← Book details Triplets Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 154 OF 168

Sashe 154

Triplets Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka shi ma sir Safwan, ya fi kula da Jehan ɗin sama da yanda yake kula da matarsa Maryam, wani lokaci abin har yana neman ya zamar masu faɗa a tsakaninsa da Maryam ɗin, sai ta rinƙa cewa meyasa ya fi bawa cikin dake jikin Jehan kulawa sama da nata cikin? Ita da cikinta ma karami ne, ita ya kamata ya bawa kula sosai, dan kada a samu matsala, amma sai ya fi kula da cikin Jehan ɗin, kullum yana part ɗin Lion wajenta, da ta yi motsi kaɗan zai tambayeta tana lafiya kuwa? Abin ya fara bawa Maryam ɗin haushi, kun san mata da kishi, kada kuga laifinta, haka muke........😂

Duk yadda gwaggo ta kai ga son Jehan a wannan karon sai da ta hakura ta barwa Lion da sir Safwan kula da Jehan É—in, domin kuwa suna É—aukar Jehan É—in ne a matsayin Areef É—insu, cikon QUADRUPLE nasu, kuma kowa yasan sir Safwan da Areef É—in sun fi shakuwa sosai, dole kunga ya mayar da hankali wajen kulawa da É—an uwan nasa kayansa fiye da komai.

Wasa wasa har cikin Jehan ya shiga watannin haihuwa, su Areef shiru basu babu labarinsu, Lion yasa an tura wasu runduna na sojoji ma, amma still shiru, suma rundunar sun tafi basu dawo ba, ba wani labari.

Kullum cikin kuka a ɓoye Jehan take yi, duk da Lion ya ce mata Areef sun je ƙasar China ne yin wani aiki, zasu dawo bada jimawa ba, amma ta kasa samun nutsuwa, tana jin kamar ma Areef ɗin baya raye a duniya ne, ga rashin iyayeta na tsawon watanni da dama, abin sai ya haɗu ya yi mata yawa, ga uban ciki haihuwa yanzu ko anjuma, duk ta rame, ta yi wani irin duhu sosai. Amma Lion yana iya ka bakin ƙoƙarinsa wajen ganin ya kwantar masu da hankali ita da Rimsha da kuma gwaggo, abin ne yana neman ya fi karfinsu.

Ƴanƴan Akila sun fara wayo, ta tare a part ɗin gwaggo abinta, kullum na Allah Aseef yana manne da baban ɗan nan nasa wanda ya fi kama da shi, ba'ayi shagalin suna ba, sun ce sai Jehan da Anaya sun haihu za'a haɗa dukka ayi party, daga nan a shirya zuwa Nigeria, sai dai an sanyawa yaran suna kamar yadda addinin musulunci ta tanada, Aseef ya yi wa Abban Akila takwara, ya kuma yi wa Dr William sai kuma sunan Lion ya sakawa autar cikinsu, baya taɓa yarda wani ya ɗauka yaran nan idan ba gwaggo ba, ko su Anaya ya hanasu, sai dai ka kalli yaran da ido suna kwance a saman bed nasu, gasu gwanin ban sha'awa, ƴan ɓul ɓul da su, amma baka isa ka ɗauka ba, ubansu ya ce kar a karya mashi su, a barsu a kwance a rinƙa kallonsu.

Yau ni PRINCESS TEEMA ina ganin ikon god a wajen Aseef, wai kada ayi a karya mashi su, Kai jama'a, yara masu daÉ—i, Allah mai iko, Allah ka bamu masu albarka

Shi kuma fa zai ɗauki yaransa son ransa, kuma koda yaushe idan ya zo ɗauka bai iya ba sai gwaggo ta ɗauka ta miƙa mashi su, amma a haka yake cewa kada wasu su karya mashi yara basu iya ɗaukarsu ba, Aseef duniya.

Yau ta kama Monday, tun karfe 7 Lion ya hau shiri. A tunanin Rimsha office zai tafi, sai kuma taga akasin haka, dan ba shirin zuwa office yake yi ba, abin ya yi mugun bata mamaki.

Yana gaban mirror yana gyara dark black curly hairnsa ta fito daga cikin toilet É—aure da towel a kirjinta ta same shi.

Karisowa wajensa ta yi tana faÉ—in. "Noorish ina zaka je da irin wannan shiga haka? Yau kuma me ya haÉ—aka da Army's shirt?".

Yana aiki sauri sauri ya bata amsa a takaice da cewa. "Wajen su Areef".

Da yake bata san ina su Areef É—in suke ba, bata san ina suka tafi ba, sai ta ce. "Amma Noorish tafiya zaka yi ne da irin wannan shiga haka? Kuma naga kamar harda gun ka É—auka, to dai nima zan bika".

Shiru ya yi bai bata amsa ba, domin harshensa ma wani irin azababben nauyi take yi mashi, yau ba zai iya hakuri ba sai ya bi bayansu Areef, sai dai duk abin da zai faru ya faru, tun da ya tashi barci yau da asuba, zuciyarsa take tsananin buga mashi da karfi karfi, kuma already kunsan zuciyar QUADRUPLE tana irin wannan bugawar ne idan wani abin ya sami É—ayansu, so yana kyautata zaton akwai abin da ya sami Areef, hakan yasa ya ji ba zai iya zama ba, duk bala'i yau da izinin Allah sai ya kai in da É—an uwansa yake!!. To fa babbar magana.

FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA CE.....✍️🔥

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️❤️🔥

*KINDADE KINA NEMAN ABUN DA ZAI SANYAKI QIBA,QIBA MEKYAU KIYI DIMIMI DUK INDA KIKA SHIGA BABU RAINI KINYI TA SIYA KINA ASARAR KUDINKI🤔
ALBISHIRINKI NAZO MIKI DA ABUN DA ZAKISHA BA TARE DA KINYI ASARAR KIDINKI BA 💃 Yana da matiƙar kyau sosai ko'ina naki zai chiko ki xama abar sha'awa duk mai buƙata ta nemeni ta wannan number 09067614054, kada ki bari ayi babu ke, kayanmu tested and trusted ne, guarantee ne*.

*KINDADE KINA NEMAN ABUNDA ZAI SANYA KISAMU XAMAN LFY TARE DA KWANCHIYAR HANKALI? TO BABYN HABIBI KIXO UMMU AFFAN TAXO MIKI DA SHAHARARRUN KUMA INGANTATTUN MAGUNGUNAN MATA, KAMA TUNDAGA KAN HUMRA, TURAREN WUTA,
INFECTION KILLER,
COLACCA,
SAI KAYAN GYARA PAGE.
KACA KACA.
YALLAGWADA.
JIGIDA.
RUWA RUWA.
BANI BANI.
WOMEN JELL BATA BATA.
DAFIN KAXA.
TANTABARA.
XABUWA.
CICCIƁI.
AND EXCLUSIVE, XUMA TASTED AND TRUSTED INA FARIN CHIKIN SANAR DA KU MUN FARA RAMADAN PROMO GAME BUQATA XA A IYA TUNTUBA NA TA WANNAN NUMBER
09067614054 JIGAWA STATE MUNA AIKAWA KO'INA CIKIN AMINCI DA YARDAR ALLAH,
BABYN HABIBI KARKIMANTA DA KAYANMU FIRST CLASS NE, DAGA KANSA AN RUFE KOFA, YANA DA INGANCI NA WUCE TUNANINKI*.

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥

https://whatsapp.com/channel/0029VaMOfZZI7BeKXPU9gK2S

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥

TSARAWA DA RUBUTAWA......✍️

❤️FATEEMA ZAHRA MUSA (💫PRINCESS TEEMA💋)

*Domin samun damar karanta littafin nan daga farko har karshe zaki iya nemana ta wannan number 08161390581*

E51

"Noorish baka ce komai ba, na ce fa zan bika". Ta yi maganar kamar zata yi mashi kuka.

Ta cikin mirror ya zuba mata idanu yana kallonta, ta rame sosai, ga wasu kasusuwa da suka bayyanar mata a wuyarta, tamkar ba Meesharsa Æ´ar dumur mur da ita ba, yanzu ta dawo sai a slow, sai dara daran fararen Sleeping eyes É—in nan zaka gani, hakan yana nuni da cewa kullum a cikin damuwa take.

Sai ƙoƙarin latsa wayarta take yi tana son kiran number Anaya a kan ta zo su haɗu a part na gwaggo, sam bata lura da yana kare mata kallo ta cikin mirror ba, ga shi daga ita sai ɗan ƙaramin a kirjinta, wanda kuma tsawonsa sam bai gama rufe mata rabin santala santalan cinyoyinta ba.

Tun ranar da aka sace daddyta, tun ranar Lion ɗin bai sake kusantarta ba, saboda suna cikin wani hali, sam baya ma jin wata sha'awa face damuwa, daddynta ya zamar mashi wani ɓangare ne na rayuwarsa, hakan tasa baya jin sha'awar komai face tunanin daddyn nata.

"Meesha". Ya ambaci sunanta in a cool voice.

ÆŠago da idanuwa kawai ta yi ba tare da ta É—ago da kanta ba.

Juyowa ya yi gareta da kyau tare da buÉ—e mata hannayensa a kan ta zo gare shi.

Cool murmushi ta sakar mashi da ramammiyar kumatun nan nata, da sauri ta taho ta faÉ—a saman Lion chest nasa.

Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya sa hannu ya rungumota da kyau da kyau.

Ƙanƙame shi ita ma ta yi, kamar nace zan kwace mata shi......😒

"Meesha kin rame sosai". Ya faɗa can kasan maƙoshi.

"Kai ma ai ka rame sosai Noorish". Ta bashi amsa tana É—an É—ago da kanta.

Zai sake yin magana Tvn dake manne a bangon É—akin nasu wanda yake haÉ—e da camerar É—akin Jehan ya fara fitar da sauti mai kama da sautin numfashi.

A hanzarce ya É—ago da blue eyes nasa tare da kai kallonsa saman screen É—in Tvn.

Ai bai san lokacin da ya saketa a dubu É—ari ba ganin abin da yake faruwa. Ita kanta bata san lokacin da ta waro idanuwanta waje tana kallon Jehan É—in ta cikin screen É—in ba.

Kafin ta yi mashi wani magana tuni ya fice daga É—akin cikin sauri. A hanzarce ta bi bayansa ko mayafi bata É—auka ba, daga ita sai wannan towel É—in.

Yana saka kafarsa a cikin bedroom ɗin da Jehan ɗin take ciki, baby na faɗowa, ashe tun ɗazun naƙuda take yi, kun san halinta da dakiya tare da juriya, duk azabar nan da take ji ta daure ta kuma jure, sam bata nuna alama ba, sai da abin ya fi karfinta ne haihuwar ta zo gadan gadan, shi ne ta rasa ya zata yi, kuma karfinta duk ya kare, ta rasa mada fa, hakan yasa ta zamo ta sauko kasa daga saman bed ɗin nata, a nan ta cigaba da murkusoso tana fafutuka har sautin numfashinta ya fara fita da karfi karfi, ta so ta lallaɓa ta tafi wajen gwaggo a lokacin da ta sauko kasan gadon, amma ina karfinta duk ya kare, ta jigata sosai, hakan yasa ta kasa iya tafiya koda da ja a kasa ne, ta kasa, shi ne kawai ta hakura ta zauna a kasan tana ta fama ta kuma zubawa sarautar Allah iso.

Duk tsananin kin yara da Lion yake yi yau da hannunsa ya É—auki babyn Jehan a cikin jini, saboda babyn ta haife shi da riga, abin da ake nufi da babyn da aka haifa da riga shi ne, wanda ake haifarsa yana zuwa da wani abu mai kamar yana da yake rufe mashi fuska, wanda idan ba'ayi saurin cirewa ba yana kashe yaro nan take, dan yana tare mashi numfashi ya hanasa yi, hakan ce tasa Lion É—in ya É—auke shi cikin jinin ya yi saurin yage abin ya cire.

Da gudun gaske Rimsha ta shigo cikin ɗakin, kan Jehan ɗin ta ƙariso tana ambatar sunanta da karfi.

"Get out Meesha". Shi ne abin da Lion ɗin ya ce da ita yana ƙoƙarin janyo duv dake saman bed ɗin dan ya kwantar da babyn dake hannunsa.
Chapter 154 · 0% Book details