← Book details Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 157

Sashe 13

Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Takowa yayi gabanta ya hadeta da Radhiya ya kankame.
"Gidanmu dai Mairam"

Zaunar da ita yayi ya mata bayanin kudin gadonsa da ya narkar a wannan gini domin inganta rayuwar iyalinsa. Ya zabi zuwa Kano saboda gujewa fitina daga bangaren su Jume. Dama yanzu matsanancin fushi suke yi dashi saboda an gama taron suna basu ga komai ba. Da Jume da tado zance yace gida dai shima na mahaifinsa ne, idan basa son ya rabesu a raba gado ko dakin mahaifiyarsa a bashi. Sunyi rigima ba kadan ba ya fito musu gar da gar dinsa a soja mara daukar raini ko kadan. Suna ji suna gani dole suka hakura da haram din da suka kwallafawa rai.

Addu'a ta rinka jerowa yana amsawa daga nan yace to fa ta shirya jiya da ya taho cikin Kano siyayya yayi musu yana so ko sati suyi a gidan kafin ya koma aiki.

Kitchen ta leka ya siyo karamin risho, tukwane biyu da yan kayan bukata. Wani sabon shafin amarci su ka bude a gidan ga diyarsu a gefe tana samun kulawa. Wasa-wasa kwanansu goma sha biyu sannan su ka fara shirin komawa Birnin Shehu. Duk yadda taso kuwa yaki kaita gidan Salame don baya kaunar duk wani dalili da zai sa su hadu.

**********

Watansu biyu da komawa Zainab ta haihu. Sai dai ita a gidan iyayenta ta zauna su Mairama da Mami ke zuwa kullum har akayi suna. Jariri yaci sunan kanin baban Hadir da ya rasu gabanin haihuwarsa Ibrahim.

Rayuwar wadannan bayin Allah haka ta cigaba da tafiya cikin so, yarda da aminci. A kowane mataki su na kokari wurin ganin sun tsayawa juna cikin dadi ko akasinsa. Da Salame ta haihu ya barta taje ta kwana hudu a Kano inda ta rinka fuskantar Gadara da wulakanci daga wurin yayarta ta. Da yake ta fara sabawa da wannan bakon hali sai ta daure zuciyarta don kada ayi batacciya.
[7/4, 7:39 PM] +234 806 334 4334: ....ALLAH NA NASA

"Ummin Awwab me yake damunki ne kwanakin nan sai wata rama kike yi kamar wadda za'a yiwa kishiya"

Dago kai Mairama tayi jiki a sanyaye "Mami ni kaina na rasa gane dalilin wannan rama. Kuma ke shaida ce ina cin abinci sosai"

"Kinbi kin dashe kinyi fayau. Jiya ina ji baban Radhiya yana fadawa Hadir wai kinki bari ku je asibiti. Baki ga yadda ya damu ba fa"

Mairama tayi shiru ita kanta ramar da take yi tana damunta. Dadinta ma dai Radhiya kullum kara habbaka take. Suna wannan hirar Fauziyya ta shigo da Radhiya tana nishi anyi daukan rungumarni mu fadi.

Kafin su shigo kukan Radhiyan ne ya isar da zuwansu. Mairama ta girgiza kai tana takaicin wannan kukan banza na Radhiya. Tana jaririya babu ruwanta amma yanzu rigima da kuka ga fada duk ta iya. Idan ta raina girman mutum ya dauketa sai yakushi tana doke doke duka wataninta tara a lokacin. Zayyan dariya yake yace 'yar Soja bata daukar raini. Wasu lokutan kuma sunanta na gaskiya yake kira idan yana jin nishadi. Har ta gane indai taji Alheran tasan babanta ne.

A cinyar Mairama ta ajiyeta ta kalli uwar tasa dariya. Zainab tace "kunji min mara kunya ko? Mu da take gani kullum yanzu dariyar ma sai mun roka. Dadinta dai har Awwab bata yiwa"

Homework yake yi a gefe yana jin tsokanar da ake masa ya taso ya kinkimeta yana cewa "Ummi wallahi tayi nauyi da yawa ki dena bata abinci"

Me zasu yi banda dariya kuwa. " to sarkin wauta, an taba hana mutum abinci saboda kiba ne?" Cewar Mami

Shi dai bai ga aibun maganarsa ba ya dauketa gashi siriri sai tsayi da yake faman yi ya tafi dakinsu Zahra. Kayan wasa ya baje mata yana cewa sai tace Ummi da Daddy. Gajiya tayi da wasan ta soma rigima sai ya dauketa. Duk da haka kukan take masa ya sabata yana haki "gaskiya kin fiye kuka Alheran dinnan"

Kamar taji me yace kuwa ta kai masa duka a fuska harda yakushi. Zafin da yaji a gefen idonsa na hagu yasa shi sakinta tim a kasa ta fasa wata gigitacciyar kara. Zainab da Mami ke rige rigen shiga dakin ya dafe gefen idonsa da yake jini ko ta kanta bai bi ba a kasan. Zainab tayi saurin daukarta yayin da Mami babu tambayar ba'asi ta dauke Awwab da mari.

"Me kayi mata take wannan kukan?"

Shima kukan yake sosai Mairama ta taho ta rike shi murya na rawa ya nuna mata wurin "yakushi na tayi fa"

"Sai kayi mata me?" Mami ta kuma tahowa kamar za ta doke shi.

Da karamar murya ya amsa "Faduwa tayi daga hannuna"

Takaici ne ya kamata kuma wai Mairama tana kare masa. "Bari Daddynku ya dawo sai na fada masa" ta koma ga Mairama rai a bace "ke kuma kin karbi yarinyar nan kin rarrasheta ko kuwa"

Mairama tace to yau abin harda ita. Karbarta tayi ba shiri an tabo Mami yau ta fara shayar da ita amai ya taso mata da gudu tayi bandaki. Abu kamar wasa sai gata ko tashi da kafafunta ta kasa. Mazajen nasu ba ma sa cikin barrack din an turasu wani training cikin jeji sai sunyi kwanaki. Dalilin ma da suke tarewa gidan Mamin kenan.

Abu na taron mata tare su ukun da yaransu suka tafi asibiti. Ciki aka gano a jikin Mairama har wata uku. Kuka ta saka ganin Radhiya duka duka nawa take. Kuma ga kunyar ace yarinya bata shekara ba ta sake ciki. Su Zainab kuwa sai murna. Mami tace mata ya kamata kafin su Zayyan su dawo ta yaye Radhiya saboda cikin yana wahalar da ita ga tsotso. Da yake akwai kawaici a daren ta tafi ta barwa Mami ita sai kayanta da ta turo Awwab dasu.

Yadda Mami ke bawa Radhiya kulawa ya kara tabbatar musu da cewa zaman mutumci da amana ba sai da jini ba. Da ita da yaranta duk sun tare a jikin Radhiya an bar Mairama da uban laulayi sai Zainab dake sintirin zuwa wurinta.

A kwana na biyar su Zayyan su ka dawo. Sun sha wahala sosai sai dai kuma aiki ne na sabo. Da murnarsa ya shigo yana kiran 'yar soja Mairama tace masa tana gidan Major ta tafi yaye.

"Yaye Mairam? Ko shekara bata yi ba"

Hannunsa ta kama suka zauna ta dora kanta a kafadarsa "Sojana bani da lafiya ne"

Ya dago kan ta "na sani kuma asibiti zan kaiki, amma meyasa baki bari na dawo ba sai yaye?"

Baki ta tura masa "to ba..."

"Me?"

"Ciki" tace tana rufe fuska da tafukan hannayenta

Sungumarta Zayyan yayi yana murna "Mairam kice Tureta ya tureki a karo na biyu"

Salati ta hau yi tana mai jin kunyarsa shi kuwa ko a jikinsa. Dama ta samu sai sabon amarci don ma laulayin yana hana sakewa. Sai da Radhiya ta cika kwana goma sannan Mami ta dawo da ita da kaya da tarkacen wasa.

******

Bayan wata guda da yaye Radhiya wata litinin Mairama tana gyaran wake za ta yi alala da rana Zayyan ya shigo ba lokacin dawowarsa ba. Hannunta ta dauraye ta fito wurinsa.

"Sojana ya dai yau ka dawo da wuri"

Mikewa yayi akan doguwar kujera yana riko hannunta ta zauna a wurin da ya matsa mata.

"Me kike dafa mana ne?"

"Alala zanyi"

Hanci ya dage "Uhmm kayan bata ciki"

Hancin nasa ta riko tana dariya "nasan ba ka ci, banyi tsammanin dawowarka yanzu ba ne. Sai na canja abincin, waken...."

Kofar falon da taji ana bugawa da karfi kuma kamar muryar Zainab yasa bata gama fadin me tayi niyar fada ba. Da sauri ta bude kofar tayi baya a tsorace ganin Zainab tana rusa kuka kamar ranta zai fita ga Hadir a bayanta dauke da Ibrahim.

Hanya ta basu su ka wuce cikin falon Zayyan ya hada ido da Hadir yayi murmushin dole jikinsa a sanyaye yace "ka fada mata ne?"

Zainab kuka take har lokacin Mairama ta rude sai tambayarta take me ya faru. Hadir take kallo tana jiran bayani daga baya tace "ko dai aure za ka kara?"

"Wallahi dama auren ne Ummin Awwab da ya fiye min da wannan tashin hankalin"

Kanta ya sake shiga duhu "ba dai saki bane ko?"

"Liberia zai tafi"

Dif Mairama tayi sakon yana sauka a kwakwalwarta. Liberian da babu wanda yake cikin barikin da bai san tashin hankalin da suke ciki ba. Nigeria ta shiga cikin lamarin tana basu gudunmawar sojoji domin a kwantar da tarzoma. Dibansu akeyi lokaci lokaci ana turawa. Rawa taji jikinta yana yi ta kasa tsayuwa da kyau sai da Zayyan ya riketa ya zaunar da ita a kusa dashi.

Cikin tsantsar tashin hankali tace "da kai za'ayi tafiyar?"

Abinda ya dawo dashi gida da wuri kenan ya kasa fada mata. Kai ya gyada kawai ta kalli yadda Zainab ke kuka itama ta soma hawaye. Duk wata kalmar rarrashi da ban baki abokan sun lalubo domin kwantarwa matansu da hankali. Zainab ta fi gigicewa itama tana son Hadir fiye da zato da tsammani. Da kyar ya samu ta tashi su ka koma gidansu aka bar Zayyan da Mairama.

Ranar bata iya yin girkin ba jikinta yayi mugun sanyi. Abincin Radhiya ma sai shi yake bata. Ita kwanciya tayi a daki kawai tana zubar da hawaye. Bai ce mata komai ba sai cikin dare ya kwantar da ita a jikinsa yana rarrashi

"Mairam nayi zaton zaki bani goyon baya sosai har naje na dawo mu koma Kano"

"Yaushe zaku dawo?" Ta tambaye shi murya a dashe.

Tsokanarta ya fara yi don ta sake "tafiyar wata uku ce fa, zan dawo kafin ki haihu in Allah Ya yarda"

Sake shigewa jikinsa tayi yana jin cikinta da ya fara tasawa ya dora hannu a kai "Ashe haka ki ke so na ban sani ba?"

Shiru tayi ya cigaba da maganarsa shi kadai "a iya zamana dake Mairam bani da wani abu da zan fada akanki sai alkhairi. Duk abubuwan da na rasa a baya zuwanki ya wanke min kuncinsu. Shiyasa nake matukar son ki. Wannan tafiya da ina da yadda zanyi ko dai na tafi daku ko kuma na hakura ne. Ina rokonki da ki karfafa min gwiwa naji dadin bautawa kasata."
Chapter 13 · 0% Book details