← Book details Triplets Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 103 OF 168

Sashe 103

Triplets Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A ɓangaren su Lion kuwa, a wannan dare dai sun yi barci cikin rashin daɗi daga shi har Rimshar, washegari da safe misalin karfe 9 na safe, shirye cikin tsadaddun kaya iri ɗaya Lion da Areef suka fito, komai na jikinsu iri ɗaya ne, sai suka fito a ainahin TRIPLETS nasu, harta black glass da yake a face nasu iri ɗaya ne, idan ba ka lura da kyau ka ga gashin kansu ba, to ba zaka iya banbantasu ba, saboda jini ya wuce wasa, sai kuma Lion ya fi tsawo da cika.

Sun yi matukar kyau na wuce misali, bedroom na daddyn Rimsha suka fara shiga. Jim kaɗan suka fito suka nufi bedroom ɗin Aseef. Yana ta zuba barcinsa, zuba mashi idanu suka ɗan yi suna kallonsa, bawan Allah yana sanye cikin tsadaddun kayan barcinsa, riga ce da wando launin ash color, ya yi matuƙar kyau, yana rungume da pillow a kirjinsa, da alama dai hira da Heartbeat suke yi barci ta yi awon gaba da shi.

Saman bed É—in suka hau kusan a tare, sumbata Lion ya fara kai mashi a saman lallausan kumatunsa kafin ya kai hannu ya É—aga mashi wayarsa da take a kusa da kirjinsa, juyo da screen É—in wayar ya yi izuwa face nasa, har lokacin call É—in bata yanke ba, da alama ita ma Akilar ta yi barci ne suka bar wayar a kan call.

Katse kiran ya yi tare da ɗaura wayar a saman bedside drawer yana mamakin halin Aseef, shi dai soyayya kawai abinsa, bashi da wata damuwa a rayuwarsa, baya tunanin matsalar kowa da komai, baya ajiye wata damuwa a cikin ransa, kawai harkar gabansa na hira da Akila su kashe juna da love shi ya sa a gaba.........(😂 Allah ya yafewa Aseef ya shirya mana shi😂)

Sumbatarsa Areef É—in ma ya yi a saman jajir É—in kumatunsa dai'dai in da Lion ya sumbacesa, sannan suka diro kasa daga saman bed É—in a tare. Fitowa suka yi suka nufi harabar gidan mai gabaÉ—aya.

Already anfitar masu da motoci anjerasu layi biyu dan zuwa airport, tsayuwa suka yi a harabar gidan, sannan suka juyo suna fuskantar juna gwanin birgewa.

Areef ne ya fara magana cikin nutsuwa. "Please Lion idan ka sauka ka kira Rimsha a waya, ina son ka san abu guda, Rimsha tana sonka ne yasa ta damu da kazo in da take, idan ba tana sonka ba wlh ba zama ta damu da tafiyarka ba, kayi tunani da kyau, she love you over and then su mata ƴan a lallaɓa ne, ita fa Rimsha ma ka yi sa'a tana da hankalin manya, banda haka da wlh yarinya under 15 ba zata iya ɗaukar abin da Rimsha ta ɗauka ba, wata ma mai 30 years idan ta zuba maka wata shirme Allah sai ka ji kamar ka kasheta dan haushi, kuma serious ka sani ko mace mai 30 years ba zata iya ɗaukarka ba, amma duk zafin zuciyarka Rimsha ta danne, tsawon shekaru tana azabtuwa a kan sonka! Kasan da haka, and then ka duba abin da ya faru a tsakaninku 30 days back, a gaskiya ta yi mugu mugun ƙoƙarin da baki ba zai iya faɗa ba, now kaga bata da lafiya, please kada ka kara mata ciwo a kan ciwo, wannan mu zaka yi wa ba kanka ba, idan wani abin ya sameta ba zamu iya jurewa ba, please ka yi tunani a kan maganar". Ya kai karshen maganar yana ƙoƙarin ciro wayarsa daga aljihunsa.

Matsowa Lion É—in ya yi suka rungumi juna kawai ba tare da ya yi magana ba, sumbata Areef É—in ya kai mashi a kumatu kafin shi ma Lion É—in ya sumbacesa. "Take care". Shi ne kawai abin da Lion É—in ya furta tare da sakinsa ya wuce izuwa wajen nasa jerin motocin.

Juyawa shi ma Areef É—in ya yi ya nufi nasa motocin. A tare motocin suka fice daga gidan.

After some minutes suka sauka a airport, jirgi daban daban suka shiga, Lion ya shiga jirgin kasar China, shi kuma Areef Nigeria zai je, amma da yake jirgin kasuwa ya bi, sai ya bi jirgin Spain, daga can zai hau jirgin Nigeria, shi kuma Lion da yake da nasa jirgin zai tafi, sai ya zama direct kawai zai nufi China, dama idan baku manta ba ya taɓa cewa Rimsha zasu je kasar China da ita, so yanzu yanayi yasa ba zai tafi da ita ba, kun ga dai halin da take a ciki, tafiya da ita ba zai yiwu ba, suna ma wajen daban daban da ba zai yiwu su tafi a tare ba, shi ne yasa ya wuce shi kaɗai. Shi kuma Areef zai je ya ɗauko su gwaggo ne gabaɗaya, Lion ya ce duk su tattara su dawo, shi ya sallami Nigeria kenan, ba zai sake komawa ba, so Areef ya je ya tattarosu su haɗu a U.s kawai nan da kwana uku zuwa biyar......... Babbar magana, akwai aiki kam!!.

After some hours.

Lafiya lou Lion ya yi landing a Daxing international airport Beijing dake a South Beijing É—in. Da yake shi da wasu daga cikin bodyguards nasa kawai suka zo, sai ya ce da bodyguards É—in su fita su nemi hotel su zauna a ciki yana zuwa, idan ya kammala abin da yake yi zai nemesu, ya yi maganar tare da sanya face mask a face nasa, sannan ya fito daga cikin jirgin bayan.

Yana fita kai tsaye wajen masu taxi ya nufa da yake a wajen airport ɗin, kun san kasar China da abin hawa kala kala, wata ma sai ka saki baki ka ɓata lokaci kana kallonta, sam su basu gajiya da kere kere, Allah ya yi masu fikira da basira ne over.

Wata kyakkyawar taxi ya hau, kai tsaye address na *GOLD CROSS HOSPITAL (GCH)* ya ce a kaisa. Su kuma bodyguards É—in nasa suka fito tare da trolleynsa suka nufi waje dan su je su aiwatar da umarnin da ya ce masu su yi na neman hotel.

Lion baka gane gabansa baka gane ina ya dosa, yanzu duk rikicin da tarzomar da ya haÉ—a a U.s ya tashi kura, hakan bai hana shi ya shiryawa kansa zuwa kasar China kamar yanda ya yi niya a baya ba, yana da karfin hali sosai, komai zai aikata yana aikatawa ne cike da kwarin gwiwa É—ari bisa É—ari tare da yakiyi da kuma sanyawa a ransa tabbas zai yi nasara, ba komai ne yasa hakan ba kuma face rike Allah a zuciyarsa da ya yi, komai zai yi Allah yake fara sakawa a gaba, shi ne yasa yake samun kwarin gwiwar na cewa zai yi nasara a komai, kuma ya yi gaskiya, duk wanda ya saka Allah a gaba, to babu abin da zai hana shi yin nasara, babu wata barazana da zata tsorata shi, babu wata shamaki da zata gifta a tsakaninsa da nasararsa, shiyasa a koda yaushe TRIPLETS namu suka zamana masu yin nasara a rayuwarsu!! Allah ka bamu dacewa.

Kafin ya tako kafarsa a cikin ƙasar China, sai da ya shiryawa kansa komai da komai, harta in da zai je sai da ya nemo address, ya jima yana bincike a kan Cherish, tun lokacin da ya gano cewa an canza ɗaya daga cikinsu, idan baku manta ba tun bai zo U.s ya ji gaskiya a wajen kakansa ba ya yi maganar zuwansa kasar China ya nemo Cherish, so tun a lokacin ya fara bincike a kanta, duk wata hukunci da ya yanke har da shiga siyasa da ya yi, duk basu hana shi yin binciken nasa ba, dama after primary election ya tsara zai shiga ƙasar ta China, to shi ne ya cika abin da ya tsara a yau.

Yau dai ga mai kama da Arvin a cikin Beijing, ga kuma shi ma Arvin É—in a nan, dama yana cewa zai je U.s ya haÉ—u da mai kama da shi, za su haÉ—u ko ba za su haÉ—u ba? Idan sun haÉ—u ya haÉ—uwar zata kasance?..... PRINCESS TEEMA ce kawai zata iya gaya maku wannan amsa!!.

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️❤️🔥

*KINDADE KINA NEMAN ABUN DA ZAI SANYAKI QIBA,QIBA MEKYAU KIYI DIMIMI DUK INDA KIKA SHIGA BABU RAINI KINYI TA SIYA KINA ASARAR KUDINKI🤔
ALBISHIRINKI NAZO MIKI DA ABUN DA ZAKISHA BA TARE DA KINYI ASARAR KIDINKI BA 💃 Yana da matiƙar kyau sosai ko'ina naki zai chiko ki xama abar sha'awa duk mai buƙata ta nemeni ta wannan number 09067614054, kada ki bari ayi babu ke, kayanmu tested and trusted ne, guarantee ne*.

*KINDADE KINA NEMAN ABUNDA ZAI SANYA KISAMU XAMAN LFY TARE DA KWANCHIYAR HANKALI? TO BABYN HABIBI KIXO UMMU AFFAN TAXO MIKI DA SHAHARARRUN KUMA INGANTATTUN MAGUNGUNAN MATA, KAMA TUNDAGA KAN HUMRA, TURAREN WUTA,
INFECTION KILLER,
COLACCA,
SAI KAYAN GYARA PAGE.
KACA KACA.
YALLAGWADA.
JIGIDA.
RUWA RUWA.
BANI BANI.
WOMEN JELL BATA BATA.
DAFIN KAXA.
TANTABARA.
XABUWA.
CICCIƁI.
AND EXCLUSIVE, XUMA TASTED AND TRUSTED INA FARIN CHIKIN SANAR DA KU MUN FARA RAMADAN PROMO GAME BUQATA XA A IYA TUNTUBA NA TA WANNAN NUMBER
09067614054 JIGAWA STATE MUNA AIKAWA KO'INA CIKIN AMINCI DA YARDAR ALLAH,
BABYN HABIBI KARKIMANTA DA KAYANMU FIRST CLASS NE, DAGA KANSA AN RUFE KOFA, YANA DA INGANCI NA WUCE TUNANINKI*.

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥

https://whatsapp.com/channel/0029VaMOfZZI7BeKXPU9gK2S

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥

TSARAWA DA RUBUTAWA......✍️

❤️FATEEMA ZAHRA MUSA (💫PRINCESS TEEMA💋)

*Domin samun damar karanta littafin nan daga farko har karshe zaki iya nemana ta wannan number 08161390581*

Date: 15/5/2024

E32

Dedicated to Halimatus Sadiya ƴar amanar Jehan ❤️ yau dai amanar Jehan page ɗin naki ne😂

A ɓangaren shi ma Areef ya sauka Nigeria lafiya lou, Tga ne ya zo airport ya ɗauke shi zuwa gida.

Sam Jehan bata san da zai zo ba, bata da labari, tana can tana fama da zazzabin sonsa kamar zai kasheta, amma taki sauƙa daga kan bakarta. Yana zuwa bedroom nasa ya wuce, duk da bashi da burin da ya wuce ya kalleta ɗin, amma kuma bai je in da take ba, sai ya wuce bedroom nasa.
Chapter 103 · 0% Book details