← Book details Triplets Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 168

Sashe 15

Triplets Part 4 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Nan fa taga bala'i a karo na uku, dan kuwa Abba a lokacin ma bai gama dawowa cikin hanyacinsa na abin da amarya ta yi mashi ba. Dan haka sai ya yi wa gwaggo tatas, ya koreta daga gidan, wai ta zubar masu da kimar gidansu, ta je wata ƙasa ta haifi yara, shi sam bai yarda da aure ta haifesu ba, dan haka ba zai karɓo ƴaƴan shegu ba, da ace ta zo da su ma, wlh karɓarsu zai yi ya mayarwa da ubansu su, dan babu ƴaƴan shegu a kaf zuri'ar Dr Salman. Haka dai ya yi ta surfa ruwan bala'i, ta in da yake shiga, ba ta nan yake fita ba. Daga karshe ya korata waje tare da rufo gate ɗin gidansa, ya ce ta je ya yafeta a matsayin kanwa!!.

A lokacin da yammane, wuraren karfe 6:30, bai yi wani tunani ba ya daketa ya koreta. Tana kuka tana rantse mashi da Allah wlh ba shegu bane Æ´aÆ´anta, Æ´aÆ´an sunna ne, dan Allah ya dai'na shaigantasu, amma ina haka ya sa kafa ya yi ball da ita. Ya ce bai san wannan ba.

Ganin zai yi mata illah ne yasa ta baro bakin gate ɗin gidan a guje kamar mahaukaciya, tana gudu tana kuka, Ammien su Imran ta yi ƙoƙarin dakatar da Abban, amma ina, sam abin ya ci tura, yaki sauraronta, ya hau dokin zuciya, dama idan baku manta ba, a baya na gaya maku, shi mutun ne mai bala'in zuciya da zafin rai!.

Bazama cikin gari gwaggo ta yi kamar mahaukaciya, da kamar zata je gidan Abbi, amma da ta tuna cewa, da Abbi da Abba halinsu iri É—aya, sai ta gwammaci gara ta shiga duniya. Tamkar zautatciya haka ta zama. Tun tana iya gane hanyar da take tafiya a kai, har ta dai'na ganewa, ta fara ganin dishi dishi, da alama hankali ya gushe a tattare da ita. Daga karshe ma sai ta zube kasa a kasar wata bishiya ta bakin titi, kan ka ce me ta sume a wajen, saboda tukukin bakin ciki da yake cikin zuciyar baiwar Allah nan!!.

Nisawa ta yi tare da goge hawayen fuskarta, sannan ta ce "Tun daga wannan suma da na yi, ban sake sanin in da kai'na yake ba, sai da na shafi shekara kwance a gadon asibiti, lokacin da na farka kuma, da fuskar kanina Nawazuddeen na fara cin karo, shi ne yake gaya mani shakarata ɗaya a sume a gadon asibiti, tsabar bakin ciki ban ko tambaye shi daga ina ya tsintoni ba, kawai na bar maganar, shi ya cigaba da kula da ni, na bashi labarin komai na daga auren da na yi, har da yayana TRIPLETS, hakuri ya yi ta bani, ya kuma biya kuɗin jirgi muka je har Washington DC, sai dai bamu sami su Dr William ba, mun yi tambayar duniyar nan, basu ko ɗaya daga cikin gidajen iyayensu da suka bari, kowa sai ya ce bai san in da suke ba. Daga karshe dai muka hakura muka dawo, zuciyata cike da kaunar yarana, ina jin tamkar zan mutu. Kullum Nawazuddeen ajiye duk wani abin da zai yi yake yi, ya dawo gida ya zauna ya yi ta bani hakuri, yana kwantar mani da hankali, a lokacin ko aure bai yi ba, shi kaɗai yake rayuwarsa shi ma. Haka muka cigaba da rayuwa a tare, na zama tamkar mahaifiyarsa, yana yi mani biyayya over, ban taɓa yin magana ya saɓa ba, ya mayar dani islami, a nan na sami ilimin addini sosai da sosai, daga nan kuma nayi danasanin abubuwa da dama na rayuwar da muka yi da Dr, da na sami ilimin addini sosai, na fahimci wani abin, na fahimci da ni da Dr mun aikata saɓon Allah sosai a cikin soyayyarmu, kila shi ne yasa Allah ya jarrabeni da wannan kaddara, dama irin wannan saɓon da muka aikata ai ba zai taɓa yiwuwa aurenmu ta yi albaraka ba". Ta kai karshen maganar tana goge hawayen fuskarta.

Kowa da yake cikin palon sai da zuciyarsa ta raunata, ta kuma taɓu sosai, daddyn jelly kam kuka ya yi sosai, dan kun san shi dama, akwai shi da saurin kuka. Dayawa daga cikin jama'ar palon sun zub da hawaye.

Gyaran murya Brr Naurat ta yi, cikin dattaku da girma ta ce "Dr William ka ji bayanan A'isha ko? Me zaka ce kai kuma? Bayan A'isha ta baka yaran, ka gaya mana ya ka yi da su? Ina suke? Menene kuma ya faru bayan barin A'isha gidan? Ina yaron da ka illatar da sanda? Meyasame shi? Muna jiran bayananka kai ma!!". Nan fa gabaÉ—aya kallo ya koma kansa. Harta Æ´aÆ´an nasa ma shi suke kallo.

Ya ɗan ɗauki ƴan mintoci kafin ya ce "Ni duk abin da ta faɗa ban sani ba, ni ban santa ba! Kuma ban taɓa ganinta ba sai yau, wata kila da wani Dr William ɗin take yi ba ni ba!"........TASHIN SENSE

Brr Naurat tana ƙoƙarin sake yin magana Areef ya daka musu tsawa cikin tsananin ɓacin rai tare da tashin hankali. "Daddy kada ka mayar da mu mahaukata mana? How comes zata bada dukka wannan labari kuma ka ce karya ne? How comes ta san su kaka? How comes ta zayyano sunayen unguwar da gidajen kaka yake da sauransu?Kawai daddy ka gaya mana gaskiya!!". Ya kai karshen maganar tare da miƙewa tsaye yana huci tamkar wani mayunwacin zaki. Tamkar ba Areef mai saukin kai da wasa da dariya ba.

Miƙewa shi ma daddyn ya yi yana faɗin "James a said a don't know her, what do you want me to tell you again?!". Ya yi maganar cikin tsawa shi ma.

Buɗe baki Areef ɗin ya yi da nufin ya yi magana. Bai kai ga yin maganar ba sai ganin Lion suka yi ya damki wuyar daddyn nasu da hannu ɗaya, ya maka shi da jikin bango tare da matse shi. Gabaɗaya ya canza lokacin guda, tamkar ba NooRin Meesha ba, idanuwansa sun yi jajir da su kamar wuta, har wasu jijiyoyi sirara ne suka fito mashi a damatsan hannunsa da kuma wuyarsa, sai wani irin numfashi yake yi mai kama da gurnanin zaki, jikinsa sai wani tsuma yake yi, ran maza ya ɓaci!.

Shi kuwa Aseef miƙewa ya yi daga kwanciyar da ya yi daga saman cinyar daddyn Rimsha, ya kifa kansa da jikin hannun sofa yana hawaye, sam baya son ganin abin da yake faruwa.

Sosai Lion ya shake daddy har sai da idanunsa suka juye, harshensa ya zazzago waje, yana daf da bakontan lahira. Ga shi Lion ɗin yaki ko da sassauta mashi, kuma ya ki yin magana, saboda tsananin ɓacin rai, dan daddy yana neman raina masu wayo.

Can kuma cikin tsawa ya ce da daddyn nasa. "Tell us the truth, if not I'll make you regret! Me muka yi maka da zaka yi mana haka? Me bamu yi maka ba? Saboda kai muka ɓoye cewa mun musulta na tsawon shekara ɗaya yanzu, duk gudun kada mu sa ciwonka ya tashi, dan mun sanka da kishin addininka, zaka iya mutuwa idan ka ji mun zama musulmai, saboda kai muka ɓoye hakan! Duk dan mu faranta maka rai, mu kuma sauke hakkin iyaye da yake a kanmu, amma kai kuma ka gaya mana meyasa ka yi mana haka? Meyasa ka bari muka taso cikin kafurci? Ka yi mana karya! Ka ɓoye mana ainahin mahaifiyarmu, ka haɗamu da wata banza a matsayin uwa, bayan kuma sisterka ce uwa ɗaya uba ɗaya! Ka cutar da rayuwarmu! Ka cusa mana tsanar abubuwa da dama a rayuwarmu wanda bai kamata mu tsanesu ba! Ka ɓoye mana gaskiya, amma da yake, ita gaskiya komai daren daɗewa sai Allah ya bayyanata, sai ga shi Allah ya haɗani da Imran, na kaunace Imran sosai! Bana son kowa bayan TRIPLETS na, amma rana tsaka na tsinci kaina da son Imran, ta dalilinsa na dawo ainahin addinina, ta dalilinsa na tako kafata na zo Nigeria, wanda a baya ban taɓa tunanin zan zo ba, da Allah ya tashi kamaka daddy, kai ma da kafarka ka tako kazo Nigeria, ba wanda ya sanyaka dole, daga kan Imran kuma ban sake kaunar wani ɗan adam ba sai Uncle ɗin James, haka kawai shi ma rana tsaka na kaunace shi, har mamaki nake yi wani lokaci, na kasa banbance da shi da Imran wa ye na fi so a cikinsu, ashe dan Allah ya gwada mana wani aya ne yasa muke kaunarsu......". Da kyar ya kai karshen maganar saboda wani tukukin bakin ciki daya tokare mashi maƙoshi. Daga haka ya yi shiru bai sake yin magana ba, sai dai sauke dogon numfashi tamkar gurnanin zaki da yake yi, ya kuma kara shake daddyn da karfi sosai!!.

Kallon Areef Abban Imran ya yi cike da tsananin tashin hankali ya ce "Areef ka dakatar da É—an uwanka, idan ba haka ba, zai yi kisan kai, dan daddynku dab yake da ya mutu!".

Ganin da gaske hakan ne yasa Areef É—in ya nufi Lion É—in da sauri dan kuwa da gaske ne daddyn nasu na dab da mutuwa.

"Lion wlh zai iya mutuwa, dan girman Allah ka sake shi haka nan ya isa, ba kaga yanda yake numfashi ba ne?".
Chapter 15 · 0% Book details