← Book details Triplets Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 168

Sashe 22

Triplets Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kallon mum ya yi yana murmushi kaÉ—an kaÉ—an, ya sani, ba wata gwaggon da take son zuwa ta gani, Areef take son ta je ta gani, yana ganinta da asuba da ta É—auka mashi waya tana kallon hoton Areef É—in, kawai bai kula ta bane, duk yana ganinsu, kuma ya yi alkawarin ba zai saka baki a maganar ba, idan suka ji uwar bari, za su mayar da kansu kamar yanda suka kawo kansu gidan, nasu wasa ne, har yanzu su yara ne, ba su san sharrin so ba, ita dai Rimsha ga idanu sun kunbura luhu luhu kamar ba lafiya ba, Akila kam ba'a magana.

"Mummy ki saka baki mana, daddy ya kaini wajen gwaggona da wuri, Allah ji nake ba zan iya kara minti goma ban kalleta ba". "Gwaggo ko ko Areef surikina zaki je gani?". Mummyn ta tambaya tana ƙoƙarin zuba abincin a cikin plate.

ÆŠaure fuska ta yi tamkar irin basawan nan, cikin fushi ta ce "Mummy waye kuma Areef?".

Galala daddyn ya saki baki yana ganin ikon Allah, Jehan akwai taurin zuciya kamar gwaggon nata, ai wanna yarinyar ba in da ta baro halin Lion, dan shi ma ya É—auko gwaggon ta wani fannin, kamar taurin zuciyar da sauransu, tana kewar Areef kamar ta mutu a cikin zuciyarta, amma a fili ta wani dake kamar bata ma san shi ba, bayan kuma harda satan hotonsa ta yi tana ta kallo har barci ya É—auketa.

Kawar da zancen mum ta yi da cewa "To zauna mu yi breakfast tukun nan, idan kin ƙoshi, sai a kaiki wajen gwaggo naki ". "Mum nifa ba zan iya cin komai ba tare da na kalli gwaggo ba". Ta kai karshen maganar tana matsowa kusa da daddyn, shi dai sai kallonta yake yi, ƴar karama da ita wai zata yi masu wayo, kamar ba su suka haifeta ba.

Mum zata sake yin magana Areef da ya shigo yanzu ya ce "Mum don't west your time, ba zata iya cin abinci ba har sai taga mijinta farincikinta, to gani na zo, nima dai na kasa cin abincin har sai na zo na ganki rigimammiya kawai".

Nan take daddaÉ—ar kamshi perfume nasa ya bule ko'ina a palon, fuskarsa É—auke da murmushi ya kariso cikin palon.

Wani irin nauyayyar ajiyar zuciya Jehan É—in ta sauke tare da sunkuyar da kai kasa tana satar kallon shi, ya yi kyau matuka over, ji take yi tamkar ta je ta rungume kayanta, amma ina jiji da kai ba zai barta ba.

Yana karisowa wajen yasa hannu ya É—an ja kumatunta yana faÉ—in "Sarkin rigima, da sanyin safiyar nan ma sai kin tasa mum a gaba da rigima ko? To gani nan na zo, sai ki kyale mani mum É—ina ta huta".

Harara ta wurga mashi tare da sa kai da nufin ta kowa sama abinta. Cikin sauri ya riko hannunta tare da jawowata jikinsa yana faÉ—in "Good morning my uncle, mum good morning".

Mummy dai kunya ya hanata ta É—ago idanu ta kalle shi, kun san Jehan ce Æ´ar farinta, ga shi babu kunya Areef É—in ya zo ya wani rungumeta a gabansu ko a jikinsa, dole mum ta ji kunya, shi kuwa daddy, ko a jikinsa, shi da ya kalli fin haka ma, sau nawa yana kallon Aseef yana É—aukar Akila cancak a gabansa, sau nawa yana kallon Lion da Rimsha a garden suna sha'aninsu, Areef da Jehan É—in ma me basu yi a gabansa? Ai shi ya ga komai, dan haka basu wani bashi kunya.

"Ni ka sakeni Hai!". Ta faÉ—a cikin fushi, da tsawa kuma. Saketa ya yi dan shi ma baya son ya ja magana sosai a tsakaninsu, kasancewar yaga mum ta takure waje guda, duk sai ya ji wani iri.

Zama ya yi a saman ɗaya daga cikin tables chars ɗin, ita kuma Jehan ɗin ta haura sama da gudu abinta. Miƙewa mum ta yi dan ta basu waje, a cewarta, ba zata iya cin abinci tare da Areef ba, dan yana surikinta, miji ga ƴar fari.

Ta zo dai'dai zata hau step na stair case ta haura sama, kamar daga sama suka ji voice É—in Lion da ya shigo yanzu yana faÉ—in "Ke where is my wife?".......BABBAR MAGANA, LALLAI LION DA SAURANKA, MUM ÆŠIN CE KE! KAI LALLAI KUWA.

Baki Areef ya saki yana kallon Lion É—in da mamaki, a cikin zuciyarsa yana faÉ—in "Yau Lion ne yake cewa ina matarsa? Da bakinsa yake tambayar, bama ina Rimsha ba, ina matarsa kai tsaye? Wato yanzu kenan ya yarda matarsa ce? Kenan ya yarda yana sonta? Lallai kuwa abin da mamaki, ko da yake, dama duk É—a na halak idan ya ji irin kyautatawa da daddyn Rimshar ya yi wa mahaifinsa, to dole zai so su Rimshar suma, ko dan daddyn nasu, ai dole ma Lion ya yarda da cewa yana sonta, kuma dole soyayyarta ta karu a cikin zuciyarsa over.

Sai dai sam Areef É—in bai ji daÉ—in yanda har yanzu Lion baya girmana kowa ba, ya shigo musu har cikin Palo, sallama ma kasa kasa ya yi ta yanda babu wanda ya ji, ko sannu bai ce masu ba, babu gaisuwa a matsayinsu na kannen mahaifiyarsa, kawai yana wani yi masu magana tamkar shi ne ubansu, kai Lion har gobe dai akwai izzar bala'i, wato yafi karfin ya ce wa mummy mum ina kwana?! Tab lallai har yanzu da sauran aiki.

Shi dai daddy, da yake yasan izzar da ta fi hakan ma Lion zai iya nuna masu, sai bai ce komai ba, idan da sabo, ai ya saba da halinsu. Mum da bata saba ba, sai abin ya ɗaure mata kai, ya yi mata wani irin banbaraƙoi, amma haka ta daure ta nuna mashi a in da ɗakin Rimshar yake.

Bai sake cewa da su komai ba, ya wuce ya nufi saman tamkar shi ya gina masu gidan, akwai shi da bala'in nuna isa na wuce misali.

Matsa mashi a hanya mum É—in ta yi, ya wuce abinsa, da kallo suka bi shi, Areef yana mamakin irin tsantsar nuna wannan uban isa na É—an uwan nasa, tamkar baza'a mutu ba.......... GASKIYA DAGA KAN LION AN RUFE ISA DA IZZA, IN DAI NUNA ISA DA IZZA NE, TO SHI KARSHE NE, SHI FA JI YAKE YI TAMKAR KOWA DOLE YA KASANCE A KARKASHINSA, KUMA DOLE AYI MASHI BIYAYYA, KO ANA SO KO BA'A SO, KAMAR SHI NE UBANSU!!.

Bayansa mum É—in ta bi, ita ma ta haura saman kenan, a in da ta wuce bedroom nata.

Rimsha tana zaune a saman tsakiyar bed nata, sai kuka take yi kamar ba gobe, kayan barcin jiya ne a jikinta, wando guntu zuwa santala santalan cinyoyinta, sai ƴar riga mai siririn hannu zuwa cibiya, fararene kal kal kayan, sun yi mata kyau over, gashin kanta a sake, duk ya barbazu kamar mahaukaciya, saboda kukan da ta rinƙa yi tana burgima a saman bed ɗin, shi ne yasa gashin nata ya bazu haka, ko wanka ta kasa tashi ta je ta yi, fuska ta yi jajir kamar tumatir nunanne.

A hankali ya turo kofar ya shigo, bakinsa É—auke da sallama kasa kasa. Kamshin perfume nasa ne ya fara kai mata karo, a zabure ta É—ago kanta tare da kai kallonta izuwa bakin kofar.

Ganin da gaske shi ɗin ne yasa ta miƙe da sauri tare da dirowa kasa daga saman gadon, da sauri ta nufe shi da nufin ta rungume shi, ko me ta tuna, sai kuma ta ja birki. Yana tsaye a bakin kofar yana kallonta.

Zubewa kasa ta yi a saman gwiwowinta tare da sake rushewa da wani sabon kukan. Yau ga ikon Allah.

Ya É—an É—auki Æ´an mintoci kamar biyar haka, kafin nan ya tako a hankali izuwa cikin É—akin.

A kusa da ita ya tsaya, hannun rigansa ya gyara kafin ya É—auketa cancak izuwa saman bed É—in. Zama ya yi da ita a jikinsa, yama rasa me zai ce mata, shi dai bai san kukan me take yi ba, bai kuma san ta ya zai tambayeta ba, sai ya É—an zuba mata idanu yana kallonta.

Goga fuskarta ta fara yi a saman kirjinsa tana É—an bubbuga kirjin nasa da hannunta É—aya, tamkar wadda ta aikata mummunar laifi kuma tana babbar danasani.

"Meesha". Ya ambaci sunanta a hankali.

Kamar jira take yi ya yi magana, cikin kuka ta ce "Yaya Saif me ya kawoka gidanmu? Me kazo yi to? Ni ka tafi!". Tana kuka tana surutan.

Jinjina mata kai ya yi tare da sauketa daga jikinsa, ya kuwa mike da gaske zai tafi É—in, kofar futa ya nufa, yana taku a nutse cikin kwanciyar hankali.

Da gudu ta diro kasa daga gadon, ta baya ta zo ta rungume shi tana mai cigaba da kukanta.

Nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya juyo gareta, dama yasan ba zata iya jurewa ya fice daga É—akin ba, ai yasan irin tsananin son da take yi mashi, da gangan ya nuna mata cewa komawar zai yi kamar yanda ta ce bata son ganin shi.

Juyowa ya yi ya rungumota yana É—an bubbuga bayanta a hankali, alamar rarrashi. Kara saka mashi kuka mai sauti sosai ta yi. ÆŠaukarta ya yi suka nufi waje, dan ba zai iya jurar kukan nan nata ba.

A haka ya zo ya wuce daddy da Areef a palon, ya nufi waje da ita a saman kafaÉ—arsa.

Kai tsaye sai cikin mota, a gidan baya ya sakata, shi ma ya shiga gidan bayan, Donal ne dama ya ja motar suka zo. Har lokacin sai kuka take zuba mashi. Umarni ya yi wa Donal É—in a kan ya fita ya basu waje. A hanzarce ya fice.

Rungumota sosai ya yi a jikinsa, sai a lokacin ne ya tambayeta meyafaru take yin wannan uban kuka haka. Kankame shi ta yi, ta kasa magana, sai yii, yi, yi, take yi tamkar wata Æ´ar baby.

"Meesha, meyasa kike son sakani a cikin damuwa ne? Kin san halin da nake ciki kuwa a yanzu?". Ya yi maganar yana ɗago haɓarta.
Chapter 22 · 0% Book details