← Book details Triplets Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 117 OF 168

Sashe 117

Triplets Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*KINDADE KINA NEMAN ABUN DA ZAI SANYAKI QIBA,QIBA MEKYAU KIYI DIMIMI DUK INDA KIKA SHIGA BABU RAINI KINYI TA SIYA KINA ASARAR KUDINKI🤔
ALBISHIRINKI NAZO MIKI DA ABUN DA ZAKISHA BA TARE DA KINYI ASARAR KIDINKI BA 💃 Yana da matiƙar kyau sosai ko'ina naki zai chiko ki xama abar sha'awa duk mai buƙata ta nemeni ta wannan number 09067614054, kada ki bari ayi babu ke, kayanmu tested and trusted ne, guarantee ne*.

*KINDADE KINA NEMAN ABUNDA ZAI SANYA KISAMU XAMAN LFY TARE DA KWANCHIYAR HANKALI? TO BABYN HABIBI KIXO UMMU AFFAN TAXO MIKI DA SHAHARARRUN KUMA INGANTATTUN MAGUNGUNAN MATA, KAMA TUNDAGA KAN HUMRA, TURAREN WUTA,
INFECTION KILLER,
COLACCA,
SAI KAYAN GYARA PAGE.
KACA KACA.
YALLAGWADA.
JIGIDA.
RUWA RUWA.
BANI BANI.
WOMEN JELL BATA BATA.
DAFIN KAXA.
TANTABARA.
XABUWA.
CICCIƁI.
AND EXCLUSIVE, XUMA TASTED AND TRUSTED INA FARIN CHIKIN SANAR DA KU MUN FARA RAMADAN PROMO GAME BUQATA XA A IYA TUNTUBA NA TA WANNAN NUMBER
09067614054 JIGAWA STATE MUNA AIKAWA KO'INA CIKIN AMINCI DA YARDAR ALLAH,
BABYN HABIBI KARKIMANTA DA KAYANMU FIRST CLASS NE, DAGA KANSA AN RUFE KOFA, YANA DA INGANCI NA WUCE TUNANINKI*.

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥

https://whatsapp.com/channel/0029VaMOfZZI7BeKXPU9gK2S

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥

TSARAWA DA RUBUTAWA......✍️

❤️FATEEMA ZAHRA MUSA (💫PRINCESS TEEMA💋)

*Domin samun damar karanta littafin nan daga farko har karshe zaki iya nemana ta wannan number 08161390581*

Date: 22/5/2024

E37

ÆŠan zaro idanu matashin ya yi kafin ya basu amsa da cewa "Kai wannan waje fa ba wajen zuwa bane! Yana da uban nisa sosai daga nan, sannan kuma kungurmin daji ne sosai, zaku sha tafiya".

Kallon Jehan Areef ya yi, saboda da Hausa matashin ya yi magana, su kuma TRIPLETS kun san basa jin hausa ko kaÉ—an, so bai ji me guy É—in ya ce ba.

Mayar mashi da abin da guy É—in ya faÉ—a da turanci ta yi, sannan ta É—aura da cewa guy É—in ta ina ne hanyar da zasu je wannan waje?.

Kwatance ya yi masu ta hanyar, sai ka fita daga cikin Abujar, sannan ka sauka daga titi ka fara kutsawa cikin daji, sai sun yi tafiyar sama da awa guda kafin su kai wajen, a wajen akwai wani katon dutse mai aman ruwa, daga wajen wannan dutse nen wannan address É—in yake, tashin hankali!!.

Sake gayawa Areef É—in abin da guy É—in ya faÉ—a Jehan É—in ta yi. Shiru ya É—an zubawa guy É—in idanu yana tunanin to ya akayi guy É—in ya san da wannan waje kenan?. Kamar zai tambaye shi, sai kuma ya share, saboda mugaye a duniya dai ba zasu kare ba, sai dai kawai Allah ya yi mana tsari da su!.

Kunna motar ya yi bayan sun yi wa guy É—in godiya, É—aukar hanya suka yi babu kama hannun yaro, gudu sosai Areef yake shararawa kamar babu gobe, ita kuwa Hjy D.P.O lefewa ta yi a jikin kujerar motar tare da lumshe idanuwanta tana jin sanyin A.c na ratsa ta.

A ɓangaren su Lion kuwa, sun isha Washington DC lafiya, kasancewar ba tafiyar sirri bace, kamar yadda kuka sani ne airport ɗin a cike take tab da manya manyan jiga jigan masu faɗa a ji a kasar, ga jiga jigan sojoji ta ko'ina rike da jiga jigan bindigu masu aika sako babu saɓa saiti, suma ƴan'sanda ba'a barsu a baya ba, sun cike ko'ina suna shawagi, sannan ga ƴan jaridu rirrike da cameras a hannunsu ta ko'ina, jira kawai ake yi ya fito su fara aikin ɗaukarsa a hoto.

Sai dai kuma fitowarsa ta tada hazo mai matuƙar kurar gaske, dan kuwa ya fito ne ɗauke da sir Arvin a saman kafaɗunsa, wadda kuma kunsani kamansu ɗaya sak, wasu daga cikin mutanen dake a airport ɗin ma sun kasa banbance Lion na gaskiya, wasu su ce shi aka ɗauko a saman kafaɗa, wasu kuma su ce shi ne ya ɗauko wani mai kama da shi. Kan kace me magana ta karaɗe kasa bakiɗaya, kowa so yake yi yasan wanene ɗayan? Sai dai kuma an rasa mai iya tunkararsa ya tambayesa wanene sir Arvin? Abin da kuka sani ne, kowa tsoronsa yake ji.

Aseef dake cikin mota yana jiransu ma bai san time da ya fito waje daga cikin motar ba, saboda sir Arvin, sam Lion bai gaya masu zancen sir Arvin ba, ko Areef yaki sanarwa, kai har gwaggo bata sani ba, ya barsu ne sai ya dawo gidan kawai suga zahiriya da idanuwansu, so abin ya girgiza Aseef sosai, ya kasa hakuri ma har sai da ya tambayi Lion É—in wanene sir Arvin?. Jama'a duk sun kasa kunne dan su ji amsar da Lion É—in zai bada, duk wasu Æ´an siyasa dake a wajen burinsu kenan su ji amsar da zai bada. Sai dai kuma kamar yadda kuka sani ne ko kallon Aseef É—in ma bai yi ba bare ya amsa mashi, ya wuce kawai ya kwantar da sir Arvin a cikin mota, sannan ya shiga gidan gaba.

Da dai Aseef É—in yaga da gaske ba zai amsa mashi ba, sai ya daure ya juya ya nufi motar, sai dai bai kai ga shiga ba su Handsome suka fito daga cikin jet É—in, bodyguards na Lion É—in suna a biye da su a baya.

Da sauri Aseef ya kara zaro idanuwa yana kallon Handsome mai kama da shi, ba shakka Handsome ya yi kama da shi, sai dai ba cancan sosai ba, kama ce dai ta jini, amma Handsome ya fi kama da jinin Chinawa, bai yi zubin Americawa sosai ba.

Gabaɗaya jama'a haɗe da Aseef ɗin basu gama tsinkewa ba sai da suka ɗaura idanuwansu a kan Pinky dake rike da hannun Handsome gam, yarinya kyakkyawar gaske kamar ita ta yi kanta, ga shegen shiga rai kamar Rimshar Lion, sannan babbar abin rikitarwa shi ne kama da su Lion ɗin da take yi, kunga kuwa dole ta yi kyau iya kyau ai, saboda wannan kama, ga idanuwanta dara dara kamar nasu, kuma idanuwan blue eyes, ya kuke tunanin kyanta zai kasance? Kama da Lion fa aka ce maku, ai dole nema kowa idan ya kalleta sai ya sake kallonta, mummynta ta ɗaure mata kyakkyawar gashin kanta gida biyu, an zuba mata rebons masu flowers, sai gashin ya yi matuƙar kyau, ga shi dark black, sai kyalli yake yi, sai dai bai kai nasu Lion curly ba.

Kai tsaye wajen sauran motocin dake a bayan na Aseef É—in suka nufa. Sai da suka shiga ciki, sannan ne Aseef É—in ya iya shiga cikin motarsa shi ma, banda haka ya tsaya ne yana kare masu kallo, ga Dr William a tare da su, sai ya ji tamkar ya je ya tambayi Dr William É—in cewa shi ne na gaske ko? Kada a sake ra'ina masu hankali, amma ganin yadda airport É—in yake cike da mutane, kuma kowa jiran kiris yake yi a saki magana wa duniya, hakan tasa ya ja bakinsa ya yi shiru tare da komawa cikin mota zuciyarsa cike tab da mamakin wannan al'amari.

Bayan sun kammala shiga ne motocin suka tashi a tare, jama'a kowa bakinciki yake yi na rashin buÉ—e bakin Lion ya yi magana ko da word É—aya ne, kowa so yake yi ya sami abin faÉ—a, sai dai Lion ya wuce tunaninsu, shi ko a gida ma yaushe yake buÉ—e baki ya yi magana balantana a wajen, wajen ma a airport, a airport É—in ma wajen da yasan abokan hamayyarsa suna wajen, bugu da kari ga siyasar da yake a gabansa, ai dole ma su datse bakunansu dan samun zaman lafiya, in ba haka ba yanzu sai a canza masu magana idan suka yi, saboda mutun É—an adam ya wuce tunanin mai tunani!!.

Su Cherish sun ga duniya a lokacin da suka sauke idanuwansu a gidan Lion, sai suka ga nasu gidan ma ashe kurkuku ne, su suna jin cewa su masu kuÉ—i ne, ashe ga nan in da kuÉ—in kam yake, su nasu ma duk wasan yara ne! Gidansu ko kwatan na Lion É—in bai kai ba a girma, kyau da kuma tsaruwa, komai ma basu haÉ—a hanya ba, Lion ya yi masu nisa, dan ma sun yi sa'a sun zo a time da ya kwashe gabaÉ—aya sojojin an mayar da su barack, ai da sai sun san cewa yes nan fa gidan General of the Army's suka zo, a yanzu kuma His Excellence mai jiran gado, kai gaskiya Lion duniya ne, His Excellence ne mai jiran gado da kansa!.

Kauyanci ne karara ya bayyana a fuskokinsu, dan wasu abubuwa da suke cikin gidan Lion sam basu taɓa ganinsu ba, tun daga kan tsarin ginin gidan sun san Daula ce mai zaman kanta, sun san ba wajen wasan yara bane, Handsome dai sai kalle kalle yake yi abinsa, ba zai bari kansa ta kulle ba, duk abin da ya yi mashi kyau sai ya kallah ya sake kallah, ita ma Pinky sai kallo ko'ina take yi, idan ta ga wani abin da bata taɓa gani ba, sai ta tambayi Handsome menene wannan? Shi ma sai dai ya ce mata bai sani ba ta bari anjima zai tanbaya mata sir Arvin idan ya tashi daga barci, Okey kawai take amsa mashi da shi.

Basu kara tsinkewa da lamarin wannan Daula ta Lion ba har sai da suka shiga parlourn kasa, a nan ne suka zama ainahin Æ´an kauye.

Shi kuwa Lion kai tsaye saman doguwar sofa ya wuce ya kwantar da sir Arvin ɗin, sannan ya buƙaci Aseef da ya bashi ruwa. Cike da mamaki Aseef ya wuce ya ɗauko mashi ruwa roba guda, kawo mashi ya zo ya yi, bayan ya karɓa sai ya tsaya a gefensa yana kallon wannan iko na Allah.

Su Pinky kuwa har tsoron zama a saman sofas ɗin suke yi, saboda yanayin yadda tsaruwan sofas ɗin suke, sun sha banban da sofas da kuka sani, idan ka gansu ma kai kace wasu jiragene, saboda wasu irin luntsuma luntsuma ne masu numfashi, sun ƙoshi ainun.

Shafawa sir Arvin ruwan ya yi. Ajiyar zuciya bawan Allah ya sauke, sannan ya fara É—an motsa idanuwansa da suke a rufe a hankali hankali. Ganin ya farfaÉ—o ne yasa Lion É—in ya mike daga kusa da shi ya koma saman wata sofar, zama ya yi tare da ciro wayarsa ya kunnata, dama ya yi off nata ne, saboda tafiya.
Chapter 117 · 0% Book details