← Book details Triplets Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 116 OF 168

Sashe 116

Triplets Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kallon Areef É—in Jehan ta yi tana faÉ—in "Yah Areef ka bani izini ni zan tuna mata da su waye ne su Adiva". Jinjina mata kai ya yi. "Na baki izini my D.P.O".

Cool murmushi ta sakar mashi kafin ta tako izuwa gaban Hjyr daÉ—in, kallon sama da kasa ta yi mata kafin ta sanya hannu ta É—auketa da wani gigitaccen mari. Wani irin ihu Hjyr daÉ—in ta kurma. "Weeeee hooooooo ni zaki mara Jehan?!".

Kallon Areef Jehan É—in ta yi ta ce "Yah Areef kaga yanzu ta tuna sunana, saura nasu Adiva, in kara saitata a kan hanya ne?".

Jehan ba dai karfin hali ba, shi mamakin jajircewarta a kan gaskiyarta ma yake yi, ko zaka kashe Jehan sai dai ka kashe ta, amma ba zata taɓa kaucewa gaskiyarta ba, bata da tsoro a zahiri, ga karfin halin, yanzu da wata ce ko kusa ko alama ba zata iya marin mace babba kamar Hjyr daɗin nan ba, koda kuwa ace bata da kirki, wlh ba zata iya marinta ba, duk da tasan akwai mai tsaya mata a wajen, amma Jehan with her full confidence ta ɗauke ta da mari, kuma har tana ikirarin kara mata wani.

A tare su Zinariya da Æ´ar gold suka shigo cikin office É—in, jin Hjyr ta yi ihu ne yasa suka shigo da gudu, sun warke daga dukan haukar da Jehan É—in ta yi masu before ta fita daga gidan.

Ganin su Jehan É—in yasa suka tsaya cirko cirko suna kare mata kallo, ko kallon in da suke bata yi ba ta ce "Ke Hjyr daÉ—i kike ko waye? Zaki gaya mana in da su Adiva suke ne ko sai na kara maki wani marin?". Yadda ta yi maganar tamkar wata hamshakiyar hukuma mai doka a hannu, cike da confidence abinta.

Zinariya ce ta ce "Au Jehan kin dawo kenan? To kuwa yau zaki ci ubanki ne, babu mai karbarki shegiya!". Sam basu lura da Areef É—in a wajen ba, duk hankulansu na'a kan Jehan da Hjyr kawai.

Wani kallon walaƙanci Jehan ɗin ta wurgawa Zinariyar kafin ta ce "Keeeeee ni bance zaki ci ubanki ba sai kece zaki ce zan ci ubana? Kin manta karon mu ta farko kenan? To a da can baya ma kenan, bare kuma yanzu da ke ko da ido kika ganni kin san na wuce dukan kato ko katuwa, sai dai dukan ruwan sama da kuma iyaye wanda suma nasan ba zasu ɗaura hannunsu mai albarka a jikina da nufin duka ba, sai dai su ɗaura hannunsu a jikina dan su samin albarka, ke yanzu kinsan zaren ba kalar yadin bane, ni yanzu bani da lokacinku, kawai ku bani su Adiva nake so, banzaye kazaman banza, sai warin bleaching kuke yi, kamar mutun ya yi amai, shashasshu, karyoyi, kadangarun bariki masu bakin iyaye kawai!!".

Hannu Zinariyar ta cire zata zabga mata mari, cikin hanzari Jehan ɗin ta yi ƙoƙarin kai hannunta ta tare mari, sai dai bata kai ga yin hakan ba Areef dake tsaye a gefe yana binsu da kallo yana mamakin confidence irin ta matar tasa ya rigata, damke hannun Zinariyar ya yi tare da ɗauketa da wani gigitaccen mari da ɗayan hannunsa, kafin kuma ya sauke hannun nasa daga marin da ya yi mata ɗin, tuni numfashinta ya ɗauke diff ta sume, dama kunsan ita Zinariya ƴar a lallaɓace, duk duniya ya cinyeta, ta zama ragwaɓaɓɓiya, maza sun yi bidirinsu a kanta ba iyaka, babu wani abin azo a gani da ya saura a jikinta, sai uban talauci, ga muni da bleaching kamar ya kashesu, shegu sai wari suke yi, sun sayar da duk wasu albarkatun da ni'imar da Allah ya yi wa jikinsu, amma har yau sun kasa yin dukiya, kullum suna cikin talauci, dama in dai ta hanyar saɓon Allah ne ba zaka taɓa yin arziki ba, sai dai ka rasa komai naka, daga karshe ka faɗa cikin musifa, ga tsinuwar Mala'iku ga kuma fushin Ubangiji, bugu da kari ga azabar da Allah zai maka, me ribarka na saɓawa Allah to? Tun farkon duniya har kashenta babu wanda ya taɓa cin riba a saɓon Allah, hakan ma ta isa bawa ishara da kuma aya mai girman gaske, duk wanda ya saɓawa Allah tasa bata kyau, Allah ka iya mana ka mana mai kyau, su dai su Zinariya tasu bata yi kyau ba sam sam.

Ganin ta sume ne yasa ya saki hannun nata ta zube kasa wanwar kamar wata kayan wanki, guntun tsaki ya ja tare da ɗago da kallonsa a kan Hjyr daɗin. Duk sun yi wani tsuru tsuru da su, tsantsar tsoro ya bayyana a saman face nasu. Jiki na rawa Hjyr ta fara ƙoƙarin kiran waya dan mutanenta masu ɗaure mata gindi su kawo mata agaji.

Shiru Areef ɗin ya yi mata, ko a jikinsa, dan yasan call ba zata tafi ba a wannan gida dai, bai shigo ba sai da ya shirya, tsawon watanni huɗu yana bincike a kansu, ya sha aiki kafin ya iya gane komai a kansu, har waɗan da suke ɗaure mata gindi a kasar duk ya sansu, sai dai a yanzu bashi da isasshen lokacin da zai tsaya ya ce zai bisu ɗai ɗai ya kashesu, saboda kurar da suka tayar a U.s ma kawai ta ishesu, ga zaɓe na gabatowa, bugu da kari a yanzu basu da goyan bayan His Excellence, hasalima faɗa suke yi da shi, kuma wasu manya ne daga cikin manyan kasar suke tallafawa Hjyr, so dole sai a gwamnatance za'ayi maganinsu, hakan yasa kawai ya bar batun rushe gidan sai bayan zaɓen U.s, su Adiva ɗin ma abin da yasa ya zo ɗaukarsu shi ne, Jehan tana damuwa sosai a kansu kullum, yasan da hakan, sannan Adiva ƴar uncle ɗin su Jehan ɗin ce, ba zai so wani abin ya sameta ba, ko dan amanar da mahaifinta ya rike wa daddyn Rimshar, shi ne yasa yazo ɗaukarsu kawai.

Sam call yaki tafiya, ganin haka yasa Hjyr ta fara ƙoƙarin gudu ta fita daga cikin office ɗin, ita ma ƴar gold ƙoƙarin guduwa ta fara yi dan ta fita.

Tsawa ya daka masu wanda yasa dole suka dakata, cikin fusata ya ce ko ta gaya mashi a in da su Adiva suke, ko kuma ya kasheta a nan ya kashe banza! Shi su Adiva kawai ya zo É—auka, babu ruwansa da su.

Bata da zaɓin da ya wuce ta gaya mashi, murya na rawa ta gaya mashi cewa Maryam tana cikin ɗakinsu bata da lafiya, ita kuma Adiva jiya a daddare an fita da ita.

Idan ransa ya yi dubu to ya ɓaci a wannan lokaci, sam bai san time da ya ɗauke Hjyr da wani ɗan iskar matsiyacin mari ba.

Wani irin ihun azaba ta saki, tsabar azaba bata ma san time da bakinta ya furta masu address É—in in da aka kai Adiva É—in ba, sake kara mata wani matsiyacin lafiyayyen marin ya yi, sai gata a kasa ta zube kamar kayan wanki, kamar wata mushen doki.

Ita kuwa Jehan tana jin abin da ta ce ta juya a guje ta nufi ɗakin nasu tun da already ta san hanya. Ƴar gold kuwa, tuni idanu ya rai'na fata, jiki sai kerma yake yi, tana jiran ta ji nata saukar marin. Sai dai bai bi ta kanta ba, juyawa ya yi ya bi bayan Jehan ɗin.

A kwance rai a hannun Allah suka isko Maryam, sam bata a cikin hayyacinta, bata iya gane su waye ne ma a kanta, ga dai idanuwanta a buÉ—e, ta yi wani uban rama tamkar wata figaggiyar kaza mai kwanci, harta gashin kanta sai da ya sauya launi, sai Allah ne kaÉ—ai yasan me wannan tsinanniyar Hjyr ta yi mata, ko da Jehan ta ambaci sunanta ma, sam bata iya amsawa, bata iya magana, kusan irin ciwon da A'isha ta yi suka je suka jefar da ita, to kusan hakance ita ma Maryam É—in take fama da shi.

A hanzarce Areef É—in ya É—auketa cak, dan gani suke tamkar zata mutu kafin ma su fita da ita daga cikin gida, dan idan baku manta ba a tsakanin ginin farko ba gidan da kuma in da su Jehan É—in suke da akwai tazara mai yawa, hope baku manta yadda tsarin ginin gidan yake ba?.

A hanzarce suka fito da ita, bai sake bi ta kan kowa da yake a gidan ba suka fice. A gidan baya na motarsu suka sanyata, da gudu Jehan ta shiga gidan gaba, shi ma ya shiga mazaunin driver, a haukace ya tashi motar suka bar gidan.

Ita kuma Hjyr daɗi tana baje a kasa kamar mushen doki, sai Allah ne ma kaɗai yasan tana raye ko ta mutu, haka zalika ita ma Zinariya, sun ji hannun maza, ƴar gold kuwa, gabaɗaya a tsorace take, sai mamaki take yi ta yaya aka yi su Areef suka iya shigowa wannan gidan nasu da mutane basu iya ganinsa sai wanda Hjyr ta zaɓa zai shigo mata? Abin ya ɗaure mata kai, basu san cewa a shirye da addu'a sosai Areef ɗin ya zo ba.

Hospital mafi kusa da gari suka fara kai Maryam É—in, idan baku mance ba gidan Hjyr daÉ—i yana É—an bayan gari ne. Sai da suka tabbatar da likitoci sun dukufa a kanta, sannan ne ya ce su je su É—auko Adiva kuma a wannan address É—in da Hjyr daÉ—in ta gaya masu, haka kuwa aka yi, suka baro asibitin, sun baro likitoci a kan Maryam É—in sunata fama, a haka suka nufi in da Hjyr ta gaya masu.

Bayan sun fito daga cikin hospital É—in, tambayar Jehan É—in ya yi a kan ko tasan wannan address É—in da Hjyr daÉ—in ta faÉ—a?.

"A'a Yah Areef ban sani ba, amma mu tambayi mutanen da suke wucewar nan mana, kila zasu sani".

Jinjina mata kai ya yi tare da yin parking na motar a gefen hanya ya sauke glass É—inta kasa.

Can wani matashi yazo zai wuce, dakatar da shi ya yi tare da yi mashi sannu, sannan ya gaya mashi abin da suke nema.

ÆŠan zaro idanu matashin ya yi kafin ya basu amsa da cewa "Kai wannan waje fa ba wajen zuwa bane, yana da uban nisa sosai daga nan, sannan kuma............

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️❤️🔥
Chapter 116 · 0% Book details