← Book details Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 99 OF 157

Sashe 99

Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jirgi na sauka da suka fito motoci biyu na jiransu daga gidan gwamnatin Kwara. Gwamnan mutumin Baban Arifah ne kuma ya fada masa dalilin zuwan nasu. A cikin gidansa aka tanadar musu masauki. Bayan sunyi wanka sunci abinci aka kaisu suka gaishe shi sannan suka kama hanyar Moro inda Radhiya zata yi hira da Maman Dolapo matar da ta fara yi mata wanka ranar da aka haifeta.

[7/4, 7:39 PM] +234 806 334 4334: Radhiya bata kwanta ba sai da ta gama tsara yadda za ta yi da Hajiyayye gobe. Ba'a taba mata kaka a kwana lafiya. Yadda ta rabe mata abinci bata sami ko loma daya ba haka da daren ma dan kadan ta ce Na'e ta zuba musu ita da yaran. Bakinciki yasa Hajiyayye ta kasa komai saboda sau uku tana kokarin zuwa dakin Malamijo sai ta tarar da Ibrahim da Emzee a kofar dakin kamar suna gadinsa.

Bayan kowa yaci abincin safe ne Radhiya ta fito tsakar gida tana tambayar waye mai girki yau. Yadikko ta kama kunnenta ta rike.

"Na fada miki babu mai girki a gidan nan sai amaryar kakanki. Na'e ma da tayi tuwon dare jiya kawaici tayi miki bata ce komai ba"

Hajiyayyen rabewa tayi a jikin kofar dakinta tana jinsu tayi murmushi. Ashe dai Yadikko tasan matsayinta. Idan suka yi kuskuren biyewa wannan yarinyar za ta barsu da jidali ne idan ta tafi don duk wanda ya shiga gonarta sai ya gane kurensa.

"Tunda babu mai girkin dole ni zanyi kenan da kaina. Bari na leka Malamijo ya bada shanu uku ma sun isa da za'ayi yanka"

"Yanka kuma? Radhiya idan kika zo gidan nan bakya zama kiyi ta mana jaye jaye. Nama kuma kema kin sani ba'a kawowa gidan nan har kike kiran yanka."

Bata ankara ba sai ga Malamijo ya fito yau dai sanyi ya saka shi saka kayan kirki ya rufe kasusuwan jikinsa. Daure fuska yayi yana hararar Yadikko.

"Kinji nace bazan bada shanun bane da zaki yanke min hukunci? 'Yar Soja guda nawa kuke bukata?"

"Uku tace" inji Emzee da suka gama sanin me take da niyar yi.

"Amma shanu uku 'Yar Soja waye zai taya ku aikin naman? Yayi yawa. In baku daya dai yau kowa yaci"

Murmushin mugunta tayi da Ibrahim yayi mata alama cewa fa Hajiyayye ta leko daga dakinta tana sauraronsu. Haka take so taji ko wani nata yaji a kai mata rahoto. 

"Kada ka damu naman nan ba mune zamu ci ba. Wadanda za'ayiwa yankan kuma danye suke so"

Idanu Malamijo ya zaro "Hajiyayye zaki yiwa yanka?"

Sai da ta kula kowa ita yake sauraro ta dare kan turmi ta zauna "Bakina dai da zasu zo. Jiya da na ga yadda gidan nan ya koma shine na kira Sarkin mayun Faransa...can inda nake karatu. Dayake muna mutumci da 'ya'yansa sai ya daukeni kamar 'yar cikinsa. To shine nayi masa maganarka na cewa ka auro mayya. Yayi ta mamaki tunda yasan ni ba mayyar bace. Shine fa yau da sassafe ya kirani wai ya kai maganar can ofishin majalisar dinkin duniya akan harkar mayu sun ce zasu turo wakilai azo ayi bincike ke"

Idanun Malamijo tuni suka raina fata ya hau rawar jiki "ni nace kiyi zancena da wasu ne? Haba Radhiya ashe baki da hankali ban sani ba. Mayun Najeriya basu cinyeni ba sai na Faransa"

Yadikko tana ji tasan sharrin Radhiya ne amma yadda idanun Malamijo suka kada suka yi ja sai ta kyale ko banza ta rinka tunawa tana dariya.

Cikinsu Ibrahim ne ya iya daure dariyarsa yace "Turawan mayu inajin kince basa cin mutane sai mayu 'yan uwansu ko" 

"Eh mana, matsalar dai bincike zasu zo yi. Wai ashe daga last year aka haramtawa duk wanda ba maye ba auren maye saboda gudun rigingimu da suke tasowa." Ta yi kamar ta rage murya za ta yi rada bayan ta san sarai kowa yana ji "yace zasu kama duka mayun gidannan ne a tafi dasu. Hukuncin take dokar shine kisa ta hanyar babbakaraisin din mayun a baiwa oganninsu su ci da bredi"

Tsuuuu zawo ya nemi saukowa daga jikin Hajiyayye cikinta na murdawa tana matse shi da kyar saboda tsabar kaduwa. Babban yaron da tazo dashi gidan ashe shima yaji ko takalmi bai saka ba ya fito daga dakin nata a guje Radhiya tana a kamo shi. Dayake ba niyar kama shi da gaske suka yi ba da gangan suka bari ya gudu. Ragowar yaran nata ta kalla tace kowa ya tashi tana uban gumi kamar wadda tayi tsere. Muryar Radhiya taji tana magana da yaren da bata ganewa.

Wayar karya ta gama da French ta juya ta kalli Halifa da yake jindadin wannan drama yayi ta dariya kamar cikinsa zai kulle "ka rufe kofar nan. Yanzu suka kirani wai ashe sun ga fitar daya kuma sauran ma sun gama shiri yace idan wani ya sake fita daga gidannan harda mu za'a ci da bredin"

Hajiyayye da gudu ta saki mayafinta hankalinta gabadaya ya tashi. Ta ma rasa da me zata ji. Talle da yaki daukar wayarta tun safe taji ya ake ciki game da shannun ko kuwa wakilan majalisar mayu da za'a turo su kama ta. Acinyeki da bredi wata zuciyar ta tuna mata. Harda guntun hawaye sai da tayi bata ankara ba kafin ta daure ta fito inda suke.

"Uhmm nace Malamijo yau me za'a dafa da rana ne? Naga ana ta hira shine baku kirawoni ba" wai ita nan za ta bagarar kamar bata san me suke yi ba. Daga nan ta samu ta arce. Ofishin 'yan sanda zata je ta shigar da kara kafin turawan mayun su iso azo a fitar mata da yaranta.

To shima ba wai yana cikin hayyacinsa bane duk ya gama tsorata ya fara danasanin kiran Radhiya. Yarinyar nan da ya gama sanin halinta me ya kaishi kiranta da kansa. Wayarta ce tayi kara a lokacin taken wakar Celine Dion ta film din Titanic wanda ta sanyawa Awwab. A wurinta wakar bata tsufa sai ma nishadin da take saka ta idan ta tuna masoyinta.

Idanun Malamijo da na Hajiyayye basu da na biyun kwatance a lokacin. Tsoro ne karara ya bayyana ita kuwa tana dauka da turance tace masa "Chèri please follow my lead i'll explain everything later. Say something in German" (ka biyewa duk yadda kaji nayi, zanyi maka bayani daga baya. Ka yi magana da yaren Jamus)

Yana cikin office dinsu a lokacin ya kirata. Abinda tace kawai ya isa ya saka shi gane cewa akwai abinda take yi. Alheran dinsa bata ji, sai dai kuma idan ta canja daga yadda take ta tashi daga yarinyar da ya fara so daga haduwar farko kenan. Fitinanniyar dai ita ce tashi mai sanya shi nishadi a kowane lokaci. 

Speaker ta sanya kowa na ji ya rinka yi mata kalaman soyayyar da yasan cewa ba fahimta take yi ba ita ma.

"Amaryar Malamijo kin dai ji me yace. Wai ku jeru a daki ke da yaran naki yanzu zasu shigo. Idan anyi binciken sun ware mayu a cikinku sai su saki sauran"

"Inji uban wa akace mu mayu ne? Garin nan waye bai san gidan iyayena ba? Malamijo kace wani abu mana" ta fada a raunane hawaye na zuba.

"Ince me? Na auro mayya tayi sanadin da majalisar dinkin duniya ta mayu zata zo gidana" ya ce gumi na karyo masa. Gidan gabadaya yayi masa zafi dari bisa dari ya yarda da zancen Radhiya.

Wayar ta dan kara a bakinta "ranka ya dade ko za ka danyi mata hausa ta fahimta. Mayyar da ta auri kakan nawa ce ta fito" ta kalle su "shine wakilinsu da yake kula da hausawan mayu"

"Bata wayar" Awwab yace dariya na ciwo shi. Wace mai tsautsayin ce wannan ta shiga tarkon Alheran?

Ai Hajiyayye na jin haka ta zube a kasa ta fashe da kuka. Tsoro yayi mata yawa zawon ya fara tsartuwa daga ma'ajiyarsa saboda tsoro. Muryar Awwab dama irin wannan deep voice din ce mai tahowa daga kirji. Mata da yawa suna fadawa soyayyarsa a kanta yayin da take razana marasa gaskiya irin Hajiyayye.

"Kayi min rai ranka ya dade aradun Allah karya nake ni ba mayya bace. Mutum ce kamar kowa kuma indai aurene ko bai sakeni ba ni na saki kaina yanzu zan tafi ba sai kun zo ba"

Dariya yake neman yi Radhiya tace da sauri "ranka ya dade bari na tayaku binciken kafin ku iso zan tabbatar da gaskiyarta" kashe wayar tayi ta ga kowa ya fara ja da baya saboda zawon Hajiyayye. Wari ya isheta amma haka ta daure bata matsa ba.

"Me kike cewa?"

"Nace ba, aurena da Malamijo wallahi duk shiri ne tsakanina da Talle. Rabonmu kawai muka zo yaga mu tafi amma bani da alaka da mayu. Kuyi hakuri yarana akwai marayu a ciki. Waye zai kula dasu?" 

"Tunda har kun iya kulla cuta ki shirya ko ba'a kamaku an cinye ba zaki shiga prison. Kurkuku nake nufi" Emzee yace yana cin magani.

Rarrafawa tayi wurin Malamijo wanda hankalinsa ya kwanta da ya gano me Radhiya ta shirya. Dage hanci yayi ga wari ya dame shi "ki kwashe yaranki kada ki koma min cikin dakin Hajjo. Daga nan ki tsaya ki kirawo su. Sannan shanuna...."

Tana kuka tuni ta mike tana gyara zani babu kyan gani tace "suna gidan Talle"

"Me kike jira ne baki fita ba sun kusa isowa" Radhiya ta dada tsorata ta. Yaran ta kira suka fito a gurguje kan kace meye wannan sun fita Malamijo yana daga murya yana sanar da ita saki uku yayi mata.

Suna fita gidan ya kaure da hayaniya da murna. Malamijo tsananin farinciki yace "kowa ya shaida wallahi na bawa 'Yar Soja kyautar tunkiya, akwai wata mai ciki ta zama taki"

"Ahhh nifa gaskiya tayi min kadan" tace tana tura masa baki.

Baiyi fushi ba ya saki fuska "to me kike so Alherin babanta"

"Alheran ne fa ba Alheri ba"

"To ni dai sammakal...me kike so? Kai ku fito kowa yayi shaida zan yiwa babbar jika ta kyautar bajinta"

"Ni dai kada ka kasa fa"

"Ke! Dube ni nan da kyau Ali Gidado nake. Ciki lafiya baka lafiya. Da kudina a jikina"
Chapter 99 · 0% Book details