Sashe 122
Triplets Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Karbar Adiva É—in ma suka yi, duk da basu da tabbacin tana raye ko ta mutu, fitowa Areef da Jehan É—in suka yi daga cikin hospital É—in, dan su je su nemi abin da zasu ci, almost 12 na rana yanzu basu karya ba, gara shi Areef zai iya jurewa, ita kam Jehan ba zata iya ba, sai kukar yunwa take yi mashi, ga uban gajiya, duk a galabaice suke.
A takaice. After some hours.
Sun koma Kaduna lafiya, a lokacin Tga ya yi wa su gwaggo jagoranci sun gama duk wasu shirye shiryen da zasu yi, suna isa gida ya bawa Tga ragamar yi wa su Maryam É—in shirye shiryen tafiya, ya yi masu na majinyata ya ce mashi, dan komai ya tafi normal cikin sauri.
A bedroom na Aseef dake a kasa Areef É—in ya kwantar da Maryam da kuma Adivar, sannan ya sanar da gwaggo da ta É—an kula da su, ta cigaba da duba lafiyarsu zuwa gobe su tafi.
Haƙiƙa gwaggon ta tausaya masu, har kwallah sai da ta matsa masu duk da bata san meyafaru da su ba, ta yi masu kwallah sosai, a haka ma dan dai bata gansu tun ɗaukosu da aka yi ba, yanzu ai sun ɗan yi kyan gani.
Bedroom nasa Areef ya wuce, wanka ya yi tare da fitowa ya shirya, sannan ya biya bashin sallar azabar da kuma la'asar da ake binsa.
Bayan ya idar sai ya zauna a bakin bed nasa tare da É—auko wayarsa da ya fita ya barta a saman bedside drawer, ba da ita ya tafi ba. Number Lion ya fara kira bayan ya kunna wayar, a lokacin kuma Lion ya tashi daga barci ya baro wayar a cikin bedroom nasa, ya fita zuwa parlourn kasa dan ya sanya a fitar da gawar Dr Cherish zuwa mortuary, so baya tare da wayar tasa, two miss call Areef É—in ya yi mashi, ganin bai É—auka bane yasa ya kyale shi tare da yunkurawa zai mike.
Kasa miƙewar ya yi, bai san time da ya koma ya zauna ba yana mai binta da kallo, tsaye take a bakin kofar shigowa cikin bedroom ɗin, hannunta ɗauke da kayan abinci, ta yi wanka ta canza kaya izuwa kananan kaya, wandon jeans fari tas da T-shirt maroon color, ta yi matuƙar kyau sosai da sosai, ta gyara gashin kanta, sai kai mashi karo daddaɗar kamshi perfume nata yake yi.
Duba time ya yi karfe 5 saura Æ´an mintoci, wani irin murÉ—a mashi cikinsa ya yi, saboda yunwa, dama abincin zai tashi ya je ya ce ta kawo mashi, sai kuma gata ta zo.
Karisowa cikin ɗakin ta yi bakinta ɗauke da sallama, har ƴar rama sai da ta yi, saboda shiga damuwa na halin da su Adiva ɗin suke a ciki. Sam basu ɓata lokaci ba wajen cin abincin a tare, dan suna jin bakar yunwa over.
Bayan sun kammala sai suka zauna hirar yadda aka yi ta tsinci kanta a gidan na Hjyr daÉ—in.
Da daddare misalin karfe 8 bayan sallar isha kenan, gabaÉ—aya family sun zo yi masu sallama, su Abban Imran duk sun zo, a nan ne gwaggo ta sanar da Abbi cewa zasu tafi da Aafia, bai ce komai ba, saboda gwaggo yayarsa ce, ba zai iya ja da hukuncinta ba idan ta yanke, dan haka sai ya ce Allah ya kaisu lafiya kawai.
Sun sha hira da family kamar ba gobe, Akila sai kuka take yi akan wai ba zata iya rabuwa da Ammienta ba, har da cewa ita gaskiya ba zata bi su gwaggo ba, zata zauna da Ammienta ya fi mata daɗi. (Ni kuwa nace iskancin kawai, anjuma kaɗan zaku ganta da waya tana faɗawa Heartbeat ta ƙosa ta ganshi😂 mu da mun san komai😠yo Aseef da Akila ai sai Allah, halinsu sai su😌)
Sai aikin rarrashinta Ammien take yi, haka shi ma Abba, sai rarrashinta suke yi.
Suna a tare cikin farinciki Akil ya kirasu a waya ya sanar dasu Umaisha ta haifi ɗa namiji yanzu, murna a wajensu ba'a magana, Ammien tafiya ya kamata zuwa Madina kenan, su Umaisha anzama maman baby, Akil kuma za'a dawo sabon aiki.............😂
A takaice dai family basu bar gidan ba har karfe 10 na dare, sannan suka yi masu sallama a kan da safe zasu zo su rakasu zuwa airport, sai bankwana ake yi kamar antafi kenan, Rimsha har da rungumar Ayla tana kuka, Malika ma tana wajen, sai dai babu mai ganinta, harta Rimshar ma bata san da zamanta a wajen ba, dan bata bayyanar masu yadda zasu ganta ba.
Ammien dai baki har kunne ta sami jika, ga shi Akil ya turo masu hoton babyn, yaron kamarsa É—aya sak da Akil É—in......... Ni dai nace Allah yasa ta tsaya a iya kamar ta fuska, kufa my readers?.
Bayan kowa ya wuce gida, yanzu gidan ya rage daga Areef and Jehan wadda suke cikin ɗakinsu, sai Dr Salman da Brr Naurat suma suna ɗakinsu, Adiva da Maryam suna a kwance a ɗakin Aseef, ko motsi basa yi dukkansu biyu, sai dai jikin ba laifi ya ɗan yi kyau. Gwaggo da Aafia suna ɗakin gwaggon, Akila tana bedroom nasu manne da waya tana yi wa Aseef kuka a kan ita fa wlh gobe ma ya yi mata nisa, ta ƙosa da gan shi, kamar ba yanzu ta gama cewa ita ba zata je U.s ba, zata zauna da su Ammienta, sai rarrashinta yake yi, suna nan dai suna aikin da suka saba, ita kuma Rimsha yau ɗakin mummynta ta tafi, saboda ta san Lion ya zai kira gwaggo a waya, sai ta gudu ta koma wajen mum ɗinta, dan ma kada gwaggon ta ce ta karɓi wayar su gaisa, ga shi ba zata iya ce da gwaggon a'a ba, shi ne yasa kawai ta gudu abinta.
Ta je kuma ta sami mum idanunta biyu, zama ta yi a saman bed suna hira, sai nasiha mum É—in take kara yi mata, tana kara tunantar da ita mahimmancin miji da kuma hakkokinsa a kanta, sannan tana kara koyar da ita dabarun zaman gidan miji, tana ta koya mata abubuwa dai kala kala, haka suka raba dare har wuraren karfe 2 suna hira na tsakanin uwa da Æ´a, sai da mum É—in ta ce yanzu kam su yi barci, tun da da asuba jirginsu zai É—aga.
A gado É—aya suka kwanta, sai dai ita dai Rimsha bata yi barci ba, saboda tunanin Lion, haka zalika shi ma bai yi barci ba, ya kasa iya yin barcin ba tare da ya ji muryarta ba, ya kira gwaggo kuma ya kasa iya tambayar ina take a bata su yi waya, saboda jikinsa yana bashi cewa fushi take yi da shi, so yasan ba lallai ta yarda ta yi waya da shi ba, shiyasa ya daure bai tambayi ina take É—in ba, ya bari kawai gobe ai zata zo har in da yake.
A takaice dai dukkansu haka suka kwana cikin kunci, sun kasa yin barci har aka kira sallar asuba. Suna yin sallah kuma su Abban Imran suka zo rakasu zuwa airport, ansha koke koke kam kamar babu gobe, shi dai Areef sai binsu da kallo kawai yake yi, wani maganar ma da Hausa suke yi, shi kuma baya ji, dan haka sai ya zama É—an kallo shi da Tga.
An jima ana koke koke da sallama da juna tun daga gida har airport kafin su wuce zuwa cikin jirgin, Abban Imran É—in Areef ya dankawa makullan gidan Lion É—in, suna tsaye suna kallonsu har sai da jirgin ya É—aga, sai Allah ne kuma yasan yaushe zasu sake ganin juna, Dr Salman da Brr Naurat ma da su aka wuce, dan Lion ya ce lallai dole su dawo U.s, dan yana da bukatar ganin kakanninsa a kusa da shi, hakan yasa suka wuce da su, Abban Imran ya so a bar mashi iyayensan a nan ya kula da su, amma ba yadda ya iya, dole ya hakura aka tafi da su.
Tun da jirginsu ya tashi Rimsha ta gyara kwanciya a jikin gwaggo ta hau zuba barci abinta, kamar wata mai ƙaramin ciki, ita kuwa Jehan babu kunyar kowa ta zauna kusa da mijinta, har da kwantowa a jikinsa tana shaƙar kamshin perfume nasa, Akila sarkin waya, dole dai ta hakura ta kashe wayar tata sai sun isa, Tga sai kallon Aafia yake yi tamkar wadda aka bashi gadinta, sauran sojoji biyu da suka rage a gidan wanda da su za'a koma kuma, suna kujerun can baya suna zaune abinsu, shi ma Alex yana a tare da su, mummyn Rimsha tana zaune kusa da Brr Naurat, ta sunkuyar da kanta kasa shiru, ita kuma Aafia sai satar kallon Tga time to time take yi, Maryam da Adiva suna a kujerun da yake a kusa da sojojin nan, kasancewar suna sume, sai aka ɗan kwantar masu da kujerun kaɗan, akwai wani part na rufe karnika a cikin jirgin, so a ciki aka rufe su copper, wayyo sun yi wa Nigeria bye bye suma, Aafia bata yi sallama da Ummin Dr Nawid ba, basu ga juna ba, saboda idan baku mance ba Ummin tana Katsina baiwar Allah, bata san zasu tafi ba, da alama kuma su Abbi sun sha'afa ne basu sanar da ita ba.....................
To fatan mu dai Allah ya sauki wannan ahali lafiya a cikin garin Washington,