Sashe 125
Triplets Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ÆŠago idanuwansa ya yi ya sauke a kan yaran nasa, yanzu su dukka biyar É—in nan Æ´aÆ´ansa ne bai sani ba, iya cikin su QUADRUPLE kawai ya sani, bayansu bai san komai ba, suma QUADRUPLE É—in bai san su huÉ—un bane a cikin gwaggon, saboda a lokacin cikin nata karami ne, so ya É—auka ma yaro É—aya ne.
Suma kallon shi suke yi, alama ya yi masu da hannu a kan su zo gare shi, dukkansu suka miƙe amma banda Lion, dan shi da aka sake bada wannan labari ma an sake ɓata mashi rai ne, ji yake yi meyasa suka yi sakaci har Cherish ta kashe kanta? Ai da hukunci mai tsauri zata fuskanta, sannan wlh ba zai bar su His Excellence ba, sai sun ɗanɗani kuɗarsu, dan haka ya kasa tashi ya karisa wajen Dr William ɗin ma, ya zauna yana ta binsu da idanu kawai.
Rungume juna suka yi da Dr William É—in, a gefensa suka zazzauna, sai shafa fuskokinsu yake yi kamar ance za'a kwace mashi su, sam bai nuna cewa baya son ko É—aya daga cikinsu ba, harta Æ´aÆ´an Cherish É—in ma, dan idan baku manta ba ai ya musulunta kafin su juyar mashi da kwakwalwa, so yana da ilimin addini ai, yasan laifin wani baya shafan wani, dan haka sai ya haÉ—asu ya rungume, yana shafa fuskokinsu yana kallon Lion da yake zaune yana binsu da kallo.
Alama ya yi mashi da hannu a kan yazo mana shi ma. Nisawa ya yi tare da miƙewa a hankali, yana isa wajen bed ɗin Aseef ya tashi ya bashi waje, kusa da Dr William ɗin ya zauna tare da ɗan sunkuyar da kansa kasa kaɗa, bawan Allah ƙoƙarin dannar zuciyarsa kawai yake yi, dan yazo har wuya, gaskiya an cucesu da yawa, jikinsa har tsuma yake yi a kan su His Excellence, barema wannan tsinanne Anderson ɗin, ji yake yi tamkar ya yi mashi gashin kazar Hausa, kun san kazar Hausa ce sai ta ji wuta sosai take gasuwa, to haka Lion yake ji zai yi wa Anderson idan ya kama shi............. Lallai Anderson zai gasu ba karya😂
A takaice yau dai sun yi wunin farinciki, duk bayan ƴan mintina sai Dr William ya tambayi Lion yasu gwaggo, sai dai Lion ɗin ya ce mashi suna hanya, sun kusa sauka, duk ya damu yana son ganinta bawan Allah, shin zata yarda ta karɓe shi kuwa?.
Sai can rana ta yi sanyi jirgin su gwaggo ya sauka a cikin Washington, sam Lion yaki sanar da Dr William cewa sun sauka lafiya, yana son kawai suzo gida su haɗu, baya son su tada mashi da tarzoma a airport, dan yasan wlh gwaggo ba zata karɓi Dr William a cikin sauki ba, ko da ta ji meyafaru, shi kuma Dr William ba zai iya ganinta ya daure har sai sun dawo gida ba tare da ya yi mata magana ba, so zasu iya tada masu da rigima a cikin airport ɗin, shiyasa sai ya boye mashi, suka barshi a gida suka tafi airport shi da sir Arvin da kuma daddyn Rimsha, shi ma Aseef yana wajen daddynsa ai, bai ma san su gwaggon sun iso ba, Pinky ma tana wajen Dr William, saboda ita ta saba da shi a rayuwar da suka yi a kasar China, dan haka sai ta sake jiki ta manne mashi.
Kafin su Lion su isa airport ma airport É—in ta cika makil da jama'a, saboda kowa ya ji labarin jet É—in Lion ta sauka a airport É—in, so kowa zai so ya san daga ina jet É—in ta fito? Su waye kuma a cikinta? Dan haka manya manyan mutane masu faÉ—a a ji, sojoji da kuma Æ´an'sanda sun cika airport É—in tab, ga kuma Æ´an jaridu kala kala makil a cikinta.
Sai dai su gwaggo basu fito daga cikin jet É—in ba har sai da motocin su Lion suka danno hancinsu a cikin airport É—in, sannan ne Areef ya yi umarnin da a boÉ—e masu jet É—in su fita.
Sojoji biyun nan ne suka fara fitowa, sannan Alex ya rufa masu baya, sai Dr Salman and Brr Naurat da suka biyo bayansu suna shawagi kamar wasu taurari, kun san hasken Brr Naurat ba irin nasu bace, ta fi su Aseef haske sosai da sosai, duk da suke Turawa dukkansu, amma ta fisu haske, tayi fari over har haske ya so ya yi mata yawa, shiyasa gwaggo take sajewa da Turawar ai, saboda hasken Brr Naurat ke gareta, dama ita gwaggo ai Baturiya ce ba bakar fata ba, duba da yanayin yanda take ga ta girman kasar Russia.
Gwaggo da Æ´an matanta tare da Areef sune a karshen fitowa, mummyn Rimsha ma ta rigasu fita, sun bar su Adiva a cikin jet É—in, daga baya za'a É—aukesu.
GabaÉ—aya wajen motocinsu Lion É—in suka nufa, Æ´an jaridu da shegen gulma duk da basu san su waye bane, sai É—aukarsu a hoto suke yi, saboda sun gansu daga cikin jet É—in Lion suka fito.
Wani irin birki gwaggo ta ja a dai'dai tsakiyar airport ɗin lokacin da idanuwanta suka sauka a kan Lion da sir Arvin da suke tsaye a jikin motar Lion ɗin suna ɗan tattaunawa. Sam sam bata san da zancen sir Arvin ɗin ba, sun ruɗar mata da ƙwaƙwalwa, ta kalli Lion ta sake kallon sir Arvin, ga shi sun yi shigar kaya iri guda, Lion yasa nasa shi kuma sir Arvin ya sanya kayan Areef, so kayan iri ɗaya ne sak, dama haka kayan TRIPLETS suke, abin da ɗaya yake da shi sauran ma suna da shi, so sun fito tamkar mutun ɗaya ne, mai iya rabe su sai Rimsha da Pinky, dan Rimsha idan Lion goma masu kama ɗaya za'a kawo mata, to ba shakka zata fitar da nata Lion ɗin daga cikinsu........... Haƙiƙa ta yi wa masoyinta farin sani🤌😂
Sam gwaggo bata san time É—in da ta saki hannun Rimsha ba, dama ta rike hannunta É—in ne saboda É—ingisa kafa da Rimshar take yi, shi ne yasa ta rike hannunta dan ta taimaka mata, amma ganin sir Arvin da Lion yasa ta saki hannun nata tana binsu da kallo, ta kasa iya cigaba da tafiya.
Ganin hakan yasa Lion da sir Arvin É—in suka nufota a tare, a lokacin kuma tuni su Brr Naurat sun shiga cikin motocin da suke jiransu, shi kansa Areef kasa cigaba da tafiya ya yi, duk wanda yasan cewa TRIPLETS mutun uku ne ba huÉ—u ba, sai da ya dakata da tafiya a lokacin, Rimsha ma ta sha ruwan mamaki sosai, amma Akila da Jehan basu wani sha mamaki ba, wucewa ma suka yi izuwa cikin motocin, dan su dama can ba wani sanin Lion suka yi ba, bare su sha mamaki dan an sami mai kama da shi, dama basu gama sanin su waye TRIPLETS É—in ba.
Tga ma dai tsayawa ya yi yana kallon ikon God.
A tare suka iso wajen gwaggon, welcome suka yi mata, sir Arvin ya riga Lion rungumeta, dan Lion É—in ya gaya mashi ita ce mommansu, kuma shi ma ya ga hakan a face nata, saboda tana kama da Aseef idan ka ganta a fisge, kuma ita gwaggo na gaya maku farar baturiya ce, bata da banbanci da su.
Shi kuma Lion a ɗan gefe guda ya tsaya yana karewa Rimsha kallo, ƙunshin jikinta kawai yake kallo, sam baya so, amma a yanzu dai bashi da zaɓin da ta wuce ya kawar da kallonsa daga kan ƙunshin nan, shi ne zamansa lafiya, dan haushinsa ake ji..........😂
Sam gwaggo bata san wanenen ya rungumeta ba, bata san sir Arvin ne ko Lion ba, ita dai ta shiga ruÉ—ani, kanta ya kulle, sai kawai ta rungume shi ita ma.
Areef ne ya matso kusa da su yana tambayar Lion wanene wanda ya rungumi mommansun nan.
Harararsa Lion É—in ya yi kafin ya ce "Saif ne mana".
Siririn dariya Areef ɗin ya yi yana faɗin "Sai dai biyunin Saif, wai kai Lion kana tunanin ko mutuwa nayi na dawo ba zai iya tsamoka daga cikin dubu irinka bane? To idan ma haka kake tunani ka makara, ni dai nasan TRIPLETS nawa TRIPLETS nawa ne babu in da zasu je su ɓuya mani ban iya gane su ba, yanzu dai gaya mani wanene ya rungumi momma? Dan brain nawa tana dab ta tarwatsewa, irin wannan kama haka".
Kin kara tanka mashi Lion É—in ya yi, saboda bai son buÉ—e baki a cikin taron wannan uban jama'a haka.
Ko'ina hasken ɗaukar hoto ne kawai yake tashi a airport ɗin, daga masu cameras har masu wayoyi, abin ya girgiza jama'a, sun rasa wannan baki da gidan The General of the Army's yake yi na menene? Suna son jin su wanenen suke ta zuwa gidan, jiya wasu sun je, yau kuma ga wasu, anya lafiya kuwa? Babban abin da yafi damun jama'a ma shi ne, yadda yau suka ga Lion a cikin bakaken fata, shi da kowa ya sani a baya sam baya son bakaken fata, dan ma dai Allah yasa yawancin familyn gwaggon turawan ne ita ma, saboda kal kal suke kamar ka taɓa jini ya zuba, musamman daddyn Rimsha da Azharuddin Bature, so mix nasu da bakaken fata dai kaɗan ne, iya gefen Dr Salman ne, wanda kuma mutun biyu ne kawai daga cikin ƴaƴan nasa suka fito chocolate colors irinsa, sauran duk brr Naurat suka yo, shi kam Alex ma ai ba'a magana, harta blue eyes ke gare shi, sak su yake.
WaÉ—an da basu ganin abu su yi shiru har sun fara tofa albarkacin bakinsu a kan su waye ne su gwaggo?.
Kasa hakuri gwaggon ta yi har sai da ta tambaya ya aka yi suka zama su biyu masu kama É—aya? Ta manta da cewa jariranta biyu ne masu blue eyes kuma kamanninsu É—aya sak, sannan Lion bai sanar da ita abin da ya je yi a kasar China ba, ya dai ce mata ya je yin wani aiki, so bata san da zancen komai a kan su Cherish ba.
Kasa kasa Lion ya ce mata "Idan mun je gida kun huta zuwa gobe zan gaya maki".