← Book details Triplets Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 120 OF 168

Sashe 120

Triplets Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan dutsen suka nufa, tafiya suna rinƙa yi mai ɗan nisa kafin su isko wani abin da zukatansu suka kasa yarda da abin da idanuwansu suke gani, kallon juna suka yi kafin su sake mayar da kallonsu a wajen. Wani katafaren gida na alfarma ne a wajen, gini ne wanda ya amsa sunansa gini, tsabar kyan wannan gida sai ka ɗauka aljanu ne suka kera shi ba mutane ba. Tashin sense!! Waye zai zo cikin wannan kungurmin daji ya yi wanna tampatsetsen gida haka? Shin gidan mutane ne ma ko na al'janu? Dan dai wannan gini tsarinsa bai yi kama da tsarin gine ginen gida nan Nigeria ba.

BuÉ—e baki ta yi zata yi magana, cikin sauri ya rufe mata bakin da tafin hannunsa, a kunne ya raÉ—a mata ta yi shiru kawai su je. Ba musu ta ja bakinta ta yi shiru, hannunta ya riko cikin nasa, sannan suka nufi cikin gidan babu ko alamar tsoro a tattare da shi.

Tamkar wani jarumin sadaukin yaki ya sa hannu ya buÉ—e tampatsetsen gate É—in wannan gida. Gida ne dai tamkar gidan sarauta, komai na more rayuwa da akwai a cikinsa, sai dai kuma a tsakiyar dokar daji yake!!.

Ciki suka shiga, tsorata iya tsorata Jehan ta yi, sai dai bata nuna mashi ta tsorata ba, ta daure tare da dakewa suka kutsa har can cikin gidan. Katafaren parlourn ya ji komai na more rayuwa. Fasa shiga can cikin parlourn Areef ɗin ya yi, saboda ya hango wata ɗaki mai matuƙar abin tambaya a tattare da ita daga ɗan can gefe a harabar gidan ta wajen flowers, ko'ina a gidan fentin yellow da fari ne, amma shi wannan ɗakin fentinsa baki ne da jajir kamar jini, daga ta sama rabin ginin ɗakin fentin jajir ne kamar jini, daga ta kasa kuma bakin kirin kamar zunubi. Hakan yasa Aseef ɗin ya dasa ayar zargi a kan wannan ɗakin, shi ne yasa ya fasa shiga cikin parlourn ya juyo suka nufi wajen ɗakin.

Yana zuwa babu ko shakka bare tsoro yasa hannu ya wangale tampatsetsiyar kofar É—akin wadda take baka kirin kamar zunubi. Saman É—akin ma dakin ne ba kwano bane ba, hakan yasa É—akin yake da duhu sosai, ga kuma babu Windows a cikinsa. Suna buÉ—e kofar wani irin haske ne ya kauraye cikin É—akin.

ÆŠakin empty yake babu komai, floor nasa ma siminti ne ba tiles ba, tamkar irin waÉ—an nan gingima gingiman storys na manyan kasuwanni da ake yi dan ajiyar kayan hatsi kada su lalace.

Can suka hango mace a kwance zindir babu kaya a jikinta a kasar floor ɗin, gashin kanta a barbaje kamar wata mahaukaciya, ko motsi bata yi, ga jini dake zuba ta karkashinta, kamar wadda aka yi wa fyaɗe, jikinta ya yi wani irin green color tamkar wadda ta jima da mutuwa ta fara ruɓewa, kafafunta duk a kumbure tamkar ruɓaɓɓen alala, sam babu numfashi a tattare da ita.

Ihu Jehan ta kurma tana faÉ—in "Adiva!! Adiva!! Wlh she's.........". Bata kai karshen maganar ba ta kwasa a guje ta afka cikin É—akin, ba tare da yin wata tunani ba.

A dubu ɗari Areef ɗin ya yi ƙoƙarin dakatar da ita, sai dai ina ta rigada ta shige ciki da gudun gaske. Nan take ɗakin kuma ya fara wani irin kururuwa tamkar kukan zaki a lokacin da yake jin yinwa, wani irin kura mai haɗe da hayaki ne ya bule gabaɗaya cikin ɗakin, daga ita Adivar har Jehan ɗin da ta afka cikin ɗakin Areef ɗin ya dai'na ganinsu, saboda wannan turnukin hayaki da kuma kura, ga kurar da shiga hanci da ido, shi kansa a haukace ya ja da baya, saboda wani irin azababben tari da yafara yi, kan kace me jini ya fara fitowa daga cikin bakinsa da hancinsa na wannan tari da yake yi.

Daga ina wannan hayaki da kura suka fito⁉️bayan kuma kasar ɗakin siminti ne ba kasa ba bare ace dama akwai kasa za'a iya samun kura! Gidan wanenen a dokar dajin nan⁉️ ina su Jehan ɗin suka yi da suka bacewa Areef ⁉️ meyasami Adivan⁉️ ta mutu ne ko tana a raye⁉️.

Kai, kai, kai TRIPLETS dai ba zai dai'na cazamun kai ba sai ranar da na ajiye alkamanina, ma'ana na dasa aya a littafin kenan, ina ga a ranar ne zan huta da cakwakiyarsa🥲 irin wannan cakwakiya haka?! Duk fa wannan daɗi, sugar da karɗi tare kuma da cakwakiya na littafin TRIPLETS wasa ne a kan next book nawa da zan sakar maku! Kada kuma fa ku manta na gaya maku shi littafin TRIPLETS tamkar ina barci haka na rubuta shi, shi kuma next book nawa da zai zo maku idan Allah ya kaimu na kammala littafin TRIPLETS, shi sai da na waro idanuna,👀 na nutsar da kwakwalwata🧠 na taushi zuciyata🫀 sannan na iya fara typing nasa, saboda na daban ne, idan nace maku na daban ne, to fa ina nufin na daban ɗin ne, salonsa ya sha banban da kowani story, tafiyar ta manyan kai ce,🔥 dan za'ayi ɓarin wuta🔥dan haka kada ki yarda baki karanta wannan book ɗin ba, ayi babu ke, idan littafin TRIPLETS yazo da zafinsa, to shi kuma wancan da tafasa yake tafe, tafasa yake yi bul bul bul!🙃 Yana hayaki mai tashin kai!!🔥 Ba zan gaya maku sunansa a yanzu ba😂 sai a karshe littafin TRIPLETS sunansa da ɗan takaitaccen bayani a kansa zai zo maku❤️🔥 MA'ASSALAMA, TAKU HAR KULLUM FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA ZERO TENSION❤️🔥

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️❤️🔥

*KINDADE KINA NEMAN ABUN DA ZAI SANYAKI QIBA,QIBA MEKYAU KIYI DIMIMI DUK INDA KIKA SHIGA BABU RAINI KINYI TA SIYA KINA ASARAR KUDINKI🤔
ALBISHIRINKI NAZO MIKI DA ABUN DA ZAKISHA BA TARE DA KINYI ASARAR KIDINKI BA 💃 Yana da matiƙar kyau sosai ko'ina naki zai chiko ki xama abar sha'awa duk mai buƙata ta nemeni ta wannan number 09067614054, kada ki bari ayi babu ke, kayanmu tested and trusted ne, guarantee ne*.

*KINDADE KINA NEMAN ABUNDA ZAI SANYA KISAMU XAMAN LFY TARE DA KWANCHIYAR HANKALI? TO BABYN HABIBI KIXO UMMU AFFAN TAXO MIKI DA SHAHARARRUN KUMA INGANTATTUN MAGUNGUNAN MATA, KAMA TUNDAGA KAN HUMRA, TURAREN WUTA,
INFECTION KILLER,
COLACCA,
SAI KAYAN GYARA PAGE.
KACA KACA.
YALLAGWADA.
JIGIDA.
RUWA RUWA.
BANI BANI.
WOMEN JELL BATA BATA.
DAFIN KAXA.
TANTABARA.
XABUWA.
CICCIƁI.
AND EXCLUSIVE, XUMA TASTED AND TRUSTED INA FARIN CHIKIN SANAR DA KU MUN FARA RAMADAN PROMO GAME BUQATA XA A IYA TUNTUBA NA TA WANNAN NUMBER
09067614054 JIGAWA STATE MUNA AIKAWA KO'INA CIKIN AMINCI DA YARDAR ALLAH,
BABYN HABIBI KARKIMANTA DA KAYANMU FIRST CLASS NE, DAGA KANSA AN RUFE KOFA, YANA DA INGANCI NA WUCE TUNANINKI*.

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥

https://whatsapp.com/channel/0029VaMOfZZI7BeKXPU9gK2S

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥

TSARAWA DA RUBUTAWA......✍️

❤️FATEEMA ZAHRA MUSA (💫PRINCESS TEEMA💋)

*Domin samun damar karanta littafin nan daga farko har karshe zaki iya nemana ta wannan number 08161390581*

Date: 23/5/2024

E38

Tari sosai Areef ɗin yake yi tamkar maƙoshinsa zai fashe, wannan kura da kuma hayakin sai kara yawaita a wajen yake yi.

Sun ɗauki a kallah 5 mins a haka kafin wannan kura da kuma wannan hayaki ya dakata cak, haka zalika shi ma Areef ɗin tarin nasa ya tsaya cak, abin mamakin kuma jinin dake fita daga bakin nasa shi ma sai ya ɓace ɓat, nan take ya koma normal kamar babu komai. A wani irin zafafe ya nufi ɗakin gadan gadan.

A sume ya isko Jehan ɗin, ta sume kwance kusa da Adiva ɗin. A zafafe ya karisa cikin, kai tsaye kanta ya nufa, cikin zafin nama ya kai hannu yana ƙoƙarin taɓata, tamkar daga sama wata halitta mai kama da shanuwa ta bayyana a gabansu. "Hasbunallahu wani'imal wakil ". Ya furta tare da ɗago da kallonsa izuwa kan wannan halitta.

Nan tane wannan Halitta ta kurma wani irin kururwa mai matuƙar doɗar da kunnuwar mai sauraro, kururuwar sai da ta amsa a gabaɗaya ilahirin dajin, wani irin amon sauti mai bala'i kara mara daɗin ji take fitarwa, bakinta na fitar da wata iriyar bakar hayaki, ko kaɗan wannan halinta bata da kyan gani, tsabar muninta ma sai idan kana da karfin imani ne zaka iya ganinta, ga wani ɗan iskan kaho a tsakiyar hancinta tamkar kawon shaiɗan, hancin nata kam sai dai mu ce subhanallahi, saboda wani irin bala'i muni, ga wasu garman hakwara tamkar kopaton doki. Duk wannan hayaki da kurafa kenan alama ce ta bayyanar wannan halitta.

Sake furta hasbunallahu wani'imal wakil Areef ɗin ya yi tare da miƙewa tsaye suna fuskantar juna da wannan halitta, ko kaɗan bata bashi tsoro ba, saboda yasan abu ne na tsafi, shi kuma ya riki Allah, yana da kwarin gwiwa, sannan yana jin zai iya karawa da kowa da komai, dan haka ko a jikinsa.

Wani irin kururuwa wannan halittar ta sake zunduma tare da durkushewa kasa a saman gwiwowinta. Kafin Areef É—in ya yi wani yunkuri halittar ta daka uban tsalle! Ta haye kansa.

Kokawa suka fara yi da gasken gaske, cikin ikon Allah, Allah ya bawa Areef É—in dama ya samu ya murÉ—e wuyar halittar, nan take ta kurma wani ihu wanda sai da ya sanya Jehan ta farfaÉ—o daga sumar da ta yi, shi kuma Areef ya yi maza ya toshe kunnuwarsa da hannayensa, saboda bala'in karar wannan halitta.

Kasa wanwar halintar ta zube, nan take ta rikiÉ—a ta koma ainahin halittar mutun. Cikakken namiji ne kuma babban mutun, ba kowa bane kuma face Abbon Nawid!! Tashin sense, dama kenan nan ne wajen tsafinsa kenan? Meyake yi da Æ´an matan idan ya kawosu nan? Ga dai Adiva ko me ya yi mata? Ta mutu ne ma ko tana raye?.

Kawar da kallonsa daga kan Abbon Areef ɗin ya yi, ya mayar da kallon nasa a kan Jehan da ta miƙe tsaye cikin fitar hayyaci, gabaɗaya a birkice take, waje ta nufa da gudu. A hanzarce ya rikota tare da jawota jikinsa yana ambatar sunanta kasa kasa. Baiwar Allah wannan kururuwar da Abbon ya kurma lokacin da yake wannan halintar ne ya birkita mata kwakwalwa.

Jin ya ambaci sunanta yasa ta dawo dai'dai, ƙanƙanme shi ta yi tare da sakar mashi kuka mai tsuna zuciyar mai sauraro, rarrashinta ya fara yi cikin nutsuwa yana mai da numfashi.
Chapter 120 · 0% Book details