← Book details Triplets Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 168

Sashe 62

Triplets Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk cikinsu babu mai ko raina biyar, haka suka cigaba da tafiya har suka fito cikin babban gari. Kai tsaye shagon sai da wayoyi Lion ya fara nufa, dan already dama basu zo da wayoyinsu ba, sun barosu kashe a gida. Sai ya ce su Areef É—in zauna su jirasa, kada su bisa wahalar zata yi yawa, bari shi ya je, daga baya zai zo ya É—aukesu.

Abin hawa ya tara, wato mai mashi, ya hau ya ce da mai mashin É—in ya kai shi katafaren shop na sai da wayoyi, su kuma suka zauna a wajen wani babban masallacin suna jiransa.

Sun yi tafiya mai nisa kafin su kai challenge, wani kasuwar waya ce a cikin Ilorin state É—in.

A tare da mai mashin É—in suka shiga cikin wani katafaren shagon sai da wayoyi. Kun san yarabawa da shegen son kyawawan kuma fararen mutane, sai kallon shi suke yi kamar zasu cinye shi, haushi tamkar ya kwakwale masu idanu yake ji, dan ya tsani kallon nan da suke yi mashi. Amma ba yadda zai yi, dole ya yi abin da yake a gabansa kawai.

Yana zuwa ya zaɓi irin wayar da yake da bukata, sannan ya tambayi mai shagon suna karɓar transfer? E guy ɗin ya amsa mashi, da yake katafaren shago ne, akwai yaran gida dayawa a ciki, idan ka zo sayan abu, to za'a sami ɗaya daga cikin yaran shagon ya kula da kai, ainahin Managernsu kuma yana zaune a ciki, gabansa da tarin computers.

Tambayarsa Lion ɗin ya yi a kan zai tura masu 2 million Naira, sai su ɗauki kuɗin wayarsu, su bashi sauran kuɗin, sun yarda za su karɓar?. Kasancewar babban shop ne, akwai kuɗi sosai a ciki, sai Manager ya ce ba damuwa ya tura kuɗin. Kum san eƴamurai da bala'in son kuɗi, da kuma daraja costumers, sun iya business over, to shagon na eƴamuri ne bana yarabawa ba, shiyasa suka yarda cikin aminci.

Shi ma Lion É—in cikin mutunci ya ce da guy É—in da ya yi attending É—in nasa, ya É—an ara mashi wayarsa na minti biyar bari ya yi kira. Kun sansu akwai daraja costumers, dan haka ba musu guy É—in ya ara mashi wayar.

Karɓa ya yi, number Imran ya saka ya kira, dan ya haddace number a kansa, sama da shekarun 8 suna a tare da Imran ɗin, kunga kuwa dole ya haddace numbersa, bare ma shi da yake da kaifin kwakwalwa sosai, duk wata number da take a wayarsa idan ka tambayesa zai zayyano maka ita.

Bugu É—aya Imran É—in ya É—auka, a tsananin kasale ya ce da Imran É—in zai turo mashi wata account number ya saka mashi 2m a ciki yanzu.

Jin muryarsa yasa Imran ɗin bai san time ɗin da ya miƙe tsaye zubur ba, a hanzarce ya fara tambayarsa suna lafiya? A ina suke yanzu? Kuma yaushe za su dawo?. Cikin ƙaguwa ya rinƙa jefo mashi tambayoyi.

Kasancewar a galabaice over yake, sai kawai ya katse kiran, dan ba zai iya biyewa Imran É—in ya tsaya amsa mashi tambayoyin ba.

Yana katse kiran ya ce da guy É—in ya bashi account number shop É—in nasu. A hanzarce ya kira mashi, ya yi typing ya turawa Imran É—in.

Ko minti biyu ba'ayi ba sai ga kuɗin Imran ɗin ya turo. A takaice haka suka gama ya biyasu kuɗin wayar ya karɓi saura chanjinsa, daga nan ya tambayi mai mashin ɗin ina hotel nasu mai tsananin kyau take.

Mai mashin da kuɗi yake so, sai ya ce su je ya kai shi, ba ɓata lokaci suka nufi hotel ɗin.

Katafaren hotel ne mai matukar kyau da kawatuwa, sai da suka tsaya a hanya ya sayi kayan sakawa a wani katafaren super market, sannan suka karisa hotel É—in. Duk rana É—aya ra'ina dubu É—ari biyu za su biya kowani É—aki É—aya. ÆŠaki biyar ya kama masu, 1 million a rana kenan, Imran ya sake kira da number É—aya daga cikin ma'aikatan wajen, sannan ya saka shi ya tura masu kuÉ—in É—akunan.

Daga nan ya karɓi keyas dan ya shiga ciki, mai mashin ɗin zai tafi, sai ya ce a'a ya jira shi bari ya zo zasu koma wajen da su Areef suke a tare, daga nan sai ya sallame shi. Okey mai mashin ɗin ya amsa mashi. Sama wajen ɗakunan da ya kama ya nufa, ɗaki ɗaya ya zaɓa ya buɗe ya shiga.

ÆŠaki ne aljannar duniya, tamkar É—akinsa na gidan nasa na Kaduna, haka É—akin take, sai tashin kamshi air freshener mai daÉ—i take yi, komai very clear. Wayar da ya saya ya sanya a charji kasancewar da akwai wutar nepa, yana so ya yi charjinta dan ya saka sim card ya kira his excellence a turo masu jirgi su bar garin nan.

A hanzarce ya yi wanka, sannan ya shirya sosai cikin ƴan mintocin da basu fi 30 ba, ya fito suka tafi da mai mashin ɗin, dan ya je ya taho da su Areef. A hanya sai da ya tsaya ya saya masu ruwar roba mai bala'in sanyi da yawa, dan yasan suna jin kishin ruwa. Ganin yanda yake pacaka da kuɗi ba karamin mamaki ya bawa mai mashin ɗin ba, kasancewar shi ba wani sanin kan kuɗin Naija ya yi ba, ida zai sayi abu, ɗibar kuɗin kawai yake yi ya basu, ko sun bashi canji kuma baya karɓa, ko kallon canjin ma baya yi, hakan ce ta yi mugu mugun bawa mai mashin ɗin mamaki, duk da ya gan shi Bature jajir da shi, amma dole ya sha mamaki, dan akwai Turawa mazauna Nigeria sosai, so a tunaninsa irinsu ne, bai san Lion kam wannan karon ce zuwansa Naija ta farko ba, sai kuma ya haɗu da jarabawa, in ba haka ba ai before bai ma san Naija ba, bare kuma ya san ya take ko ya kuɗinta yake da sauransu! Shi ne yasa yake kashe kuɗin tamkar bai san ta yaya ake nemosu ba.

Kai tsaye wajensu Aseef É—in mai mashin É—in ya mayar da shi, shi kansa mai mashin É—in sai satar kallonsa ta cikin mirror gaban mashin É—in yake yi, saboda ba karya Lion fa duk wanda ya gan shi, in ma mace ko na miji, to sai ya saki baki ya yi ta kallon shi babu gajiyawa, saboda tsananin kyan da Allah ya yi mashi! Ga uban farinjini da kwarjini, bugu da kari ga waÉ—an nan dara daran idanuwan nasa masu rikitar da mutun idan ya kallesu.

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️❤️🔥

*KINDADE KINA NEMAN ABUN DA ZAI SANYAKI QIBA,QIBA MEKYAU KIYI DIMIMI DUK INDA KIKA SHIGA BABU RAINI KINYI TA SIYA KINA ASARAR KUDINKI🤔
ALBISHIRINKI NAZO MIKI DA ABUN DA ZAKISHA BA TARE DA KINYI ASARAR KIDINKI BA 💃 Yana da matiƙar kyau sosai ko'ina naki zai chiko ki xama abar sha'awa duk mai buƙata ta nemeni ta wannan number 09067614054, kada ki bari ayi babu ke, kayanmu tested and trusted ne, guarantee ne*.

*KINDADE KINA NEMAN ABUNDA ZAI SANYA KISAMU XAMAN LFY TARE DA KWANCHIYAR HANKALI? TO BABYN HABIBI KIXO UMMU AFFAN TAXO MIKI DA SHAHARARRUN KUMA INGANTATTUN MAGUNGUNAN MATA, KAMA TUNDAGA KAN HUMRA, TURAREN WUTA,
INFECTION KILLER,
COLACCA,
SAI KAYAN GYARA PAGE.
KACA KACA.
YALLAGWADA.
JIGIDA.
RUWA RUWA.
BANI BANI.
WOMEN JELL BATA BATA.
DAFIN KAXA.
TANTABARA.
XABUWA.
CICCIƁI.
AND EXCLUSIVE, XUMA TASTED AND TRUSTED INA FARIN CHIKIN SANAR DA KU MUN FARA RAMADAN PROMO GAME BUQATA XA A IYA TUNTUBA NA TA WANNAN NUMBER
09067614054 JIGAWA STATE MUNA AIKAWA KO'INA CIKIN AMINCI DA YARDAR ALLAH,
BABYN HABIBI KARKIMANTA DA KAYANMU FIRST CLASS NE, DAGA KANSA AN RUFE KOFA, YANA DA INGANCI NA WUCE TUNANINKI*.

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥

https://whatsapp.com/channel/0029VaMOfZZI7BeKXPU9gK2S

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥

TSARAWA DA RUBUTAWA......✍️

❤️FATEEMA ZAHRA MUSA (💫PRINCESS TEEMA💋)

*Domin samun damar karanta littafin nan daga farko har karshe zaki iya nemana ta wannan number 08161390581*

E17

Date: 27/4/2024

Kamar yanda ya baro su Areef ɗin, haka ya dawo ya samesu. Ruwan ya fara basu, a hanzarce suka karɓa, Areef shi kaɗai sai da ya shanye roba biyu na ruwan, sannan ya kama mayar da numfashi, shi ma Aseef roba biyu ya sha, Akila rabin roba, Dr Salman ya shanye sauran rabin nata, sojojin Lion guda biyun nan kowannansu sai da ya sha roba ɗaya da rabi rabi, shi ma Mark roba biyu ya sha.

Daga haka Lion ya ce su tashi su karisa hotel ɗin, daga nan su yi wanka su huta kafin ya kira His excellence. Ya kai karshen maganarsa tare da juyawa ya hau bayan mashin ɗin da suka zo, sanna ya ce da mai mashin ɗin ya tara masu taxi su hau, ba musu ya tara masu taxi guda biyu, da yake a bakin babban hanya suke, sai aka yi saurin samun taxi ɗin. Rayuwa kenan, ba ta yanda bata juyawa mutun, wai yau TRIPLETS ne da shiga taxi? Idan ba ƙaddara ba, babu abin da zai kawo su Naija ma da kanta bare har wata Ilorin state, amma da yake kana naka Allah na nashi, sai ga su har ma Daular Mutuwa ba iya Naija kawai ba.

Haka suka shiga taxi É—in, Mark da sojojin nan taxi É—aya, Areef da Akila da Ayla suka shiga É—ayar taxi É—in a gidan baya, Aseef kuma ya shiga gidan gaba na taxi É—in su Areef, Dr Salman ya shiga gidan gaba na taxi É—in su Mark, haka suka kama hanya.

Gaba mai mashin É—in Lion ya yi, masu taxi É—in suka rufa mashi baya, bayan su Areef É—in sun gama shiga kenan, har lokacin Areef ne yake ruke da Ayla baiwar Allah, ko motsawa bata yi ba har izuwa yanzu, ba dan zuciyarta na bugawa ba, to da sai ma su ce rai ya yi halinsa.
Chapter 62 · 0% Book details