← Book details Triplets Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 168

Sashe 47

Triplets Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Su kuwa bayan sun dira a cikin gidan, kai tsaye kofar da zata sadasu da babbar palon gidan Lion ya nema, babu tsoro ko É—arÉ—ar a tattare da shi, kai tsaye ya shige cikin gidan, kamar gidansa ne, yana shiga har da kunna wutar palon, dan ya gani ko suna aiki, sai dai a ganin sojojinsa ne suke ganin ya kunna wutar ne dan yaga ko suna aiki, shi kuma akwai dalilin da ya sanya ya kunna wutar, kunsan baya abu haka kawai, sai da dalili.

Yana kunna wutar ya nufi wata É—aki da take fuskantar kugu maso gabas, tsohowar É—aki ce sosai, dan da alama a kaf cikin gidan, É—akin ce kawai ba'a buÉ—e kofarta, saboda kofar ta kama sosai. Har lokacin idanun Queen na'a kansu, ta kuma cire duk wasu matakan tsaro na koforin dake gidanta wanda zai sadasu da cikin Daular Mutuwar, ma'ana ta buÉ—e masu hanya kenan, jira kawai take yi su shigo. Su kuma bayin Allah, sam basu sani ba, babu wanda ya kawo wa ransa cewa Queen É—in tana kallonsa, É—an gara Lion É—in ma, shi dama yasan matsafan nan babu abin da ba za su iya yi ba.

Yana isa wajen kofar, babu tsoro bai yi wata wata ba ya kai hannu ya murɗa handle ɗin kofar, nan take kofar ta buɗu, ganin ta buɗe ne yasa ya gane cewa lallai akwai wata a kasa, dan wannan kofa ta jima a rufe, bai kamata ace daga ya ɗan taɓata ta buɗe ba, dole da akwai wata a kasa, ga shi kuma gidan babu mutane ma, tun daga nan ya fara zargin wani abin a ransa, sai dai bai nunawa sojojinsa da alamar matsala ba, saboda kada ya sare masu gwiwa, ita kuma Queen bata taɓa tunanin cire makullan kofofin da ta yi zai iya sanya Lion ya fara zargi ba, bata kawo haka a ranta ba ,dan bata san kaifin basirarsa da kwakwalwarsa ba, sai dai hakika ta jinjinawa jarumtarsa, musamman yanda ya shigo mata gida kai tsaye, ya kuma nufi wannan kofa babu ko tsoro a ransa, yana acting tamkar shi ya gina mata gidan..........

(ni kuwa na ce in dai lion ne fin haka ma zai yi, shi gida nawa ma ya shiga ya nuna masu izza tamkar shi ya gina masu gidan? ya kuma aikata abin da zai aikata ya fito lafiya lou, ya shiga gidan Abba tamkar gidansa, ya je ya ɗauki Akila, ya kuma ɗaura mata aure da Aseef, sannan ya taka kafarsa har kasar Russia, ya je ya ɗauko Brr Naurat, su ma ya shiga gidansu tamkar shi ya gina masu, har ma da ɗaure gabadaya ƴan gidan ya yi, haka kuma ya fito kasar Russia lafiya lou, saboda tsantsar karfin hali da nuna isa, haka ya shiga gidansu Rimsha kamar gidansa, ya ɗaukota ya fito, ai shi Lion dama dai'dai yake da kowa, ko ya kuka ce READERS? Yanzu kuma ga shi a gidan Queen of Daular Mutuwa, kamar gidansa ya shige😂 Queen taga iko da nuna isa😂)

Cikin É—akin suka shiga, gabaÉ—aya cikin É—akin babu komai, wayam yake, sai lallausan carpet na alfarma dake sumfuÉ—e a cikinta. Zuba masu shegun idanunta Queen É—in ta yi ta cikin ruwan tsafinta dake kwance a tsakiyar faÉ—arta kamar pool, sai kallonsu take yi, tana son ganin gudun ruwansu. Areef dai yana goye da uban jaka a bayansa, sai Allah yasan me ya lodo a cikinta!.

Sai bin É—akin da kallo sojojin suke yi. Wani irin sihirtatcen kamshi ne ya fara tashi a cikin É—akin, shi dai Lion har cikin ransa bai yarda da wannan kamshi ba, dan haka sai ya ce da sojojinsa su sanya face mask a face nasu dan kada su shaki kamshin.

Bai kai ga rufe baki ba, nan take sojojin nasa suka fara zubewa kasa kamar gawarwaki, dama wannan kamshi wani tuggune da Queen É—in ta haÉ—a masu, ta ha kance kawai zata É—aukesu izuwa cikin Daular Mutuwar.

Lion kafin ya yi wani yunkuri shima sai ya ji gabaɗaya jijiyoyin jikinsa sun tsaya, nan take ya ji tamkar an sare mashi ƙafafuwansa, dole shi ma ya zube kasa, dan already dukkansu sun shaki wannan kamshin turaren.

Areef yana ƙoƙarin yin kan Lion ɗin, shima sai ji ya yi tamkar an raba kafafunsa da jikinsa ne, nan take ya zube kasa, duk suka zama kamar gawarwaki, ga dai idanuwansu a buɗe, amma sam jikinsu babu karfi, babu mai iya motsa ko da ɗan yatsansa.

Haka suka cigaba da shaƙar wannan daddaɗar hamshin duk wasu gaɓɓai na jikinsu suna mutuwa, har idanunsu ma ya rufe ruf, kamar babu rai a tattare da su.

An ɗauki tsawon lokaci suna a haka, har sai da yamma ta yi, rana ta faɗi, sannan ne Queen ɗin ta fara ɗaukar mataki a kansu. Wasu zaratan mazaje jarumai masu ji da lafiya da karfi Queen ɗin ta aiko, zu ashirin cif, haka ta aikosu aka kwashi su Lion ɗin gabaɗaya, ɗakin dai babu wata kofa bayan wanda su Lion suka bi suka shigo, daga ta sama waɗan nan zaratan maza suka ɓullo, haka kuma da suka ɗauki su Lion ɗin, suka bi da su ta saman suka fita, ɓacewa suke yi ɓat........ KAI QUEEN SHEGIYA CE, TA WUCI TUNANIN MAI TUNANI TUNKARARTA SAI AN SHIRYA.

Kai tsaye sai cikin Daular Mutuwar aka wuce da su Lion, basu san ta hanyar da aka bi da su ba, dan Daular Mutuwa fa a yanzu bata da hanyar shiga sam sam. BABBAR MAGANA TASHIN HANKALI DA BA'A SAKA MASHI DATE, SU LION ZA SU FITO KUWA?.

A takaice dai a wani killatatcen waje Queen tasa suka kulle su Lion ɗin, waje ne mai cike da abubuwan ban tsoro da juya kwakwale, ashe ita Rimsha a cikin kaso ɗari ko kaso ɗaya na bala'in da kuma ɓangarorin dake a cikin Daular Mutuwar bata gani ba, akwai abubuwa da dama sosai. Gabaɗaya su Lion ɗin an kasasu ɗakuna daban daban, ba'a haɗasu waje guda ba, da alama Queen ta fi tsanar Lion a cikin tawagar, shi wani waje na daban mai cike da tsaro na bala'i ta kai shi, babu wani abin da idanu zai iya gani a wajen, saboda tsananin duhu dake a cikin ɗakin, ta sanya sarka ta ɗaure shi, ko motsi baya iya yi. Su kuma sauran sojojin ɗakunan da aka kai'su da akwai haske, suna iya ganin komai, kuma bata ɗaure su ba, kawai an zubasu a saman tiles ne aka barsu.

Tsawon kwana biyu suna a sume, Queen kuwa tana ta harkar gabanta, bata bi ta kansu ba tukun nan.

A can gida kuwa, sai adduo'i ake ta yi masu babu kama hannun yaro, kowa hankalinsa a tsananin tashe sosai, Rimsha kam har da zazzaɓi take fama da shi, ko sallar dare bata iya tashi ta yi, saboda rashin lafiya, abin kamar ba lafiya ba, sam ta kasa yi wa Noorish ɗin nata addu'a, ta zama tamkar kurma, ciwon nata ma akwai ayar tambaya a kansa, dan fa ko kallonta mutun ya yi sai ta daka mashi tsawa, ta zama tamkar ba ita ba........

Wannan shi ne abin da ya faru a cikin kwanaki biyun da suka wuce, dan haka mu koma kan story.

Yau shi ne kwana na uku na kasancewar su Lion a Daular Mutuwa, sai a yau kuma Queen ta waiwayesu, a in da ta fara yi masu ɗauki ɗai'ɗai tana bawa dodan tsafinta, wayewar garin yau, ta kashe sojoji biyu daga cikinsu, kafin ta kashe su kuma, sai da ta dawo masu da hankulansu jikinsu cif, a kan idanunsu tasa aka ɗauresu, suna ji suna gani ta sanya aka fasa cikinsu, ta ɗebi abin da zata ɗeba, jininsu kuma kamar yanda kuka sani ne, an kaiwa dodan tsafi, sauran sassan jikinsu kuma tasa aka wuce da shi izuwa wajen da suke kulla harkokinsu da sauran gidajen matsafa dake a duniya, dan ta sayar masu da abubuwan da suke buƙata daga ciki....... Innallilahi wa Inna ilahirrajiun, ya ilahi ya lillahi, wannan musifa dame ta yi kama?.

Mutun na uku a yanzu shi ne a kan layi da za'a kashe, ba kowa bane kuma face Areef na Jehan, shi Lion ma sai Allah ne kaÉ—ai yasan halin da yake a ciki, shin yana raye ne ko ya mutu?.

ÆŠakin da Areef É—in yake kwance yana sume suka nufa, babu Queen É—in a cikinsu, waÉ—an nan zaratan kyawawan matasan igbo É—in ne, sune masu aiwatar da komai, ita Queen idan an gama fasa cikin mutun, da tsafinta take É—aukar abin da take so dan gane da sassan jikin wanda aka kashe, a takaice dai, ita bata fitowa, komai tana daga cikin faÉ—arta take aiwatarwa.

Kamar yanda suka kwantar da Areef É—in tun ranar da suka kawo su, haka suka zo suka same shi, bawan Allah, ko motsawa bai yi ba.

Turo wannan gadon da suke yanka mutun a kai ɗin suka yi izuwa tsakiyar ɗakin. Zaratan maza biyu ne suka ɗauko Areef ɗin, suka kwantar da shi flat a saman bed ɗin, sannan suka zura hannayensa a cikin lock na bed ɗin, suka rufe, ta yanda ko an dawo mashi da hankalinsa, ba zai iya yin yunkurin komai ba, haka kafafunsa ma suka zurata a cikin lock suka datse gam. Sannan ɗaya daga cikinsu ya fito da wata sharɓeɓiyar wuka, sai kyalli take yi, har wani ɗaukar idanu take yi, ga kaifin bala'i, dama su shidda ne zaratan mazan, da mai rike da wukar sun haɗu bakwai dai'dai kenan.

Tsayuwa suka yi shiru a kan Areef É—in suna jiran Queen ta dawo mashi da tunaninsa, dan bakar zalinci da mugunta, sai mutun yana cikin hayyacinsa ma suke yin duk abin da za su yi, yana ji yana gani babu yadda ya iya da su, a da can baya, sai sun gusarwa da mutun hankali suke yanka shi, yanzu kuma tun bayan fitar su Rimsha suka kawo sabbin tsare tsare da wasu abubuwa na tsubbace tsubbacensu.

Cikin Æ´an sakannin da basu fi 30 ba, sai ga Areef É—in ya buÉ—e ash eyes nasa, tamkar wanda aka tasa daga barci, idanuwansa sun kumbura sosai, saboda kwana biyu yana sume.
Chapter 47 · 0% Book details