← Book details Triplets Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 158 OF 168

Sashe 158

Triplets Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shi kuwa samun tabbacin su Areef zasu iya tashi ko yanzu daga bakin Sheikh Sultan ne ma yasa ya dawo cikin bedroom nasa dan ya yi wanka, Sheikh Sultan ya ce kowani lokaci tsafin zai iya sakinsu, yana sake su kuma zasu koma normal kamar babu abin da ya taɓa taɓasu.

Bayan ya yi wanka, cikin pajamas ya shirya, sannan ya sanar da cewa kada wanda ya dame shi a yau, dan yana da abin yi nasa na kansa.

A saman bed ya iskota, sai latsa mashi waya take yi tana jiransa ya zo ya buÉ—e mata kofa ta fita.

Kwanciya ya yi tare da kurawa Tv idanu yana kallon kyawawan baby's É—in Areef, sai É—aga hannayensu sama suke yi, ga Jehan É—in kuma sai zuba barci take yi, su gwaggo sun gasa mata jikinta da ruwa mai zafi, sannan suka yi mata alluran barci, dan ta huta.

Ganin yana ta kallon yaran ne yasa Rimshar ta ce. "Noorish mu kuma sai yaushe zamu haifi namu?".

Dogon numfashi ya ja tare da saukewa a hankali kafin ya dawo da kallonsa a kanta.

"Ai ina ganin ma yanzu zaki karɓi naki baby's ɗin, ba dai kin shirya ba?". Ya yi maganar yana ɗaga mata gera ɗaya.

"Wlh Noorish na shirya, ko yanzu ka bani".

"To zo ki karɓa". Ya faɗa tare da jawota jikinsa.

"Noorish iya baby's fa kawai zaka bani, irin na Jehan ko Akila nake so".

Kasa kasa ya ce mata. "Fin haka ma zan baki, mu our baby's special ne". Ya kai karshen maganar tare da haÉ—e fuskokinsu, cikin salo ya fara aiwatar da abin da yake da niyya.

"Noorish baby fa kawai zaka bani". Ta faÉ—a a É—an tsorace.

Katseta ya yi ta hanyar zuwa mata tongue nasa a cikin ɗan bakin nata, hakan yasa ta yi shirun dole ta fara karɓar sako.

Ai yau ma ba shi ya kyaleta ba har sai da ya fanshe kewarta na tsawon watannin nan da ya yi, sannan ya rabu da ita.

Ban da kuka hawaye bibbiyu babu abin da take yi mashi, ta ji a jikinta ne ba karya.

Rarrashi ya hauyi babu kama hannun yaro, sam taki kula shi.

Ganin haka sai ya ce ta yi shiru bari ya je ya yi mata wanka sai suje wajen mummynta.

Jin hakan yasa ta danne ta yi shiru, tana jin raÉ—aÉ—in zafi kam, amma a haka ta danne, dan tana son ganin mummynta.

Sumbatar lips nata ya yi yana faÉ—in. "I really love you my Meesha".

Turo bakin nan ta yi, kamar zata sa kuka ta ce. "Love you too". Ta yi maganar kamar wadda aka saka dole.

Kamar zai sake yin magana, sai kuma ya fasa tare da miƙewa ya ɗauketa sai cikin toilet.

Wanka ya yi mata kamar yadda ya faÉ—a, sannan ya naÉ—ota a towel ya dawo da ita saman bed, ya koma cikin toilet, dan ya yi nasa wankar, taki yarda su yi a tare ne, har wa yau kunyar yin wanka tare da shi take yi, shiyasa yake fara yi mata kafin ya yi nasa.

Kafin ya fito daga wanka har ta shirya cikin wata abayar, ta haye saman bed ta kwanta, ta yi shiru tana jin raÉ—aÉ—in da gabanta yake yi mata.

Har ya fito ya gama shiryawa bata sani ba, ta afka duniyar tunani.

Bayan ya kammala ne ya dawo wajen bed É—in.

"Let's go". Ya faÉ—a yana É—aure dark black curly hairnsa a bayan wuyarsa.

Make mashi kafaÉ—a ta yi, ta ce sai dai ya É—auketa cak, dan ita bazata iya tafiya da kafafunta ba.

Bashi da zaɓin da ya wuce ya yi hakan, dan shi ne nan ya ja mata ai. Dan haka sai ya ɗauketa cak suka nufi wajen.

Sai shafa kyakkyawar bakin gashin sajensa take yi tana sumbatar wuyarsa.

Kasa kasa kamar mai raɗa ya ce "Zaki fara ko? Ki cigaba, ai ban yi nisa da bedroom ba, sai na juya na mayar dake ciki, dama ni ban ƙoshi ba, kawai ragwantarki yasa na barki".

Ganin sun É—an yi nisa da part É—in nasu ne yasa ta ce.
"Allah Noorish ni ba raguwa bace ba".

Cak ya tsaya da tafiyar yana tambayarta. "Are you sure?".

Ganin ya tsaya ne, kuma tasan tsab zai iya juyawa da ita su koma ciki ya bata ajikinta ne yasa ta yi sauri girgiza kai tana faÉ—in.
"Am not sure, wlh yanzu ma wajen ciwo yake yi mu"
Ta kai karshen maganar kuma tare da saƙalo wuyarsa ta ɓuye fuskarta a wajen wuyar tasa.

Cigaba da tafiya ya yi ba tare da ya sake ce mata komai ba, Æ´ar rigima kawai.

Bai direta a ko'ina ba sai a cikin room É—in, a lokacin kuma Allah da ikonsa mum ta farfaÉ—o, ta kuma dawo normal kamar yadda Sheikh Sultan ya faÉ—a, shi kuma Areef bai dawo normal ba, yes ya farfaÉ—o, amma kuma bai dawo dai'dai ba, dan lokaci da ya farfaÉ—o ya farfaÉ—o ne da karfi tare da fara yunkurin barin cikin É—akin, su Uncle T ne suka danne shi, sai fisge fisge yake yi.

Da kyar suka samu suka dannesa ya nutsu Sheikh Sultan ya cigaba da yi mashi addu'a, daga haka barci ta É—aukesa bawan Allah.

Mummy kuwa, ta dawo dai'dai sai hira da su gwaggo ma take yi, dama tsafin ne ya taɓata, a wajen faɗar tasu ne ma aka samu akasi su Anderson suna ƙoƙarin jefar daddyn Rimsha da abin tsafin, sai ya taɓata ita, shi ne ya kandarar mata da jiki kamar ta mutu.

Amma da yake babu abin da yafi karfin Allah, ayar Allah ba wasa ba, sai ga shi cikin hukuncin Ubangiji ta dawo dai'dai normal abinta.

Shi kuwa Areef sai washegari suka samu ya dawo dai'dai. Yana dawowa dai'dai kuma Jehan ya fara nema, a nan ne Lion ya gaya mashi tana nan lafiya kuma ta haifa mashi Æ´an huÉ—u jiya, ita ma tun jiyar take ta faman barci kamar me, ta gaji ne over, shiyasa take ta zuba barci kamar ba gobe baiwar Allah.

Mummyn Rimsha baki har kunne, ta ji daÉ—in samun jikoki QUADRUPLE, sai uban murmushi take yi abinta.

Cikin zumuÉ—i Areef É—in ya ce zai je ya kalli Jehan É—in. Hana shi Lion da sir Safwan suka yi, suna son ya É—an huta, Lion ya ce da gwaggo a kawo mashi baby's É—in nan ya kallesu, sai zuwa dare idan ya kara hutawa, sai ya je ya kalli maman babyn.

Haka kuwa aka yi, gwaggo ta je tare da Josephine suka É—auko baby's É—in, gwanin ban sha'awa.

Ana miƙa mashi ɗaya ya karɓa yana sakin cool murmushi.

A fili ya furta "Ga takwaran Saif nan, na hannun momma kuma takwaran Safwan, É—ayan na hannun Josephine takwaran Aseef, É—ayan kuma takwaran uncle ne (daddyn Rimsha)". Ya kai karshen maganar yana É—ago da kallonsa izuwa kan Lion É—in.

"Lion yakamata ka rike takwaran nan naka fa". Ya faɗa yana miƙo mashi babyn.

Sam Lion ɗin bai so ɗauka ba, amma kuma saboda babyn yana tsananin kama da Areef ɗin, ga shi kuma takwaransa ne yasa ya kai hannu ya karɓi yaron, sam baya son ya kalli wannan murmushin dake a saman face ɗin Areef ɗin ta kau, shi ne yasa ya karɓi baby, dan in bai karɓaba tabbas wannan murmushin zata kau daga saman face ɗin Areef ɗin.

Karɓar yaro na biyu daga hannun Josephine Areef ɗin ya sake yi yana kallon babyn sosai, nan take wasu siraran hawaye suka fara bin kuncinsa.

Zuba mash idanu Lion É—in ya yi yana kallonsa da mamaki.

"Areef meyasa kake kuka kuma?". Cewar sir Safwan, ya yi maganar a É—an ruÉ—e.

Nisawa Areef ɗin ya yi kafin ya goge hawayen nasa yana faɗin. "Dole nayi kuka, Allah mai kyauta mai kari, ya bani ƴaƴa maza har guda huɗu, tamkar fa yadda aka haifemu mu huɗu, kamar yadda Allah ya albarkaci daddynmu da samun mu mu huɗu, haka ya sake kara mana da wasu huɗun, wasu suna can suna haukar neman haihuwa, abin da kuɗi, mulki, isa, taƙama, izza, kai komai bai isa ya bada haihuwa ba, Allah shi kaɗai yake bayarwa, dole na zubar da hawayen farinciki".

Gwaggo ce ta ce mashi "Bama iya kai kawai ba, Aseef ma Allah ya bashi TRIPLETS kuma dukka maza".

Zaro ash eyes nasa ya yi yana mamaki, abin kamar a mafarki yake jinsa.

Haka suka kasance cikin tsananin farinciki har Allah ya sauki Anaya lafiya a cikin wannan sati da Jehan É—in ta haihu, ratarsu kwana huÉ—u, ita kuma Anaya ta haifo TWINS kamar daddynta kenan, idan baku manta ba daddynta ai Æ´an biyu ne da daddyn Rimsha, so ita ma TWINS ta haifa, ta gado kenan.

A nan ne fa gwaggo ta ce yana da kyau su shirya gagarumin walima na murnar samun wannan ni'ima da Allah ya yi masu, dan haka yana da kyau su Abban Imran su Abbi da sauran dangi duk su zo, su zo ayi taron suna tare da wannan walima, idan ya so daga baya sai su koma.

Haka kuwa aka yi, Brr Naurat ta buƙaci kowa da ya zo, harda daddyn Anaya da mum nata sun zo, su Irfan harda Ummin Dr Nawid kowa ya zo, daddyn Adiva shi ma yazo, mummynta ne dai shiru ba'a san in da take ba, ta mutu ko tana raye, Allah masani.

An shirya walima sosai na wuce misali, amma ba'a gidan za'a gabatar da walimar ba, a wani tapkeken hall za'ayi shi, sai shirye shirye suke yi, gobe ne walimar, sai hidima ake yi tamkar baza'a mutu ba. Su gwaggo anje shopping ya kai sau biyar, sai ta sawowa Æ´aÆ´an nata kuma matan Æ´aÆ´an nata kaya, sai taga bai yi mata ba, haka zata sake tasan jiga jigan motoci ta sake komawa shopping É—in, sai sharholiyarta take yi, tana so ne matan Æ´aÆ´an nata su tashi kan al'umma da haÉ—uwa ranar walimar.
Chapter 158 · 0% Book details