← Book details Triplets Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 168

Sashe 29

Triplets Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A gefen gadon Ummi ta zauna, shi kuma Akil ya matso kusa da shi da nufin ya tofa mashi adduo'i. Kallo É—aya ya yi mashi ya san cewa rai ya yi halinsa, babu rai a tattare da shi. Zaro idanu ya yi, sannan ya kalli Ummi dake ta faman ruwan hawaye, nan take zuciyarsa ta karaya, ya ji ba zai iya gaya mata cewa Dr Nawid ya rasu ba, dan shi ne kaÉ—ai gareta, idan ta ji zuciyarta zata iya bugawa wlh, Innallilahi wa Innallilahi ilaihir raji'un, hasbunallahu wani'imal wakil.

Daurewa ya yi ya tofawa gawar addu'a, sannan ya ce mata yana zuwa, to kawai ta bishi da shi.

Fitowa waje ya yi ya kira Abbi a waya, ya sanar mashi wlh Dr Nawid Allah ya yi mashi rasuwa, Allah ya karɓi abinsa. Ba karamin girgiza Abbin ya yi da jin wannan bakin labarinba, dukkansu Ummin kawai suke tausaya, baiwar Allah, da ma ace tana da wasu yara ne, to da da sauki, amma shi kaɗai, ga shi Allah ya karɓi abinsa, innallilahi wa innallilahi ilaihir raji'un, yanzu ta yaya za su iya gaya mata wannan bakin labarin? Matar da kullum take zarya a kan rashin lafiyar nan tasa, ko abinci bata iya ci, ta rame fiye da tunanin mai tunani, duk ta fita a cikin hayyacinta, ta firgice kamar ba ita ba, ashe maganar da Dr ya yi wa Aafiar nan shi ne maganarsa ta karshe a duniya, ya ilahi ya lillahi.

Cewa Akil É—in Abbin ya yi a kan suna zuwa yanzu, amma kada ya bari Ummin ta gane komai. Okey ya amsa tare da katse kiran ya dawo cikin palon.

After some minutes sai ga su Abbin sun iso, har da Abban Imran da daddyn jelly, shi dai Abbo shiru babu shi babu labarinsa, kuma babu wanda ya iya tunawa da shi.

Wayo suka yi wa Ummin, suka ce mata za su tafi da Dr wani asibiti ne mai kyau kafin komai na su ya kammala su wuce kasar India, dan haka ta bi Akil ya kaita gidan Abba ita da Aafia, dan kada a barta ita kaÉ—ai a gidan. Ita dai ta amsa masu da to ne kawai, amma har cikin ranta tana jin ba lafiya ba, gabanta sai faÉ—uwa yake yi, sai dai bata musa masu ba, ta bi Akil bayan an saka Aafia a motar, haka ya wuce da su izuwa gidan Abba, su Imran kuma, sun É—auki hanyar Kano dama already.

Suna tafiya su Abba suka kira jama'a, aka yi wa Dr wankar gawa irinta addinin musulunci, sannan aka shirya shi a cikin likkafani, dan su kai shi makwancinsa kuma gidansa na gaskiya......... To masu karatu zan dakata a nan wajen, sai Allah ya kai mu gobe.

*Yau na san kwakwalwarku zata shiga ruÉ—u sosai, to ina mai bada hakuri a kan hakan, labarin ne yake a haka, dole kuma zan rubuta abin da na tsara tun farko, ba zan iya canza komai na labarina ba, na san ba zaku so hakan ba, amma ina bada hakuri dai!!*

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️❤️🔥

*KINDADE KINA NEMAN ABUN DA ZAI SANYAKI QIBA,QIBA MEKYAU KIYI DIMIMI DUK INDA KIKA SHIGA BABU RAINI KINYI TA SIYA KINA ASARAR KUDINKI🤔
ALBISHIRINKI NAZO MIKI DA ABUN DA ZAKISHA BA TARE DA KINYI ASARAR KIDINKI BA 💃 Yana da matiƙar kyau sosai ko'ina naki zai chiko ki xama abar sha'awa duk mai buƙata ta nemeni ta wannan number 09067614054, kada ki bari ayi babu ke, kayanmu tested and trusted ne, guarantee ne*.

*KINDADE KINA NEMAN ABUNDA ZAI SANYA KISAMU XAMAN LFY TARE DA KWANCHIYAR HANKALI? TO BABYN HABIBI KIXO UMMU AFFAN TAXO MIKI DA SHAHARARRUN KUMA INGANTATTUN MAGUNGUNAN MATA, KAMA TUNDAGA KAN HUMRA, TURAREN WUTA,
INFECTION KILLER,
COLACCA,
SAI KAYAN GYARA PAGE.
KACA KACA.
YALLAGWADA.
JIGIDA.
RUWA RUWA.
BANI BANI.
WOMEN JELL BATA BATA.
DAFIN KAXA.
TANTABARA.
XABUWA.
CICCIƁI.
AND EXCLUSIVE, XUMA TASTED AND TRUSTED INA FARIN CHIKIN SANAR DA KU MUN FARA RAMADAN PROMO GAME BUQATA XA A IYA TUNTUBA NA TA WANNAN NUMBER
09067614054 JIGAWA STATE MUNA AIKAWA KO'INA CIKIN AMINCI DA YARDAR ALLAH,
BABYN HABIBI KARKIMANTA DA KAYANMU FIRST CLASS NE, DAGA KANSA AN RUFE KOFA, YANA DA INGANCI NA WUCE TUNANINKI*.

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥

https://whatsapp.com/channel/0029VaMOfZZI7BeKXPU9gK2S

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥

TSARAWA DA RUBUTAWA......✍️

❤️FATEEMA ZAHRA MUSA (💫PRINCESS TEEMA💋)

*Domin samun damar karanta littafin nan daga farko har karshe zaki iya nemana ta wannan number 08161390581*

E8

Suna tafiya su Abba suka kira jama'a, aka yi wa Dr wankar gawa irinta addinin musulunci, sannan aka shirya shi a cikin likkafani, dan su kai shi makwancinsa kuma gidansa na gaskiya.

A takaice su Abbi suka kai shi kabarinsa, ma'ana su suka yi jana'izarsa, sai dai duk cikinsu an rasa wanda zai iya gayawa Umminsa ga abin da yake faruwa, sai faman nuku nuku suke yi, dan suna tsananin tausayawa baiwar Allah'n nan.

A ɓangaren su Imran kuwa, sun isa Kano lafiya, kuma sun haɗu da baban Muneer a companynsa, a cikin office nasa, ya yi masu iso.

Ba tare da ɓata lokaci ba Areef ya fara jefa mashi tambayoyi, sai dai Areef ɗin da kallo ɗaya zaka yi mashi, kasan yana cikin tsananin tashin hankali, duk da bai san abin da yake faruwa da Lion ba, amma a jikinsa yana jin lallai ba shakka ɗaya daga cikinsu bashi da lafiya, dan bugawar zuciyarsa sauri take yi tamkar yanda na Lion ɗin take bugawa da sauri, duk ya firgice tamkar ba shi ba, har Imran ya iya ganewa, ya tambaye shi ko bashi da lafiya ne? Ko kuma tafiyar da suka yi a mota mai tsayin ne ya jijjiga shi?.

A'a ya amsa masu da shi, sannan ya É—aura masu da cewa, shi ai idan ya je kasar da bai sani ba, yana yin tafiya mai tsawo a cikin mota, dan ya zagaye wasu daga cikin states na garin, dama dai Aseef ne ko Lion, sune za'a ce ba lallai su iya jure tafiya mai tsawo a mota ba, dan basu saba ba, ko'ina za su je, to wlh suna zaune a cikin gida, basu fita yawace garinma bare sauran states dake makwabtaka da garin, amma shi ai yana yawo sosai abinsa, su kwantar da hankulansu, kawai dai yana jin jikinsa ba daÉ—i ne.

Bawan Allah bai san cewa Lion yana kwance a gadon asibiti ba, kuma kamar yanda yake kwance bashi da lafiya, haka shi ma Areef É—in yake tafiya da ciwo a jikinsa, da alama zuciyoyinsu a haÉ—e take over.

Kafe masu baban Muneer ya yi a kan shi bai ma san waye daddyn Jelly ba, kallon Imran Areef É—in ya yi, sai ya yi mashi magana da larabci a kan, su kyale shi da mutumin bari ya gyara mashi zama!.

Da baban Muneer ɗin yaga za su matsa mashi, sai ya ɗauko wayarsa ya yi ƙoƙarin ɗaura videon daddyn Jelly da ya ɗauke shi a media kowa ya gani, ya yi ƙoƙarin cin zarafin familyn Dr Salman kenan. Ganin yana latsa wayar jikinsa har wani kerma yake yi, ga shi kuma sai musa masu yake yi a kan shi bai san wanenen ma daddyn Jelly ba, sai yasa Areef a cikin tunani.

Duk cikin office ɗin, cikin Imran da Irfan babu wanda ya lura da abin da baban Muneer ɗin yake yi, shi kuma Areef ya lura da lallai ba abin arziki yake yi da wannan wayar tasa ba, dan kuwa ga jikinsa sai kerma yake yi, hannunsa sai ɓari take yi, dama haka mara gaskiya yake, duk in da za'aje a zo, baya ɓuya.

Shammatarsa Areef ɗin ya yi ya fusge wayar da karfi, har wani miƙewa baban Muneer ɗin ya yi tare da nufin ya kwaci wayar, wani irin wawan mari Areef ɗin ya ɗauke shi da shi, nan take hakwaransa biyu suke fita daga bakinsa. Tsawa ya daka mashi a kan ya koma ya zauna, idan ba haka ba, yanzun nan ya yabawa aya zaƙinta, an gaya mashi su sha'anin wasan sa ne?.

Ƙoƙarin gudu ya yi ya fita daga cikin office ɗin, Areef yana daga zaune yasa kafa ya kwashe kafafunsa, sai ga baban Muneer ya zube a kasa wanwar yana baza babbar riga, ya yi shiga ta mutunci tamkar mutumin kirki, ashe dai babbar rigar ce kawai.

"Prof ɗaure mani shi mu tafi da shi, dan jikina duk a mace, i can't do anything yanzu, ina son in je gida first, dan haka mu wuce da shi gidan kawai". Cewar Areef, yana maganar yana duba wayar baban Muneer ɗin. Ganin abin da yake cikin wayar na shirin yin posting na video a media da ya yi ne ya kara ɓatawa Areef ɗin rai, sannan ya kara mashi shakku da zargin baban Muneer ɗin a cikin zuciyarsa, idan ba rashin gaskiya ba, menene na yin yunkurin posting na video daga tambayarka ina Ayla? Da farko ma cewa ya yi shi bai san daddyn Jelly ba, to a ina ya samo wannan video kuma? Ga shi dai daddyn Jelly ne a cikin videon.

Ƙoƙarin kurma ihu baban Muneer ɗin ya yi, dan ma'aikatansa su kawo mashi agaji, sai dai ina, bakinsa ma ya yi muguwar kumbura, saboda hakwaransa guda biyu da suka fita, ga jini da yake malala kamar me, kun san hakori ba wasa ba, fitarta akwai azaba ga zubar da jini, bare ma shi da hakwaran suka fita ba shiri, dama gasu ba kyan gani, duk sun yi baki, saboda busar sigari, nan take bakin ta sunduma suntum, tamkar ruɓaɓɓen alala.

"Areef ni fa ba zai iya É—aura mutumin nan ba, wannan aikin sai ku". Cewar Imran.

Harara Areef É—in ya wurga mashi, da dara daran ldanun nan nasa, kafin ya ce "Prof ba zaka canza ba har gobe, ka yi auren ma baka gyaru ba?".

Shi ma hararar ya wurga mashi yana faÉ—in "Kai kam da ka yi auren ka gyaru ne? Ko dama akwai wanda ya ce maka aure yana gyara mutun ne? Kai ma ai gaka a yanda kake da shegen mugunta kamar Saif, yanzu kawai ka kama ka cirewa mutun hakwara da mari, dan tsabar zafin zuciya".
Chapter 29 · 0% Book details