensu basu son aure, saboda iyayensa sun ce a'a, kuma sun hana shi musulta.

Duba da yanayin kasar tasu, ba musu limamin ya bashi kalmar shahada tare da tambayar gwaggo shin da gaske tana son Dr William, sosai ta tabbatar musu da hakan, ba ɓata lokacin limamin ya ɗaura musu aure bayan an fito sallar azzahar, a cewarsa, ai sun fi shekaru goma sha takwas, dan haka suna da ƴanci da kansu, suna da ƴanci su yi abin da suka ga dama, shi ne yasa aka ɗaura musu aure bayan musultar Dr.

Ita kuma gwaggon a lokacin idanunta sun rufe, tana ganin kamar iyayen Dr William za su zo su rabata da shi, ba zata iya rayuwa babu shi ba, shi ne kawai yasa duk abin da liman ya ce mata, sai ta ce mishi e, dan a lokacin bata da burin da ya wuce Dr William ya musulunta, a ɗaura musu aure, su mallaki juna, shi ne yasa ta yarda, bata bi ta kan iyayenta ba, dan tana ganin suma zasu tsaya ɓata mata lokaci ne har a rabata da Dr.

Bayan an É—aura musu aure, kai tsaye gidan Gwaggon suka wuce abinsu, yau sun zama sabbin mutane. Ko da suka je gidan, komai na kayan kallo a kashe, basu sami labarin abin da yake wakana a gari ba. Rungume juna suka yi suna tsananin murna da farinciki, yau sun mallaki juna na har abada.

Kissing nata ya fara yi, cike da so da kauna ta fara mayar mishi da martani. Sun ɗan yi nisa cikin abin da suke yi, tamkar wanda aka muskula ta miƙe tana faɗin "My Dr bari na kira mum ɗina na gaya mata yanda aka yi komai, dan kada asamu matsala ka ji?".

Idanuwansa a runtse ya jawota jikinsa yana faÉ—in "A'a kada ki gaya musu yanzu, kada suma su rabani da ke, ki bari sai mun sami hutu a school, sai mu je gidan a tare ko?".

Jinjina mashi kai ta yi cike da gamsuwa da kuma yarda da shi É—ari bisa É—ari, dan ta faÉ—a makauniyar soyayya, baiwar Allah, ba laifinta bane, laifin so ne, da bashi da adalci idan ya shiga mutun.

"My Dr ka bari, bari na je nayi wanka nazo ko?". A kunne ya raÉ—a mata yau kam a tare za su yi. Bata yi mashi musu ba, dan sun mallaki juna, kafin su mallaki juna ma, dama wani lokaci ko tana toilet yana shiga ya yi abin da zai yi, bare kuma yanzu, ai sai abin da hali ya yi.

A tare suka wuce cikin toilet É—in. After some minutes suka fito rungume da juna, tamkar wani ya ce zai kwace musu junansu. Yau dai a tare suka yi komai, kama daga shafa lotions, shiryawa cikin kananan kaya, da yake da akwai kayansa sosai a gidan, dan idan baku manta ba, wani lokaci a gidan nata yake kwana a baya, hakan tasa ya sayi wasu kaya ya zuba a dressing room nata. Komai suke yi suna yi ne suna wasan masoya cike da so da kauna.

Da zata shiga kitchen ma, a tare suka shiga da shi. Duk da cewa bai iya aikin komai na kitchen ba, amma ya tayata da hira na kalaman soyayya masu daÉ—i, tare kuma da tana aiki yana rungumeta, ko ya shafi mazaunanta. Kayan kwalama ta haÉ—a musu tare da green tea mai zafi sosai.

A palo suka baje abinsu, a lokacin kuma har an kaisu Jacob mutuware an dawo, duk basu da labari. Sai da suka fara shan tea ne ta É—auko wayarta tare da kunna data dan ta yi wa Cherish massage a Whatsapp na yau sun yi aure da Dr, sun mallaki juna, ta zo ta tayata murna.

Tana kunna data sakon Cherish É—in ya shigo wayar nata na tayata alhinin rasa iyayen saurayin nata Dr William wanda yake a matsayin mijinta a yanzu kenan. Wani irin ihu ta kurma wanda bata san time É—in da ya fito daga bakinta ba, jikinta na kakkarwa ta yasar da wayar kasa.

Cikin tashin hankali ya riko kafaɗunta yana tambayarta lafiya? Ihun me take yi. Kasa magana ta yi, nan take hawaye suka cika mata idanuwa, domin tasan Cherish ba zata taɓa yi mata karya ba, tun da ta yi mata wannan massage ɗin, to gaskiya ne, iyayen Dr William sun mutu. TASHIN SENSE!!!.

Ganin taki amsa mishi tambayar da yake yi mata ne, yasa ya É—auki wayar tata dan ya duba me ta gani take wannan ihu. Dubawa da zai yi bai san time da ya saketa ya wani irin mikewa a razane ba.

Ita ma mikewa ta yi tana hawaye jikinta duk sai ɓari yake yi, abin mamaki yanzu bai fi awa biyar da suka rabu da su ba, amma ace sun mutu dukkansu biyu? Wannan dole bawa ya shiga tsananin tashin hankali.

A hanzarce Dr ya wuce ya ɗauko wayarsa, cikin tashin hankali, idanuwansa suna gani bibbiyu, ya fara ƙoƙarin kunna wayar. Ya kasa saboda kerma da jikinsa yake yi, wayar ta kasa tsayuwa waje guda a hannun nasa.

Daga karshe ita ta karɓa ta kunna mashi. Number uncle Herry ya fara kira, bugu ɗaya ya ɗauka. Cikin tsananin tashin hankali da razana ya fara magana yana haɗe word, a in da ya tambayi uncle Herryn ɗin ina dad da mum.

Ba ɓoye ɓoye ya gaya mashi sun mutu. Ya ilahi ya lillahi, bai san time ɗin da ya saki wayar tasa ta faɗi kasa ba. Kasa tsayuwa waje guda ya yi a in da ya zube gwiwowinsa a kasa a wajen, yana wani irin numfashi mai kama da gurnanin zaki.

Tsugunnawa ta yi a kusa da shi tare da É—an rungumo shi a jikinta, sai ruwan hawaye take yi. Muryarsa tamkar mara lafiyar da ya yi shekara cikin mawuyacin hali ya ce mata. "My.....my beauty.... Don't tell me that what i heard now about my dad and mum is true, say it's not a true to me".

Rarrashinsa ta fara yi tare da kara mashi karfin gwiwa. Ina ai kasa hakura ya yi, zuciyarsa ba zata iya É—auka ba, idanuwansa sun yi jajir da su. Ta yi ta yi a kan ya tashi su je gidan, amma ina ya kasa koda motsawa, dan yana bala'in kaunar iyayen nasa fiye da tunanin mai tunani, sune duniyarsa, duk abin da yake yi musun nan yana tsananin sonsu, ace lokacin guda ya rasasu? Kai abu ne wanda zuciyarsa ba zata iya É—auka lokaci guda ba, dan ma dai yana da taurin zuciyar ce, ai da abin ya wuce hakan.

Sai da ya É—auki almost 1 hour a durkushe a wajen, sannan ne ya iya É—an motsawa. Da kyar ya mike. Da dafa bango ya fito palo. Da sauri ta É—auki bakullin mota ta biyo bayansa.

A takaice ita ta ja motar suka nufi gidan. Har lokacin jama'a na cike taf a gidan. Bai kula kowa ba ya wuce ciki, yana tafiya tamkar zai faɗi kasa, ya rike hannun gwaggo gam dan kada jama'a su rabasu, ta je ta ɓace mashi kuma.

Kai tsaye hawa na biyu suka wuce, a nan suka sami su uncle Herry da su yayyun dad É—in nasu, sun sha kuka tamkar ba gobe, shi kuwa Dr William ya daure, idanuwansa sun yi jajir kamar wuta, amma sam bai yi kwallah ba.

Sai bayan sati biyu da mutuwar iyayen nasu ne ya fara gane kansa, nan ma da taimakon gwaggo da take kwantar mashi da hankali, ba karya ya shiga tsananin damuwa da tashin hankali na wuce misali, har wata iriyar mummunar rama ya yi, tamkar ba shi ba, iyaye ba wasa ba! Kuma dukkansu a lokacin guda, a hakan ma su Uncle Herry basu gaya mashi cewa sanadiyarsa ne yasa hawan jinin dad ɗin nasu ya tashi har ya mutu ba, sun ɓoye mashi, wata kila da sun gaya mashi shi ne sula, tashin hankali ne shi ma zai kashe shi.

Haka suka kasance a daddafe har tsawon wata da rasuwar iyayen nasu, sannan ne ya ce shi ba zai iya zama a wannan gidan ba, dan idan har ya zauna, kullum zai rinƙa kwana ne cikin kunci da bakinci tare da ganin tamkar iyayensu suna tare da su a gidan kamar baya, dan haka shi zai koma ɗaya daga cikin gidajen daddyn nasu ya zauna tare da gwaggon, za su ɗauki Tga su rike tun da a lokacin shekararsa biyu da ƴan watanni.

Uncle Herry da Josephine suka ce suma za su bishi, ba za su iya zama ba. Tambayar gwaggo ya yi a kan zata iya zama da familynsa, cike da murna ta ce mashi e, dan haka sai suka tattara duk wani abin da za su buƙata, suka rufe gidan tare da sallamar gabaɗaya ma'aikatan, sannan suka tafi zuwa wani gidan bene mai hawa ɗaya, shi ma ɗaya ne daga cikin gidajen daddyn nasu, ba karya ya kawatu iya kawatawa gidan.

A nan suka fara sabuwar rayuwa, gwaggo da Josephine sun zama very close friend, dan a lokacin shekarunsu kusan É—aya. Cherish tana zuwa suna rayuwar farinciki.
Chapter 11 · 0% Book details