← Book details Triplets Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 137 OF 168

Sashe 137

Triplets Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jinjina kai ya yi yana faÉ—in. "To Lion a goge dukka fa".

Sumbata a kumatu kawai Lion É—in ya kai mashi kafin ya mike ya sauko kasa daga saman bed É—in, sannan ya riko hannun Rimshar suka nufi waje ba tare da ya bari Aseef É—in ya kalleta ba, dan idan ya kalleta tabbas amai zai yi ta sake fara kwarara masu.

Suna fita bedroom nasu suka koma, shi kuma Aseef ya tashi ya nufi toilet dan ya yi wanka kamar yadda Lion É—in ya faÉ—a masa.

A ɓangaren gwaggo kuwa, abu ne da kuka sani, wato kwararriyar likita ce, ta yi wa Jehan aiki cikin nasara, sai dai Jehan ɗin bata farfaɗo ba har safiyar yau ɗin, Areef duk hankalinsa a tashe, duk ya yi wani iri da shi, dan ma sir Arvin yana kwantar mashi da hankali ne, da abin sai ya fi haka, da alama sir Arvin da Areef jikinsu yafi haɗuwa sosai kamar yadda Lion yafi kusa da Aseef, idan baku manta ba Lion ya fi kusa da Aseef sosai, shi ne pleasurensa, to shi ma Areef yanzu sun fi kusa da sir Arvin, sai suka zamana kamar twins twins guda biyu kowa da ɗan uwansa da suka fi shakuwa.

Lion yana shiga bedroom nasa ya ɗauki wayarsa ya kira Areef a kan ya zo su san abin yi a kan Akila, dan shi gaskiya ba zai iya ganin Aseef a cikin damuwa ba, kuma bai kamata su sanya mata chemical a jiki ba, domin ba ƙaramin aikin Aseef ɗin bane ya zauna ya yi ta yi masu kukar da babu karshe idan suka sanya mata chemical, so gara dai kawai su san abin yi. Ita kuwa Rimsha saman bed ta haye ta kwanta, dan dama har yanzu cikinta yana yi mata ciwo, bata gama komawa dai'dai ba duk da period ɗin nata ya zo, dan haka sai ta koma ta kwanta, luf ta lume a cikin bargo tana tunanin rayuwar da suka yi a gidan su Kausar na Ilorin.

A tare sir Arvin da Areef suka shigo cikin É—akin, Lion yana zaune a gefen bed É—in kusa da Rimshar tasa yana tambayarta har yanzu tana jin ciwon cikin ne ya yi mata allura?. Make mashi kafaÉ—a ta yi a kan ita ta ji sauki bata son allura, a haka su sir Arvin suka shigo suka samesu gwanin birgewa.

Saman bedside drawers na gefe da gefen bed ɗin suka zauna. Ba ɓata lokaci Lion ɗin ya sanar da su cewa ga abin da yake buƙata a kan Aseef da Akila, koma ta halin yaya ne a goge wannan ƙunshi ba tare da an jimata ciwo ba.

Sir Arvin ne ya ce wannan ai mai sauki ne, zasu fita da ita, dole za'a goge shi, tattoo ma aka goge bare lalle?. Areef kuwa guntun murmushi ya saki kafin ya ce da sir Arvin ɗin "A yadda kaga Lion haka Aseef yake da bala'in kishi, sai dai mu fita da ita bai sani ba, amma idan ya sani, to wlh babu zaman lafiya, zai ce ba za'a kaita wasu su kalla mashi ita ba, shi fa yadda kaga Lion haka yake, banbancin kawai shi ya fi Lion saukin kai ne, kuma shi ma sabida abin da ya taɓa faruwa da brain nasa ne, bacin haka wlh da babu in da zai baro Lion a komai da komai, to yanzu dai zamu fita da ita ba da saninsa ba kenan?".

Jinjina masu kai Lion ya yi yana faɗin. "Yeah na baku izinin ku ɗauketa a je a goge wannan abin, is better for me da na ga Aseef a cikin ciwo, koma ina zaku kaita lallai a goge wannan abin ba tare da bata lokaci ba, kada a bar komai ƙanƙantarsa a jikinta".

ÆŠan satar kallon Rimsha da ta basu baya ta lumshe idanu kamar mai yin barci Areef É—in ya yi, ganin alamar bata yi barci bane yasa ya yi shiru, da yaso ne ya ce da Lion É—in ya cika son kai dayawa a kan TRIPLETS nasa, wato a kai Akila duk in da za'a kaita, shi dai kawai a goge wannan abin dan Aseef ya samu lafiya, kai Lion duniya, a kan TRIPLETS nasa babu abin da ba zai aikata ba. Shiru ya yi dan kada ya faÉ—i hakan ya tadawa da Lion É—in tarzoma, sabida idan Rimsha ta ji hakan dole zata saka shi a gaba da cewa baya sonsu da gaske dama, bazata yi la'akari da cewa Akilar ma causing É—in su Lion É—in bace, dama Rimsha ai sarkin rigima ce, shiyasa Areef É—in ya yi shiru.

A kan haka suka tsayar da matsaya Areef and sir Arvin suka wuce suka fita. Suna fita basu zame ko'ina ba sai ɗakin su Akila ɗin, tana ƙudundune a cikin bargo ita ma.

Kasancewar su Areef ne suka zo yasa ta miƙe zaune da kyar, kanta na wani sara mata sosai sabida ciwo, ta ɗaga masu gaisuwa cikin girmamawa. Sorry suka yi mata tare da ce mata ta tashi ta shirya su tafi, bata tambayesu ina zasu je ba, kawai ta hau yin shiri abinta, jiki duk babu kwari, su kuma suka fice daga cikin ɗakin zuwa parlourn dan su bata damar shiryawa.

After some minutes ta fito cikin shirin doguwar riga, kallo ɗaya zaka yi mata kasan cewa bata da lafiya, duk tana wani firgice, ga idanuwa duk sun faɗa. Sai da Areef ya sake leƙa Jehan kafin ya fito suka tafi. Har lokacin Jehan ɗin bata farfaɗo ba.

Bayan sun kaita an goge mata ƙunshin tas, a hanyarsu ta dawowa sai suka biya asibiti suka duba su Adiva. A nan ne Dr yake sanar da su cewa Maryam an cire mata kodarta guda ɗaya ne, shi ne ya hassasa mata wannan ciwon, Allah ma yasa tana da ragowar shan ruwa a gaba, kuma sun yi ƙoƙarin wajen miƙata ga kwararun likitoci cikin lokaci ne, basu bari lokacin ya ƙure masu ba, sannan abin da yasa ta yi ta wannan ciwo da aka cire mata kodar tata, ba'a bata kulawar likitoci ba, ana cirewa aka barta ba wani cimar kirki, dan ma likitan da ya cire mata kodar kwararren likita ne, da wlh mutuwa zata yi. Ita kuma Adiva sai dai su danganata da wajen malamai, dan su dai a asibitin nan sun gama nasu, kuma bawani ciwon kirki wanda ya isa ya sanyata doguwar suma da suka gani a tattare da ita, ɗan crash ne, kuma sun yi treated nata, sai dai har yanzu bata da niyar motsawa ma bare ta farfaɗo, kamar babu rai a jikinta, so wannan sai an haɗa da malamai, dan da alama tsafi aka yi da ita.

Areef É—in ne ya tambaya ba dai dukkansu suna raye ba?. Tabbatar mashi da suna raye likitocin suka yi, sannan suka kara masu da cewa ita Maryam ai zata iya yin rayuwa da koda guda É—aya, babu wata matsala, sai dai an cucuta ne, duk wanda ya yi sanadiyar cirewar kodar nan tata ya yi mugu mugun cutarta a rayuwarta.

Shiru Areef ya yi yana tunanin kalar azabar da zai ganawa Hjyr daÉ—i idan ya kamata, sai ta gwammaci dama bata zo duniya ba.

Sallama suka yi wa Drs É—in, suka É—auki Adiva zuwa wajen Shaikh Sultan, suka bar Maryam a hospital É—in dan a cigaba da bata kulawa ta sami lafiya sosai da sosai.

Suna miƙa Adiva ga Sheikh Sultan ya gane menene matsalar tata, dan haka sai ya hau aiki, su kuma suka wuce gida da Akila.

A saman table na cin abinci suka isko gabaÉ—aya familyn ban da Jehan and Aseef, su basu da lafiya, basu fito ba, Jehan ma bata farfaÉ—o ba har yanzu, Aseef kuma É—aki Lion yasa aka kai mashi nasa breakfast É—in, amma kowa yana waje, yau ba'ayi breakfast da wuri ba, almost 10 yanzu, sai lokacin zasu yi breakfast.

Saman table ɗin suka haye suma, bodyguards ɗin ne suka fara yin serving nasu ba tare da ɓata lokaci ba. Kaɗan Areef ya ci abincin ya miƙe ya bar wajen, sabida baya jin daɗin jikinsa, hankalinsa yana a kan Jehan, yana barin dining room ɗin ma part nasa wajenta kenan ya nufa, dan ya duba jikinta bawan Allah.

Sir Arvin ne ya sanar da daddyn Rimsha halin da ake ciki dan gane da Adiva da kuma Maryam, addu'a sosai jama'ar da suke a saman table ɗin suka yi masu kafin daddyn Rimshar ya ce. "Arvin da kai da Alex tun da yau Friday, zamu wuce masallaci a tare da ku dan ku karɓi kalmar shahada".

Okey uncle sir Arvin ya ce, shi kuma Alex ya ce Okey brother, dan idan baku mance ba shi daddyn Rimsha yayansa ne uwa É—aya uba É—aya, dan haka da Yaya yake kiransa.

Shi dai Lion suna cin abinci ma idanuwansa da hankalinsa yana a kan Rimsharsa, sai faman shan ice cream take yi, sam baya son ya yi mata magana a cikin mutane, amma wannan ice cream ɗin da take sha har cikin ransa yake jin hakan, sabida yasan a wani hali take ciki, tana period ne, ga ƙasarsu da bala'in sanyi sosai, shan abu mai sanyi yana da matuƙar illah a gareta a yanzu, ga shi taki ɗagowa bare su haɗa ido ya hanata sha, daga karshe da ya ga ta shanye zata ɗauki wani, sai ya ce mata "It's okey, kada ki sake ɗaukar wani, momma ku zuba mata tea mai zafi sosai ta sha".

Binta da kallo kowa da yake a saman table É—in ya yi, shi kuwa Lion ya sha kunu ya murtuke kamar ba shi ya yi magana ba, dan baya son ra'ini.

Turo baki ta yi, dan tana son kara wani ice cream É—in, sam bai isheta ba, shegen daÉ—i ne da shi, amma kuma bata isa ta ce zata kara ba, idan ta yi gigin yin hakan zata ci duka a hannun daddynta ma ba Lion É—in ba, dan tun da suka ji Lion ya hanata sha, to sun san ba haka kawai ba, akwai dalili.
Chapter 137 · 0% Book details