← Book details Triplets Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 168

Sashe 26

Triplets Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bai zame ko'ina ba sai ɗakin gwaggo. Zaune ya iskota ita da Aseef, sai kukan shagwaɓa yake zuba mata, ya haye mata gado tare da tada kai da cinyarta, shi dole sai an ɗauko mashi matarsa, ta ce ya yi hakuri tun da sun kira Areef a waya ya ce zai zo da ita, to ya dai'na kuka zata dawo, kwafa ya yi tare da gayawa gwaggon Allah yau ba zai kyale Heartbeat ɗin nan ba, sai ya bata wahala fiye da tunanin kowa, ita dai gwaggon, sai rarrashi kawai take yi.

A gefenta ya zauna, tare da zaunar da Rimshar a gefensa. Cikin sanyin murya ya ce "Momman i want to ask you something!".

Dawo da kallonta a kansa ta yi tana faÉ—a mashi tana jinsa.

"Momma a wani gidan kaka É—aya kika kaiwa daddy mu time É—in? And them a wani gida kuka zauna da Josephine?".

Ba tare da ɓata lokaci ko wani dogon tunani ba ta bashi amsa kai tsaye, dan bata manta komai ba, komai yana nan a cikin brain nata.

Wayarsa ya ɗauko, cikin sauri ya kira Tyrone, dan dama already Tyrone ɗin ya koma shi kam. Bugu ɗaya ya ɗaga, ba tare da ɓata lokaci ba ya ce mashi ya je gidan da su Dr William ɗin suka zauna, dan gidan yana nan yanda yake, babu abin da aka taɓa a ciki tsawon shekarun nan, sai ma zuwa da ake yi ana gyara shi kowani sati, so komai yana nan normal, dan haka Tyrone ya je gidan da akwai camera a palon gidan, ya ciro mashi camerar yanzun nan, ba tare da ɓata lokaci ba, sannan ya shiga ainahin computers room da yake cikin gidan, ya duba stories, ya ɗauko mashi memory na shakaru 31 zuwa 32 baya.

Okey Tyrone ya amsa da shi. Katse kiran ya yi tare da miƙewa ya nufi waje, bin shi da kallo dukkansu suka yi, harda Rimshar.

Sai bayan ya fita ne Rimshar ta ce "Yaya Aseef ni ka tashi mani a saman cinyar gwaggona zan kwanta".

Kin kulata ya yi, sai aikin tura baki yake yi abinsa. Gwaggon ce ta ce mata ta zo ta kwanta a gefe, ta rabu da Aseef É—in nan, rigima yake ji dashi, yanzu ya tashi barci, ko breakfast bai yi ba, ya tsayar masu da rigimar sai an É—auko mashi Akila.

Tuna cewa Lion bai ci komai bane yasa ta miƙe tare da cewa Gwaggon a'a tana zuwa dai.

Ɗakin da suka fito ta koma, abinsa ta ɗauko mashi, sannan ta dawo cikin bedroom nasa. Zauna a saman bed ta iskosa, ya sanya laptop a gaba yana ƙoƙarin kunnata. A saman carpet ta ajiye abincin, sannan ta dawo kusa da shi ta zauna.

A tsananin shagwaɓe ta ce "Noorish, idan baka jin yunwa, Meeshan ka fa tana jin yunwa, ban fa ci komai ba, kuma ni da kai nake son muci abinci".

Yanda ta yi maganar tasa bai san time da ya juyo gateta ba. Yana juyowa ta faɗa jikinsa tana zuba mashi shagwaɓa.

Nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke, wani irin sanyi ya ji a ransa, hannu ya kai ya shafi kanta, ƴar karama da ita, amma ta samu tarbiya sosai, ta kuma iya soyayya sosai, duk fushi da halin mara daɗi da mutun zai shiga, ta san ta yanda take kwantar mashi da hankali, yanzu ga shi dai a kage yake da ya fara binciken nan, har ya mance da cewa yana jin yunwa, amma daga zuwanta, ta zuba mashi shagwaɓa, har ya ji yunwar ta dawo sabuwa, sai ya ji hankalinsa ya kwanta sosai.

"Muje to na baki abincin a baki ko?". Ya faɗa a sanyaye. Da sauri ta ɗago kanta, tana ƙoƙarin ta yi magana, sai ga Brady ya shigo ɗakin da gudu. Kai tsaye ta kanta ya bi ya haye jikin Lion ɗin, da alama bai ma lura da ita ba.

Ihu ta zunduma tana ƙoƙarin ta gudu, rikota da sauri ya yi, sannan ya dakawa Bradyn tsawa a kan ya sauka mashi a jikinsa, zai haukata mashi ƙwaƙwalwar Meeshansa, yasa tana zunduma ihu haka.

Haushi Bradyn ya daka masu, irin ya ji haushin nan shi ma. Hannu Lion ɗin ya ɗaga zai mare shi, ai a dubu ya diro kasa, da gudu ya nufi waje, dan ya san marin Lion fa ba wasa ba, ya taɓa marinsa sau ɗaya, a lokacin ya yi mashi ɓarna, ya kuwa wanke shi da mari, to shi ne har yanzu bai mance da marin ba, da Lion ɗin ya kara marinsa, gara ya gudu abinsa.

"Kin cika tsoro Meesha, Brady is your friend, ki dai'na tsoronsa, babu abin da zai yi maki, kuma shi ba zai dai'na shigowa nan at anytime ba, yakamata ki saba". Ya kai karshen maganar tare da ruko hannunta suka mike tsaye.

Wajen abincin suka nufa. Ita ta zuba masu abincin a plate. Spoon ya ɗauka tare da ɗebo abincin, yana ƙoƙarin kaiwa bakinsa, ta yi maza ta kwace tare da fara tauna. Ko sannu bai ce mata ba, ya sake ɗebo wani ya kai bakinsa. Haka suka cigaba da cin abincin cikin nishaɗi da tsantsar farinciki.

A ɓangaren gidan Abba kuwa, bayan sun tashi da safe, su daddyn Anaya sun zo, haɗuwa suka yi a palon gidan Abba, sai hira suke yi, suna jiran gwaggo da TRIPLETS nata, sai daddyn Rimsha, zasu yi magana ne a kan abubuwan da suka faru a baya.

Sai hira suke zubawa kamar ba gobe. Can wuraren karfe 12, daddyn Rimsha, mummy, Areef da kuma Jehan da Akila suka zo gidan. Nan fa hira ta kara armashi, abin ba kama hannun yaro.

Brr Naurat ce ta dakatar da su ta hanyar gabatar masu da Alex duk da cewa baya wajen, yana gidan Lion, a kage suke da son ganinsa, amma bai zo ba, yana tare da Mark.

"Zahradeen ina matanka da Æ´aÆ´anka?". Cewar Brr Naurat, ta tambayi Abbi kenan. Cikin girmamawa ya nuna mata, Aunty, Irfan, da kuma Umaisha da take a wajen, sai ya rufe da cewa Aafia tana gidan mijinta.

Murmushi Brr ta yi tare da zuba masu addu'a da ruwan albarka, sannan ta tambayi Abba ma, shi ma haka ya gabatar da nasa matar da Æ´aÆ´an, haka shi ma ta zuba masu addu'a, sai da ta bi gabaÉ—aya Æ´aÆ´an nata ta tambayesu, daddyn jelly shi ne na karshen da ta tambaya.

Kallon Jelly dake zaune kusa da Ammie ta yi shiru kamar wata mara lafiya ya yi, cikin sanyin murya ya ce "Wannan ita ce kaÉ—ai Æ´ata, Allah ya yi wa mahaifiyarta rasuwa, sai matar da na aura a yanzu". Ya kai karshen maganar yana juye juye dan neman Ayla, bata a wajen sam.

Fuska É—auke da mamaki ya ce "Sadiya ina Ayla take?". Da sauri Aunty ta É—ago kai tana Æ´an waige waige, sam babu ita a cikin palon. Tambayar juna suka fara yi, kowa yace tun safe shi bai ganta ba. Abba ne ya ce jelly da Akila su tashi su je su dubata a É—akunan gidan, wata kila tana can tana barci ne saboda ciki.

A hanzarce suka miƙe suka haura sama. Suna tafiya Abbi ya ce "Hossain me ya sami Akila a idanunta kuma?".

Girgiza kai daddyn Rimsha ya yi yana faÉ—in "Kuka ta yi mana". "Kukan me kuma?". Daddyn jelly ya tambaya da sauri. Zai sake yin magana su Akilar suka sauko suna gaya masu bata cikin É—akun dukka sun duba, har a cikin toilet dukka sun duba bata ciki. Nan fa hankulan kowa ya tashi, wannan ya kalli wannan, wannan ma ya kalli wannan.

Kasancewar da turanci suke magana, sai Areef ma ya saka masu baki, dan ya ji komai da suka ce, da turanci suke yin magana, saboda Brr Naurat bata wani iya hausa ba, Hausan nata a kwaɓe yake, dama bata iya shi sosai ba, sai kuma ta sake komawa ƙasar Russia tsawon shekaru, hakan tasa ɗan Hausar da ta iya ma shaf ta gudu daga bakinta, shi ne yasa suke magana da English.

Mikewa suka yi gabaÉ—ayansu, harabar gidan suka fito, duk suka rarrabu aka fara nemanta. Amma ina, shiru, babu ita babu alamarta, nan take mamanta ta fara kuka, dan ita ma tana wajen, daddyn Jelly tamkar zuciyarsa zata fashe, amma ya daure suka cigaba da nemanta.

JAMA'A INA AYLA TA SHIGA⁉️

Shiru shiru fa babu ita, Areef ne ya tambayi daddyn Jelly a kan ko ta ce mashi zata je wani waje ne ya hanata, shi ne ta yi tafiyarta, nan fa ya yi masu bayani, ita Ayla bata da kowa, bata san kowa ba face su Abbi, sai su Rimsha, kuma ko harabar gidansu bata taɓa fita ba tare da shi ba, kullum tana ɗaki abinta, idan kunganta a waje, to a tare suke za su fita unguwa, ita ko waya ma yanzu bata da shi, saboda cikin nata ma ya tsani ana latsa waya a kusa da ita, dan haka in dai Ayala bata gidan nan, to wlh hannu ne ya ɗauketa, tabbas ɗaukarta aka yi!!. Tashin hankali!!!

Shiru Areef É—in ya yi kafin ya sake cewa "To waye kake tunanin zai É—auketa? Shin kana da abokin gaba na bayyane ne?".

Jinjina masu kai ya yi yana faÉ—in "Baban Muneer, shi ne kawai abokin gaba na wanda ya yi niyar É—auke Jelly ya haÉ—ata aure da Muneer a lokacin baya, to bayan shi kuma, ni bani da wani abokin faÉ—a".

"Waye baban Muneer É—in? Kuma a ina yake?". Areef ya sake tambaya.

Kasancewar daddyn bashi da burin da ya wuce yaga matarsa ta dawo, sai ya basu labarin tsamar da take a tsakaninsu da baban Muneer ɗin, bai ɓoye masu ba, harda videon da ya yi mashi na sharri duk ya gaya masu.

"Aina yake to yanzu?". Areef ne ya sake tambayarsa, nan ma basu amsa ya yi da shi dai a Kano ya barosa, so bai san a ina yake ba yanzu.

Kallon Imran Areef É—in ya yi yana faÉ—in "Zamu je wajen yanzu ko prof?". Jinjina mashi kai Imran É—in ya yi.

Nan take hankulan kowa ya kara tashi, ganin da gaske Ayla fa ta ɓata ne, babbar magana.
Chapter 26 · 0% Book details