Sashe 38
Triplets Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kowa binsu da idanu yake yi sosai, sun ƙagu su ji menene abin da zata ce. Ita kuma shiru ta yi tana nazarin maganganun Ammien, ta ɗan ɗauki lokaci kafin ta fara magana cikin nutsuwa. "Tun farko kune ma muka yi kuskure, ko in ce shi Abba shi ne ya yi kuskure, tun da ka san ga daga in da ka ɗauko mace, ai da sai ka san irin babban matakin da ya kamata ka ɗauki, wani faɗan ai baka isa ka yi shi kai kaɗai ba, tun kafin ka shiga gidanka da kuka zauna, sai ka sanya ayi maka saukar Alqur'ani mai girma, ayi walima ayi maku adduo'i, ta yanda zaku ɓacewa ita Queen ɗin gabaɗaya, karfin addu'a zai taimaka maku Allah ya tsareku, sauran ƴan uwanka ma, sai ka gaya masu su ga halin da ake ciki, sai suma su shirya su tsananta addu'a, tun da a gaban idanunka Queen ɗin ta sha alwashin ba zata rabu da kai da familynka ba, sai baka yi hakan ba, ka ɗauka abin wasa ne, yanzu koma me ya faru da ƴan uwanka, to laifinka ne, dan su basu san ma daga ina take ba, suna rayuwarsu ne yanda suka saba, kuma shi karatun Alqur'ani sai wanda yake da kokari sosai ne yake iya yinsa kullum, saboda shaiɗan ba zai barsu ba, amma kaga idan sun san da wannan matsala, dole za su yi taka tsantsan sosai, dole zasu yi ƙoƙarin yin addu'a sosai, za su kula da askar, dan su kare kansu daga irin wannan musifu haka". Ta kai karshen maganar tana mai kara jinjina wannan al'amari, dan ita wlh sam bata taɓa tunanin ire iren waɗan nan matsafa akwaisu a gaske a zahiriya ba, kun san Turawa dama, su sam basu damu da irin waɗan nan shirme ba, to yau dai ga shi ta samu gagarumar matsafiya a cikin surukanta!.
(Anya da Brr Naurat tana nan a lokacin zata yarda Abba ya auri Ammien kuwa?🤔 Shiyasa Allah ya kawar da ita a lokacin, ta koma kasar Russia, domin rabon su Imran da yake a tsakanin Abba da Ammien, kun san shi fa rabo har kisa yanayi, to Allah ya ƙaddara akwai auren ne, shi ne ya matsar da Brr Naurat, dan yasan ba zata taɓa yarda da auren ba!!)
A hankali sautin zazzaƙar muryar Rimsha ya fara tashi, kasa kasa take magana ta lafe a jikin Noorish nata. "Noorish Allah ni bana son komawa Daular Mutuwa, please kada ka bari Queen ta ɗauke ni, Allah Duna ya ce mani cinyeni zata yi idan na sake komawa". Tana magana wasu siraran hawaye suna zubo mata a kuncinta.
Shafa face nata ya yi tare da goge mata hawayen, a hankali ya motsa laɓɓansa, ba sai na sake faɗa ba, dama kun sani already shi idan yana magana, kasa kasa yake yinta, idan ba kana kusa da shi sosai ba, to ba zaka taɓa jin meyake faɗa ba, a yanzu ma haka ne, duk cikin palon ban da Areef dake zaune kusa da shi sosai, to babu wanda ya ji abin da ya ce mata, kasa kasa ya yi maganar.
"Babu wanda ya isa ya mayar mani dake can, just calm down kin ji ko?"
"Noorish Allah tsoro nake ji". Ta yi maganar tare da kankame shi sosai. Tabbas yaga tsananin tsoro kwance a cikin idanunta, hakan ya kara tabbatar mashi da cewa ba ƙaramar ɓarna suke aikatawa a cikin wannan Daular Mutuwar ba!,.
"Meesha bai kamata ki ji tsoron wani abin ba idan kina a tare da ni, ba zan bari ayi maki komai ba". Ya yi maganar yana mai cigaba da goge mata hawayen da suke ta gangaro mata.
"Is okey, a tsayar da kukan nan haka nan". Ya kai karshen maganar yana É—ago da idanuwansa izuwa kan Brr Naurat dake kallonsu.
"Brr just close this case like that, ni ban ga abin dawo da abin da ya wuce ba, a have alot of things da nake son zuwa na yi, so momma I will going to leave". Cewar Lion É—in.
"No Saif, wannan ba shi ne maganar da na kiraka ka zo mu yi ba, tsaya ka ji maganar mana". Cewar gwaggon.
Shiru ya yi bai sake magana ba. Rimsha ce ta sake ce mashi "Noorish am feeling hungry too much". "Okey you can go and eat". Ya bata amsa.
Su Imran dai mamakin Lion ya hanasu yin magana, wai yau shi ne ya zauna yake hira da mace haka, macen ma ƴar yarinya kamar Rimsha, komai ta ce mashi zai bata amsa, mutumin da a baya sai ka yi magana goma sannan yake bada amsa ɗaya, ba ya taɓa baka amsa a kan kowace magana, wani lokaci ma amsar ma ba zaka samu ba, amma ita Rimsha kowani maganarta sai ya amsa, Allah mai iko!!.
Zaro idanu ta yi tana faÉ—in "No ina tsoro sosai gaskiya, ba zan iya zuwa kitchen ba". Shiru ya É—an yi kafin daga bisani kuma ya sake cewa "Jeki cikin É—aki, a cikin trolleyna da muka je Abuja dake É—in nan, ki duba zaki ga wani littafin adduo'i, ki É—auko ki kawo mani bari na koya maki wata addu'a dan ki rage tsoro".
Kasancewar a palon sama suke, sai ta ji tsoron ya ragun mata, dan daga palon suna iya hango cikin bedroom ɗin nasa, so tana jin motsin mutane, dan haka sai ta miƙe ta nufi cikin bedroom ɗin. Su kuma suka cigaba da tattaunawa, ana mai da yanda aka yi wasu abubuwa a baya.
Da shigarta ɗakin bai fi da minti uku ba, ta zunduma wani irin uban ihu mai tsananin rikita ƙwaƙwalwa. Mazan dake a cikin palon suna yunkurin mikewa su nufi cikin bedroom ɗin, sai gata ta fito a guje. Tsayawa suka yi suna kallon ikon Allah, kowa ya yi tunanin wani abin ne ya kamata, ko Queen ce ta ɓullo a gabanta, amma sai suka ga akasin haka, gata ta fito lafiya lou hannunta na rike da wasu hotuna tana zunduma ihun kuma again.
Bata zame ko'ina ba sai wajen daddynta, jikinsa ta faɗa tare da miƙa mashi hoton, tana kuka tana faɗin "Daddy wlh tallahi wannan ma ɗan uwan su Queen ɗin Daular Mutuwa ne, na gan shi a cikin Daular Mutuwar, sunansa baba, muna zama muyi hira da shi ni da su Ayla, Allah ban manta shi ba, wayyo nashiga uku, yanzu kenan har ɗakin yaya Saif akwai ƴan Daular Mutuwa a ciki, daddy Dan Allah mu koma gidanmu na Abuja kawai, ni dai wlh bana son Daular Mutuwar nan". Tun da ta fara surutan nan suka zuba mata idanu, baiwar Allah duk ta firgice yau.
Shi kuwa daddy karɓar hoton ya yi dan ya kalli wanene. Ai kuwa yana gani ya yi wani irin zabura, a hanzarce ya sauketa daga jikinsa tare da miƙewa tsaye yana faɗin "Daddy kuma a Daular Mutuwa?!!".
Da sauri shi ma Abba ya karɓi hoton yana kallo, zaro idanu shi ma ya yi ganin cewa hoton Dr Salman ne, to su a saninsu mutuwa Dr Salman ya yi, ya haka kuma, anya Rimsha shi ta gani kuwa? Wannan shi ne tambayoyin da suke yi wa kansu.
Masu karatu idan baku manta ba, time da Lion ya je Abuja, akwai wasu hotuna na familyn daddyn Rimsha daya kwasa daga ɗakin mum, kun tunasu? To a cikin waɗan nan hotunan ne da akwai hoton Dr Salman, shi ne yanzu da ta je ɗaukar littafin addu'ar, sai taga hoton, ita kuma kunga yanzu tunanin Daular Mutuwa kaf ya dawo mata a cikin ƙwaƙwalwata, ta san Dr Salman a can, tana tsaka da kallon hotunan ne, sai taga hotonsa a ciki, kunga kuwa dole ta birkice ai, tun da ita dai a Daular Mutuwa ta san shi, yanzu kawai taga hotonsa a cikin trolleyn Noorish nata, ai dole ta yi hauka, dole ta yi tunanin ko dai ƴan Daular Mutuwa sun fara biyota har nan ne kuma, to shi ne abin da ya faru.
Mamaki ya hana kowa magana, sun jima shiru kamar waÉ—an da ruwa ya cinyesu, sai al'ajabin wannan al'amari suke yi. Can Brr Naurat ta ce "Meesha kin tabbatar shi kika gani a can?".
Da sauri Lion ya É—ago idanu yana kallon Brr, saboda ya ji sunan da ta kira Rimsha da shi, shi dai yasan sunansa ne, shi kaÉ—ai yasa mata wannan suna. (Brr Naurat ya da haka kuma? Ina ruwanki da sunan masoya?ðŸ§)
Tamkar Brr tasan kallon me yake yi mata, sai ta ce "Ka yi mani kishi, na yi shiru bai yi magana ba, har da sake mata suna, to ba zai yiwu ba, nima dole ka sake mani suna, kuma nima da wannan suna zan kirata, dan ni ce uwar gida ai, duk ido zan saka maku".
Kawar da kallonsa ya yi ba tare da ya yi magana ba, wannan tsohuwa akwai sa ido, ya faÉ—a a cikin zuciyarsa, a cikin jirgin ruwa fa ta ji yana faÉ—in Meesha, shi ne har ta rike sunan, Brr kenan!.
Cikin kuka Rimshar ta ce "Brr wlh shi ne, shi ne baba na Daular Mutuwa, Allah ban manta shi ba, kullum yana zaune a É—akinsa, ya tsufa, muna zuwa mu yi hira da shi".
Ammie ce ta karɓi zancen da cewa "Ba shakka tun da Rimsha ta faɗi haka, to wlh haka ne, ni dama na ce wannan accident ɗin shirya shi Queen ta yi, ai kunga ko gawar Dr dama ba'a kawo mana ba, sai dai aka ce babbar motar da ta bi ta kansu ta yi raga raga da su over, sai dai kasusuwansu, to wlh ba shakka Dr Salman yana raye, kuma yana cikin Daular Mutuwar kamar yanda Rimshar ta faɗa!".
Jin ance wannan baban kakanta ne yasa ta sake zunduma ihu tana faÉ—in "Wlh ba kakanmu bane, shifa yaron Queen ne, dan Allah ku dai'na cewa kakanmu ne, a Daular Mutuwa fa yake, wai daddy ka san Daular Mutuwa nan kuwa? Wlh ina gaya maka shi ma baban namar mutane yake ci, dan Allah ku dai'na cewa kakanmu ne, ni kam zan mutu yau".