← Book details Triplets Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 168

Sashe 1

Triplets Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️❤️🔥

*KINDADE KINA NEMAN ABUN DA ZAI SANYAKI QIBA,QIBA MEKYAU KIYI DIMIMI DUK INDA KIKA SHIGA BABU RAINI KINYI TA SIYA KINA ASARAR KUDINKI🤔
ALBISHIRINKI NAZO MIKI DA ABUN DA ZAKISHA BA TARE DA KINYI ASARAR KIDINKI BA 💃 Yana da matiƙar kyau sosai ko'ina naki zai chiko ki xama abar sha'awa duk mai buƙata ta nemeni ta wannan number 09067614054, kada ki bari ayi babu ke, kayanmu tested and trusted ne, guarantee ne*.

*KINDADE KINA NEMAN ABUNDA ZAI SANYA KISAMU XAMAN LFY TARE DA KWANCHIYAR HANKALI? TO BABYN HABIBI KIXO UMMU AFFAN TAXO MIKI DA SHAHARARRUN KUMA INGANTATTUN MAGUNGUNAN MATA, KAMA TUNDAGA KAN HUMRA, TURAREN WUTA,
INFECTION KILLER,
COLACCA,
SAI KAYAN GYARA PAGE.
KACA KACA.
YALLAGWADA.
JIGIDA.
RUWA RUWA.
BANI BANI.
WOMEN JELL BATA BATA.
DAFIN KAXA.
TANTABARA.
XABUWA.
CICCIƁI.
AND EXCLUSIVE, XUMA TASTED AND TRUSTED INA FARIN CHIKIN SANAR DA KU MUN FARA RAMADAN PROMO GAME BUQATA XA A IYA TUNTUBA NA TA WANNAN NUMBER
09067614054 JIGAWA STATE MUNA AIKAWA KO'INA CIKIN AMINCI DA YARDAR ALLAH,
BABYN HABIBI KARKIMANTA DA KAYANMU FIRST CLASS NE, DAGA KANSA AN RUFE KOFA, YANA DA INGANCI NA WUCE TUNANINKI*.

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥

https://whatsapp.com/channel/0029VaMOfZZI7BeKXPU9gK2S

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥

TSARAWA DA RUBUTAWA......✍️

❤️FATEEMA ZAHRA MUSA (💫PRINCESS TEEMA💋)

*Domin samun damar karanta littafin nan daga farko har karshe zaki iya nemana ta wannan number 08161390581*

E1

Tashin hankali, nan fa kallo ya koma kallon kallo a palon. Wannan ya kalli wannan, wannan ma ya kalli wannan. Gwaggo tana nema ta juya musu lissafin ƙwaƙwale.

"Aunty Aisha wai me kike faÉ—a ne? Ki yi mana bayani dallah dallah mana!" Cewar daddyn Rimsha. Aseef ne ya katse su da cewa "Ya za'ayi mu yarda da maganarki? Ya za'ayi ki ce Josephine sister daddy ce kuma yi expecting zamu yarda, kada ki kawo mana wasa da rainin hankali a nan, dukkanmu babu yaro a cikinmu!". Ya yi maganar on a serious note! With his full confidence!.

Bin shi da kallo ta yi na Æ´an sakanni kafin ta ce "I thinking nima bakaga nayi maka kama da yarinya or mara ilimi ba ai! Yanzu ni ban ce ku saka mini baki a maganata ba, da Dr William nake yi first, idan har kune TRIPLETS da gaske, to idan na gama da shi zan dawo kanku, idan kuma ba ku bane, kana iya yi mini shiru dan ni ba sa'ar yin ka bace! Ka bari babanka ya bani amsa!!."

"Daddy amsa us, who she is?! Otherwise I will break her legs to pieces!!". Cewar Areef, ya yi maganar cikin fushi, dan fa shi ya zo har wuya gaskiya, cin mutuncin da Gwaggo take yi wa daddynsu ya ishe shi.

"James i don't know her, i have never seen anyone like her until today!". TO FAH

Dawo da kallon shi a kanta Areef É—in ya yi yana faÉ—in "Get out, if not I will get you out after I break your legs!!". Ko sannu bata ce mishi ba ta juyo da kallonta kan Dr William tana faÉ—in "Zaka bani Æ´aÆ´ana ne ko kuma sai na gwada maka nan a Nigeria kake? Ai ta Allah ba taka ba, da yake Allah ba azzalumin bawansa bane, ina zaman zamana ga shi ka kawo kanka har in da nake, kuma a yanzu zaka san da A'isha kake yi!!".

A tsananin fusace Areef ya É—aga hannu zai wanke mata fuska da wani wawan mari. Cak Lion ya rike hannun nasa tare da cewa "Kada kayi wannan ganganci, ina son kowa ya sami waje ya zauna, kuma kada na sake jin muryar kowa a palon nan, ido shi ne naku!!".

Dama da wuya kaga Lion ana hayani ta family a waje ya saka baki, baya yin haka sam, shiru yake yi ya zuba musu ido, idan suka yi, suka yi, zai natsu ya gane mai gaskiya a cikinsu, shiyasa a koda yaushe yake yanke hukuncin da ta dace, dan a nutse da kuma basira da ƙwaƙwalwa yake aiki. Yanzu ma zuba musu ido ya yi tun da suke hayaniyar yana tace maganganunsu har sai da yaga Areef zai mareta ne yasa baki, shi har ga Allah a jikinsa yana jin tabbas suna da alaƙa da Gwaggo, ko da ba mahaifiyarsu ba ce, to tabbas suna da alaƙa da ita, sannan bugu da kari, sai da ya kare mata kallo da kyau ya fahimci ita ce yake kallo a tare da Josephine, to a ina? Wannan ne ya kasa iya tunawa, ya kuma kasa ganewa, amma tabbas ita ce ya kallah tare da Josephine, kuma ita ce yake kallon fuskarta a tattare da Rimsha, sau da dama idan ya kalli face ɗin Rimsha, sai ya ji kirjinsa ya buga, to ba jinin kowa yake fusgarshi a fuskar Rimsha ba fa ce jinin Gwaggo. Natsuwa ya yi sam bai tada hankalinsa ba, ya nutsa cikin tunaninsa yana aiki da basira da hankali tare da kwarin gwiwa dan ya gane gaskiya.

Tamkar yanda ya faÉ—a, zama kowannansu ya yi a saman sofa. Sai lokacin suka lura da Brr Naurat dake ta faman binsu da kallo, ita ma ta natsu ne tana tunanin waye mai gaskiya a cikinsu?.

A tsananin razane Abba da Daddyn Rimsha har suna haÉ—a baki wajen ambatar mummy!!.

Jinjina musu kai Brr Naurat É—in ta yi alamar yes ita É—in ce, tana murmushi tare da sanya musu yatsa É—aya a saman baki, alamar su yi shiru kamar yanda Lion ya ce, dan ita kanta dama abin da zata ce musu kenan, tana son ta ce musu kowa ya natsu dan a san menene gaskiya!!.

Cikin sanyin murya ta ce da Lion É—in "Jikana kai ma ka samu guri ka zauna, A'isha zo nan kusa da ni ki zauna bari na tambayeki". Sam Lion bai yi mata musu ba, dan har cikin ransa yake jin kaunar tsohuwar nan.

Saman sofa ya zauna yana É—an shafa lallausan kumatunsa. Da hannu Brr Naurat É—in ta yi wa Rimsha alama a kan ta zo ita ma ta zauna, dan ita Rimsha kawai ta sani a cikin jikokinta, shiyasa ta kirata a kan tazo kusa da ita ta zauna. Ba musu ta nufo kakan nata. A gefenta ta zauna tare da É—an kwantowa a kafaÉ—arta. Rimsha sarkin son jiki. Daddyn ma komawa ya yi ya zauna, su Akila duk samun waje suka yi suma suka zauna. Gwaggonma kusa da Brr É—in ta koma ta zauna tana cika tana batsewa.

Cikin natsuwa Brr ta fara magana kamar haka. "A'isha a iya sani na dai baki yi aure ba, kuma har na bar Nigeria baki yi aure ba! Amma yanzu ki duba waÆ´an nan zaratan matasa da kike ikirarin Æ´aÆ´anki ne, a yaushe kika yi aure har kika haifo su? Sannan a ina kuma kika san shi Dr William É—in? Idan ma har da gaske kike yi Æ´aÆ´anki ne, to ina sone ki bamu labarin ya akayi suka zama naki? Kafin mu san abin faÉ—a, ba zuwa zaki yi kawai ki ce mana Æ´aÆ´anki ne sai mu yarda ba, wannan abin dai kin san da akwai É—aure kai, to yanzu dai ki yi mana bayani". Sarai Brr ta san cewa maganganun Gwaggo gaskiya ce, babu karya a ciki, dan ta yi wa Æ´aÆ´anta dukka farin sani, ta kuma san irin tarbiyar da ta basu, amma sai bata nuna mata cewa gaskiyar ba ce take faÉ—a, sai kawai ta nuna mata a kan basu yarda ba, dan dattaku irin na dattijuwa mai adalci, ai Brr ta yi a rayuwa, mutuniyar kwarai ce sosai, kowa ya zauna da ita sai ya so ta.

Shiru gabaÉ—aya palo suka yi, kowa jiran bayanan Gwaggo kawai yake yi. Shi dai Lion ya jingina kansa da jikin head na sofar yana binsu da idanun.

Tamkar ba ta son yin magana, haka ta fara da cewa "Mummy ina so ne kafin na fara baku labari a kira mini Deen da Maik sai Azharuddin, ina son kowa ya zo nan dan kowannensu da akwai tambayar da zan yi mishi a cikin maganata".

Kallon daddyn Rimsha Brr ta yi tana faɗin ya kira mata su dukkansu, yanzun nan su zo ba ɓata lokacin, dan a warware komai. Okey ya amsa cikin girmamawa. A hanzarce ya ciro wayarsa ya fara neman numbersu, dan duk yana da su a email ɗinsa.

Ya kuwa yi sa'a dukkansu ya samesu. Ba ɓata lokacin ya isar musu da saƙon Brr ɗin, a in da yake ƙara jaddada musu da su yi sauri.

Ba ɓata lokaci. Cikin kankanin lokacin sai ga su sun iso. Da Abbi da daddyn Jelly ne suka fara zuwa kafin Azharuddin Bature ya biyo bayansu, kowannansu da iyalansa ya zo jin cewa Brr ce take nemansu. To fah yau ake yinta, yau za'ayi cakwakiya kenan, kowa yazo, duk sun haɗu saura Hjy Batoola da Aafia ta Dr Nawid, su ne basu nan.

Kowa ya natsu a palon bisa umarnin Brr Naurat. Shi ma dai Lion ya zuba musu idanu dan wannan babban case ne da yake buƙatar nazari dan tantance mai gaskiya a cikinsu!. Areef ma binsu da idanu yake yi, a matsayinsa na jami'in CIA yana ƙoƙarin tantance mai gaskiya ta hanyar amfani da ƙwaƙwalwasa da kuma basirarsa. Shi kuwa Aseef ya kwantar da kansa a saman cinyar daddyn Rimsha, dan ciwo kan nasa yake yi mishi sosai, bawan Allah sam baya son hayaniya, lokaci guda azababben ciwon kan ya sauko mishi.

Tga, Uncle Herry duk sai binsu da ido kawai suke yi, amma fa dukkansu idan ka kalli face nasu, zaka ga razana da firgici a tattare da su!!. To razanar me suka yi haka?!. Dr William É—in ma kusan haka ne, sai dai shi ya fi su dakiya da taurin zuciyar iya jure komai. Jay and John, su kuwa ko a jikinsu, su ji suke yi ma an takura musu, dan sam basu yarda da abin da gwaggo take faÉ—e ba, kallon mahaukaciya ma suke yi mata.

Gyaran murya Brr Naurat ta yi kafin ta fara magana a nutse cikin girma da dattaku tare da nuna tsantsar kauna da farinciki na kasancewarta yau gata a cikin Nigeria, kuma a cikin iyalanta. "A'isha ga su Zahradeen É—in sun iso, sai ki gaya mana a ina kika san wannan mutumi? Ya aka yi kuma kike da Æ´aÆ´a a wajensa?!".
Chapter 1 · 0% Book details