Sashe 165
Triplets Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Har suka ɓacewa ganinsu Iya da Kausar suna zube a saman gwiwowinsu suna aikin zuba godiya, iya har da kukanta da hawaye, dan ba kuɗin wasa Rimsha ta basu ba, idan zasu canza wannan kuɗi a kallah zai kai 5m, dan dollars ne, Lion bashi da wani kuɗin da ya wuce dollars, ga shi dama suna cikin halin babu, abinci ma idan sun sami na safe basu sa ran zasu sami na rana, sai ga shi yau Allah ya aiko masu Rimsha ƴar albarka ta zo ta basu kuɗin da basu taɓa tunanin zasu same shi ba a rayuwarsu, ai dole su yi kukan murna.
Suna barin unguwarsu Kausar kai tsaye airport suka nufa, dan su koma Abuja.
Su Akila kuma sun je Kaduna gidan Abbanta, a nan ne Ammienta take sanar da ita ɗan uwanta Duna ya dawo, ashe dama bai mutu ba, kuma ya musulunta shi ma, ya bar harkar tsafi, sannan ya gaya mata gaskiyar cewa Queen ba Mahaifiyarsu bace, yayarsu ce da suke uwa ɗaya uba ɗaya, dan haka ba Queen ce ta haifesu ba, sosai Ammien ta yi mamaki jin hakan, dama ita ta ra'ina girman Queen ɗin nan a ce uwarsu ce, ashe uwarsu ta mutu tun kanwar Ammien tana jaririya, kwananta uku da haifar kanwar Ammien ta rasu, Queen kuma ita ce babbar yayarsu, shi ne yasa ta rikesu tamkar ita ce uwarsu, dan ta girmesu sosai. Alhaji Mustapha mijin Hjy Zainab ma ya dawo, ashe bawan Allah yana a tare da Duna, tare suka gudu daga Daular Mutuwar lokacin da Queen ta yi ƙoƙarin kashesu, sun samu sun kuɓuta da kyar, sai dai ita Hjy Zainab kam ta mutu, Queen ta kasheta kamar yadda ta kashe Amarya matar Dr Salman, sai dai muce Allah ya sakawa Hjy Zainab kasheta da aka yi bada hakkinta ba, ita kuma Amarya dama mugun iri ce, sai dai muce masu hali irin nata su yi ƙoƙari su tuba su dai'na, ko kuma suma karshensu ta yi irin ta amarya ko fin haka.
Sosai Akila ta yi murna da jin cewa dan uwan mamanta Duna ya dawo, kuma ya musulunta, ko ba komai yanzu tana da uncle guda É—aya musulmi.
Sun je gidan Abbin Irfan ma, a nan Abbi ya sanar da Aafia cewa kidnappers sun sako kawarta Rufee ta dawo gida, shi ma last week ya samu labari, amma sun yanke mata kafa guda ɗaya, dan kafar ta ruɓe, da kyar ma suka sakota, dan sun mayar da ita parkarsu ce, bada aure ba suke kwanciya da ita, kuma ba mutun ɗaya ba, wannan ya yi ya bawa wannan, tamkar wata karya haka suka mayar da ita, kawai Allah ya kaddara tana da rabon fitowa daga hannunsu ne ma yasa ta fito, badan haka ba da ai ita kam shikenan tata ta kare, yanzu ma cututtuka kala kala ta ɗauko, sai dai muce Allah ya bata lafiya ya kawo mijin aure, masu hali irin na Rufee ishara gareku, ku tuba ku da'ina.
Aafia ko a jikinta da ta ji wannan labari, sai ma cewa da ta yi Allah ya kara.
Sosai Aunty ta kara yi mata nasiha a kan ta zauna ta rike mijinta da kyau, ga shi ta samu miji jarumi É—aya tamkar da dubu, ga kuÉ—i, mulki, ga shi soja, sannan ba karo mata kishiya zai yi ba, dan su mata É—aya suke aura, dan haka ta kula da shi sosai su mori kuruciyarsu, ita ma Aunty ta haifi É—anta namiji É—aya. Godiya sosai Aafiar ta yi mata.
Misalin karfe 1 aka daura auren Irfan da Pinky a kofar gidan Abbin, sannan suka je gidan Azharuddin Bature, a nan aka É—aura auren Handsome da Zaira, daga nan suka wuce Kano wajen daddyn Jelly, nan suka sami Ayla da babynta kyakkyawan gaske, ita ma Maman Ayla tana gidan, dan dama daddyn Jelly ya mayar da ita wajen iyayenta ta nemi yafiyarsu, ta kuma yi sa'a albarkacin daddyn sun yafe mata, to shi ne ta cigaba da zama a gidan nasu, da Ayla ta haihu ne sai ta zo zama da ita.
A hanyarsu ta dawowa Abuja daga Kano ne Jehan ta kalli A'isha ta gidan Hjyr daɗi a kan hanya kamar mahaukaciya tana tafiya, sai tsince tsince take yi, Allah sarki ashe har Kano su Hjy daɗi suka zo suka jefar da ita, ƙwaƙwalwarta ya taɓu.
Sosai Jehan É—in ta ji babu daÉ—i, sannan ta roki Areef da yasa a kaita asibiti a nema mata lafiya.
Hakan kuwa aka yi, yasa sojoji suka É—auketa dan su kaita asibiti.
Akil da Umaisha dai suna Madina hankalinsu a kwance da É—an babynsu gwanin ban sha'awa.
Sun je kauyensu Maryam, a nan suka tarar da babanta ya mutu bayan fama da ya yi da jinya na tsawon lokaci, cutar daji ce ta kashe shi, É—an banza ko alhakinsu Maryam É—in ma ai ba zai barshi ba, haka zalika ita ma yayarta Allah ya yi mata rasuwa shekara É—aya da suka wuce, Maryam ta sha kuka sosai da sosai, sai rarrashinta Sir Safwan yake yi. Masu hali irin na Baban Maryam aya gareku! Tun lokacin bai kure maku ba ku tuba!!.
Ita kuma Adiva sun yi sa'a da suka je Maiduguri sun sami mamanta a can, dan haka uncle Shitu ya É—auko matarsa suka dawo Abuja.
Gaskiya ba karya family fa sun yi ziyara sosai, sun leƙe yan uwa da abokan arziki sosai. A takaice dai wata guda suka yi a Nigeria kafin su tattara su koma ƙasarsu.
Lion ya cigaba da renon cikin Rimsha yana tarairayar kayarsa har sai da cikin ya bayyana kowa ya gani.
Sun sha ruwan mamakin ganin cikin nata, a lokacin cikin nata ya kai almost 7 month, abin da yasa kuma basu gane da wuri ba, kowa dai yasan Rimsha bata fita, ko nan da part É—in gwaggo Lion baya barinta ta je, kullum zaman É—aki kamar wata mai takaba, matar kowa daga cikin QUADRUPLE suna yawonsu a cikin gidan, amma ban da ita, sai tafi sati bata fito daga cikin bedroom ba, abin ku da mai ciki, daga barci sai wanka, cin abinci da sallah, to da yake kowa yasan halin Lion da bakar kishi, sai babu wanda ya damu kansa ko ya yi tunanin wani abin a kan rashin fitowar tata, kawai sai suka zuba masu ido, basu ankara ba sai ganin Rimshar suka yi da katon ciki kamar me.
Murna iya murna sun yi, Brr Naurat ta rinƙa yi wa Lion tsiya, abinku da Turawa ba kunya ke garesu ba, haka ta rinƙa yi mashi tsiya tana faɗa mashi cewa ashe abin da ya aikatawa ƴar mutane kenan yasa yake ɓoyeta a daki, sai dai ya ce mata ya yi ɗin ba kayarsa bace?.
Dukkansu ba mai alamar kunya a idanunsa ko kaÉ—an, waÉ—an nan family guda biyu suna sha'aninsu son ransu.
Rayuwar farinciki ya wuce baki ya faɗa suke yi, Anderson da His Excellence Lion ya turasu bakin gida, wani gidan kurkuku ne da yake a cikin teku, ba halin gudu daga wannan gida, dan a tsakiyar ruwa yake, ga bakar azabar da ake ganawa prisoners ɗin, abinci sau ɗaya ake basu a rana, kuma abincin ma rabin plat ne, ga uban duka da suke sha na safe daban na yamma daban, wannan gida shi ma Areef yasa aka jefa Hjyr daɗi da kuma Zinariya and Ƴar gwal bayan ya ruguje gidan nasu kenan.
Rungunar sojoji ya sa suka dira a Nigeria bisa umarnin shugaban kasa, yasa suka yi pata pata da gidan Hjyr daɗin, aka saki duk yaran da suke a ciki dan su koma gidajen iyayensu, sannan suka kwaso Hjyr daɗin ita da masu goya mata baya, aka zubasu a bakin gida, wannan bakin gida sai mutun ya gwammaci mutuwa da shiga gidan, dan ɗakunan dake a cikin gidan ma a tsaye bawa yake kwana, ba halin kwanciya, kafafu duk su kumbura, idan kunga bawa ya miƙe kafafu ya ɗan kwanta, to sai da safe idan sun fito tsakar gidan, kuma ba kullum ake fito da su tsakar gidan ba, a sati sau biyu suke fitowa, sauran kwanaki duk suna cikin ɗaki a tsaye kamar gumaka, suna ganin izayar rayuwa. To masu hali irin nasu aya gareku, mugu dai karshensa bata kyau!!.
Su kuma family yanzu komai zam zam, rayuwa mai tsabta tare da farinciki mai kawa suke yi har izuwa ranar haihuwar Rimsha, a lokacin kuma Maryam ta haifi yaro ɗaya, Adiva ta haifi yarinyarta mace, Aafia ta haifi ƴan biyu dukka mata, Ummin Dr Nawid tuni ta karɓe yaran wai ita zata renesu, Allah sarki tana son yara sosai, ga shi har yanzu Jellynta kuma Jellyn Yah Imran bata haihu ba.
Gida ya kara cika sosai da yara da jikoki, yanzu kowa dakon jiran yaran Lion yake yi.
Tun safe Rimshar take naƙuda har karfe 2 na rana, amma shiru bata haihuwa, da alama ba zata iya haihuwa da kanta ba, hakan yasa Lion ya ce ayi mata aiki a cire babyn kawai, dan hankalinsa ya kai makura wajen tashi, ya shiga damuwa na wuce misali, ya ji ba zai iya jurewa ba, dole kawai ayi mata aiki a cire yaran nan kada matarsa ta mutu.
Dan dole su Dr William suka karɓi maganar Lion ɗin a in da aka shirya tsab aka yi mata aiki, cikin ikon Allah aka ciro mata baby's nata Maza guda uku da mace ɗaya, duk cikin QUADRUPLE ita kaɗai ta haifa masu ɗiya mace, yarinyar tamkar Pinky, ma'ana kamar Lion ɗin, harta kalar idanunta, duk yaran babu wanda ya biyo Rimshar, dukkansu Lion ɗin suka ɗauko, harta kwayar idanuwansu blue eyes ne, sak irin nasa.
Gwaggo baki har kunne, dama burinta kenan, ga shi Lion ya samu É—iya mace, abin ba'a magana, gwaggo kamar baki ba zai rufu ba, kowa idan ya zo ganin baby's macen yake É—auka, sun fi son macen sama da sauran mazan, dan sun gaji da rike maza, yanzu sun samu canji, harta su Areef da suka zo ganin yaran macen suka É—auka, kowa santin macen kawai yake yi, daddyn Rimsha ma macen ya É—auka da ya zo.