Sashe 90
Ku Dube Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bai barta ta karasa maganar ba domin kuwa shima wannan tunani yana damunsa kuma Ya san wata kyauta ce kawai daga Allah da yanzu labari ya sha bamban. A take ya soma nuna mata wata irin zazzafar kauna mai tsayawa a rai, ruhi da gangar jiki. Soyayya bata tsufa sai dai ma'abotanta su tsufa. A wannan rana abinda suka kwana suna tunawa junansu kenan.
**********
WATAN DA YA GABATA
Malamijo ne ya coge a jikin bango yana ta kamshin turare dan d'uri. Sanye yake da manyan kaya babbar rigar nan kamar a nade shi dukkansa a ciki. Ga jar dara wasu bangarorin sun dan cinye ta koke. To amma dai ita ce ta fi dama dama cikin hulunan nasa. Kafarsa kuwa cover shoe ne na maza mai dan tudu ta kasa da tsukakken baki ya coko gaba.
Wata mata ce ta fito ta kofar gidan da yake tsaye a gefe taci kwalliya foundation tayi kuka. Kallo daya kacal zaka gane irin matan nan ne da ake kira da masu kirar coca cola. Murmushi ta saki da ta ganshi shima ya maida mata jikinsa har rawa yake ya ga mace irin wadda yake so. Amintaccen yaronsa Talle da yake taya shi nemo 'yan mata ne ya tallata masa 'yar makotansu sakin wawa kyakkyawar mace son kowa kin wanda ya rasa.
Sai gashi kwalliya ta biya kudin sabulu. Matar tayi ta ko ina ga ta gwanar kwarkwasa bata sha wahalar tafiya da imanin Malamijo ba. Da zai tafi kyautar dubu biyar yayi mata a ziyara ta farko. Yana zuwa gida dakinsa ya fada hankali a tashe. Ga mace har mace fa ya samo amma babu guri a gidansa, mata hudu ne a gidan. To yanzu wa zai sallama?
Yadikko dai yana da yakinin duk ranar da ya sallameta 'ya'yansa kaf sai sun masa rashin mutumci irin wanda bai taba tunani ba. Banda Mairama da ta dage yanzu wurin ganin ta hada kan kannen nata babu wata shakuwa a tsakaninsu. Akwai nutsatsu akwai fitinannu duka ya tara amma tarayyarsu daya shine girmama Yadikko da Hajjo da itama tayi nisan kwana a gidan. Atine tsohon ciki gareta, Na'e kuma ko wata uku bata cika ba. Idan ya saketa yanzu ya cuci kansa tunda bai gama more kudin da ya kashe mata na aure ba. Ranar Malamijo kasa baccin kirki yayi tunani ya addabe shi.
Bayan kwana biyu Atine ta sauka aka sami 'yan biyu mata. Da murna Hajjo ta tare shi da wannan zance ya hade rai.
"Don bala'i tun ana daidai din kuma yanzu abin ya koma bibbiyu? Wai ni bazaku barni na sha iska bane? Mata kowa tazo bata da aiki sai haihuwa. Mtswww"
Hajjo tasan halin mijin nasu sarai kuma dayake da ita aka je asibitin ta ga irin wahalar da Atinen ta sha sosai.
"Idan ka gama tsakin sai ka kawo kudin da za'a siyo abubuwan karin jini ayi mata girki mai kyau. Kuma dai wannan karon a daure a bamu na yin kauri. Yarinyar nan taji jiki"
Abin da bai taka kara ya karya ba dama neman rigimar yake ido rufe da daya daga cikin matansa don sosai Hajiyayye ta gama tafiya da imaninsa da wani salon soyayya da take gwada masa. Ji yake kamar bai taba aure ba.
Ya karkace kai ya kankance idanu "Rashin kunya zaki yi min Hajjo? To sai ki kwata tunda da uban mutum muka tara ki yiwa kishiya girkin bikin jiki"
Ranta ya sosu da zagin da yayi mata "Nagode madallah sai dai ka sani uban nawa da bai ajiye ko dan marakin sa ba duniya bata yi masa shaidar auri saki ba."
"Wuyan wata yayi kauri. To sai ki tattara ki koma gidan wanda baya auri saki. Ali mai auri saki kema yayi miki saki daya"
Da farko kunnenta har nema yayi ya toshe saboda abu ne da ta sakankance bazai taba faruwa ba. Shiyasa ma ta saki jiki ma ta saki jiki kuma ta dauki salon Yadikko na ganin sun rungumi duka yaran da babu uwayensu musamman masu kananun shekaru. Barta da fada da rashin barin ta kwana amma duka matan Malamijo bai taba auren wadda take sonsa soyayya ta gaske ba zaman hakuri ba irin na Yadikko kamarta ba. Kuntata musu da yake yi yasa da wahala soyayyar ta fito ana kokarin ci a koshi.
"Me kace Malamijo?" Ta fada a razane.
Shima kuma sai jikinsa ya dan so rissina "nace a tattara a tafi na sauwake miki. Idan akwai nama a gidan tsoho sai kije kuyi ta ci"
Duk wani abu da take tunanin fada masa domin ragewa kanta bakinciki sai ta ga yayi kadan. Zuciyarta tana zafi ta shige dakinta. Mayafi kawai ta dauka ta fita daga gidan batare da ta leka dakin Na'e ba tunda Yadikko ma tana asibiti wurin maijego.
Kafin ta karasa bakin titi sai kuka ya kufce matan. Da kyar take ganin gabanta haka ta tafi gidan iyayenta a cikin gari.
Malamijo kuwa tunda ta fita yaji duk ya shiga damuwa sai dai wayar Hajiyayye a lokacin ta mantar dashi komai sai gashi a washegari ya tura wakilai gidansu. Abin mamaki basu bar gidan ba sai da suka bada sadaki don iyayenta sun ce basu ga dalilin jan lokaci ba.
Yadikko tayi kukan wannan wulakanci da ya yiwa Hajjo taje ta fadawa abokinsa da suka yi hannun riga wato Mal Kallamu. Ko kadan baiji dadi ba amma yasan Malamijo baya jin shawara. Duk da haka yaje gidan basu kwashe da dadi ba kuwa. Abin takaici cikin 'yan matan nam hudu da yayiwa aure lokacin da idanun Ummi suka bude biyu an sakosu. Sauran kuwa zaman wulakanci da kaskanci suke a nasu gidajen. Sun auri mazan da basu san darajarsu ba ko kadan. Kina magana kuma a goranta miki cewa babanki ma yafi haka.
Daga nan dai Malamijo ya shiga gyaran gida amarya zata tare. Yadikko hakurinta ya kare ta kudurta a ranta cewa Atine na yin arba'in zata bar gidan. Yarinya ce karama marainiya. Babu wata mace tsayayyiya da ta gani daga danginta da zasu bata kulawa ita da 'yan biyun nata. Ana sauran kwana biyar ne amarya ta tare Mairama taje kafin ta wuce Abuja. Yadikko sai ta kasa fada mata an saki Hajjo tunda tasan sun shaku daga baya. Kuma ma dai tana gudun ta fada ta hanata nata niyar barin gidan. Ita dinma ba zama take ba tana ta zagayen dangi amma bata leka Salame ba a niyarta sai ta dawo.
Washegarin tafiyarta amarya ta tare. Malamijo ana ta zumudi yayi aski an gyara ko ina. Da kullin kazarsa ya shiga dakin amarya da zummar kiranta zuwa turakarsa sai ya samu bata ciki sai wasu yara dugwi dugwi da yabi ya lissafa su shida cif kwance wasu akan gadon da shi ya biya aka yi mata kayan daki. Wasu kuma an yi musu shimfida a kasa. Juyawa yayi zai fita nemanta yaci karo da wani yaro dan kimanin shekaru sha uku. Bangaje Malamijo yayi ya haye kan doguwar kujerar dakin da babu kowa a kai ya kwanta.
Abin ya daure masa kai ya tafi dakinsa zai ajiye ledar da hannunsa ya fita neman ba'asi sai ya sami Hajiyayye zaune akan katifarsa da ya sauya saboda zuwan amarya ya saka maigida kar ka taka.
"Sannu da zuwa Angona" tace tana make murya.
"Sannunmu dai" ya daure ya amsa kafin kuma ya soma fada "su waye a dakinki?"
"Dakina kuma? Mtsw anya da mutane a dakin kuwa? Ni dai da zan fito ban bar kowa ba sai yaran namu"
Idanu ya zaro "yaranku ke da wa? Sun kai goma fa inajin"
"Bakwai ne ba yawa. Biyu ne kawai babansu daya. Sauran..."
"Kowa da nasa?" Ya tambaya hankali a tashe.
Murmushi tayi masa tana tasowa gabansa tana rangwada jiki na juyawa.
"Daren yau namu ne ni da kai ka bar batun yara zamuyi maganarsu gobe"
Ledar ta karba ta bude kamshi ya doki hancinta. Kaji ne uku dakwale sun gasu an yanka musu albasa, kabeji da tumatir. Yawunta ya tsinke bata ankara ba ya tsiyayo ta gefen baki akan idanun Malamijo. Haka ya tsaya kamar gunki ta kamo hannunsa ta zaunar dashi jiki na bari zata ci nama. Biyu ta raba naman ta kwashe daya a wata ledar ta ture gefe.
"Wannan yara sa samu su lamusa da safe. Idan ban basu ba gobe bani da zaman lafiya"
Tashi yayi kawai yana tunanin ko bulala zai samo ya tafka mata. Don yana sonta sai a ha'ince shi. Ance sakin wawa baifi a ce tana da yara biyu ba. Kuma don jaraba sai a kawosu su tare a gidan tare. Hannunta da tayi rabon naman tabi ta lashe tas yana neman abin duka bata sani ba ta tashi itama.
"Cin nama irin wannan yafi dadi idan mutum ya rage kayan jikinsa yadda ana gamawa sai a fadawa angwanci ko Malamijo nawa na kaina" ta shiga kifta masa idanu.
"Zaki ci kwal ubanki ne" yace a zuci ya kama kofar dakin ya fita.
Wurin ajiyar itace yaje ya sami wata sanda ya dauko wata sanda ya dawo ya jingine ta a kofar dakin ya kutsa ciki sai ya hadu da wata dattijuwa a zaune da daurin kirji ta saka ledar naman a tsakanin kafafunta tana ta tauna kashi.
"Ke kuma daga ina" yace yana huci.
"Maigida lafiyarka kuwa?"
Murya dai ta Hajiyayye ce amma wannan ai tafi kama da dattijuwa. Sosai ya shiga kallonta yau babu foundation fuskar ta nuna da kyau. Da gani a kalla tayi arba'in da biyar ko ma fin haka. Kayanta da jibge a kasa ya kalla ya kuma kallonta.
"Ke tashi tsaye" ta kuwa mike tana sunne kai wai ita kunya.
"Ya na ganki a bushe kamar ni? Ina abubuwan jikin naki?"
"Au" ta juya ido "kayan da nake ciko dasu kake nufi? Gasu can. Wai naga bacci zamuyi ne nace bari na cire nasha iska"
"Wai tsaya, kece dai Hajiyayye da muka yi magana yanzun nan kika ce min yaranki bakwai?
"Kai dai ka damu da son sanin yaran nan naka. To zauna muna ci ina fada maka. Su goma sha daya ne amma biyu babansu daya nace ma ko..."