← Book details Triplets Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 115 OF 168

Sashe 115

Triplets Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A kusa da shi ta zo ta zauna, cikin nutsuwa ta ce mashi "Yah Areef am coming, zan je bedroom namu ne". Murmushi kaɗan ya sakar mata kafin ya gyaɗa mata kai alamar to, mikewa ta yi ta nufi waje, sai dai kafin ta fita sai da ta kashe wutar ɗakin, bai damu ba ya miƙe ya haye saman bed ya kwanta yana jiranta.

30 mins a tsakani, yana kwance shiru cikin duhu, sai jinta ya yi a saman jikinsa tana tashin wani fitinannen kamshi mai sanyayya zuciya. Wani irin nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya kai hannu ya rungumota sosai a jikin nasa, kasa kasa ya furta "Dama na ce your special my baby".

Face nata ta matso da shi dab da tasa, kasa kasa kamar mai raÉ—a ta fara magana "Like the way you're special ba? Kai makura ne my husband, I really love you more than your expectations".

Tsabar daÉ—i wani irin juyawa da ita ya yi, ya zamana ya yi mata rumfa da faffaÉ—ar kirjinsa, lips nata ya fara tsotsa cikin salo, cike da kwarin gwiwa ta fara taya shi ita É—in ma. Haka suka raba dare suna aiki É—aya, sai wuraren karfe 2, sannan ya rabu da ita, ya je ya yi wanka, ya fito ya fara sallar dare, ita kuma duk ya gama kashe mata jiki da wasanninsa, ya wahalar da ita son ransa, hakan yasa yana kyaleta ta jawo bargo ta shige, ba jimawa barci ya yi awon gaba da ita. Ba shi ya kwanta ba sai wuraren karfi biyar da ya yi sallar asuba, sannan ne ya É—an kwanta dan ya É—an yi barcin awa É—aya kafin su wuce gidan Hjyr daÉ—i.

Da misalin karfe 6 suka shirya shi da ita, ita ta koma bedroom nasu ta shirya a can, shi kuma ya shirya a nasa, bayan sun kammala shiri dukkansu suna fitowa suka haÉ—u da juna a parlourn sama.

Cool murmushi ta sakar mashi tana sunkuyar da kai kasa, abubuwan da suka faru daren jiya na sambatun da ya rinƙa yi mata ne ya dawo mata cikin ƙwaƙwalwarta, duk sai ta ji kunyarsa ya kamata, ga shi ita ma tai ta yi mashi kuka a kan ya bari ba zata iya jurewa ba.

Tsayuwa suka yi shiru a tsakiyar parlourn, ya tsareta da idanu babu ko kyaftawa, ita kuma ta sunkuyar da kanta kasa tana ɗan murmushi. From head to toe yake kare mata kallo, atamfar Rimsha ce ɗinki riga da sket a jikinta, kasancewar kayan Rimsha ce, sai kayan suka kamata sosai, duk wasu shape nata yana bayyana ne, a Duniya Areef yana tsananin son yaga ta sanya atamfa, kyau yake yi mashi sosai, yana son mace ta yi dressing na Hausa Fulani, hakan yasa idan ta sanya zai ɓata lokaci mai tsawo yana kallonta.

Jin bai ce komai ba kamar babu shi a wajen ne yasa ta É—an É—ago idanuwanta dan ta saci kallonsa, yana a cikin dressing nasu kamar kullum, wato shigar kananar kaya, ya É—aure gashin kansa a baya.

Tana É—ago idanuwa suka yi 4 eyes da shi, da sauri ta yi kasa da kanta tana mai kara faÉ—aÉ—a murmushin dake a saman face nata. A hankali ya tako kafafunsa ya matso kusa da ita, kafin ta É—ago ta kalle shi ya jawota jikinsa.

A tare suka sauke nauyayyar ajiyar zuciya, haɓarta ya ɗago suna fuskantar juna, ɗan bakinsa ya kai saman tata, ya shanye mata lips balm data sanyawa lips nata dikka, sannan ya saketa yana wurga mata kallon waye ya ce ta sanya lips balm ɗin?.

Juya fararen idanuwanta ta yi tare da kwace hannunta ta wuce gaba bata ce mashi komai ba, da kallo ya bita har sai da ta shige bedroom na gwaggo tukun nan ya bi bayanta.

Gwaggo na zaune a saman bed suna hira da Aafia da kuma Rimsha, magana suke yi a kan zasu je wajen gyaran jiki kafin gobe su wuce U.s, Rimsha ta ce tana son ayi mata kunshin flowers masu kyau, daga hannunta har wuyarta, da alama da gangan ta buƙaci yin haka. (Rimsha anya kuwa?🤔 Na dai yi shiru babu ruwana, amma dai kada a mance our Lion baya son ƙunshi🥲🧐)

Saman bedside drawer ya zauna, ita kuma Jehan gefen bed ta haye ta zauna. Cikin girmamawa ya É—agawa gwaggo gaisuwa.

Wani irin tsananin farinciki gwaggon ta ji na ganinsu a tare da ta yi, wani sanyi ta ji zuciyarta yana yi mata, hakan yasa ta amsa gaisuwar tasa tana farinciki, sannan ta É—aura da tambayarsa ko ya yi magana da Lion? Dan tana ta kiran numbersa a kashe.

A takaice ya amsa mata da cewa kafin Lion É—in ya baro kasar China ya yi mashi massage a kan jirginsu zai É—aga zuwa U.s, so wata kila basu sauka bane yasa numbersa a kashe, amma dai babu damuwar komai ta kwantar da hankalinta.

Shiru ta É—an yi kafin ta ce "Ka yi magana da Auta na ne?". ÆŠan kawar da kansa ya yi yana faÉ—in "Ai idan kina son yin magana da autanki sai kin nemo Heartbeat ta baki wayarta, idan ba haka ba ko kin kira shi ba zaki same shi ba! Wayarsa bata zaman banza, kullum a kan call yake, kawai ki nemo Heartbeat ta haÉ—aku".

Murmushi ta yi tana faÉ—in "A'a in dai yana lafiya kyale su suyi ta yi, ba ma sai kun nemo mani Akila ba, barshi ya ji daÉ—insa abinsa". Ta kai karshen maganar tare da shafa kan Jehan dake zaune tana ta faman satar kallon mijin nata, tamkar wani ya ce zai kwace mata shi.

Miƙewa ya yi tare da miƙawa Jehan ɗin hannunsa ɗaya a kan ta kama ta miƙe yana faɗin "Momma bari mu je, take good care of yourself, zamu dawo anjima".

Miƙa mashi hannu Jehan ɗin ta yi, rikota ya yi tare da jawota jikinsa, ko kunyar gwaggon basu ji ba a haka suka fice gwaggon tana yi masu Allah ya kiyaye su dawo lafiya. Da harara Rimsha ta bisu kamar su ne suka yi mata laifi, ita kuwa Aafia miƙewa ta yi tare da cewa da gwaggon tana zuwa.

Waje ta fito, ba komai ne ya fito da ita waje ba kuma face ta duba ko zata ci karo da Tga, dan da tunaninsa ta kwana, ya tsaya mata a rai, dama shi ne first love É—inta kafin Dr Nawid.

Garden ta nufa, a hankali ta lallaɓa ta shiga, tamkar wani zata leƙa. Babu kowa a ciki, zama a saman sofa ta yi tana tunanin rayuwa.

30 mins a tsakani tana zaune tana tunani, kamar daga sama ta ji an taɓata. A hanzarce ta ɗago kai, daga shi sai pajama launin milk color a jikinsa, fuskar nan dai kamar kullum, a ɗaure kamar hadari, sai tashin daddaɗar kamshi perfume yake yi.

Ganinsa yasa ta miƙe tsaye da sauri, cike da tsantsar tsoronsa ta raɓa gefensa zata wuce, tana tsananin sonsa, kuma tana tsoronsa, dan dama da face ɗin Lion dana Tga da kuma Mark idan kaci karo dasu dole ka ji tsoronsu, saboda babu alamar wasa ko kaɗan a tattare da su, yanzun nan zaka nemi nutsuwarka ka rasa! Saboda kwarjini.

Hannunta ya riko tare da juyowa gareta da kyau "Where are you going?". Ya faÉ—a a sanyaye.

Girgiza mashi kai cikin tsoro ta fara yi, ta kasa iya buɗe baki ta yi magana. Binta da kallo ya fara yi from head to toe, wani irin yanayi ya tsinci kansa a ciki. Sun jima a haka, sai ƙoƙarin kwatar hannunta take yi, amma ta kasa, daga karshe ma jawota jikinsa mai gabaɗaya ya yi. Fargaba da faɗuwar gaba tare da tsorata yasa numfashinta ya ɗauke diff ta sume mashi a jiki. Sai a lokacin kuma ya dawo cikin hayyacinsa.

Rikota da kyau ya yi tare da ɗaukarta cak zuwa saman sofa ya kwantar da ita, mamaki kansa yake yi a kan meya haɗa shi da wannan yarinya bakar fatar kuma? (Ni kuwa nace mashi ai dama mu bakaken fata muguwar shiga rai gare mu😒 wlh duk in da muka shiga dai sai an zauna da mu, kuma ko ba'a so sai an kaunace mu, kalar baiwar ƴan Nigeria kenan!!😏😌)

Zama ya yi a gefenta yana ta kallonta kawai.

A ɓangaren su Areef kuwa, suna fita Abuja suka nufa, kai tsaye gidan Hjyr daɗi ya nufa, tamkar ya san hanya, sai mamakinsa Jehan take yi, ita da farko a tunaninta ta yi mashi wayo, zata sanya shi yazo gidan ya fitar da su Adiva, bata san cewa already Areef kam ya wuci nan ba, ya wuce tunaninta.

Sam ba da niyar tarwatsa gidan na Hjyr daɗin ya zo ba, su Adiva kawai yazo ɗauka, saboda a binciken da ya yi tarwatsa wannan gida sai an shirya, dan haka sai sun koma U.s, idan suka gama da case ɗin zaɓen nan nasu Lion, daga baya zai shirya yadda za'a ruguje wannan tsinannen bakin kazamin gidan.

Kai tsaye ya danna motarsa har cikin gidan abinsa, a tare suka fito da shi da ita bayan ya yi parking. Jehan bata karasa tsinkewa da mamaki ba sai da ta kalli yasan hanyar shiga har can cikin in da suka yi rayuwa a baya, tafiya yake yi cikin nutsuwa tamkar wanda zai shiga cikin gidansu, ko a jikinsa.

Kai tsaye office na Hjyr daÉ—in suka nufa, sun kuma yi sa'a tana nan, ta hakimce a saman office chairta, ta É—aura kafa É—aya bisa É—aya, sai wani taunar chewing gum take yi.

Ko sallama bai yi mata ba, kawai ya afka abinsa, dan sallama ta masu daraja ce, ita kuma kazamar kadangariyar bariki ina ta ga wani daraja?.
Ita ma Jehan ɗin ciki ta bi shi. Ba tare da ɓata lokaci ba ya ce da ita ina su Adiva?.

Tun daga yanayinsa da ta kallah yasa ta sha jinin jikinta, dan bata ga wajen wasa a tattare da shi ba, sai dai kuma da yake Æ´ar duniya ce, sai ta nuna ita bata san akan me yake magana ba, ta nuna ita fa sam bata san su waye kuma Adiva ba, hasali ma ita dillaliyace mai fitar da ma'aikata masu yin aikatau izuwa kasashen waje, bayan haka ita bata da wata sana'a.
Chapter 115 · 0% Book details