Sashe 57
Triplets Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Cikin kuka ta fara magana kamar haka "Gwaggo ko na kira number Yah Areef bata shiga, kuma yau tsawon kwanaki fa basu dawo ba, babu wani zancensu ma, ni na rasa ya zan yi, wlh kirjina ciwo yake yi mani, please gwaggo ki ce ya dawo, ba zan iya ba..........." Kasa karisa maganar ta yi, saboda wani kuka daya kubce mata. Soyayya muguwar wasa, ta yi mata mummunar kamu, Allah sarki baiwar Allah, ba zata iya jurar rashin shi a kusa da ita ba.
Rarrashinta gwaggo ta fara yi, yau ga uwar miji tana rarrashin matan ɗanta a kan matar tana kewar ɗan, Allah mai iko, abin mamaki dai baya karewa, sam babu kunyar gwaggo a tattare da Jehan, babu wani abin da ya sauya a yadda suke da, ita bata yi mata ma kamar gwaggonce ta haifi TRIPLETS ɗin ba, ita dai iya abin da ta sani shi ne, Gwaggo, gwaggonta ce, kuma abokiyar rigimarta, ta zuba mata shagwaɓa san ranta, ita kuma gwaggon ta biye mata, bayan haka ita bata wani san da cewa ana jin kunyar uwar miji ba.
Da kyar da suɗin goshi gwaggon ta samu ta shawo kanta, da kyar ta yi shiru, ta hakura ta dai'na kukan, sai dai fa na ciki na ciki, kewar dai babu abin da ya ragu, har wani zazzaɓi take ji.
Haka suka kasance har Anaya ma ta shigo ta same su, ita ma nata sabon babin kukan ta zo ta buÉ—e masu, yau dai suna ganin ikon Allah, haka suka fara rarrashinta ita ma, har sai da ta hakura ta yi shiru, daga haka kuma barci ne ya yi awon gaba da ita. Ba su suka farka ba har sai da gwaggo ta tashe su a kan lokacin sallar mangariba ta yi, su tashi su yi sallah su yi wa mazan nasu a addu'a. A nan ne Gwaggo ta ga abin mamaki abin al'ajabi. Wannan abin mamaki ba komai bane face Rimsha, tana tashi ta barci da aka ce ta je ta yi sallah, buÉ—ar bakinta sai cewa ta yi menene kuma Sallah? Babbar magana.
Zaro idanu suka yi, gwaggon zata daka mata tsawa, Brr Naurat ta yi saurin dakatar da ita, saboda ta lura tamkar da kawai matsala a tattare da Rimshar, abin ku da manya, ƙwaƙwalwarsu da tunaninsu ba irin na yara bane, har ta harbo da akwai gagarumin matsala a tattare da jikar tata, wanda su gwaggon kuma basu gane ba.
Dan haka sai ta ce kowa ya je ya yi sallah, ita kuma Rimsha ta kwanta ta cigaba da yin barcinta, su kyaleta kada su sake yi mata magana. Da mamaki cike fal a fuskar gwaggon ta ce "Mummy sallah fa zata yi, kuma kice a barta kada ta yi? Ya haka kuma? Ai Rimsha yanzu idan ta ce ba zata yi sallah ba, to wlh da itace zamu karya mata kafa, dan ai ba yarinya bace tun da har da ciki a jikinta, uwa fa take shirin zama".
Jama'a ina ganin ikon Allah, karfi da ya ji gwaggo ta mayar da Rimsha mai ciki, ko me ta gani a jikinta da har ta dage a kan lallai ciki ne da ita? Ku tayani dubawa my readers, ita dai Rimsha bata taɓa yin sunna da Lion ba, har yanzu virgin ce ita, amma an zage a kan tana da ciki, to koma me dalilinsu na cewa hakan, lokaci zai nuna mana komai.
"Aisha tun da na ce ku bar Rimsha, to ku kyaleta kawai, idan kika cika matsawa, to ba makawa zaki tabka danasani mai girma, dan haka ku kyaleta ki je ki yi sallarki". Cewar Brr Naurat.
Okey kawai gwaggon ta amsa mata da shi, sannan ta miƙe tsaye tare da nufar toilet, ita kuma Brr Naurat ta karisa tashin su Jehan a kan su je su yi sallah.
In takaice maku wannan labari, Rimsha dai bayan wannan uban barci, to bata iya aikata komai, ko wanka bata yi, baiwar Allah, sai Allah ne kaÉ—an yasan menene matsalarta!.
Haka Brr Naurat ta rinƙa lallaɓata tana ririta ta, sai dai kuma ba abin da take cewa face su gaya mata su waye su? Bata sansu ba. Abin ya ƙullewa gwaggo kai, ita kuwa Brr Naurat sam bata damu ba, dan izuwa yanzu ta gama yardanwa kanta cewa jikar tata ba lafiya take ba, da akwai gagarumin matsala a kasa, hakan yasa bata wani damuwa.
Su Abba kuwa, suna can hankalinsu a tashe, sai adduo'i suke yi tare da bincikar ina Aseef, securitynsa Abban Imran ya kira a waya, ya sanyasu suka je suka shigar da report a kan ɓatar na Aseef, su kuma suna gida Lion ya hana fita.
A ɓangaren Aafia dai babu wani sauki, sai ma abin da ya cigaba na rashin lafiya, duk ta kara ramewa, ta bushe sosai, ta yi wani irin duhu mai munin gaske, abin gwanin ban tausayi, kuma har yanzu bata amsawa kowa komai, daga ido sai ido.
Akil, Imran da Irfan gabaÉ—aya tarewa suka yi a masallaci suna zubawa TRIPLETS addu'ar fatan nasara a tafiyarsu, Allah ya karesu ya dawo da su lafiya.
A ɓangaren Katsina gidansu Sadiq kuwa, Allah mai iko, shagon Yusuf dai sai kara bunƙasa take yi, yanzu har da fridge ya sanya a ciki, yana sayar da kayan sanyi, abubuwa sun cigaba, shi ma Sadiq Alhamdulillah, abubuwa suna tafiya mashi yadda ya kamata, sai dai kuma kullum yana cikin tunanin Jehan, bawan Allah, yana tsananin sonta, bai san cewa matar wani ce a yanzu ba. Maman Sadiq a yanzu abubuwa sun saukaka mata, girkinta har da nama da kifi, sau uku take girki a rana, gabaɗaya ta fita daga harkar baban Sadiq ɗin, dan dama baya tsinana mata komai, yanzu Allah yasa ƴaƴanta sun fara tsayuwa gam da kafafunsu, abu dai sai dai muce Alhamdulillah, wani lokaci har kaji biyu Sadiq yake sayo mata, ya yanka mata, ta gyara masu, ta zuba mashi miya mai shegen daɗi, Allah ya taimaketa ya bata ƴaƴan masu zuciyar nema da kuma zuciyar taimaka mata dukka biyu, dan wani yaron yana da zuciyar nema, amma kuma kuɗinsa bata ciwuwa, ba zai taimaka ba, ita dai ta yi sa'a, daga Sadiq ɗin har Yusuf ɗin burinsu kawai suga sun yi mata abu, su ganta a cikin tsananin fariniki suna kyautata mata, shi ne muradinsu, kuma hakan ce tasa Allah yake taimaka masu, komai suka saka a gaba, sai sunga dai'dai, dan uwa ba wasa ba!!! Uwa ba wasa ba!!! Uwa ba wasa ba!!! Ku ruke wannan da kyau, duk mai son yaga dai'dai, to ya sanya mahaifiyarsa farinciki, ko da iya murmushi kawai kasanya mahaifiyarka a rana, to ba makawa wannan rana ba zata wuce ba har sai wani abin alkhairi da zai sanyaka farinciki ya wanzu a gareka, bare kuma ace ka yi wa mahaifiyarka abin da har zata buɗe baki ta zuba maka albarka da ruwan adduo'i, haba ai ranar abin alkhairi da zaka fuskanta sai Allah ne kawai zai san adadinsa, ina mai kara jan hankulanku ƴan uwa, a kula da uwa, abi umarninta koda babu daɗi matuƙar bai kaucewa dokar Allah ba, hakan zai sanya muga dai'dai a dukkan al'amuranmu, mu jikanta, mu tausaya mata, iyayenmu sun yi mana komai a duniyarnan, komai muka yi ba zamu taɓa biyansu ba! Sai dai mu kwatanta iya abin da zamu iya sanyasu farinciki kawai.
To haka dai rayuwar su Sadiq take a yanzu, shi kuma baban nasu, gaula wanda ya rako maza duniya, yana can har iyanzu yana tare a gindin amarya, sai yadda ta ce haka za'ayi, yadda ta dama haka zai sha, naira na aiki, duk zaginsa da Æ´an unguwa suke yi, wlh ko a jikinsa, haka Amarya zata yi mashi É—inki, ko kunya baya ji zai saka kayan a jikinsa yana washe baki, Sadiq bakinciki kamar ya haÉ—iyi zuciya ya mutu, yana ji yana gani idan baban nasa ya yi wa Amaryar ba dai'dai ba, a tsakar gida zata kwashe mashi duk wasu albarka dake a tattare da shi, ta tsine mashi, ta yi mashi zagin kare dangi, amma dan rashin zuciya, zuciya ta mutu, haka zai yi ta bata hakuri, kuma bata hana shi ya sake komawa gindinta ya tare, abin dai ba'a cewa komai, Sadiq dai ba dan mamansa ba, da yaronnan ya haÉ—iyi zuciya ya mutu, saboda kunci da bakin cikin irin wannan hali na babansa, yarinya karama kamar amaryar nan da bata wuce sa'arsa a wajen shekaru ba, ta tsaya tana cin mutuncin mahaifinsa, ai kunsan dole zai ji zafi, dan fa uba uba ne komai lalacewarsa, Allah Ubangiji ka bawa kowa iyaye masu zuciya, masu sanin yakamata, masu sanin darajar kansu, masu sanin mutuncin kansu, ba masu kwaÉ—ayin duniya ba, Allah ka karawa namu muku iyayen lafiya, ka kuma saka masu da mafificin alkhairi.
Wannan shi ne rayuwar su Sadiq kuma. Idan muka dawo Kaduna kuwa, bayan sallar issha, Brr Naurat ce ta taka da kanta har izuwa part nasu daddyn Rimsha.
A lokacin suna tare da mum suna hirar duniya. A palo ta zauna tare da yi masu sallama. Jin cewa ita ce yasa dukkansu har su Abba basu ɓata lokaci ba wajen fitowa. Da mamaki suke kallonta har suka kariso izuwa in da take, a saman sofa kowannansu ya zauna, sai binta da idanu suke yi, suna jiran karin bayani.
Ta ɗan ɗauki mintina da a kallah za su kai biyar tana tunani ba tare da ta yi magana ba. Can kuma sai ta fara magana a nutse. "Nawazuddeen a gaskiya Rimsha tana cikin gagarumin matsala, kuma ga halin da muke ciki a yanzu, babu wanda aka yarjewa ya shiga gidan nan ko ya fita sai su Imran, Akil da kuma Irfan, suma dan tarewa da suka yi a masallaci ne, amma yana da kyau mu san matakin da zamu ɗauka, ba zai yi wu mu barta a cikin ciwo har haka ba, babban tashin hankalin ma shi ne rashin sallah, ba zai taɓa yiwuwa mu barta bata sallah ba har zuwa su Saif su dawo, dole kafin su dawo mu san abin yi". Ta kai karshen maganar tana jan doguwar numfashi tare da saukewa a hankali.
Har suna haÉ—a baki wajen cewa "Me kuma yake damunta?".